MUTALLAB ASAD

Shafi na uku

by @billysfari

*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*

        (MAM)


NA


BILLY S FARI &

NANA DISO


  *SHAFI NA UKU.*


_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._

_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_


  Cikin azama ya bankaɗo ƙofar palourn da ƙarfi ya shigo yana faɗin Meenal..Meenal me yake faruwa? me ya sameki? a jajjera ya jefo mata tambayoyin cikin tsananin tashin hankali, ba tare data amsa ba ta ɗauki wani glass flower dake kan center table ɗin ta ƙara fasashi tana kallon yadda jikin mahaifin nata yake rawa yana riƙeta. " Yi haƙuri Meenal faɗamun waye ya taɓaki yanzun nan ya haɗu da fushina saboda akan ɗiyata babu wanda bazan hukunta ba!" ya ƙare zancen yana kallon Mommy data kasa motsawa daga inda take tsaye tana kallon ikon Allah ganin yanda yake faman ɓaɓɓata rai. duk da tasan komai zata faɗa masa bai isa ya zamo hujja a wajensa ba da zatasa ya sassauta mata akan hukuncin da ako yaushe baya gajiya da yanke mata akan Meenal ta sauke ajiyar zuciya ranta a ɓace itama tace "Yanzu Alhaji ba nida ikon yiwa Meenal faɗa kenan? Kawayenta fa takawomin har cikin falona suka ware kida sunata rawa sai kace club....".


Sai daya watsa mata wani banzan kallo haɗe da ƙoƙarin dakatar da ita daga maganar da takeyi sannan yace, "Daƙata malama! so what don tayi hakan gidanki ne? Ko kuma waninki ya gina min? Ɗiyata ce fa kuma gidan ubanta ne don me da baza'a barta tasamu nutsuwar da take buƙata acikinsa ba? Look! Masha gayamiki cewa Meenal tafi kowa iko da duk wani abu dana mallaka a gidan nan koda kuwa yayanta ne balle ke, don haka wannan ya zama shine karo na ƙarshe dazan kara yimiki magana akan nunawa ƴata iko da duk wani abu daya zamo mallakina domin ita ɗin rayuwata ce kuma farincikina". ba tare da Mommy tayi mamakin zafafan kalaman nasa da yayi amfani dasu akanta ba taci gaba da kallonsa, tsaki ya ja sannan ya sake cewa, "Finally you have to apologise her yanzun nan!" Da hanzari Mommy ta ɗago ido tana kallonsa kafin ta maida kallonta ga Meenal data saki wani makircin murmushi tana kallonta sama da ƙasa, wani irin takaici ya tasowa Mommy domin idan da tasamu haihuwa ta tabbatar ɗiyarta tafari sai ta girmewa Meenal, amma tsabar wulaƙanci ace itace zata bata haƙuri duk da Meenal ɗin ce tayi kuskure, Muryarsa taji a tsawace yana cewa, "Bakiji me nake cewa bane?"

"Am sorry". Mommy tafaɗa ranta na matuƙar wani irin zafi ta juya tabar wajen ta shige daƙinta. 


Da kallo Dady ya bita kafin yayi kwafa ya maido kallonsa ga Meenal yace "kin haƙura Babyn dady?." Ciƙe da shagwaba ta ƙalli mahaifin nata haɗe da kwantar da kanta saman kafaɗarsa tace. "Nidai Dady kaƙara yimata faɗa gaskiya tadaina shiga sabgata sai..." "Is okay baby jeki ki huta abunki, ko akwai wani abunda kike so?" "No Dadyna, but want pepper soup na kaza kasa tayi mun kuma tasaka spices". Kallonta yayi cike da soyayya irin ta uba da ɗiyarsa yace "zatayi miki yanzun nan kuwa kin ji Dady girl". yana shafo kanta haɗe dayin murmushi, cike da jin daɗi Meenal ta rungume mahaifin nata tace "I love you Dadyna" "Dadynki yana sonki sosai fiye da haka shima".


Daga haka ta hau sama inda ɗakinta yake, ko data shiga tuɓe komai tayi najikinta kama daga mayafin kanta da wandonta, ƴar ƙaramar rigarta har ma da bra ta cillar dasu ƙasan dakin sannan ta faɗa bandaki ba tare da tunanin tayi addu'a ba, ta ɗauki kusan mintuna talatin ciki sannan tafito tasaka towel wanda bai wuce iya gwuiwarta ba, zama tayi akan dressing mirror tafara ƙoƙarin shafa mai sai data gama sannan ta buɗe wardrobe ɗinta. Yadda ta zubawa kayan nata idanu zaka tabbatar tunanin wanda zata saka takeyi. Cikin damuwa ta shiga watso da kayan kasa tana neman wata long rigar da take don sakawa, sai data zubo da fiye da rabin kayan duka sannan ta dakata ta tuna suna ciƙin ɗayar wardrobe ɗin nata, ba tare da damuwa da kuma tunanin gyara kayan data zubo dasu ba ta shiga taka kayan dake azube ta nufi ɗayar wardrobe ɗin ta ɗauki rigar tata tasaka, kasancewar bata da jiki kwatakwata sai rigar tayi luf ajikinta. sake tattaka kayan da suke ƙasa azube tayi tafice daga dakin ta nufi falon sama dan akwai series ɗin da take so ta kallah ba tare da tayi duba da magariba ta nufo ba, ko kaɗan hakan bai dameta ba dan ko sallar la'asar batayi ba, kawai ta saka a ranta za tabari ta haɗa duka da magrib da isha'i da la'asar tayi idan zata kwanta.


