General NASEER Zaki

13

by @azizat

*GENERAL NASEER ZAKI*

(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03

Arewabooks: Azizat


                          Page 013

Abu na farko da Fatima ta fara lura da shi game da mijinta tun dawowarsu shine rashin samun bacci.

Kwata-kwata baya iya bacci. Da ya rufe ido ko minti ishirin ba zai ka ba sai ya zabura ya tashi.

Ko kuma sai yana cikin bacci sai ya fara magana da ƙarfi yana bada command kaman yana filin daga.

Shirunsa shi ya sake kashe mata jiki ta tabbatar ba lafiya ba. Duk da dai ba wai dama can yana da yawar magana ba amma kuma yanzu idan yana gida idan ba ita ta masa magana ba haka zai yi shiru ya yi ta kallonta.

Ranan da ya je ya duba wani abokinsa da suka dawo tare wanda ya ke Asibitin mahaukata ɗaki ya shiga ya yita dukan gini.

"Baban Al'amin!"

Da ƙyar ta iya riƙe shi tana bashi haƙuri. Hannunsa sai jini ya ke.

"Kamal ya haukace Fatima. Kamal ya haukace"

"Ka yi haƙuri. Zai samu lafiya" ta rungume shi tana lallaɓashi kamar ƙaramin yaro.

Komai ya canja sanda Naseer ya dawo daga Delta. Ya koma mata wani sabon mutum ba mutumin da ta aura a farkon shekarar 1999 ba.

Ranan suna bacci da ke ana sanyi ta tashi fitsari sai ta ga bargon data rufa musu ya zame. Ta jawo bargon zata rufa masa ta ji an damƙo ta.

"Ba..ban... Al'... ni ce" ta faɗa da ƙyar

Sai da ya ƙyafta ido sannan yai saurin sake mata wuya yana faɗin "Fatima, ki yi haƙuri ban san ke bace"

"Baban Al'amin ya kamata ka ga likita. Tunda ka dawo kake wasu abubuwa da suke bani tsoro"

Jawota yayi jikinsa ya ce " ki yi haƙuri. Gajiya ce kawai"

Washegari numbar abokinsa da ta san yana jin maganarsa ta kira ta faɗa masa abun da yake faruwa.

Lokacin da Faruk Lawanti ya kira Naseer suka gaisa shi kansa yanayin yadda Naseer ɗin ke amsa masa ya tabbatar masa Naseer ba ƙalau ya ke ba.

Sun saba da sun yi waya da juna Naseer ya ke tsokalarsa da *Anty Faruƙ* shaƙiyancin da ya ke masa kenan tun lokacin da ya ajiye aikin soja ya faɗa harkar siyasa.

"Mutumina kana buƙatar ganin Likita. Kada ka cuci kanka, ba gazawa ba ce soja ya je rehabilitation. You need it, iyalinka suna buƙatar lafiyarka"

"Ƙalau na ke Lawanti"

"Na sani Zaki. Na san ƙalau kake. Amma dole ne ka je ka ga Likita saboda kwanciyar hankalin Iyalinka"

Naseer yai shiru yana sauke numfashi. Akwai abubuwan da ya gani da ba zai iya faɗansu ba. Akwai abubuwan da suka faru a sanadinsa. Akwai rayukan da suka tafi ba za su sake dawowa ba.

"It's okay to cry, Zaki" abinda likitansa ya fara faɗa masa kenan lokacin da Naseer ya ke ta ajiyar zuciya saboda abubuwan da ya tuno da suka haɗu suka taru masa a maƙoƙoro.

"Ka yi kuka, za ka samu sauƙi. Kuka ba gazawa ba ce. It's a sign of strength"

Shi kansa a zama na biyu da likitan nasa da ya bari hawaye suka zubo masa sai ya ji wani sanyi a ransa. Sai ya ji kamar an sauke masa wani dutse mai nauyi a kansa.

Kukansa na farko kenan tun da ya shiga aikin soja kuma yana fata ya zamo na ƙarshe.

Fatima ta ji daɗin canjin da suka biyo bayan wata ɗaya da Naseer ya fara ganin Likita. Ya fara samun bacci, ya dena zabura.

Sai dai wani abu ya tafi da Naseer ɗinta mai sakin fiska wannan Naseer ɗin idan ta ga haƙoransa to magana ya ke.

Wani lokaci da gangan ta ke wani abun ko zai yi dariya amma sai dai ya motsa baki kawai.

Ko lokacin da ta gano tana da ciki ta faɗa masa ba ta ga ya yi dariya ko murmushi ba.

Alhamdulillah ya faɗa ya fara tambayarta ina bata jin wani ciwo.

Shi kansa Al'amin ya fuskanci canjin mahaifin nasa. Dan yanzu wai yai ta masa wasa suna dariya irin na da babu shi.

