JAHILCI KO AL'ADAH? By Uwar batoorl
19&20
๐ ๐ผ๐๐๐๐พ๐ ๐๐ ๐ผ๐'๐ผ๐ฟ๐ผ๐?๐ฅบ
๐ฝ๐ฎ
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
Free book
Kyauta bada kuษi ba duk wanda aka sayar wa to ba ruwana nidai littafina a kyauta nayi shi.
ุงูููู ุตูู ู ุณูู ุนูู ุณูุฏ ูุง ุฑุณูููู
Wannan page naku ne masu daraja, sharhinku na qaramin qwarin guiwa ๐ค
Surayyatou nah
Dr Seeyerth
Jeddatulkair
Basira montakha
Ummeey Aliyu
Momsi
Maman kausar
my dearest
ukhtynh
Duk mai SHARHI dole Uwar batoorl ta ambato sunansa.
LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION ๐ค shugaba adali da ษauka cin member's ฦดan uwana wannan littafi tukuici ne garemu ๐ 2 YEAR'S ANNIVERSARY
FAN'S GA NAKU
๐๐ก๐๐ฌ๐๐ก๐๐จ
๐๐ก๐ ๐ฆ๐ข๐ก๐๐จ
๐๐ก๐ ๐๐ ๐๐ ๐๐จ
๐๐ก๐ ๐ค๐๐ ๐ก๐๐ฅ๐๐จ
๐๐ก๐ ๐ ๐จ๐U ๐๐๐ง๐๐ก ๐๐๐๐๐๐ฅ๐ ๐๐จ๐ ๐๐ก๐๐ ๐๐จ๐๐ ๐ ๐๐'๐๐๐ก ๐๐จ๐ก๐๐ฌ๐๐ฅ ๐ก๐๐ก.
๐๐๐ฎ๐ฟ ๐ฏ๐ฎ๐๐ผ๐ผ๐ฟ๐น ๐๐ฎ๐ธ๐ ๐บ๐ฎ๐ถ ๐๐ผ๐ป ๐ณ๐ฎ๐ฟ๐ถ๐ป ๐ฐ๐๐ธ๐ถ๐ป๐ธ๐.
๐๐ ุงู ู ุจุชููุฉ๐
๐๐ฟ๐ฒ๐ฒ ๐ฏ๐ผ๐ผ๐ธ ๐ ฟ๏ธ 19_20
Washe gari Innai ta tashi da mugun zazzaษi ga ciwon ciki, hankalin Baabaa Mero in yayi dubu to ya tashi.
Hanata zuwa makaranta tayi tunda bata da lafiya ta huta, amma Innai ta tirje sai taje dan suna da test.
Sai da Magaji yazo da kansa kaman zai mata duka tukunna ta haqura da maganan zuwa makarantan amma idanuwanta har da qwalla tana tunanin test na yau da zasu yi.
Baabaa ta kalleta tace "ja'irar yarinya shawaragiya wai ace baka da lafiya ka huta zuwa boko hakanan ka sanya mutane a gaba kana sheshsheqa da gulmammen kuka dan staษar tijara, kai kace uwarku da ubanku ake raba muku a makarantar, Aradu takwara kika yi wasa daga yau kinbar zuwa makarantar sai na aurar dake in yaso kije can mijin yayi haquri ya raineki kiyi nunu a gidan sa" .
Tura baki Innai tayi tace "nikam tunda an hanani zuwa makarantar a bar damu na da magana".
Buษe baki baabaa tayi ta jero salati tace "eh tabbas ya tabbata bayan yaren 'yan wuta har da halayyar 'yan wuta ake koya muku yanzu wai du yaushe kika fara zuwa makarantar? Inaji baki cika wata biyu ba amma har kin koyo fistara yarinya shiru-shiru sanyi-sanyi ba ruwanki kaman kazar da aka sanya a ruwan sanyi amma yau ni kike cewa na dameki da magana to takwara kinyi da uwaki Indo, shashashar yarinya kawai ai inba tambaษanci ba da rashin kunya baki gayamun magana, to Allah kawo ubanki daga yau an daina karatun da zuwa makarantar tunda rasar kunya ake koyowa a can".
Innai fashewa tayi da kuka ta tashi tana riqe ciki ta shige cikin ษakin Baabaa Mero, binta da harara tayi tace "ja'ira 'yar kutun-kutun dubi yacce take tafiya kaman stohon da yasha sanda a baya amma wai ki dage zaki makaranta".