A ɓangaren Mommy tsananin baƙin cikin da take ciki acikin gidan nan da kuma cikin ranta bazai iya faɗuwa ba. rayuwar da takeyi agidan babu daɗi ko kaɗan ga daula da tarin arziƙi kama daga kan suttura, abinci da kuma muhalli, komai na rayuwa babu abinda ta rasa saboda Alhaji Abdulmalik mu'azzam mutum ne mai arziƙi da wadata baɗan ƙarami ba, ya sauya mata rayuwarta data iyayenta daga tarin rashin wadatar da suke ciki, duk wanda ya santa ya kuma san yanda tafito daga gidan mijinta na farko yasan cewa tana cikin wadata yanzu saboda yanda ta canza tayi dumurmur da ita fiye da lokacin da tayi aurenta na farko, sai dai duk da haka tana samun tauyuwar farinciki sanadiyar yarinya ƙarama data fitineta, tana yawan jin ana faɗar matsaltsalun yaran miji batasan haka suke ba sai da Allah ya jarrabeceta yanzu da masifar Meenal, yarinyar da sam bata ganin girmanta da ganin mutuncinta duk da hidimtuwar rayuwar da tayi mata tun tana ƙanƙanuwa har zuwa girmanta. Wayarta ta dauƙo tashiga kiran numbar ƙanwarta da take bima, bugu ɗaya ta dauƙa nan ta shiga gayamata abunda yafaru yau tana share ƙwalla. Murmushi ƴar uwar Tata tayi haɗe da cewa, "kiyi haƙuri Aunty domin babu abunda ya bari a duniya, ki roƙa mata shiriya domin idan ɗiyarki ce Aunty ai dole haƙurin zakiyi da ita ko?"

 "Haba Saddiƙa ya zakice nayi haƙuri shikenan nayita haƙuri yarinya ƙarama tana takani agidannan? ko autar gidan mu fa tafita shekaru saddiƙa, wlh ban taɓa ganin inda ake sangarta yaro ba kamar gidannan, haba! Wannan wace itace masifar ce haka? tun tana ƙaramar nake faman tufƙa yana yimani warwara akan tarbiyarta gashi yanzu har ta girma tana ganin cewa ni da ita girmanmu ɗaya, A fili mahaifinta ke nuna akanta babu wanda bazai iya takawa ba hatta mahaifiyarsa da data haifesa, gaskiya ni bazan iya ba na fara gajiya".

"Subhanallahi Aunty kada kice haka, wannan wacce irin magana ce kikeyi?"


"Hmmm bazaki fahimta ba Saddiƙa, wlh Allah da gaske nake miki babu wanda Meenal take gani da mutunci har kakar tata, sun gama lalata mata tarbiyar da nake ta ƙoƙarin ganin na bata, sangarta kuwa sai kin gani da ido ki, Allah dai kashiryar da ita su kuma ya ganar dasu, amma nikam haƙuri na ya fara ƙarewa Saddiƙa, nagaji nagaji da Auran nan kawai gwara nafito ai talauci ba hauka bane." 

 "A'a kidaina maganar fitowar nan dan Allah Aunty, koma meye mijin nan naki ya gyara mana rayuwar iyaye hatta gidan ƙasan da suke ciki sai da ya canza musu, kidinga tunawa fa hatta abincin da akeci acikin gidanmu kece kike kawo mana da taimakonsa, ko don haka dan Allah kiyi haƙuri aduk lokacin da ranki ya ɓaci kina tunowa da wannan alkhairin nasa agaremu, ki ƙara jan yarinyar ajikinki kina lurar da ita in Sha Allah watarana zata daina kuma ki kauda kanki ga abubuwan da kika san zasu iya jawo Mali wannan damuwar matuƙar basu taka kara ba" Hawayen fuskarta ta goge tana jin ta ɗan samu natsuwa a zuciyarta tare da amsa wa ƴar uwar tata da "shikenan saddiƙa nagode". tana ajiye wayar taga ƙarar kiran ƙawarta hajiya Binta, sai da ta ɗaga suka gaisa sannan ta shiga labarta mata abinda ke damunta sanadiyar tambayar data jefo mata jin Muryarsa ba daidai ba, nan ta kada baki tace da ita "to shikenan zama zakiyi kina kallon yarinyar nan tana buɗe Mali shafin iska ci kala-kala? Bari kiki wallahi idan tayimiki kici ubanta, shegiyar yarinya jiki kamar na muciya kidaina dauƙar wulakancin nan nagaya miki tunda ba ita kike aure ba, ina mijinki yana sonki ba shikenan ba".

