General NASEER Zaki

17

by @azizat

*GENERAL NASEER ZAKI*

(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03

Arewabooks: Azizat


                          Page 017

Aikin Gwamnati akwai daɗi akwai wahala. Sai dai idan da rayuwa, dukkan ma'aikaci watarana zai ajiye aikinsa.

Shirye-shirye ake a gidan Teacher John Yahaya saboda bikin retirement da ya yi daga aikin koyarwa.

Tun yana matashi da ya fara aikin bai cigaba da karatu ba bai kuma canja wani aikin ba, koyarwar dai ya ke a Primary school shekaru har talatin da biyar cif-cif.

Kyauta da wata 'yar Anty Martha mai suna Naomi suka shigo cikin gidan ɗauke da markaɗen tumatur wanda za a yi miya da shi.

Dai dai Kyauta ta ajiye roban kayan miyan za ta wuce ciki Anty Bridget ƙanwar mamanta ta yafico ta suka shige ɗaki. Bayanta da yai staining da jini Anty Bridget ta nuna mata tare da tambayarta ko yau ta fara.

Kyauta ta gyaɗa kai a kunyace.

Sai da ta cire kayan jikinta ta kimtsa sannan ta fito tana wani nonnoƙewa. Ga shi Anty Bridget ta gayawa sauran matan wajen sai tsokalar Kyauta su ke duk kunya ya rufeta ta koma ɗaki da gudu.

An ci an sha an kuma yi rawan al'ada.

'Yanuwa da abokan arziƙi sun halarci bikin retirement ɗin John Yahaya. Teacher John na kowa ne. An shaide shi a matsayin mutum mai karamci.

Ɗalibansa daga wajaje da dama sun halarci bikin, an kuwa bashi kyaututtuka na karamci.





***


*2009, Jos, Plateau State*



Ƙafafuwa biyu ke harɗe cikin bargo. Baƙin ƙafar ya sarƙe fararen ƙafan da suke da tabo-tabon baƙi alamun soyewar bleaching.

Jan numfashi ta yi ta sauke tana murmushi haɗe da shafa gashin bakin mutumin da zufa ya riga ya wanke masa fiska.

"Ina son ka, My Lion"

"Say that again Baby"

"I love you" MoBaby ta faɗa tana shigewa jikin mijinta. "Za ka kasheni da daɗi, Zaki"

Daɗa rungumarta yayi yana shafa gadon bayanta.

Ƙaran wayar da ke ringing a saman wardrobe da ke gefen gado ya katse musu nitsuwar da suke ciki.

Naseer ya sa hannu ya lalumo wayar ya ƙara a kunne.

Amsa sallama yayi da dakakkiyar muryarsa da ke nuni da daga bacci ya tashi.

"Dama maganar kayan kitchen ɗin Aminatu ne, har yanzu baka turo kuɗi ba" Indo ta faɗa da zimmar wannan karan za a samu nasara dan tun farkon wata take masa maganar.

Sana'ar dillanci ta ke yi yanzu a can Kano kuma abin ya karɓeta babu laifi.

Tun da aka saka bikin Aminatu ta ke neman alfarmar a bata kwangilar kayan kitchen tunda aikinta ne.

MoBaby da ke shafa gashin ƙirjin Naseer ya saka shi shaƙar numfashi kafin ya iya yin magana.

"Ki yi haƙuri akwai ƙanin Munira da zai kawo kayan"

"Amma Baban Al'amin..." sai ta yi shiru.

Ba sai ta yi dogon turanci ba ta san kwanan zancen. Tun ba a je ko'ina ba suka fara ganin abinda Iya take ta faɗa tun kafin ayi aure.

Munira ta fara zame musu tsani tsakanin Naseer da su 'yan'uwansa.

Kafin a maida shi Jos lokacin da ya ke can Maiduguri da an kira shi wata maganar kuɗi ko buƙata zai ce a kira Munira.

Idan ma wani abun ne za a yi sai ya ce a tuntuɓi Munira kawai.

Lokacin da aka dawo da shi Jos kuwa dukkansu sun yi zaton zai zo ya ɗauki 'ya'yansa a hannun Iya ya tafi da su Jos ɗin amma watanni biyar suka wuce bai tada maganar ba.

Duk da dai ba abinda yaran suka rasa a wajen kakarsu amma da daɗi ace koda Al'amin ne ya ɗauka a gabansa.

Yana gama wayar MoBaby ta ce " waye ne?"

"Aisha"

"Waccar ta Kano ɗin?"

Ya gyaɗa kai.

"Me take so wai?" Bai amsa mata ba sai ya miƙe tsaye yayi miƙa. Munira ta bi bayansa da kallo. Gaskiya Zakinta namijin gaske ne. Yadda bayansa ya tafi V-shape take kallo tana tuno gamsuwar da ta samu a safiyar Lahadin yau da yake gida.

Wucewa banɗaki ya yi. Ita kuwa ta ja bargo ta rufa kanta. Bayan ni'imar da ta kwasa ai sai bacci.