Fitowa tayi a ษakin tana share hawaye ko qala bata cewa Baabaa Mero ba ta fice a gidan, da kallo Baabaa ta bita ta tafa hannu tace "kai amma in akace yaro da kare basu da banbanci to haqqun anyi gaskiya, yanzu sabida Allah dan rashin sanin ciwon kai yarinya ta kwashi figaggun qafanta kaman wanda aka stoma kaza a ruwan sanyi tace zata je wancan gidan dan kawai anfaษa mata gaskiya to Inshร Allahu ni Meramu ba ni binki kuma ba ni qara shiga tsabgarki da ta uwarki kayan kunyan ya ishe ni kuje ku fama in suka barki kika mutu su binneki ko gawan kar a gwada mun 'yar ฦwal uba Allah baki lafiya, kuma makarantar ne nace ba zaki je ba babu zuwa sai Aure".
Da sallama ta shiga gidan tana riqe da cikin ta, tafiya take tana layi kaman zata faษi idonta na hawaye tayi hanyan ษakin su, Inna na zaune qofan ษakinta tana gyaran shinkafa tunda ta ษaga kai sau ษaya ta kalli Innai sai ta kau da kai ta cigaba da aikin ta, Innai na tafiya a duqe tayi tuntuษe tana qoqarin faษuwa Baffai da fitowansa bayi kenan da Mama Lami da itama fitowan ta ษaki kenan kusan rige-rigen tare Innai suka yi lokaci guda Baffai na cewa "subhanallahi Uwata jikin ne har yanzu?" hutar da mama Lami Baffai yayi ya ษaga Innai caษak ya kaita ษakin mama lami ya kwantar sannan ya fito, kallo ษaya yawa Inna ganin ko mostawa ba tayi ba ya kau da kai ya juya yana ayyana irin hukuncin da zai ษauka wannan karon, zai fita a gidan sai ga Magaji, ganin Baffai sai yace "Baffai za ka fita ne?.
Baffai yace "eh baban Baffai zan sayowa qanwarka magani ne zazzaษi na damunta" kallon Baffai Magaji yayi yace "dama Hassu ba taje makaranta ba? Girgiza kai Baffai yayi yace "ba Hassu ba Innai ce".
Da mamaki Magaji yace "Innai de da yanzu na barta gidan baabaa? "Eh ita dai yanzu shigowanta".
Karษan kuษin maganin yayi ya juya sayo wa shi kuma Baffai ya koma cikin gidan.
ฦakin mama Lami ya ษage labule ya shige ya zauna gefen Innai yana jera mata sannu.
Magaji yaje ya sayo magani ya kawo Baffai yayi-yayi da ita tasha maganin amma sai taษara take taqi amsa, da Magaji yasa baki sai ta fashe da kuka. ganin haka sai mama Lami ta bawa Baffai haquri akan ya bari sai anyi abincin rana taci sai ta sha, Baffai ba dan yaso ba ya qyale ta.
-----
Afrah tunda ta shigo makaranta take zuba ido ta inda zata ga ษullowan habibtynta dukda dai sun rabu tana fushi da habibtyn nata amma ta mastu ta kalleta dan bata jin zata iya fushi da ita.
Wasa-wasa har aka yi assembly aka gama aka shiga class malam ba wasa ya shigo ya gama ya fita shima sai leqawa yake amma bai ga idon mutumiyar sa ba, Afrah tun tana ษaukan abun wasa har taga da gaske ne dan gashi har an fita break an dawo an kuma fita sallahn azahar, nan dai duk gaba ษaya yanayinta ya sauya sai take jin kaman ta dinga ihu rashin ganin Innai, Allah ya taimake ta ba'a musu test ษin ba dan da kuwa bata san me zata rubuta ba balle ma tayi tunanin yiwa Innai.
Har aka tashe su aka zo ษaukan ta amma ta roqi drivern ya jiraata, zaman dube-dube tayi sune basu baro makarantar ba sai da ษaliban day gaba ษaya suka waste na hostel ma suka shige hostel kamun tawa drivern magana su tafi idanuwanta cike da qwalla qiris take jira tayi kuka gashi gobe Saturday ba makaranta har sai Wednesday dan ranan Monday da Tuesday hutun Esther.
Driver na parking ta sauqa ko jakan makarantar bata ษauka ba ta tura baki ta shige cikin gidan, hanyan ษakinta tayi ko kallon palourn bata yi ba balle tasan ko akwai mutane ko babu.
