TRIPLETS (YAN UKU) BOOK 1 CMPLT

Episode 40-41

by @queenofsurprise1

TRIPLET'Sđź’ž




đź’ž FATEEMA MUSAđź’ž

(đź’žSTAR LADYđź’ž)




*GargarÉ—i*


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina.





WhatsApp me for more information ***







Episode 40-41



Duk wannan badaƙala na yankewa sojoji masu yi musu girki hannaye da Michael ke shirin yi Romeo da James basu sani ba, suna nan suna aikin gaban su, Micheal na tsula tsiyar sa a palon kasa son ran sa.


Da gaske Michael ya nufe su zai yanke musu hannu, nan fa suka fasa ihu mai karfin gaske, wadda ya sanya James fitowa da gudu dan yaga meke faruwa, shi kuwa Romeo daman kome za'ayi a cikin gidan baya tankawa in dai ba yaji muryan James da Michael ko daddy a cikin hayaniyar ba baya fitowa, ba ruwan sa baya shiga harkan kowa.


Ganin abun dake faruwa yasa James saukowa kasa da yar gudun sa yana faɗin "Stop Michael" turo baki Michael yayi yana faɗin "Kifi fa suka saka a abinci" ɗan shafa kan sa James yayi dan yasan shi yasa su saka kifin, da murya irin na mai rarrashi yace "Sorry our heartbeat ni nace su saka kifi a abincin Musharraf, to nayi kuskure ban faɗa musu a nashi kawai zasu saka ba" miƙa wa John wukar AK Michael yayi yana faɗin "To suje su kwashe duk wani abun da ya taɓa kifin nan su zubar da shi, ko spoon karsu rage min bana so gani, kuma shima uncle ɗin naka ka faɗa masa ba'a cin kifi a gidan nan, ba dan ma ya sa hannu a takarda ba da ya bar gidan nan yanzu" ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun dad suka haura sama yana faɗin "My dad I'm so sorry kaji?" Gyaɗa masa kai daddy yayi yana shafa kan sa yana faɗin "Kun cika zuciya over kamar mum ɗin ku" ɗaure fuska Michael yayi kafin yace "Dad ka dai na maganar ta, I don't want" shiru dad yayi yana jin kaunar yaran nasa har cikin ransa


Part ɗin Michael suka shiga sai shagwaɓa da sangarta Michael ke zubawa daddy, daddy kuma yana biye masa, dan yasan ba laifin sa bane matsalar daga kwakwalwan sane, Allah sarki Michael shi bashi da zafin zuciya sosai kamar na James da oga kwata kwata wato lion, ciwon sa yasa wani lokaci idan ya binkice sai ya zama kamar mahaukaci kamar mai tsananin zuciya, amma a zahirin gaskiya duk cikin triplets Michael yafi su saukin kai, dan shi bai yi karatu ba, cikin sauki zaka masa wayo kasa shi yayi maka abu koda baya so, kuma yana da saurin yarda da magana idan aka masa, shiyasa ko yayi fushi yake saurin sauka, shi James ba saukin kai gare shi ba kawai basaja yake, shi kuma oga lion ma ai ba'a magana karshe ne shi a zafin kai da zafin zuciya.


A ɓangaren su James kuwa, umarni James ya bawa sojojin a kan su sake yin wani girkin wannan duk su kwasa su zubar da shi, sannan kamar yadda Michael yace duk wani kwanon da pots da suka san kifin nan ya taɓa to su zubar da kwanikan dukka har da tukanen, sai murna suke James ya cecesu Michael bai yanke musu hannu ba, har wani yar sakin fiska sukayi yau, sosai suka zubawa James godiya da fatan alkhari sannan suka amsa umarnin da ya basu, suka tashi suka koma bakin aikin su, dan su sake yiwa family'n daddy abinci, dan duka yaran daddy ba wanda ya iya cin abinci a waje, sai dai idan tafiya sukayi, shima tafiya idan suka san zasu fi kwana ɗaya a waje tofa ɗaukan mai aiki suke, duk wuya a gida suke cin abinci, su wasu irin mutane nen da suke da kyamar bala'i dukkan su karku cire kowa, suna da kyama sosai, ba kuma iya abinci suke kyama ba har da ɗan adam, haka suke, mu samman Romeo yafi kowa wannan ɗabiar yana da kyama over, sannan baya son wani ya raɓe sa, ammafa yana da kyauta sosai, ga sadaka duk wasu gidan marayu dake cikin birnin Washington DC kullun ranar Sunday yana kai musu ziyara na kyaututtuka masu yawan gaske, haka duk wani wajen bauta yana kai sada bai ware ko ɗaya ba, har masallaci, dan akoi wani babban masallacin ma wadda shi ya gina da kuɗin sa, haka akoi wani babban church da ya gina da kuɗin sa, time to time yana kai ziyara gidan tsofaffi da ga jiyayyu haɗe da makarantun gomnati, sannan a ɓangaren wasanni ma, irin su kwallon kafa da sauran su yana basu kyauta sosai, amma pannin wasanni yana bada kyautar ne saboda Michael, shi baya kallon kwallo da sauran su Michael ne mai kallon kwallo, to da Michael yaga Team nasu taci zai zo ya sanar da Romeo a kan ya musu kyauta, akoi islamiyoyi da dama da yake kai musu ziyara tare da kyaututtuka da dama, baya ware wani addini guda ɗaya yace ba zai musu kyautaba a'a idan ya tashi dukka addinan yake haɗawa ya basu kyauta, duk wasu manya manyan masallatai da church's dake birnin Washington DC ya sai musu manya manyan motocin na zuwa da'awa, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya ya kasan ce mai bala'i farinjini ta ko'ina, yana ɗaya daga cikin abun da ya sanya ya sawa ransa babu wani ɗan adam da zai soshi domin Allah sai dai dan kuɗin sa ko kyan sa ko mukamin sa a wajen aiki, hakan yasa ma baya yarda da kowa.


