14
by @azizat
*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)
Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat
Page 014
*2007, Azare Bauchi state*
"Yanzu haka zaka cigaba da zama babu aure. Nasiru ka yiwa kanka adalci kuwa?"
Naseer ya ɗaga ido ya kalli Iya sai dai bai iya ce mata komai ba. Shekaru biyu kenan da rasuwan Fatima. Kuma ko yaushe ya samu damar zuwa gida sai Iya ta saka shi a gaba da maganar aure.
Ba wai baya son auren bane. Sai dai har yanzu ya kasa samun nitsuwar da zai tsaya ya nemi wata mace. Zaɓa masa Fatima aka yi kuma ya riƙeta da hannu bibbiyu, bai taɓa nadamar haka ba saboda Fatima mace ce ta gari. Duk da ba auren soyayya suka yi ba, a zaman aurensu akwai zaman lafiya da farin ciki.
Wannan karan yana so ya zaɓo matar da zai aura da kansa ne, sai dai har yanzu bai ga wacce ta dace da shi ba.
Iya ta masa tayin 'yanmata kusan uku yana ƙi, yayyensa mata ma ba a barsu a baya ba, kowa da wacce take biɗar ya aura.
Akwai wata cousin ɗin abokinsa Faruƙ Lawanti da ta nace masa ita ma, amma bai tunanin zai iya aurenta dan bata kwanta masa ba.
Yana buƙatar mace a tare da shi. Yana buƙatar 'ya'yansa Al'amin da Zahra su koma hannunsa da zama.
Akwai kaɗaici idan ya dawo daga office ya shiga gida ya ji wayam babu ɗuriyar mutum a cikin gidansa.
Yana da niyyar shekaran nan ba zai ƙare ba zai yi aure.
Ko ina matarsa take zai samota ba sai an nemo masa ita ba.
Kamar yadda ya saba zuwa ya yi kwana biyu a Azare wannan karan ma kwana biyun yayi ya shirya komawa bakin aikinsa a Maiduguri amma kafin nan zai halarci bikin wani abokinsu a Abuja. Tare da Lawanti za su wuce dan dukkansu a NDA Kaduna suka haɗu.
Kaduna zai fara wucewa ya haɗu da Lawanti su wuce Abuja.
"Maganar Aminatu baka ce komai ba"
Iya ta masa maganar lokacin da ya shigo ɗakinta sallama.
Sun yi magana da Aminatu. Itama tana son auren amma abun ne ya gagara, duk masu zuwa sai su dinga ja baya da tsoron wai tunda aikin Asibiti take ba zata samu daman zaman gida ba, masu aikin Asibiti basa hutu safe har dare kullum suna aiki.
Ya kan faɗa mata cewa za ta samu mijin da zai sota ya kuma aminta ɗari bisa ɗari da irin aikin da take. Kar ta ɗaga hankalinta.
Ita kuma Iya kullum ƙorafinta Aminatu ta doshi shekaru talatin babu aure.
Da ke a lissafinta na dikake gani take shekarun Aminatun da yawa tunda ba wai ta kama ainihin shekarar haihuwarta bane (date of birth).
Sai dai Naseer da ya san lissafin shekarun ya san shi kansa yanzu ne ya shiga shekara talatin ɗin, amma a lissafin Iya ganin ya kai arba'in ta ke. Ta manta cewa auren wuri yayi.
"Aure lokaci ne" ya bata amsa "Kamar yadda Allah ya baiwa sauran 'yan'uwanta mazajen aure itama Allah zai bata nata mijin. Ki dena ɗaga mata hankali, ki cigaba da yi mata addu'a kuma ki sa mata albarka a aikin da take. Wannan kawai shine iya abinda za ki iya yi mata"
Yana alfahari da ƙanwarsa Aminatu. Ita ce ta ciri tuta ta yi karatu mai tsayi bayan shi. Da ke Allah ma ya taimaketa dukkan karatun da ta yi cikin sa'a ta yi, babu wani tangarɗa ko kaɗan.
Akwai Alfanun karatun 'ya mace. Ita kanta Hadiza ma da ta yi NCE farkon shekara da ya zo gida take ce masa ta samu admission a ATBU da ke Bauchi za ta jona degree kuma mijin ya barta ta cigaba da karatunta.
"To ga nan Musan gidan Inna Ladi yana so ya aureta ta ƙi shi. Ka ga auren ne bata so"
"Amina ba za ta auri Musa ba" Naseer ya faɗa da wani izza wanda ke nuna maganarsa ta tsaya kenan.
Iya ta hangame baki. Dama so take ta lallaɓa shi ko zai yiwa Aminatu magana ta yarda da Musan kawai a sha biki ta huta da maganar mutane.
Wani lokaci idan Naseer yai magana sai ta ga kamar Malam ne ke maganar.
"Auren zumunci ai akwai daɗi, Nasiru. Ga shi kai ma ka yi har da Albarkar 'ya'ya biyu"
Miƙewa ya yi ya ɗan karkata hularsa ya ce " Aminatu ba za ta auri wanda bai yi karatu ba"
Daga haka Iya ta haɗiye sauran bayanin.
Dama ta san ta inda Naseer zai ɓullo mata kenan. Amma yadda Musa makaniken mota ɗan yayarta da suke 'ya'yan Baffanu ya dage da zuwa yana lallaɓata yasa ta ke sha'awar haɗa auren zumunci.
Ta yi shiru da maganar ta bi bayansa tana masa addu'ar Allah ya kare shi.
Naseer shine babban gida dan haka maganarsa dutse ce a gidan.