Kaman daga sama ta jiyo muryan yayanta yana cewa "Afrah ba magana ne? Juyowa tayi sai kawai hawayen da take riqewa suka gangaro suna bin kuncinta ta wuce wajan yayan nata ta shige jikinsa.
Afreen ce ta taษe baki tace "ke dai kinga ta kanki kuma in haka ake Auta to baki more ba duk anbi an sakalta ki kalli abinda kike yi fa kayan amai".
kamun Jay ya buษe baki Hajja ta riga sa tace "ke maimuna banson rashin mutunci fa daga zuwa zaki addabi baiwar Allah, wai ubanwa yace kizo ne ma, kai kuma jabiru baka san hanya bane ka ษauko wannan fitsaratun?
Jay bai kalli Hajja ba balle Afreen hankalinsa na kan damuwan da suke ciki yace "Auta me ya same ki? Cikin kuka tace masa "BB (big brother) ba Habibty na ce taqi zuwa makaranta yau ba" da mamaki yake kallon ta yace "wacce habibtyn? dan nasan mummy dai tana gida".
Tura baki tayi tace "qawata ce mai sunan mummy shine nake ce mata haka, jiya da zamu rabu mun ษata yau kuma ban ganta a makarantan ba kuma ina kewanta".
Afreen cikin taqaici tace "amma Allah wadaran naka ya lalace aka bincika ma wata 'yar talakawa ce har da zubar da hawayenki a kanta dan ganin arahan gabas karuwa da sallahn walha".
Hajja ma guntun tsaki taja tace "fatu ke dai kin cika abin taqaici kaman mutum yayi kashi" Jay kuwa murmushi yayi cikin sigan rarrashi yace "to tashi kije ki shirya kici abinci na kaiki gidan su ki dubo ta ko".
Tura baki Afrah tayi tace "nifa BB sunan ta kawai na sani bansan gidansu ba kuma kaman ba'a cikin Ashaka take ba amma dai ban sani ba, Allah BB sai ka ganta ga kyau ga hankali itama takawarar kakarta ce kaman ni kuma itama a gaban kakarta take zaune, BB Allah nikam ka aure ta ai sai ka ganta kaman ni take amma ta fini kyau dai sai bata da um'um" cikin jin kunyan abinda takeson cewa ษin tace "kawo kunnenka na gaya maka" kunnensa ya kawo ta faษa masa maganan tana miqewa tayi ษakinta da gudu.
Murmushi Jay yayi yace "wannan yarinya kin girma soon kema zamu nemo miji mu aura miki".
Hajja tace "fatu faษi ba'a tambayeki ba, shikkenan har ta gama rigiman ta gudu saura kuma na anjuma in ta fito".
Afreen ta jawo wayanta tana lastawa tace "anjuma kuma ke da ita dan mukam mun jima a Gombe".
Jay kallonta yayi yana murmushin mugunta a ransa cewa yake "ina Gombe ba muna Gombe ba dan barinki anan zan yi".
Nan Hajja ke tambayan sa batun mastalan da ake ciki.
Numfasawa yayi yace "Hajja har yanzu dai shiru ba wani labari cikiya ba irin wanda bamu bada ba har DMD ya bada kyauta akan wanda ya ganta amma shiru".
Qwafa Hajja tayi tace "wancan fitinannen yaro da ya gagari kowa, ina ma yake da baku zo tare ba?
"Mun taho yana bacci Hajja".
"Ya masa kyau ya fama da baqin halin sa, ita kuma uwar su Allah bayyana ta"
Da "Ameen Jay ya amsa"
Afreen ta tashi ta shige ciki tana "cewa bari na huta kamun lokacin komawa".
Harara Hajja ta bita da shi tana cewa "sai inga gidan uban da zaki koma muna nan dake ja'ira".
Jay yayi murmushi yace "Hajja ba na dawo zanje wajan wani freind na".
"To a dawo lafiya ษan albarka" faษin Hajja tana murmushi
Tashuwa Jay yayi ya fice.
๐๐๐๐๐!! ๐๐๐๐๐!! ๐๐๐๐๐!!
๐๐๐ ๐๐'๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
๐ฒ๐จ๐ฎ๐ซ ๐ฌ๐๐ญ๐ข๐ฌ๐๐๐๐ญ๐ข๐จ๐ง ๐ข๐ฌ ๐จ๐ฎ๐ซ ๐๐จ๐ง๐๐๐ซ๐ง.