Wucewa James yayi ya bar palon ya koma wajen Musharraf dan su ci-gaba da hiran su, Tga da John kwata kwata basu ji daÉ—i ba sun so Michael ya yankewa sojojin nan hannu da mugunta irin na zuciyar kafurci, cike da jin haushi suka wuce kowa ya koma bedroom na sa.


Misalin karfe 8 Na dare Romeo na tsaye a balcony bedroom nasa ya goya hannayen sa a saman faffaÉ—ar kirjin sa, saboda sanyin da ake sosai yasa ya sanya puffer Jacket nasa mai É—an girma wadda yazo masa har gwiwar sa duk tsawon nan nasa, ya sanya hulan jacket É—in a kan sa, ga wannan kyakkyawan guntun gashin gaban goshin nasa ba karamin kyau yake karawa fuskar sa ba, sai dai fuskar kamar kullun a É—aure take tamau kamar hadari, sai tashin fitinannen kamshi yake, yayi shiru yana tunani a kan James


Kamar a mafarki ya hango James a kasa harabar gidan, yana kokarin fita ta kofar sirrin su dake ta bayan wajen lambun daddy, zuba masa dara daran ido sa Romeo yayi yana kallon yadda yake lallaɓawa alamar mara gaskiya


Ganin zai fice ne yasa Romeo yayi sauri Juyawa ya komo cikin É—aki, ya shige dressing room nasa yana tunanin ina James zai je a daren nan da zai fita ta kofar sirri sannan kuma ba tare da motar sa zai fita ba, satar hanya zai yi kenan ko me.


Jim kaÉ—an Romeo ya fito sanye da takalmi Booth baki mai shegen kyau a kafar sa, sannan ya sanya face mask a fiskar sa tare da hand gloves a hannun sa, ya sa bakin glass a idon sa, a takaice baka iya ganin komai nasa kuma ba zaka gane wanene ba, wayar sa ya É—auka da sauri ya nufi waje dan yabi bayan James.


Yana fitowa Palon sa sukayo ya karo da Michael yana kokarin shigowa, baya kaÉ—an Michael yayi ya bashi hanya, da sauri Romeo ya fice ba tare da ya kallin in da Michael É—in yake ba, bin sa da ido Michael yayi yana mamakin ina zai je yake wannan saurin.


Sai da Romeo ya kurewa ganin Michael sannan ya wuce ya karisa cikin bedroom É—in, yana shiga ya faÉ—a saman lallausan katafaren bed É—in Romeo yana wani sauke ajiyar zuciya.


A hankali ya kai hannun sa ya kwance diamond watch nasu na Triplets dake hannun sa yana kokarin É—aurawa saman bedside drawer kwatsam idon sa ya sauka a bayan watch É—in, ganin wajen yayi tamkar anyi ajiya a wajen.


Matso da agogon yayi sai tin fiskarsa ya zubawa agogon ido na yan mintoci kafin ya kai hannun sa ya zaro abun da idon sa ke gane masa, memory card ne guda biyu wadda James ya ajiye cikin agogon, sosai Michael ya sha ruwan mamaki tare da shiga ruÉ—un waye ya sa masa wannan memory's É—in a cikin agogon sa, sai dai abun da bai sani ba wannan É—in agogon James ne ba na shi ba


ĆŠayan hannun sa ya kai ya jawo laptop É—in Romeo dake saman bedside drawer ya kawo gaban sa, kunna wutar screen É—in yayi tare da cire password, kasan cewar already ya san password É—in, nan fa idon sa yayi masa arba da abun da ya kara jefa kwakwalwan sa a cikin ruÉ—ani, da sauri ya kara waro brown eyes nasa waje dan ganin abun da yake gani gaskiya ne


tabbas idon sa gaskiya yake gane masa, kofar gidan mum É—in sune Romeo ya sanyawa camera dan yaga masu shiga da masu fita, Michael yayi mamaki over, kenan duk wannan kiyayya da tsana da Romeo ke nunawa mahaifiyar su yana bata kulawa da kariya to yaushe ya fara yin hakan, da sauri Michael ya fara tariye camera'n baya dan yaga yaushe hakan ta fara faruwa bai sani ba, sai yaga ashe É—azun ba jimawa aka sa camera'n bata É—auki abubuwa da yawa ba, yasha mamaki sosai, fita wajen gaba É—aya yayi ya É—auko card reader a cikin bedside drawer ya sanya memory card guda É—aya daga cikin biyun da ya fitar, É—ayan kuma ya ajiye saman laptop É—in


Sanya card reader yayi a laptop É—in ya fara duba memory dan yaga menene a ciki ko zai gane waye ya sa masa memory's É—in a jikin agogon sa.


