JAHILCI KO AL'ADAH? By Uwar batoorl
Page 5&6
๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ข ๐๐'๐๐๐๐? ๐ฅบ
Al'qalamin
Uwar batoorl ๐๏ธ
Na sadaukar da wannan shafi sukutum gare ki TATTAฦA KUNNE NA fatan farinciki a rayuwanki da na iyalanki har abada.
Masoya na ababen qaunata ba zaku irgu baโฅ๏ธ fatan alkairi gare ku
Adama Umar marubuciyar - halak ษina (inayin wannan littafi naki Allah qara basira da ษauka ka)
๐๐ฎ๐ป'๐ ๐ธ๐๐บ๐ฎ ๐ธ๐๐ป๐๐ฎ๐ป ๐ธ๐ ๐ป๐ฎ ๐ฑ๐ฎ๐ฏ๐ฎ๐ป ๐ป๐ฒ ๐ค ๐๐ฎ๐ถ ๐ฑ๐ฎ ๐ธ๐๐๐๐
๐จ๐๐ฎ๐ฟ ๐ฏ๐ฎ๐๐ผ๐ผ๐ฟ๐น ๐๐ฎ๐ธ๐ ๐ป๐ฎ ๐๐ถ๐ป๐ธ๐๐๐๐ ๐ผ๐๐ฒ๐ฟ! ๐ข๐๐ฒ๐ฟ! ๐ข๐๐ฒ๐ฟ
๐ ๐ฎ๐๐ ๐ฐ๐ผ๐บ๐บ๐ฒ๐ป๐'๐ ๐ฑ๐๐ธ ๐๐น๐น๐ฎ๐ต ๐๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ฟ๐บ๐ถ๐ป๐ถ ๐ธ๐ ๐
๐ ๐ฎ๐๐ ๐ฏ๐ถ๐ป๐ฎ ๐ฝ๐ฟ๐ถ๐๐ฎ๐๐ฒ ๐ฑ๐ฎ ๐ฎ๐ฑ๐ฑ๐'๐ผ๐ฒ ๐ฑ๐ฎ ๐๐ฎ๐ฏ๐ผ ๐ฑ๐๐ธ๐ฎ ๐ถ๐ป๐ฎ ๐บ๐ฎ๐๐๐พ๐ฎ๐ฟ ๐ด๐ผ๐ฑ๐ถ๐๐ฎ ๐๐ฎ'๐ฑ๐ฎ๐ป๐ฑ๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ป๐๐ฎ๐บ๐ ๐ป๐ฎ ๐ฑ๐๐ฏ๐ฎ ๐บ๐ฒ๐๐๐ฎ๐ด๐ฒ'๐ ๐ป๐ฎ๐๐ ๐ฏ๐ฎ, ๐ถ๐ป๐ฎ ๐บ๐ฎ๐๐๐พ๐ฎ๐ฟ ๐ฏ๐ฎ๐ธ๐ ๐ต๐ฎ๐พ๐๐ฟ๐ถ ๐ฎ๐ฏ๐๐ฏ๐๐๐ฎ๐ป ๐ป๐ฒ ๐๐๐ธ๐ฎ ๐๐ถ ๐๐ฎ๐๐ฎ ๐ฎ๐บ๐บ๐ฎ ๐ธ๐ ๐๐ฎ๐ป๐ถ ๐ธ๐ผ ๐ฑ๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ป๐ด๐ฎ๐ป๐ถ ๐ฏ๐ฎ ๐ธ๐๐ป๐ฎ ๐ฟ๐ฎ๐ถ๐ป๐ฎ ๐ฅบ๐ฏ
๐๐ก๐๐ฌ๐๐ก๐๐จ
๐๐ก๐ ๐ฆ๐ข๐ก๐๐จ
๐๐ก๐ ๐๐ ๐๐ ๐๐จ
๐๐ก๐ ๐ค๐๐ ๐ก๐๐ฅ๐๐จ
๐๐ก๐ ๐ ๐จ๐U ๐๐๐ง๐๐ก ๐๐๐๐๐๐ฅ๐ ๐๐จ๐ ๐๐ก๐๐ ๐๐จ๐๐ ๐ ๐๐'๐๐๐ก ๐๐จ๐ก๐๐ฌ๐๐ฅ ๐ก๐๐ก.