๐๐ฎ๐ณ๐จ ๐ค๐ฎ ๐ฌ๐๐ฒ๐ข ๐๐๐ญ๐ ๐ฆ๐๐ข ๐ฌ๐๐ฎ๐ช๐ข ๐ฆ๐๐ข ๐ข๐ง๐ ๐๐ง๐๐ข ๐๐จ๐ฆ๐ข๐ง ๐ ๐๐๐๐ญ๐๐ซ ๐๐ ๐ก๐ข๐๐ข๐ฆ๐จ๐ฆ๐ข๐ง ๐ค๐ฎ ๐ ๐จ๐ง๐ฅ๐ข๐ง๐ ๐ค๐จ ๐ค๐ฎ๐ฐ๐ ๐ค๐๐ฅ๐ฅ๐๐๐-๐ค๐๐ฅ๐ฅ๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐ญ๐๐ซ๐ ๐๐ ๐๐๐ญ๐๐ง๐ค๐ข/๐๐๐ญ๐๐ง๐ค๐ ๐ฒ๐๐ฒ๐ข ๐ฌ๐๐ฎ๐ซ๐ข๐ง ๐ณ๐ฎ๐ช๐๐ฐ๐ ๐๐. ๐๐ง๐ ๐ฆ๐'๐๐๐จ๐ญ๐ ๐๐ฆ๐๐๐ง๐ข ๐๐ ๐ค๐๐๐๐ซ ๐ฌ๐๐๐๐ฐ๐ ๐ญ๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐ฆ๐๐ฌ๐ฎ ๐ค๐ฎ๐ค๐๐ง ๐ฌ๐๐ฎ๐ซ๐ข๐ง ๐ช๐๐ซ๐๐ฐ๐๐ง ๐๐๐๐ ๐ญ๐จ ๐๐ ๐ฐ๐๐ง๐ง๐๐ง ๐๐ ๐ค๐๐ฆ๐๐ง ๐ค๐จ ๐ฐ๐๐ง๐ง๐ ๐๐๐ง๐ ๐ฌ๐๐ข ๐๐ง ๐ ๐ฐ๐๐๐ ๐๐ค๐๐ง๐ฌ๐๐ง ๐ง๐ ๐ช๐ฐ๐๐ซ๐๐ข ๐๐๐ง ๐ข๐ง๐ ๐๐ง๐๐ข ๐๐ ๐ค๐ฎ๐ฆ๐ ๐ช๐๐ซ๐ ๐จ ๐ ๐ ๐๐๐๐๐ง ๐ค๐ ๐ญ๐จ ๐ค๐ช ๐ณ๐ข๐ฒ๐๐ซ๐๐ข
๐๐๐ ๐๐'๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐
๐๐๐ - 250 ๐๐๐ - 2๐๐
๐๐๐ - 5๐๐ ๐๐๐ - 500
๐๐๐ - 75๐ ๐๐๐ - 750
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐ - 25๐ ๐๐๐ - 25๐
๐๐๐ - 50๐ ๐๐๐ - 5๐๐
๐๐๐ - 75๐ ๐๐๐ - 75๐
๐๐ฎ๐ง๐ ๐๐ซ๐๐ก๐ ๐ฆ๐ฎ๐ง๐ ๐ก๐๐ง๐ bashi๐ ๐ฌ๐๐ฒ๐๐ง ๐ง๐ ๐ ๐๐ซ๐ข ๐ฆ๐๐ข๐๐ ๐ค๐ฎ๐๐ข ๐ ๐ข๐๐(๐ข๐ง๐ฃ๐ข ๐ก๐๐ฎ๐ฌ๐๐ฐ๐)
๐๐๐ค๐ฎ ๐ข๐ฒ๐ ๐ญ๐ฎ๐ง๐ญ๐ฎ๐๐๐ง ๐ฆ๐ฎ ๐๐ค๐๐ง ๐ฐ๐๐ง๐ง๐๐ง ๐ฅ๐๐ฒ๐ข ๐๐๐ง ๐๐ข๐ฒ๐ ๐ค๐จ ๐ญ๐๐๐๐๐ญ๐๐ซ ๐๐ ๐ฌ๐ก๐๐ข๐๐๐ง ๐๐ข๐ฒ๐
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐/๐๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐จ๐ฎ๐ง๐ญ ๐ง๐ฎ๐ฆ๐๐๐ซ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐
๐๐๐๐ ๐๐๐๐.