Bayanai ne na duk wani abubuwan har kallan su James, bayanai ne na daga in da suke sayo makamai har in da suke sayarwa, duk wani sheɗanci da suke yana cikin wannan memory, ga kuma hotonan manya manyan jiga jigan yan ta'addan na duniya, wasu ma ba wanda ya taɓa ganin hoton su, sai sunan su na ta'addanci kawai aka sani, sunyi kaurin suna wajen ta'addancin amma James yana da hotonan su duka, kasan cewar shi Micheal ba wani karatu ya tsaya yayi ba, sai bai gane komai da ke rubuce a wajen ba, kawai kallon rubutun yake, sai dai ya shiga folder nan ya fita ya shiga wannan amma ba wani abu da ya fahimtar, ga bayanan da gomnati da kuma Romeo suke nema ruwa a jallo Michael ya same su a ɓagas amma ba abun da ya fahimtar, kallon shirme ma yakewa bayanai dan rashin karatu, ba abun da ya iya karantawa aciki.


Da yaga sai gayyan rubutu ne a wajen sai ya cire memory card É—in, kamar zai sanya É—ayan memory ma ya gani, sai ya fasa ya kwashe su ya mai dasu cikin watch É—in yana faÉ—in "Bari lion ya dawo na bashi na tambaye shi ko dai nashi ne shiya ajiye a wajen" da wannan tunanin ya mai da laptop É—in saman drawer ya kwata yana kallon sama, kamar mai tunani.


Abun da Michael bai sani ba shine É—ayan memory card É—in videos ne makare a ciki na yadda suke shirya ta'addancin su har yadda James ke canza fiska ya shiga cikin yan ta'addan yayiwa kan sa video yana cikin É—ayan memory da Michael É—in ya fasa sawa cikin laptop É—in


A ɓangaren su Romeo kuwa, shima ta kofar sirrin yabi ba tare da ya bari wani soja ya lura da fitar sa ba, dan bai son kowa yasan meke faruwa, idan ma wani abu James ke aikatawa to bai son kowa ya sani sai shi kaɗai, dan in wani yasan James na aika ta ba dai'dai ba maganar ba zata tsaya iya nan ba shiyasa yayi fitar sirri shima ko mota bai ɗauka ba.


Sai sauri James yake Romeo na biye da shi a baya ba tare da ya sani ba, dan akoi tazara mai É—an nisa a tsakanin su, saboda James ya riga Romeo fitowa.


Sai da James ya fita daga anguwar su gaba É—aya sannan ya nemi motar haya ya hau, shima Romeo karo na farko daya fara hawa motar haya, kaÉ—an kaÉ—an yacewa mai motar hayan nasa ya tafi a hankali kar James ya gansu.


Suna cikin tafiya ne wata babban mota irin mai kwantena a bayan nan, irin na É—aukan kaya tazo a guje saura kaÉ—an tabi ba kan motar su Romeo, kasan cewar hanyar akoi fitullun kan hanya masu bala'i haske, sun haske ko ina hakan ya bawa Romeo damar ganin motar da kyau, kasa kasa yace da driver motar hayan ya dakatar da mota, dan bai yarda da wancan motar da ta wuce su ba dan yadda take wannan uban gudu alamar rashin gaskiya ne, gashi kuma yana son bin bayan James, amma yafi son bin wancan motar saboda yasan ko ba komai dole James zai dawo gida kuma in ya dawo dole ya faÉ—a masa in da yaje, ita kuma motar idan ya barta ta tafi ba lallai ya sake ganin taba, dan haka sai yace da driver motar hayan daya juya subi wancan motar.


Ba musu driver ya juya duk da bai san waye ya É—auko a cikin taxi É—in nasa ba, sosai wancan motar ke tsala gudu a kan hanya duk da girman ta, hakan yasa Romeo ya kara zargin motar sosai da sosai.


Dai dai wani check point na kan hanya wasu yan sanda dake tsayawa a wajen suka dakatar da motar, shima Romeo dakatar da mai taxi ɗin sa yayi ya fito yace wa mai taxi ɗin "I'm coming" ya nufi wajen motar can, dai dai lokacin driver motar ya bawa ɗan sandan cin hanci, ba tare da yan sandan sun binciki motar ba sukace motar ta wuce dan sun karɓi cin hanci.


Driver ya koma cikin motar yana kokarin tada motar Romeo bai yi wata wata ba ya fisgo driver motar yayi wurgi da shi waje, cikin sauri sauran dake cikin gaban motar suka fito, su biyu ne, da ka gansu kaga rikakkun yan daba, ga jikin sunan duk tabon shatin yan kan wuka,


Saboda jacket da ya sa ya kuma saka hular a hansa ga face mask da glass a fiskar sa gashi dare ne hakan yasa har yan sandan dake wajen basu gane shi ba.