*

Yadda Allah ke lamarinsa sai shi. A inda kake tunanin babu sai kuma Allah ya nuna maka akwai ɗin.

Hausawa suka ce dare ɗaya Allah kan yi Bature.

Dare ɗaya Allah ya kawo mijin Aminatu. Miji wanda ya ke ƙaunar irin aikin da ta ke yi.

Lecturer ne a ATBU matarsa ta rasu yana da 'ya'ya uku.

Sun haɗu a motar haya za ta je duba Hauwa'u a Bauchi da ta yi ɓari.

Shi ma AbdulMalik ɗin ƙanwarsa da mijinta ya rasu a Azare ya je dubowa zai koma Bauchi.

Daga 'yar hira da suka yi daga Azare zuwa Bauchi da za a rabu aka yi musayar number shikenan soyayya ta ƙullu.

Da farko dai Aminatu bata amince ba dan AbdulMalik yai mata kama da irin masu tsatstsauran ra'ayi ɗin nan sai daga baya ta fahimci ba haka yake ba. Matarsa da ta rasu ma tana aikin teaching kuma a gidansa ma ta yi karatun.

Da ke a shirye ya ke watanni huɗu da haɗuwarsu ya turo magabatansa aka saka biki sati shida.



*

Tun da aka haɗu a biki 'yan'uwan Naseer ke ta maganar canjin da ya yi tun da ya auri Munira.

Lokacin da Anty Maimunah babbar yayarsu da Indo da Hadiza da Bintu da Mariya suka haɗu a ɗakin Iya zancen Iya na kan sallaya tana jan carbi bata tanka musu ba. Gobe za a yi Walima jibi a ɗaura aure amma Munira bata iso ba.

Maganar kayan kitchen ɗin da aka kawo suke suna mamakin yadda aka yi Naseer ya baiwa ɗan'uwan Munira kwangilar kayan kitchen ɗin maimakon Indo.

"Wallahi na tabbata kuɗin da ya bayar sun fi kayan da aka aiko" Mariya ta faɗa tana jijjiga 'yarta da ke ɗan kuka.

"Ni fa ba wannan ba ma. Wai kenan nufinsa Munira ba zata riƙe su Zarah a wajenta ba?" Indo ta yi tambayar Hadiza ta ce " to ai gara su zauna a wajen Iya, idan suka koma wajensu ta fara muzguna musu fa"

"Gaskiya bayan biki dole a zauna da Baban Al'amin a tattauna" cewar Bintu.

"Kuma wallahi sai da Iya ta ce bata yarda ba muka ce muna so"

"Indo wannan duk daga baya ne. Mafita za a nema tun kafin tafiyar tai nisa" in ji Anty Maimunah da ta ke shan kunu.

"Iya ba za ki ce komai ba?" Mariya ta faɗa tana kallon Iyan da ta miƙe tana naɗe sallaya.

"Allah ya rufa asiri"

To mi za ta ce. Auren nan dai fin ƙarfi aka mata ba wai tana so ba.

Ga shi shekara guda kenan har an fara ganin abinda take gudun.

Bikin Aminatu ya samu halartar 'yan'uwa da abokan arziƙi. Sai dai fa har ranan ɗaurin aure ba su ga mai kama da Munira a wajen biki ba.

Ana gobe za a ɗaura aure da dare Naseer ya iso Azare. Ganinsa shi ɗaya ya sa Iya ta tambayi ko lafiya.

Ya ce mata Munira ba za ta samu zuwa ba mamanta ba lafiya ta tafi Kano dake iyayenta sun dawo Kano da zama.

Iya tace Allah ya bata lafiya.

Abinka da social media a ranan bikin kuwa Hadiza ta ga hoton da Munira ta ɗaura a shafinta na Instagram inda ta ke tallata sabon film ɗin da kamfaninta zai fitar.

"Iya ciki ne fa da ita ta kama hanya ta tafi aikin film amma ba zata iya zuwa bikin ƙanwar mijinta ba"

Ko hoton da ake nuna mata Iya bata kalla ba tace " uhmm"

Sai bayan biki da gida ya ɗan watse ranan Sunday da yamma 'yan'uwan suka haɗa kansu suka shiga gidan Naseer suka same shi suka ce suna da magana da shi. Yana ma shirin zai shigo wajen Iya ya mata sallamar zai wuce Jos.

"Baban Al'amin yanzu ace matarka ta zaɓi tafiya ɗaukar film sama da zuwa bikin Aminatu. Dole ma ta tafi tunda bata ɗauke mu da mahimmanci ba"

"Me kike nufi?"

Anty Maimunah ke magana kuma yadda take maganar ranta a ɓace yake.

"Ka san Allah Munira bata isa ta watsar da zumuncin dake tsakaninmu ba" ta cigaba da amayar da abinda ke cikinta

" Ni bana son ƙananan maganganu, idan akwai abinda ta yi sai ku faɗa"

Tun da ya faɗi haka suka kama baki.

