18
by @azizat
*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)
Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat
*MMG'S*
_Chilli powder_
Tasty Yaji... *kin kuwa san sirrin haɗa yaji da garin ɗanwake mai kyau ko kuma dai a bar maganar kar ayi tone-tone?. To! matso Hajiyata ba sai kin wahalar da kanki ba, MMG's Tasty Yaji sun zo muku da sauƙi, ba ruwanki da jan hanci ko tari wajen dakan yaji. Kawai order za ki yi a kawo miki yaji mai kyau har gida. Ga kuma garin ɗanwake mai danƙo suɓul-suɓul Malamata . Domin gwada yajin mu da garin danwaken zaku iya tuntubar mu ta wannan lambar. *** ko ta wannan number ***.* Sayan na gari mai da kudi gida, sai an gwada akan san na kwarai, sayan daya-daya ko sari akan furashi me rahusa.
Page 018
*2014, Gulak, Madagali"
Ƙarfe uku na rana Kyauta ta shigo cikin gidansu da sallama. Uniform ɗin makaranta ne a jikinta, tun daga tsakar gida ta cire ɗan ƙaramin hijabin da ta sa ta lanƙaya shi a wayar shanyar da ke bakin ɗakinta.
"Ngwatam"
"Na'am Baba"
Bata shiga ɗakinta ba sai ta juya ta shiga ɗakin Babanta. Sati ɗaya kenan yana kwance baya fita ko'ina.
Da zazzaɓi ya fara abin kuma ya zo ya zame masa babban ciwo har baya iya tashi.
"Baba gani" ta tsugunna gaban gadonsa.
"Gobe zan je Mubi, Sɗang zai raka ni Asibiti"
"Baba zaka iya zuwa kai kaɗai? Zan raka ka"
Murmushi ne ya suɓuce masa. 'Yar tasa akwai ƙarfin zuciya.
Wani lokaci ya kan tambayi kansa anya yayi adalci da ya zauna babu mace a gidan.
A shekarun baya yayi yunƙurin sake wani auren amma abubuwa basu tafi yadda yake so ba, sai ya zo ya haƙura.
"Kar ki damu, zan iya tafiya ni kaɗai. Sɗang yana jarrabawa ba zan iya cewa ya zo gida ba"
"Baba, Allah nima zan iya raka ka. Ina da ƙarfi sosai"
"Na san kina da ƙarfi. Ki tsaya ki kula da Kaka kin ji"
"Kaka fa ya warke. Jiya ma shi da Kaka Lazarus haka suka zauna suka yi ta shan giya. Ba abinda yake sai shan giya yanzu" ta yi maganar tana ɓata rai.
"Kyauta"
"Ni kam ka bari na bika" ta faɗa da shagwaɓa.
"Kar ki damu ba zan jima ba zan dawo"
Washegari Kyauta da wani yaron maƙocinsu Joseph suka raka Baba tashar mota ya wuce Mubi.
Sɗang yana karatu a nan Federal Polytechnic Mubi. Yana ma ajin ƙarshe ne, HND II.
Da uniform ɗinsu dama suka fita. Sai da motar su Baba ta tashi kafin suka juya suka wuce Makaranta.
"Kyauta kin yi assignment ɗin Maths?"
"Wallahi ba zan baka ka kwafa ba Joseph"
"Haba mana"
"Jiya ai da aka tashi kana ji Mirabel na kirana da mai ƙwala-ƙwalan ido baka ce komai ba"
"Kyauta ba haka bane"
"Ai dama Mirabel budurwarka ce sai ka je ta baka assignment ɗin ka kwafa" ta tura baki ta yi gaba ta bar shi.
Joseph ya bi bayanta yana bata haƙuri.
A haka dai suka isa Makarantar. Suna zuwa kuwa suka samu ana dukan makara.
Joseph ya bada hannunsa aka masa bulala. Ita kuwa Kyauta da aka zo kanta tsalle-tsalle ta fara tana ihu. Ƙarshe bulala biyu aka mata aka barta ta wuce maimakon bulala biyar.
Dama duk makarantar an san Kyauta Ngwatam Yahaya wajen tsoron bulala.
Kyauta na da ƙoƙari sosai. Tana da ƙwaƙwalwa. In dai aka yi karatu ta duba sau ɗaya to ya shiga kenan. Tun daga JSS 1 har zuwa JSS 3 sau ɗaya ta taɓa ɗaukan na biyu duk sauran first position take ɗauka. Wannan yasa wasu 'yan ajinsu ke ɗan jin haushinta musamman Mirabel da take ɗaukan na biyu a ajin nasu idan Kyauta ta ɗau na ɗaya.
Lokacin da Kyauta ta dawo daga makaranta ta samu Kaka Medugu da abokansa a ƙofar gida suna shan giya. Ta gaishe su ta wuce ciki.
Tunda Kaka Medugu ya yi doguwar jinya ya tashi ya ke iƙirarin ai tunda bai mutu ba a wancan lokacin gara ya ƙaraci sauran rayuwarsa cikin jin daɗi.
Gashi kuwa ya warke sarai kamar bai taɓa ciwo ba, sai ma wani ƙarfi da yake da shi.
Idan ka cire ciwon ƙafa da yake fama da shi, Kaka Medugu garau yake kamar wani ɗan shekara arba'in.
Kwana biyu Baba bai dawo ba. Ya bugo wayar maƙotansu a faɗawa Kyauta da Kaka cewa an bashi gado ne a can Asibitin.
Lokacin da aka bawa Kyauta wayar da ya sake bugowa kuka ta fashe da shi tana cewa ya barta ta taho Mubi, yace mata ta yi haƙuri ya kusa dawowa.