A guje wayan nan yan daba biyun sukayi kan sa da nufin dukan sa, duk kan su duka É—ai'É—ai ya musu suka zube kasa kamar wasu kayan wanki


Abun ku da rashin gaskiya irin na duniyar yanzu, sai yan sandan dake wajen suka ciro bindigu suka saita Romeo da shi wai ya É—aga hannu sama ko su harbesa a kan me zai daki wayan nan mutane, saboda sun basu cin hanci yasa suke wannan hargagin, hakan da yan sandan sukawa Romeo yasa ya kara zargin su ya kara sawa a ransa kenan kullun motar tana wuce suna bata hanya kenan.


Bai É—aga hannun sa ba sai ya juyo yana kallon yan sandan, sun dage zasu harbe sa idan bai É—aga hannu ba, a hankali ya É—ago kafar sa ya fara tinkarar su, sai kokarin harbin sa suke amma bindigar taki harbi saboda tsorata da sukayi jikin su nata kerma sun kasa danna kunamar bindigar da kyau, É—aya daga cikin sune ya kira wayar over over akan a karo musu yan sanda ga É—an ta'adda sun kama yana kokarin yi musu illah.


Wannan danganta Romeo da ɗan ta'adda da sukayi hakan ya ɓata masa rai a fusace ya kwace bindugun hannun su, ya musu dukan tsiya, wadda ya sasu sumewa a wajen, da farko bai yi niyar dukan su ba, a matsayin su na jami'an tsaron yaso ya sa a cire musu kakin sune ma'ana a kore su daga aiki sannan a basu hukunci dan sune ɓata garin tun da su suke karɓan cin hanci su bar masu laifi su gudu, amma danganta shi da ɗan ta'adda da sukayi yasa ransa ya ɓaci ya musu dukan kawo wuka duk ya fashe musu fuska, shi kuwa driver taxi daya kawo Romeo tuni ya juya kan motar sa ya gudu, yaga Romeo na dukan yan daban nan kar ya shafesa dan shima bai san wa ya ɗauko a taxi ɗin nasa ba, shima cewa yake ko dai ɗan ta'adda ya ɗauko ne.


Daman yan sanda uku ne a wajen lilis Romeo ya musu da duka, sannan ya É—auki bindigar É—aya daga cikin su yana kokarin har bin kwaÉ—on da aka rufe kwantenan bayan motar dan yaga me suka É—auko suke wannan gudu haka


bai kai ga harbin kwantenan ba sai yaji diran motoncin yan sanda, wanda wancan É—an sandan ya kira office nasu a kan a turo yan sanda ga É—an ta'adda sun kama.


Zubawa motoncin yan sandan ido yayi ta cikin black glass nasa yana kallon su, motoci uku ne, suna iso wajen sukayi parking suka diro kasa suka kewaye sa da bindigun su, suna faÉ—in "you are under arrest keep this gun and raise up your hand" ka ajiye bindigar nan ka É—aga hannun ka sama"


shiru ya musu kamar bai ji me suka ce ba, abun ma haushi ya bashi, hannu yasa a aljihun sa, a sukwane yan sandan suka ja baya a tunanin su boom ko wani makamin zai ciro, haushi ma yaji kamar ya harbe yan sandan duka su mut dan a cewar sa basu da ammafa suna yan sanda suna da wannan tsoro haka, daga sa hannu a aljihun sa sun ja baya


Wayar sa ya ciro suna ta ce masa ya ajiye wayar nan amma kamar ba da shi suke ba, latsa wayar nasa yayi na É—an lokaci kafin ya mai da aljihun sa ya juya ya saita kwaÉ—on dake jikin kwantenan zai harba kenan É—aya daga cikin yan sandan ya harbe bindigar hannun sa, bindigar ta faÉ—i kasa shi kuma bullet É—in ta É—an kuskure hannun sa, a fusace ya juyo yana kallon wanda yayi harbin


Kwata kwata baya jin duka mutane yau kuma baya jin yin kisa, amma suna kure sa,

tsawa yan sandan suka daga masa wai ya zube a kan gwiwowin sa, ran sa ya fara ɓaci yanzu, yana kokarin takawa ya tinkare su dan ya musu dukan mutuwa kenan sai wajen gaba ɗaya ya karaɗe da jiniyan jiga jigan motoncin sojoji masu numfashi kai daga jin jiniyar ma kasan ba sojojin wasa ne ke tunkarar wajen ba, dakata wa yayi dan shi ya kirasu a kan suzo su tafi da gaba ɗaya yan sandan nan, dan yana da aiki a kan James sosai so baya son ransa ya ɓaci yau, yana son cikin nitsuwa idan James ya dawo suyi magana shiyasa ya kira sojojin.


A ɓangaren yan sandan kuwa sai murna suke wai an turo musu sojoji kila manyan su sun samu labarin babban ɗan ta'adda ne suka kama shiyasa suka haɗa musu da sojoji, sai dai abun da ya ɗaure musu kai, wannan jiniyar na motar jiga jigan sojojin kasan ne, kenan manya manyan sojoji kamar wayan nan zasu iya kawo wa kananan yan sanda kamar su ɗauki, abun ya basu mamaki amma dai sun zuba ido suna jiran suga me ke shirin faruwa.