๐๐๐ฎ๐ฟ ๐ฏ๐ฎ๐๐ผ๐ผ๐ฟ๐น ๐๐ฎ๐ธ๐ ๐บ๐ฎ๐ถ ๐๐ผ๐ป ๐ณ๐ฎ๐ฟ๐ถ๐ป ๐ฐ๐๐ธ๐ถ๐ป๐ธ๐.
ุงูููู ุตูู ู ุณูู ุนูู ุณูุฏ ูุง ุฑุณูููู saw๐ค๐ค
๐๐ ุงู ู ุจุชููุฉ๐
๐๐ฟ๐ฒ๐ฒ ๐ฏ๐ผ๐ผ๐ธ ๐ ฟ๏ธ 5_6
Tana tashuwa da safe bayan sunyi sallah sun idar ta ษau stinstiya ta share ษakin ta gyara musu sannan ta fito tana share tsakar gidan.
Baabaa Mero da fitowan ta kenan daga banษaki ajiye butan hannunta tayi tace "ke dai takwara Allah kawo miki sauqi ko kaษan bakya gajiya da wahala shiyasa gakinan ba auki kaman taliyar murji dan nemawa mutane wata jarabar ba ki da lafiya kin kama aiki, yarinya sai son manyance kaman wata babbar mata"
Innai tanajin stohuwar amma ko a jikinta sharan ta gama ta tattara kwanuka tace "baabaata bari nakai kwanukan gida na dawo"
Baabaa Mero taษe baki tayi ta karyi goronta sannan tace "in kinga dama karki dawo sai bayan shekara 100, wahalalliya kawai ai so kike kije ki aikatu da jikin da ba kiji sauqi ba, yarinya sai shegen jarabar rashin ji, ni dai Allah ya gani ba haka halina yake ba wai ance mutum yakan iyo halin takwaransa to aradu baki biyo halina ba dan ni nan bana barin ko ta kwana sannan bana ษaga qafa ba ruwa na da jarabar haukan stiya amma ke a masu suna Maryam ษin ma kamata yayi ace maki damo(sarkin haquri) yarinya zuciya kaman kare ya lashe, ni ษacemun daga gani kamun na qarisa ki da kaina" ficewa Innai tayi tana murmushi bata tsaya sauraran baabaa Mero ba dan tasan duk da sonda take mata yanzu zata iya kwaษa mata abu.
Baabaa Mero ta ci-gaba da mitan ta kaman zata daki babu sannan ta ษauko kwanon madaran da ta ajiye dan ta bawa takwarar tata tasha da magani sai kuma ta bostare ta tafi gidan nasu da zata mutu bamai kallonta, zama tayi ta shanye abunta tass sannan tace "Allah ganar da ke mai qaunanki takwara".
Fitowa tayi daga gidan baabaa Mero tana murmushi, tafiya take cikin nustuwa wanda wasu sukan ษau tafiyan nata akan rigima ta keyi.
Yarinyace yar kimanin shekara 14 da haihuwa amma in ka ganta sai kace takai 16 year's, domin halittan da Allah ya mata. Fara ce sol kuma Siririya ce ba mai jiki ba(qiba) abunka da bafulatana, amma rashin jikinta da qarancin shekarunta bai hana halittar da Allah yayi mata bayyana ba dan tun bata gama girman ba maqerin budurci ya bayyana gare ta.