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐......
โญโญ
DMD Miqewa yayi yace "Whatttttt!?
"Eh uwarku bata iso ba kuma na qira layinta baya shiga maza-maza ka nemeta ka faษa mata inma a ina ta staya ko me take yi ina buqatan ganinta a gida yanzun nan" kitt Abiy ya kashe qiran yana gama magana.
Layin Amminsa ya ke qira both na Nigeria da na Canada amma duka abu ษaya ake faษa masa "switch-off" huzar da iskan bakinsa yayi yana cewa "shittt! Na rasa me Ammi ke ษaukowa a Nigerian nan har na tsani qasar kullum cikin matsaloli" zama yayi ya ษau wayansa yayi dialing wani number ana ษauka aka ce "hello Sir" cikin magansn sa mai kama da rigiman yace "Mark zan turo maka layuka yanzu ka bincika mun su" yana gama magana ya kashe qiran ya tura masa, can sai numbern ya qira sa ya ษauka yace "Yes ina jinka", "am sorry Sir amma a binciken mu layin na kashe kuma ba yanda za'a yi mu bincika sai dai a samu qwararru a Nigerian su bincika da kansu, sannan layin Canada kuma anjima da sauqe shi" mutumin da ya qira ya faษa, ba tare da yayi magana ba ya kashe wayan qittt.
Main palourn ya sauqo ya tarar da sweedy na zaune riqe da waya a hannunta, kallonta yayi yace "ya aka yi" tashuwa tayi ta dawo gefensa ta zauna kaman za tayi kuka tace "Darling ina ta qiran layin Ammi baya shiga kuma fa tun da rana da muka yi waya bamu qara yi ba yanzu ga can sweetie sai kuka take wai za tayi waya da Ammi yanzu haka na barta da sweerie tana rarrashinta ne na fito na yi knocking qofanka baka ji ba" duk maganan da take cikin harshen turanci take yi sannan izuwa yanzu hawaye ya fara wanke fatan kumatun ta dake yalqi kaman na jarirai.
ฦoye damuwan da yake ciki yayi ta hanyar cewa "karku damu Ammi na lafiya nafi tunanin wayanta ne ba chaji so ki turomun sweetie ke da sweerie kuma ku kula sosai sannan in Allah ya kaimu gobe zan tafi Nigeria karki faษa musu ke dai ki kula da kanki da su sosai".
kallon sa tayi tana hawaye tace "Darling Nigeria dai? Kai da kace ba zaka qara komawa Nigeria ba sannan yanzu kace zaka je kuma kace mun lafiya, please inda wani abun ka faษamun zanfi samun nistuwa dan na qira Abiy yaqi ษauka" murmushi yayi ya shafa kanta yana share mata hawayen yace "da akwai wani abu zan faษa miki ki yarda da yayanki ko, ki kula da kanki da qannenki kaman yanda nace in naje kuma zan haษaku da Ammi yanzu je ki rarrashi sweetie in na dawo zanzo na ษauke ta".
Ba dan taso ba ta haura sama sashin su taje ta samu sweetie tayi bacci idanuwanta duk bushashshen hawaye, sweerie kuma tana zaune gefenta tayi tagumi, kallon su da tayi ya sanya jikinta ya qara mutuwa nan dai ta daure tayi yanda yayansu yace mata ta nunawa sweerie komai lafiya wayan Ammi ba chaji ne kawai sannan itama ta zauna gefen su dan yau basa jin kowa zai iya kwana shi ษaya a ษakin sa.
ฦangaren DMD yana ganin haurawan qanwan sa sama ya sauqe ajiyan zuciya yana fita driver yazo da mota ya buษe masa ya shiga yaja motan suka fice a gidan, a taqaice kawai yace ma drivern "airport".
Suna zuwa airport suka samu ba jirgi mai tafiya Nigerian sai gobe, yaso biyan kuษin jirgin gaba ษaya a tafi da shi yau amma sai ya fasa tuna sweetie dan in ba shi ya rarrasheta ba baza taji rarrร shin sweedy ko sweerie ba. Juyawa suka yi suka koma gida lokacin ma dare yayi amma abinka da qasar turawa kuma babban qasa ko ina kaman rana ga jama'a ga haske.