Jibga jibgan motoncin masu numfashi shabiyu ne suka iso wajen, wasu jibga jibgan sojojin masu jini a jika, fararen American tas da su, gasu da kirar karfi sun samu horo mai kyau, fuskokin nan nasu kamar hadari babu wasa a É—aure take tamau ba su san menene dariya ba, ganin wayan nan sojojin kawai ya isa ya sa rundunar mutane zuciyar su ya buga su mutu saboda tsoro.


Ji kake dip dip, suna dirowa kasa daga bayan motocin su, da gudu wasu suka kewaye Romeo dake tsaye, wasu kuma suka kewaye wannan motar yan ta'addan wasu kuma suka kewaye gaba ɗaya kan titi daga ta in da suke, hannun su na rike da jiga jigan bindigogi wayan da suka amsa sunan su bindiga, wadda baya saɓa saiti in da ka aikashi nan zan wuce kai tsaye, ba irin makaman kananan yan sanda da sojoji bane.


ĆŠaya daga cikin yan sandan ne yace da sojojin "Yauwa wannan shine É—an ta'addan ku kama shi, É—an tada kayan baya ne, yazo ya fara dukan jami'an tsaron mu ya.... Bai kai karshen maganar ba sojan É—aya ya daka masa wani gigitacen tsawa wadda ya sanya gaba É—aya yan sandan dake wajen zubewa kasa a kan gwiwowin su, tsabar tsoro jikin su sai kerma yake


A hankali Romeo ya zame hular kan sa tare da karɓan bindigar ɗaya daga cikin sojojin sa, ya sai ta kwaɗon jikin kwantenan motar yan ta'addan can, ya harbe kwaɗo, kofar ta buɗe


Ji kake dip dip da gudu sojoji biyu suka zo suka buÉ—e masa kofar contenan, yan mata ne cike a ciki duk basa cikin hayyacin su an musu allura fita daga hayyacin su, kallo É—aya Romeo ya musu ya kawar da kan sa gefe ya juya tare da cire hand gloves dake hannun sa ya nufi mota É—aya daga cikin motocin da sojojin sa sukazo yanzu.


Lokacin da Romeo ya cire hulan kan sa kamannin sa suka bayyana tsoro yasa yan sandan dake wajen sume saboda babu wani É—an adam dake cikin birnin Washington DC da baya tsoron Romeo bare kuma su da suka masa laifi har da harbin bindigar hannun sa tab, sun gama sadaukarwa yau mutuwa zasu yi, shiyasa suka fara da suma tun ma basu ji hukuncin da zai yanke musu ba.


Shi kuwa bai bi ta kan su ba ma dan yana da abun yi, motar sojojin sa ya nufa, da gudu jibga jibgan sojoji biyu suka nufe sa, suka buÉ—e masa kofar motar gidan gaba, shiga yayi ya zauna sannan gently yace su kai masa wayan nan yan ta'addan gida zai yi aiki a kan su da kan shi, motar yan ta'addan kuma su kai headquarter su ajiye zuwa da safe yan sandan nan kuma su kira president su sanar da shi ya soke aikin su, dan dukkan su basu san aikin da suke ba.


ĆŠaya daga cikin sojojin sane ya shiga motar ya mata key yaja sa zuwa gida, har cikin gida ya shiga da Romeo, yana yin parking ya fito ya buÉ—e masa kofar motar, gently Romeo ya sako kafar sa waje kafin ya fito gaba É—aya ya nufi cikin gida, shikuma sojan ya juya kan motar ya koma wajen sauran sojojin can dan suyi aikin da lion ya saka su.


Lokacin da Romeo ya shiga bedroom nasa, Micheal na kwance masa saman katafaren gadon sa idon sa a lumshe da alama barci yake, wuce sa Romeo yayi yaje ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kayan barci masu kyau da tsada launin sky blue riga da dogon wando mara sa nauyi.


Sai tashin fitinannen kamshi yake ya saki dark black curly hair sa har baya, ya haye saman bed nasa kusa da Michael ya jawo laptop nasa ya fara aikin bincike a kan James.


Number wayar James ya shigar cikin laptop ɗin nasa ya fara kokarin bin diddigin in da James ɗin yake, yasha mamaki ganin number James yana shararin sama niya, kenan jirgi James ya hau zuwa ina to? Shiru Romeo yayi yana mamakin ina James zai je bai sanar da shi ba, kuma dole yasan tafiya zata fita cikin Washington DC, har James zai iya fita cikin garin nan ba tare da sani na ba? Sai jerowa kan sa tambayoyi wadda bashi da amsar su yake, "gaskiya nayi sake na biye musu ina musu abun da suke so, daman dan suje suyi ta tsula tsiyar su a waje ne yasa sukace basa son bodyguards ko sojoji surinƙa binsu idan zasu fita, nayi kuskuren yarda da hakan da nayi" sosai Romeo yake tunani a zuciyar, daga karshe dai sai ya fara binciken wace jirgi James ya hau kuma ina zai je, me ya fitar da shi cikin Washington DC da daddaren nan kuma da jirgin kasuwa abun da basu taɓa yi ba, koda yawon shakatawa su James zasu je wata kasa jet ɗin sa yake badawa a kai su duk in da zasu je dan tsaro, amma yau James ya saci hanya ya hau jirgin kasuwa why.