Tana da qugu(mazaunai), kuma duba da gashin dake kwance gaban goshinta da kuma sajen fuskanta hakan ya isar da cewan Allah ya mata baiwan gashi Masha Allah! Round face take dashi mai ษauke da dara-daran idanunta (golden eyes) farare ne tass kaman madara kai kace idon jinjirine haka baqinma baqi wuluk, tana da yalwan cikan gashin gira wanda har ya haษe hakan kuwa sai ya bada wani sirri a kyau nata, Tanada dogon hanci wanda shi da biro banbancinsu kawai rubutu ne, ษan madedecin bakinta wanda inka gani za kayi mamakin anya tana ma cin abinci kuwa tsabar qanqantarsa, tabarakhallah Masha Allah don kyakkyawace ta ajin qarshe wanda qarancin shekatunta basu ษoye ni'imomi da baiwan da Allah ya azurta ta dasu ba, duk da bawai girman ya gama bayyana a gareta ba.
Innai kenan wacce asalin sunanta shine Maryam takwara ga mahaifiyar Baffanta wato baabaa Mero.
A nuste tayi sallama ta shiga gidan nasu ta kuma yi sa'a baffanta na nan, ta samu Innar su na aikin ษumame qanwarta Hassu kuma na shara.
Kallon Innar tasu sai jikinta yayi sanyi amma a haka ta qarisa wajanta, durqusawa tayi har qasa tace "jamษanduna Inna"
Inna A'i kanta a gefe tana ayyukan ta ko juyowa ta kalli yarinyar nata ba tayi ba kawai ta girgiza kai alaman ta amsa gaisuwan.
Daman in da sabo ta saba da hakan tasan iya abunda Innan tasu za tayi kenan, kanta a qasa haryanzun jiki a sanyaye kaman kullum in hakan ya faru ta wuce ษakin mama lami.
"Jam ษanduna mama"
(Antashi lafiya mama)
"Jam innai noi ษandu ma"
(Lafiya innai ya jikin ki)
"ฦandu waษu dama"
( jiki dasauqi)
"To Allah hokke en jam"
(Allah qara sauqi) Mama Lami ta faษa tana jera kwanukan ta.
Da "Ameen" Innai ta amsa sannan ta miqe ta fito a ษakin.
Hassu ta gaishe ta cikin fillanci tana tambayan ta jikin nata "Adda Innai noi ษanduma?" "ฦandu waษu dama Hassu am".
Mawanki ta wuce dan tayi wanke-wanken, Hassu tace "Adda zanyi wanke-wanken ki bari ki huta abunki kinga baki da lafiya"
Murmushi kawai tawa qanwar nata ba tace komai ba. Haษa kwanukan wanke-wanken tayi da wanda ta shigo dasu daga gidan baabaa duk ta wanke su, bayan ta kammala ษakinsu ta wuce ta gyara musu.
Tana kammala ayyukan ta Hassu ma ta gama sharan da take yi dai-dai Baffan su ya fito a ษakin Innar su sai dukansu suka nufe sa, suna zuwa suka stugunna suka gaishe sa cikin fillanci.
Amsawa yayi yana sanya musu albarka sannan ya tambayi Innai jikinta, da sauqi ta amsa masa, duk gaisuwan da suke yi da fullanci suke magana.
Magaji ya fito a ษakin sa shima ya tsugunna ya gaida Baffan nasu, Baffai ya amsa cikin fara'a. Gaishe da shi Innai da Hassu suka yi ya amsa masu sannan shima ya tambayi ya jikin Innai ษin, da sauqi ta amsa masa.
Albarka baffa ya sanya musu duka yace kowa yaje ya karya.
Inna ke madafi tana raba musu abun karyawan, Innai zuwa tayi tace "Innan mu bari in qarisa miki"
Ba tare da Inna tace komai ba ta tashi ta fice a madafin.
Qarisa wa Innan ta aikin tayi ta raba komi har da madaran da Hamman su magaji ya kawo ta raba ta sawa kowa nasa, ta kaiwa Hamman su nasa har ษakinsa sannan ta qira Hassu kuma takai na Baffai, ita kuma ta miqawa su Inna nasu, Hassu ta ษauka musu nasu suka yi ษakinsu da shi.
ฦumamen tuwon surfaffen masara da aka wanke yayi haske sosai da miyar ษaskoje bushashshe(bushashshen kuษewa) da yaji nama da man shanu, sai naman zabbi da kuma madaransu mai ษumi.