"hajiya binta kenan, bakisan soyayyar da Alhaji ke yiwa yarinyar nan ba kenan da zaki ce haka" cike da takaici Hajiya Binta tana tsaki haɗe da cewa "to ina ruwa ki da wannan, shi da yaji zai iya tunda ƴarsa ce, amma ke akan me zaki zauna tana takani don ranta don mutukar... sufa ƴaƴan miji idan bakiyi da gaske ba wallahi sai sun fiddake." "Haba ƙarara Allah dai ya kiyaye".


"To ai kece da kayan takaici bakisan sharrin su bane, yanzu ba gashi ba guda ɗaya ce sai kuma yayanta amma sun hanaki zaman lafiya? gantalalle wai yana ina shi na dena ganinsa?" 


"ya je Egypt wai ciwon ciki ke damunta kwana biyu shine mahaifinsa ya turasa can adubosa". 


"Allah ya raka taki gona ai kuwa huta kafin yadawo.." haka Hajiya Binta taci gaba da maganganunta har ta gama Mommy bata kara cemata komai ba kafin sukayi sallama ta ɗan jingina ajikin gadon da take zaune Ac daƙin na ratsamata jikinta, ta jima a haka kafin ta fito tanufi ɗakin Dady, koda ta shiga yana zaune da alamu bai jima da watso ruwa ba yana shan lemon da tayi masa ta saka masa acikin ƙaramin fridge ɗin dake cikin ɗakin nasa. " Sannu da hutawa Alhaji" a maimakon ya amsa ba tare daya ɗago ba bayan yayi sipping lemun tare da ajiye cup ɗin a gefe yace "Sau nawa zan gaya miki kidaina takurawa yarinyata? pls idan har bazaki dena ba to hakan na nuni da kin gaji da zama dani kenan, don haka ki kama gabanki don ni bazan juri ganin kina ƙuntata mata ba acikin gidannan ba" yanda zuciyarta ke bugawa yasa ta zuba masa idanuwa tana ƙoƙarin sake danne ɓacin ran dake taso mata a karo na biyu kafin a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace "kayi haƙuri Alhaji, gobenta nake don gyara mata bawai ina don takurata bane ko don ɓata maku rai." 


"waye yasaki? kibarta da gobenta mana ko ke kike da iko akanta". Dady ya ɗago kai cikin ɓacin rai yana faɗar hakan idanuwansa cikin nata ko kunyar faɗar hakan baya ji, "shikenan kayi haƙuri bazan ƙara ba in sha Allah" "zai fi kyau ki kiyaye hakan, me aka dafa a gidan?"


"Abinda kafi buƙata ako yaushe". Mommy ta faɗa tana ɗan sake fuskarta ganin alamun ya fara saukowa,


"Thanks, Meenal nada buƙatar pepper soup, Don haka a hanzarta ayi mata ƙamin nafito." 


"Nayi pepper chicken Alhaji kuma itace tace tana so" "To hakan laifi ne idan ta buƙaci a sake yin wani pepper soup ɗin? Ƙarfa ki manta Meenal rayuwata ce dole komai take so a bata tunda akwaishi".


"haka ne, bari in saka ƴan aiki suyimata." "Naki tace tana so don haka ke zakiyi mata mansura". ya faɗa kai tsaye tare da gincirawa gefen gadon yana rufe idanuwansa "Afwan Alhaji bawai bazanyi bane, naga yanzu kadawo kana kuma buƙatar kulawata ko?." 


"Yau na yafe kije kiyi abinda zaki farantawa yarinyata hakan ya wadatar." ya kare zancen har lokacin idanuwansa na arufe, Batace komai ba tafice daga ɗakin cike da damuwa, kusan awa ɗaya da ɗoriya tayi kamin ta gama haɗa wani pappe soup ɗin, tana gamawa ta ajiye mata a dinning lokacin suna zaune ita da mahaifin nata da alama wata hirar sukeyi ta kakarta da take kira grandama, kallon abinda Mommy ta kawo ta ajiye agabanta Meenal tayi kafin tace "Gaskiya kin daɗe sosai har yunwa ta soma raunat lafiyata". jin zata iya taso wata rigimar yasa Dady yayi saurin cewa "Karki damu Babyn Dady tunda dai ta haɗa maki duk da ranta baya so". Batace musu komai ba ta nufi hanyar daƙinta, tana jin yanda Meenal ke faman zuba masa taɓara yana faman yimata dariya tayi banza dasu ta shigewarta don inda sabo duka Waɗan nan abubuwan ta saba dasu, zuciya ce kawai ba tada ƙashi shi yasa har take komawa kansu suna ɓata mata rai a banza...




#Mutallab Asad

#ƴan tagwaye

#Nana Diso

#Billy a fari