Duk wani binciken da yayi a wannan daren dan gane ina James ya dosa bai samu damar gane wa ba, dole dai sai da safe yasa sojojin sa su bincika masa a wani airport James ya hau girji dan suji ina zai je, daga nan ya ajiye bincike a kan James ya shiga bincike cikin sauran criminals da basu samu damar halactar taron su James ba dan ya gano ina suke,


Bayan ya kammala wannan binciken ne kuma ya shigar da number motar da ya kama É—azun mai É—auke da yanmata nan, nan ma yayi bincike a kan motar, daga ina motar ta fito ina kuma ta nufa, dan ya san dai ba iya wayan nan yanmatan ne kawai ba, tun da motar ta kwaso wayan nan tofa tabbas ta saba kwasan yanmata ne dole ya san ina ake wannan badakala a cikin garin sa,


Da binciken nasa yayi bincike a wajen bibiyar ɗaya daga cikin driver masu safaran yanmata da suka kama, nan yaci karo da driver'n yana yiwa wani babban likita aiki, ganin yana aiki da likitan yasa Romeo ya fara bincike a kan likitan da kuma asibitin, nan yaga abun da ya tayar masa da hankali, domin kuwa a wannan asibitin ana kawo maza da dama ana cire musu kodar su, da wasu sassa jikin su irin su ido gaban su da dai sauran, ana sanyawa manyan masu kuɗi na duniya, yasha mamakin ganin duk wannan badaƙala da sheɗan ci ace a cikin garin da yake ake yin su, abun ya ɓata masa rai sosai, ji yake kamar ya tashi ya tafi wannan asibitin yanzu, sai dai dare yayi, kashe laptop ɗin yayi ya ajiye saman bedside drawer ya ɗan yi shiru na yan mintoci kamar mai tunanin wani abu, sannan ya kwanta ya ja musu bargo shida Michael yau ko abinci ma bai jin ci saboda tunanin da ya masa yawa meke shirin faruwa da su ne, ina James ya tafi wayan nan abubuwa sun dame sa, hakan yasa yaji baya jin yinwa kwata kwata.


Ko da ya kwata ya kasa barci tunanin James kawai yake, ya rasa dalilin da yasa yake ji a ransa tamkar zai rabu da James, slowly ya waro dara daran idon sa, ya zubawa Michael kallo, sai barcin sa yake bawan Allah hankalin sa kwance bashi da wata matsala, shafa kan sa Romeo yayi sannan ya mai da idon sa ya lumshe yana tunanin ya zasu yi idan akace yau babu James a tare da su, dan tabbas idan abun da yake zargi a kan James ya tabbata shi da kan sa zai harbe James ɗin da bindiga, dan ya kamanta adalci, to ya zasu yi yau idan akace ya harbe James da bindiga ya mutu, tare suka taso kullun suna tare, duk da baya shiga har kan su, yana matuƙar kaunar su fiye da tunanin mai tunani


A wannan dare dai da kyar barci ya É—auki Romeo zuciyar sa cike da tunanin É—an uwan sa.


Asuba ta gari


Mu leƙo Nigeria mu dawo jama'a


# đź’žNIGERIAđź’ž



đź’žKADUNA - GIDAN ABBOđź’ž


Almost 30mins Hajiya ta ɗauka kwance tana mai da numfashi kafin ta ɗago ta kalli Jelly, a hankali ta zuro kafafun ta kasa sannan ta miƙe ta riƙo hannun Jellyn suka nufi bedroom nata tana faɗin "Me yasa kikayi wannan kwaɓen a fuskar ki?" Toro baki Jelly tayi kafin tace "Nifa wanka da kwalliya nayi" shiru Hajiya tayi dan tasan halin Jelly yanzu idan tace zata mata wani magana ko ta mata faɗa idan ta fara kuka sai ta kai dare bata yi shiru ba, gashi bata jin rarrashi ko kaɗan, dan haka Hajiya sai ta rufa wa kan ta asiri tayi shiru taja hannun ta kawai suka wuce toilet


Suna shiga toilet a sukwane Hajiya ta zaro ido ganin lalatan da jelly tayi da sabulai dake cikin toilet É—in


Bokitin dake cikin toilet ɗin Jelly ta ɗauka ta ɗaura shi saman baf ɗin wanka ya ɗebo duk wani shower gel da su toothpaste da su sabulai su man kamshin baki shaving powder duk ta haɗe su cikin bokitin nan ta gauraye su waje guda, da farko Hajiya ta kasa gane menene ma a cikin bokitin sai daga baya data kalli robobin su shower gel ɗin a gefe ne yasa ta gane menene a cikin bokitin, salati tayi ta sanar da Ubangiji yau ga abun da ya fi karfin tunanin ta, tana tsoron yiwa Jelly wata magana, dan in ta kuskura tawa Jelly maganar da bai mata daɗi ba, idan ta fara yi mata ihu har dare bazata yi shiru ba, sai Abbo ya dawo ya rarrashe ta yayi ta yiwa Hajiya faɗa a kan me zata ɓata mata rai.