Karyawa suka yi sannan suka haษa kwanukan Hassu ta wanke masu bayan ta dawo kai wa baabaa Mero nata.
ฦakinsu suka shige ko waccen su ta kwanta dan hutawa amma kowa da abunda take tunawa a ranta.
Innai da ta faษa duniyar tunani hawaye ne ya gangaro a idonta wanda ke nuni da damuwan da take ciki, sai tace "Duk da kasancewana yarinya amma abun na damuna anya Inna ce ta haifeni anya ba tsintata suka yi ba suke ษoye mun" sai kawai ta fashe da kukan da bata san ma ya qwace mata ba.
Hassu ta tashi tana cewa "Adda Innai ษume?"
Innai cikin hawaye tace "Hassu jam, wala ko ษume"
Itama hawayen ta fara tana magana cikin harshen fillanci "Adda Innai ki faษamun bana son ganinki cikin damuwa in baki faษa wa ฦดar uwanki abinda ke damunki ba wa zaki faษa wa?"
Cikin Kukan tace "Hassu ba zaki fahimta ba ko na faษa miki, Hassu inajin kaman zan mutu bansan me nawa Inna ba bansan me yasa Inna bata qauna ta Inna bata sona kaman ba ita ta haifeni ba" ta faษa tana hawaye
Haquri take bata itama tana kukan "Adda kiyi haquri Allah Inna na sonmu kinji" cewar Hassu tana rungume ฦดar uwanta
Haka suka rungumi juna tana taya Addan nata kuka kai kace marayu ne ko kuwa mutuwa aka musu.
Baffai ne a ษakin Inna bayan ya gama karyawa yace "tom A'ishatu yanzu ke me shawaranki akan makarantan Innai da nake son tayi gaba, dan gaskiya wannan al'ada ta aurar da yara da wuri ba ruwa na, ni ba wani al'adan da zan gwada wanda yake kaman jahilci ya sanya na cuci rayuwan yara na"
Shiru Inna tayi ba tace komai ba, Baffai cikin hasala da quresa da halin ta ke yi yace "wai ke A'ishatu me yasa kika zaษi haka ne? Ko kaษan baki son gaskiya na jima da fahimtan ki, wannan ฦดar taki baki tunanin da qanqantan ta ciwon zuciya zai iya kashe miki itaุ wannan kalan banzan al'adan naki zai sanya ki tafka babban asara tunda kina uwa amma zai sanya uwa ta gagara ceton rayuwar ษiyarta sannan ta kasa mata abunda zai zama ci-gaba a gare ta har da ita uwar kanta tunda komi ษa ya samu a rayuwa ba mai amfanuwa ko morar sa irin uwarsa barin ma dai ษiya mace, A'ishatu yanzu ke baki tunanin Innai zata fara tunanin ba kece kika haifeta ba shiyasa kike mata haka? Yarinyar nan ki godewa Allah da yayo ta da haquri sannan ki kiyayi ranar qarewan haqurin ta ษan aje-aje zata daina kallonki matsayin mahaifiya irin halayen da kike nuna matan nan" ita dai Inna kanta na gefe bata ce komai ba har yanzun.
tsaki Baffai yaja a hasale ya miqe ya fice a ษakin dan in ya cigaba da zama zasu iya samun mastala.
ฦakin magaji ya wuce, ganin Baffai sai Magaji ya tashi ya zauna yana cewa "Baffai da kanka ba ka qirani ba"
Baffai cikin murmushi yace "bakomi baban baffa, yanzu dai shawara nazo muyi game da yar uwanka, yanzu kaga sunyi wannan jarabawa wai na gama firamare(primary) to kana ga ya za'ayi ta wuce gaba ina tunanin zai fi ba"
Magaji yace "Baffai gaskiya ya kamata kam ta wuce gaban inya so sai a lallaษa baabaa ta ajiye batun aure a gefe tunda ko saurayi bata da shi, kuma sai dai a nemi na zuwa a dawo dan makarantan kwanan nan sai a hankali".