Yanzu kam Fatima gani take Naseer ɗinta ya tafi, wannan Soja ne ya dawo a madadinsa.

Ko a can Azare suma sun ga canjin nasa.

Iya har tambayar Fatima ta ke ko Naseer yana sake mata fiska a gida.

Fatima ta yi murmushi ta ce yana yi.

Lokacin da cikin Fatima ya shiga wata bakwai aka tura Naseer course ɗin wata shida a China.

"Baban Al'amin wannan karan ma zaka dawo ka tarar Baby ta fara tafiya"

Naseer ya shafa cikinta yace " Baby kar ki yi fushi da Daddy kin ji ko"

Fatima ta saka dariya.

Da dare tana taya shi haɗa kaya ta ce "Baban Al'amin ni kam sai nake ganin kamar wannan karanma zamu juma bamu haɗu ba"

"Ki dena faɗin haka. Wannan karam karatu ne Fatima ba aiki ba. Da mun gama zan dawo Insha Allah."

Ya dafa kafaɗarta ya manna mata kiss a goshi ya ce " ki yi haƙuri za ki haihu bana kusa"

"Al'amin ma ai sai da ya fara rarrafe ka zo ka ganshi"

"Ki ƙara min haƙuri, kin ji" ya sake mata peck a goshi.

"Ni kam Baban Al'amin ka min dariya mana kafin ka tafi. Ka san yaushe rabon na ga ka yi dariya kuwa"

Murmushin gefen baki ya mata yana shafa kumatunta. Shi kansa ya rasa me ya ke hana shi yin dariyan. Ko ya yi yunƙurin yi sai dai kawai ya iya yin murmushi.

"Ai ban ga haƙoranka ba"

Buɗe mata bakin yayi kamar mai tallen MacClean.

Fatima ta saka dariya.

Washegari kuwa har mota ta raka shi da guntun hawayenta.

"Baban Al'amin"

Sai da ya juyo ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi. Yau kam kunyar tata a ɗaki ta baro shi kafin su fito. Sojan da zai kai shi airport ya juya fuskarsa yana murmushi saboda shi ga shi gauro ne har yanzu bai yi aure ba.

Wata ɗaya da tafiyan Naseer da aka yi hutun makarantan su Al'amin Fatima ta tattara musu kayansu suka wuce Azare. Ta faɗa wa Naseer wannan karan a Azare za ta zauna har sai ya dawo. Idan an koma makaranta za ta saka Al'amin a makaranta a nan Azare ɗin.

A gidan Iya ta zauna duk da an kammala ginin gidan Naseer sai dai ba a zuba kaya a ciki ba tafiyarsa course ya hana shi saka furnitures a gidan ya bar shi akan sai ya dawo sai a saka kafin su tare.

Wannan karam kan ba a kwana biyu uku Naseer bai kira gida ba, idan ya jima ne yai sati.

*July, 2005. Azare*

Ranan wata laraba da yamma Fatima ta fara naƙuda. Iya da Hussaina suka kaita Asibiti.

Haihuwar bai zo ba sai ƙarfe ɗayan dare.

Wacce ta karɓi haihuwar ce ta ja Dr Aminatu da ta shigo gefe tana mata bayanin abinda ya ke faruwa. Bleeding Fatima ta ke sosai.

Dr Aminatu ta je ta yi magana da Likitan da ke kan duty suka shiga dubata.

Ba a sallamesu a Asibitin ba sai da ta yi kwana huɗu bayan an ƙara mata jini. A ranan da suka koma gida kwana ɗaya kuma jikin ya sake dawowa, sai ta yi ta jin hajijiya.

Dr Aminatu ta ce su koma Asibitin a sake dubata. Suna Asibitin har aka yi suna. Yarinyar ta ci sunan Fatima Zahra. Sunan da Naseer ya zaɓa mata kenan. Dama ya ce idan mace ce to Fatima ce idan kuma namiji aka samu to zai ci sunan abokinsa.

Ba a yi taron suna ba saboda mai jego har yanzu tana Asibiti.

Kwana biyar da sunan 'yar har ana shirin sallamarsu Fatima ta rasu.

Mutuwar ta girgiza su ba kaɗan ba.

Ana ta kiran wayan Naseer amma ba ta shiga.

Sai ran sadakan uku da ya kira ake gaya masa rasuwan.

Shiru yayi lokacin da Yayarsa Bintu ke faɗa masa rasuwar.

Ya yi kusan minti biyu yana ajiyar zuciya kafin ya iya cewa " Allah ya mata rahama"

Ko da aka bawa Iya wayar kasa magana ta yi. Da ƙyar ta iya cewa "Nasiru, Fatima lokaci yayi. Allah ya gafarta mata"

Ya amsa da Amin.

Kamar yadda bai ga rasuwan Malam ba haka nan Fatima ta tafi ta bar shi ba tareda sun yi bankwana ba...