ĆŠaukan bokitin Hajiya tayi ta fitar waje, dan wayan abubuwa da Jelly ta haÉ—a sai zubarwa, dan har da su makilin na goge baki ta musu asarar makudan kaya masu tsada.


Jelly na tsaye a cikin toilet ɗin har hajiya taje ta zubar da kwaɓen da tayi ta dawo hannun ta riƙe da wani carton na sabulu mai kyau da tsada, ajiye bokitin tayi ta haɗa ruwan wanka sannan ta cirewa Jelly kaya ta fara yi mata wanka


Ba karamin wahala ta shaba wajen wanke fuskar Jelly, dan mai data damɓara kan sabulu ga foundation da kwalli abun ba'a magana, ita kan ta Jellyn sai da tayi kuka wajen wanke mata fuskar nata.


Bayan Hajiya ta gama mata wanka tsab ne ta ɗaura mata towel suka fito suka nufi bedroom ɗin Jelly ɗin, sosai Hajiya baiwar Allah ta mata kwalliya mai kyau ta sanya mata kaya dogon riga abaya wanda yaya Nawid ɗin ta ya sayo mata, sannan ta feshe ta da turare mai kamshi, tsab ta koma kamar ba ita ba, ta dawo asalin Jellyn daddy, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka fito palo.


Saman sofa ta zaunar da ita tace "Ki zauna kiyi kallo bari nayiwa Abbon ku girki kinga yau a part namu yake kuma yamma yayi" make kafaɗa Jelly tayi ta turo baki tana faɗin "Ni a'a zan biki kitchen na taya ki aikin nima" Hajiya zatayi magana Nawid da ya fito yanzu yace "Ai gara duk wani aiki da zaki nayi Ummi ki rinƙa yi tare da ita ko zata koyi wani abun arziki tun da kinga mace ce kuma ba yarinya bace nan gaba kaɗan sai aure" jin abun da Nawid yace yasa Hajiya tace eh yana da gaskiya dan haka sai ta kama hannun Jelly suka wuce kitchen tare


Aiki Hajiya ta fara yi, tana yi tana nunawa Jelly komai dalla dalla, sai gyaɗa mata kai Jelly keyi kamar mai gane duk abun da Hajiya ke faɗe, alhalin ba abun da ke shiga kan ta, miyar steew sukayi ko in ce Hajiya tayi dan Jelly kam tana tsaye a gefe tana ganin duk abun da Hajiya ke sakawa a cikin miyar, ta zuba ido tana kallon yadda Hajiya ke saka su carry kaɗan kaɗan a cikin miyar, ji take kamar taje ta karɓa robar carry ɗin ta bulbula dukka cikin miyar dan ita bata son harka da karanta so take taga ana bulbula komai yaji sosai


Bayan Hajiya ta tabbatar miyan yayi ne sai ta sauke dai'dai lokacin kuma ruwan shinkafa data É—aura a gefe É—ayan gas É—in ya fara tafasa, store ta nufa tana faÉ—in "Bari na É—ebo shinkafa" shiru Jelly tayi bata amsa ba


Hajiya na shiga store Jelly ta É—auko goran plate wash wani omo ne na wanke wanke, dan taga Hajiya ta saka su curry black pepper da sauran su, kuma taga kaÉ—an kaÉ—an Hajiya ta saka, ita kuma bata son harkan abu kaÉ—an tafi son dayawa shiyasa Hajiya na shiga cikin store ta É—auko goran plate wash dake kusa da pots da Hajiya ta wanke yanzu, dan a tunanin ta shima kayan haÉ—in miyane


BuÉ—e miyar tayi ta zuba mai É—an yawa sannan ta gauraya miyar, ta mayar da plate wash É—in ta ajiye a in da ta dauko, ta É—auko ledan gishiri shima ta zuba ta É—an kara su carry da duk wani abu da Hajiya ta sa a miyar, jin Hajiya na zuwa yasa tayi saurin gauraya miyar ta mayar ta rufe tana jin daÉ—i ta zuba abubuwa dayawa dan ita bata son har abu kaÉ—an tafi son taga komai yaji sosai zam zam.


Koda Hajiya ta dawo bata wani lura da Jelly ba kawai ta ci-gaba da aikin ta, har suka kammala, da Hajiya tazo zuba abincin a cikin warmers data buÉ—e miyar taga ya É—an canza kala amma da yake hankalin ta baya wajen tana sauri mangariba yayi zataje tayi wanka dan Abbo ya kusa dawowa hakan yasa ta zuba abincin kawai ta kwasa suka wuce palo


A saman table ta jere komai sannan tace Jelly ta zauna bari taje tayi wanka, ba musu Jelly ta koma ta zauna saman sofa tana tunanin ko dai ta É—auko su curry É—in nan ne ta kara dan kamar wadda ita ma tasa yayi kaÉ—an, sai sake sake take a zuciyar ta ita kaÉ—ai, har Hajiya tayi wanka ta fito tace taje tayi alwaya suyi Sallah


Ba musu ta tashi ta nufi toilet nata ta É—auro alwalar ta kamar yadda Hajiya ta koya mata sannan ta fito ta zo sukayi Sallah tare da Hajiya a palo.