Baffai yace"amma Magaji samun abun hawan da zai ke kai ta ya dawo da ita ba matsala ba"
Magaji yace "babu matsalan komai Inshร Allah Baffai, kawai a nema mata wanda zai ke kai ta yana dawo da ita nasan za'a samu ko yawale aka wa magana sai ake biyansa duk sati ko wata"
"Shikkenan in taji sauqi sosai sai kuje kuyi komai anan cikin Ashakan" cewan Baffai cikin gamsuwa da shawaran yaron nasa.
Magaji yace "to Baffai Allah ya qara mata lafiya ya kuma qara buษi da girma"
Da "Ameen" Baffai ya amsa sai suka ci-gaba da tattaunawa kamun can Baffai ya miqe yana faษin "Magaji ba na fita to kasan akwai wani ruga nan gefen mun nan tom akwai wata baiwar Allah ba taji daidiba an aiko naje"
Miqewa shima Magajin yayi yana cewa "a dawo lafiya Baffai Allah bata lafiya" Tare suka fito a ษakin.
Suka bi gidan baabaa mero suka gaisa kamun Baffai ya fice ya tafi rugan dake gefen nasu.
Baabaa mero ta kallesa tace "yanzu kai Magaji ka gaya wa kanka gaskiya biyewa baffanku kake yi ko, in na maka maganan aure sai ka haษa fiska kaman shanun huษa(garma), kaman wani mara ishashshen lafiya, to dan Allah in ma lafiyan ne baka da shi ai ka gaya mun na nema maka magani, yo me abun kunya a ciki ni da na haifi ubanka mene ban sani ba, kawai kace mun Baabaa abun baya tashi ko bakajin buqatuwa, shikkenan magana mai sauqi niko na bazama na nema maka magani yacce zaka koma kaman doki dan qarfi, amma ka girma ka riqa ka balage kaqi aure wai kai boko ba bokoko a wuta aradu sa'annin ka akwai masu yara huษu wasu har shida ma, shikkenan ya rage maku kai da Baffan naku in ma baqin ciki yake wa kansa na ganin jikokin sa to kansa ya wa sai nan gaba zaku san soyayyace nake muku shi yasa na matsa kuyi aure....
๐๐ฌ๐ ๐ฌ๐๐ช๐๐ก ๐ฆ๐๐๐ฅ๐๐๐ก ๐๐จ ๐๐ฌ๐ ๐ฌ๐๐ช๐๐ก ๐ฃ๐๐๐ ๐
ZANCI GABA DA POSTING NE KAWAI IN NAGA YAWAN COMMENTS NAKU
***
Mrs big barbieyh โ๏ธ
๐๐ ุงู ู ุจุชููุฉ๐
๐ฟ๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฉ๐ ๐๐๐๐๐ง๐ ๐ช, ๐ ๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐ก๐๐ฎuka:-
***
๐พ๐๐๐ฉ ๐ค๐ฃ๐ก๐ฎ.
***
๐๐ค๐ช ๐๐๐ฃ ๐๐๐ก๐ก ๐๐๐จ ๐ค๐ฃ๐, ๐ญ๐๐ข๐ช ๐ข๐๐ ๐ช ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฃ๐ ๐ช ๐ ๐ง๐๐๐ช๐จ๐ ๐ข๐๐ ๐จ๐๐ช๐ฆ๐, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐
NOTED : karku nemeni a wannan layi *** ๐ฑ๐ผ๐ป ๐๐ฎ๐ป๐๐ ๐ฏ๐ฎ๐๐ฎ ๐ฎ๐ถ๐ธ๐ถ ๐ฏ๐ผ๐๐ต ๐๐ต๐ฎ๐๐๐ฎ๐ฝ๐ฝ ๐ฎ๐ป๐ฑ ๐ฐ๐ฎ๐น๐น
# ๐พ๐ค๐ข๐ข๐๐ฃ๐ฉ
# ๐๐๐ ๐ &
# ๐จ๐๐๐ง๐