Ga shi dai shi ɗaya tilo ta haifa amma kuma ya zamto mata tamkar maza goma.
Ko cikin dangi ana alfahari da sojanta.
Shi ne ya ɗaga darajan gidan nasu. Daga Azare, Zaki har Chinade babu tamkar ɗanta Nasiru.
***
Tunda Faruƙ ya bayyana masa cewa daga Lagos zai taho Abuja Naseer ya canja aƙalar tafiyarsa. maimakon Kaduna Kano ya wuce zai duba yayarsa Indo da ke can sai kuma ya hau jirgi ya wuce Abuja daga nan.
A gidan Indo ya samu tarba mai kyau.
Mijin Indo yana da rufin asiri dai dai gwargwado sannan mutum ne da ya ke son Iyalinsa. Duk cikin 'yan'uwansa mata banda Hadiza babu wacce ta yi sa'ar miji kaman Indo. Halilu yana son Indo ba kaɗan ba. Ga shi za su kai shekara goma shabiyar da aure amma har yanzu ita ɗaya ce a wajensa. Kuma ko a taɗi baya ji ana maganar wai Indo da mijinta sun samu matsala.
Saɓanin sauran da idan matsala ta tashi shi ake kira.
Wannan yasa ya ke ganin ashe abun ba daga karatu bane, daga zuciya da ɗabi'ar mutum ne.
Halilu dai bai yi boko ba amma yana son matarsa sosai kuma yana riƙe da ita da amana. Har yau Mijin Indo bai taɓa kiransa dan neman taimako ba.
Saɓanin sauran da suke bibiyarsa akan ya taimaka musu. Mijin Hauwa'u kam ma ba zai iya misalta matacciyar zuciyarsa ba. Zai samu lokaci dai ya je Bauchin nan ya masa magana. Kullum cikin kukan babu ya ke da 'yan ƙarairayi da zai sa a taimaka masa.
Yana cin abinci a falon Indo Mukhtar babban ɗan Indo ya shigo gidan sanye da uniform ɗin makaranta. Yana ganinsa sai ya sa dariya ya ƙariso gabansa ya ƙame jiki ya buga ƙafarsa ya sara masa yace" Shun Sir"
"To ƙaramin soja, yi hankali kar ka buge masa kofin ruwa" Indo ta faɗa
"Mukhtar ne ya girma haka"
Yaron ya fara dariya yana sosa gashin bakinsa da ya fara tohowa.
Indo tace " ka san yaushe rabonka da shi kuwa. Abba ai ya zama saurayi"
Sai da yaron ya shige ciki ta ke cewa ai shima Mukhtar ɗin wai soja ya ke son zama. Naseer ya ce hakan na da kyau.
Lura ta yi da yadda ya ke cin abincin kamar hankalinsa na wani waje ta ce "Baban Al'amin na ga alama zaman kaɗaici ya fara taɓa ka"
"Uhm"
Ta yi murmushi " au baka ma ji ni ba. Na ce gaskiya ya kamata ka yi aure ko mu haɗu mu maka auren dole"
"Za ku zauna da ita kenan"
"To ai ba mu ga alamar kana da niyya ba"
"Kar ku damu zan yi aure"
"Allah ya sa. Tun bara kake cewa za ka yi"
Ko da ya gama cin abincin bai wani jima ba Sallah kawai ya yi ya musu sallama ya wuce airport dan jirginsa ƙarfe biyar da rabi na yamma ne...
***
Waya ta ke tana ta faɗa lokacin da ta ke fitowa daga cikin gidanta.
"Shi Sani Kings ɗin ne ya sakata a film ɗin? Me yasa baka faɗa min tun da wuri ba..... kai matsa min a waje"
Ta kashe wayar tana jan tsaki.
Munira MoBaby kenan da take waya da manajan ta.
Tauraronta yayi tashe daga shekarar 2002 da ta shiga film zuwa 2006 amma shekarar 2007 ya zo mata da canje-canje dan kuwa sabbin jarumai kyawawa wanda basu kaita shekaru bane suka shigo masana'antar. Wannan yasa wasu daraktocin ke rububin saka su a film.
Babu wacce ta tsaya mata a wuya irin wata sabuwar jaruma da kusan film uku kenan da take biɗa amma an bi gefe an je an sakata.
Jarumar da ke ƙoƙarin karawa da ita ita ce Zarah Beauty. Shekarunta shatakwas kuma tashin Egypt ce. Mamanta Balarabiyar Egypt, Babanta ɗan Nigeria wannan yasa ta ke da ruwa biyu.
Ita kanta MoBaby sai dai baƙin ciki amma ta san Zarah kyakykyawa ce.
Ta san yadda industry'n nasu ya ke. Da zaran ka fara tara shekaru kuma aka samu sabbin kyawawan fiska za a fara ja baya da kai.
Ga shi farkon shekaran nan da ta buɗe kamfanin film ɗinta na MoBaby Movies Production 'yan hassada suka fara wareta gefe. Film ɗinta da ta fitar a ƙarƙashin kamfanin mai suna *ni naka ne* ya samu lambar yabo saboda waƙoƙin da suke cikin film ɗin sun haɗu ga kuma sabon jarumin da ta saka shima ya haska film ɗin.
"Hajiya mu tafi ne?" Direbanta ya tambaya.
"Asabe ta saka min akwati a mota?"
"Ta saka Hajiya"
"To mu wuce"
Ya buɗe mata ƙofar baya ta shiga ta hakimce tana danne dannen waya.