Sai bayan sallar issha sannan Abbo da Nawid suka shigo, wanka sukaje suka fara yi first kafin su zo saman table su zauna, Hajiya ita tayi serving nasu dan tace bata son masu aiki ita take komai da kan ta.


Abbo shi ya fara kai abincin bakin sa, a É—ari ya tofoshi waje har yana kakarin amai, zaro ido Hajiya tayi tana tambayar menene a ruÉ—e da hannu ya mata nuni da ta É—anÉ—ana abincin taji dan ya kasa magana abincin har É—aye fatar baki yake saboda gishiri da plates wash da kuma su carry da Jelly ta banka a ciki yayi yawa over yana É—aye harshe


Nawid kam tun da yaga haka sai ya fasa kai abincin bakin sa ya mai da ya ajiye, Hajiya kuma É—aukan spoon tayi ta É—eba abincin ta kai bakin ta, a sukwane ta fito da shi waje tana salati, ita kam Jelly dama tun da suka zauna ta fara cin naman kasa hankalin ta baya kan su kwata kwata, sai bayan ta cinye cinyar kazar ne ta É—auki spoon ta É—ebo shinkafar da labcecen miya ta kai bakin ta


Wani ihu ta fasa wadda yasa Hajiya da Nawid miƙewa suna kokarin gudu, shi ma Abbo ya tsorata da ihun sai dai bai miƙe ba.


Rai a ɓace Nawid yace "Ke baby me haka?" Abbo ne ya daka masa tsawa "Haba Nawid me ta maka zaka mata wannan tsawa haka?!!" Zaro ido waje Nawid yayi yana mamakin abun da Abbon yayi, Abbo bai taɓa yi masa tsawa ba ko da wasa, hakan da yayi yanzu ya kara ɗarsa zargin sa a zuciyar Nawid ɗin, ita kan ta Hajiya sai da tayi mamaki a wannan karon Abbo bai taɓa yiwa Nawid tsawa ba sai yau


Abbo kuwa ganin Hajiya da Nawid sunyi mamaki ne yasa yayi saurin basar da maganar da cewa "Ku tashi muje restaurant kawai muci abincin tunda wannan kam dai ya tashi aiki, sannan Nawid kai kuma ka dai na yiwa baby tsawa baka ganin tana cikin ciwo ne?" Shiru Nawid yayi yana tunanin yadda zan binciko me Abbo'n sa ke nufi da Jelly, dan yasan ba haka kawai zai rinƙa yin wayen nan abubuwa a kan taba, Nawid ba yaro bane a kalla zai kai 26 years a duniya gashi da saurin fahimtar abubuwa


Ganin sunyi shiru basu da niyar tafiya ne yasa Abbo ya miƙe yana faɗin "Muje ko?" Jiki ba kwari Hajiya ta wuce bedroom nata tana faɗin "Bari na ɗauko mayafi" to kawai Abbo yace suka wuce waje shi da Nawid ita kuma Jelly tana zaune tana cin namar gazan ta, dan tun da ta saka shinƙafar a bakin ta tayi wannan ihu daya razana su Hajiya sai ta ci-gaba da cin namar ta kawai bata ma san da su Hajiya sun tsorata ba.


Jim kaɗan Hajiya ta fito sanye da mayafin hannun ta riƙe da mayafin Jelly, zuwa tayi ta sanyawa Jelly mayafin sai faman figar nama Jelly keyi, riƙo hannun ta Hajiya tayi suka bi bayan su Abbo, motar Nawid suka shiga shi yaja su suka tafi zuwa restaurant ɗan cin abinci, sai mamaki Hajiya take, me ya samu abincin da ta girka.


To masu karatu mu leƙo Daular mutuwa mu dawo


👹DAULAR MUTUWA👹


Sosai duna yake aiki a kan yadda zai samu ya kuɓutar da Rimsha daga ɗakin duhu na Queen, baba da Mustapha kuwa sun dukufa sai addu'ar fatan nasara suke masa, Ayla da Kausar ma ba'a bar su a baya ba, sosai sukewa Rimsha addu'a a zuciyar su dan ba daman kiran sunan Allah a baki, amma fa sosai Ayla ke kuka duk lokacin da ta keɓe ita kaɗai sai tayi kukan rashin Rimsha, yan kwanakin kalilan da sukayi da Rimsha sunyi sabo sosai wadda rabuwar su abune mai matukar wuya wadda zai yiwa ko wannen su balai ciwo, Ayla akoi ta da hakuri ga kirki da son mutane shiru shiru bata da hayani ta.


Allah sarki Ayla baiwar Allah ko ya akayi tazo daular mutuwa ita kuma oho, sai dai ku kasance da alkalamin princess Teema dan ita kaÉ—ai ce zata warware muku komai sannu a hankali, ammafa akoi cakwakiya, yanzu wasan zai fara.


To masu karatu kuma sai ku taya Rimsha'n ku da Addu'a kuyiwa duna addu'ar fatan nasara na barku lafiya, gobe idan Allah ya kai mu The beginning zai kare sai ku shirya, yanzu wasan zai fara bye sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu..


Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪


đź’žStar Ladyđź’ž