Shikenan Munira ta shanye musu ɗan'uwa.

Dama ance soja zai iya karawa da kowa amma banda mace.

Ai gashi kuwa Sojansu ya fara zama bawan mace.

Meeting ɗin dai bata musu daɗi ba sai ma aka watse rai a ɓace.

Yadda aka yi biki aka gama lafiya babu Munira haka har bayan biki bata zo ta gaishe su gajiyan biki ba. Kai ko kiran Iya ba ta yi ba.

Haka suka zuba mata ido suna jiran ta haihu su mata rashin mutunci.

Cikin ikon Allah kuwa a December 2009 ta haihu. Naseer ne ya kira Iya ya sanar mata cewa Munira ta haifi ɗa namiji.

Iya ta yi addu'a ta rufe bakinta.

Zuba masa ido take ta ga iya gudun ruwansa.

Tunda ya ce a Jos za a yi suna Iya ta sakawa ranta ba za ta je ba. Duk randa ya kawo Munira Azare ta ga jaririn.

Kaman haɗin baki suma 'ya'yan nata mata haka suka haɗa baki suka ce babu wanda zai je suna.

Idan yana ganin basu da wani mutunci a idanunsa za su nuna masa suma sun san darajan kansu.

A zahiri Naseer ya so ya yi sunan a Azare. Sai dai lokacin da aka yi haihuwan ya zo dai dai lokacin da aka bashi muƙamin MAJOR, ga kuma Muniran wacce CS aka mata baya so su kama zirga-zirga tun bata gama warkewa ba daga Azare zuwa Jos.

Dukka wannan da ya yiwa Iya bayani da sauran 'yan'uwansa za su fahimce shi amma girman kai gani yake da ya faɗi cewa a Jos za a yi sunan ya tura musu kuɗin mota za su taso ne kawai su taho ba tareda ya musu bayanin komai ba.

Shiru-shiru yana jiran tahowar Iya har ana gobe suna bata iso ba. Babu ma wacce ta zo sai Hauwa'u da ta taho daga Bauchi.

Ya kira Iya yana tambayarta ko ya turo mata driver ne ya zo ya taho da ita ta ce masa kar ma ya ɓata lokacinsa ba zata zo ba ƙafarta na ciwo duk randa maijego ta zo Azare za ta ga jariri.

Ya san fushi ta yi dan haka ya shiga bata haƙuri amma ta ce masa ba zata zo ba.

Haka ya haƙura ya barta.

A bakin Hauwa'u ya ke jin wai 'yan'uwansa sun yi meeting wai ba za su zo sunan ba.

Ya ɗauka barazana ne kawai amma sai ga shi har ranan suna banda Hauwa'u da Mariya babu wacce ta zo. Aminatu da ke Bauchi nan nan ma bata zo ba kuma har mijinta ya kira ya faɗa masa haihuwar.

'Yan'uwa na nesa sun zo. Dan 'ya'yan Baffa ne suka cika gidan nashi 'yan'uwansa na jini basu zo ba.

Abin ya ƙona masa rai.

Ita kam Munira ko a jikinta. Wanda suka zo ma daga ɓangaren Naseer gani take sun zo sun cika mata gida.

Anyi bikin suna da bikin samun ƙarin matsayinsa daga Captain zuwa Major amma waɗanda ya fi ƙauna a duniya sama da 'yan'yansa ba su zo ba.

Mariya ce ma ta taho da Al'amin amma Zahransa na wajen Iya ba a taho da ita ba.

Yaro ya ci suna Ibrahim Khalil.

Bayan hidimar sunan sai duk gwiwarsa ta sace da yadda 'yan'uwansa suka juya masa baya.

Ba tareda ya nemi shawaran Munira ba yace ta shirya su wuce Azare sati biyu bayan sunan.

"Haba, My Lion. Tafiya ba shiri haka"

"Ƙarfe bakwai na safe Sergeant zai wuce damu" ya faɗa fiska a haɗe

Yau dai Zakinta ya rikiɗa mata dole ta bi shi a hankali.

Koda suka je Azare ɗin sai wani shan shan ƙanshi ta ke. Ko kaɗan bata so ta bawa 'yan'uwansa fuskar da za su zo su rena ta.

Ta riga ta karanci Naseer shine bangon gidan wanda da shi kowa ya jingina.

Idan ta yi sake sai sun rushe shi da buƙatu da matsalolinsu.

Lokacin da suka shiga gaishe da Iya ta ji yana faɗin wai idan za su tafi za su tafi da Al'amin da Zahra.

Munira ta wani kalle shi. Tana fama da nata jaririn ya ke so ya haɗata da renon wasu yaran daban.

Iya ta yi shiru. Sai can kuma ta ce " ka bar min Zarah a wajena"

Hakan kuwa aka yi da suka tashi tafiya suka tafi da Al'amin aka bar wa Iya Zarah...


***