Sama ya haura ya shiga ษangaren su, ษakin sweetie ya nufa dan yasan ba zasu wuce can ba, yana murษa handle ษin sweedy ta zuba mishi ido, sweetie tayi bacci kanta na cinyan sweerie ita kuma sweerie kanta na kan cinyan sweedy, duk sai yaji sun basa tausayi rana guda kawai na rashin jin Ammi har sun rame.
Qarasa shigowa yayi ya qara kwantar wa da qanwar tasa hankali, sannan ya ษauki sweerie ya kaita ษakin sweedy yace suje su kwana a can shi kuma ya ษauki sweetie ya fito ya nufi ษangaren sa da ita.
Har bedroom ya kaita ya kwantar da ita akan faffaษan gadon sa, shi kuma yaje ya ษauro alwala yayi sallahn isha'i da bai samu yayi ba ya kuma yi shafa'i da wutiri sannan yayi addu'oen sa ya kwanta gefen qanwar tasa yayi addu'a ya shafa mata shima ya shafa.
Sama-sama yake ji ana bubbuga shi ana sheshsheqan kuka, idanuwansa ya buษe ya kalli sweetie na tukuikuya shi, tashuwa yayi ya zauna ya riqo ta yana tambayan ta menene? Cikin sheshsheqan kuka tace "Darling Ammi na nayi mafarkin bata da lafiya kuma banji muryanta ba tun jiya ka qiramun ita" shafa kanta yayi alaman rarrร shi ya miqa hannunsa ya ษauko wayan sa ganin har 3 na dare yayi sai yace "sweetie ki bari sai gobe da safe kinga yanzu dare yayi kuma kinsan wannan lokaci Ammi na bacci kar mu tashe ta" da qyar ya samu ta haqura har bacci ya ษauke ta, tashuwa yayi ya ษauro alwala yayi nafilfilu da addu'oe sannan ya sha dai-dai ana qiran sallan asuba, jan carbi ya dinga yi har aka shiga ya tashi yabi masallaci.
Yana idar da komai a gaggauce ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin qananun kayan da suka karษe sa sosai, ganin sweetie bata farka ba sai ya barta a ษakin ya fice yaja mata qofa.
Yana shiga mota driver yaja sai international airport Canada.
Suna isa komai ready, driver ya ajiye sa ya juya shi kuma cikin mintuna biyar jirgin su ya tashi sai Nigerian.
Jirginsu na sauqa ya qira jay "Hello jay ina airport ka turo mun mota" qitt ya kashe wayan.
Bai kai minti talatin ba sai Jay da kansa yazo ya ษauke sa, da mamaki ya kalle sa yace "jiya kawai muka yi waya ba zaka zo ba yau kuma sai gaka akwai wani abun da ya faru ne?
Lumshe ido yayi dan yama rasa ta yaya zai fara sai kawai yace "Jay bansan me ke faruwa ba amma dai Ammi tun jiya bata je gida ba" da mamaki Jay ya kallesa yace "shine har ka shigo Nigeria akan hakan me yasa ba zaka qira layinta ba ko ka qirani naje na ษauko ta?
Cike da gundura da magana dan kansa har ya fara ciwo yace "Jay ka fahimta mana an qira layinta both baya shiga kuma nasa ayi tracking tun acan amma ba wani labari ga su sweedy duk sun ษaga hankali qarshe ma jiya sweetie a ษaki na ta kwana dan rigima wallahi har sun rame jiya kawai basu ji muryam Ammi ba".
Jay kansa ya ษaure ga tausayin su sweetie dan yasan irin sanya ta a jiki da Ammi tayi, cikin ษaurewan kai yace "to yanzu ina muka nufa?
DMD yace "wai Jigawa fa jirginta ya sauqa tabi Companyna na can duba yanayin ayyukan sannan ta ษau mota wai za tayi driving da kanta har Gombe nace mata a'a amma Ammi taqi ji".
"Yanzu ita ษaya ce ko tare da driver? Cewar Jay....
MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE๐ค DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA
Masu sharhi waษanda basa group na JAHILCI KO AL'ADAH Uwar batoorl na godiya tana yinkuโค๏ธ
INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuษi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaษan ne
KU TUNTUฦE NI A WANNAN LAYIN NAWA
***
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
***
Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo๐ค
# ๐พ๐ค๐ข๐ข๐๐ฃ๐ฉ
# ๐๐๐ ๐ &
# ๐จ๐๐๐ง๐