Wasa wasa sai bayan kwana biyar aka sallamo Baba. Da ke weekend ne tareda Sɗang suka dawo gida. Saura masa jarrabawa biyu ya ƙare jarrabawansa.
Yadda Kyauta ta ga Babanta ya rame fiye ma da kafin tafiyarsa Asibitin, sai ta shiga damuwa. Har da yiwa Sɗang kuka akan meyasa baya bawa Baba abinci a Asibitin. Bata san Baban ne ba ya iya cin abinci sosai ba.
Ranan Sunday da yamma Sɗang ya koma Mubi. Kyauta ta cigaba da kula da Baba.
Ance zai sake komawa Asibitin bayan wata ɗaya idan ya gama shan magungunan da aka bashi.
Bayan sati biyu da dawowar Baba daga Asibiti jikin nasa ya sake tashi aka kwantar da shi a clinic a nan Gulak yayi kwana biyu ya dawo gida.
Safiyar ranan da John Yayaha zai rasu Kyauta ta tashi da mummunan mafarki.
Daga nan kuma ta ji bata son zuwa makaranta. Lokacin data kai wa Babanta kunu ya ga bata saka uniform ba sai yake tambayarta meyasa ba zata je makaranta ba, tace masa kanta ke ciwo ba zata je ba.
"Baba ya jikin naka?" Ta tambaye shi
"Da sauƙi sosai"
Sɗang ya shigo ɗakin yace "Kyauta ba zaki shirya ki tafi makaranta ba"
"Ba zan je ba"
"Ba za ki je ba kuma? ba na ji Joseph yace kuna da test ɗin English yau da safe ba"
"Bamu da shi, an fasa test ɗin" ta faɗa tana zumɓura baki.
Babanta ya yi murmushi ya ce "Ngwatam je ki shirya ki tafi makaranta"
"Baba da gaske an fasa test ɗin fa"
Joseph da ya ƙwalo sunanta yana ce mata ta fito sun makara kar su rasa test ya tona mata asiri.
"Ngwatam ki je ki shirya"
Kyauta ta miƙe tana ƙananan maganganu ta fice. Baba yace mata "Allah ya bada sa'a"
Saboda fushi lokacin da ta shirya ko ɗakin bata shiga ta musu sallama ba daga tsakar gida take ce musu ta tafi.
Sɗang ya bita da tambayar ko tana da kuɗin tara bata amsa masa ba suka fita ita da Joseph.
Kusan ƙarfe shabiyu da rabi na rana suna ajin Mr Mathias yana musu Biology sai ga Vice Principal ya shigo ya kira sunan Kyauta Yahaya.
Tana ji ance ta ɗauko jakarta ta fito jikinta ya shiga ɓari.
Ta ɗauko jakanta ta bi bayansa.
Mr Haruna Malamin Islamic ɗinsu aka ce ya kaita gida a mashin ɗinsa.
Sai tambayar me ya faru take amma babu wanda ya bata amsa.
Tunda suka kusa gidansu data ga mutane na ta yin hanyar gidansu jikinta ya bata wani abu ya samu Baba.
"Mr Haruna wani abu ya samu Babana ko?" Ta tambaya tana tuno mafarkin da ta yi daren jiya.
Mr Haruna yace ta yi haƙuri sun kusa isa gida.
A cikin mafarkin da ta yi jiya, gani ta yi Babanta ya zo yana faɗa mata wai zai yi tafiya, zai je ya dubo Mamanta, yace mata ta kula da kanta. Da ta riƙe hannunsa ta ce "Baba kar ka tafi" sai ya mata murmushi yace "dole ne na tafi Kyauta". Daga haka ta farka a mafarkin.
Yadda mutane suka taru a ƙofar gidansu ya tabbatar mata ko Baba ko kuma Kaka ɗaya daga cikinsu ya rasu.
Tana sauka kuwa wasu mata suka yanyameta suna kuka suna kiran Teacher John.
"Baba!" ta ƙwace ta shiga gidansu da gudu. Tana ganin Kaka zaune a ƙofar ɗakinsa yayi tagumi jajayen idanunsa sun kawo ruwa ta tabbatar Baba ne ya rasu.
Ɗakin Baba za ta shiga ta ji an riƙota.
"Sɗang ka sakeni. Ina Baba?, Ina Baba?"
Rungumarta yayi yana faɗin ki yi haƙuri.
"Ka bari na ga Baba"
Tare suka shiga ɗakin inda aka shimfiɗa gawar Baba akan tabarma.
An riga an masa wanka an masa sutura.
"Baba, Baba, Baba ka tashi ka ji"
"Ni ce Baba, Ngwatam ce, Baba ka tashi"
Ta cigaba da sunbatu tana kuka. Da ƙyar Sɗang ya fita da ita dan addu'ar da ake jira ta dawo ta yi masa ma kasawa tayi sai kuka da ihu.
Har aka fita da gawar John Yahaya Kyauta bata dena kuka ba.
A ƙofar gida aka masa jana'iza aka wuce da shi maƙabarta.
Kaka Medugu na ƙofar ɗakinsa ya kasa motsawa. Mutuwar ɗansa ta girgiza shi. Ji yake inama shine ya mutu ba ɗansa Adarju ba.
Har dare Kyauta bata fito daga ɗaki ba. Ta ma dena kukan kallon masu zuwa gaisheta kawai take.
Har aka yi gaisuwan uku aka watse Kyauta bata magana sai dai ido.
'Yan'uwan Mamanta sun so su tafi da ita amma ta ƙi. Yayar Babanta ma Anty Martha ta nemi Kyauta ta bita amma ta ce babu inda za ta je.
Makaranta kam ajiye shi gefe ta yi ta koma zaman gida. Ba abunda take sai kuka da bacci.
Yayanta Sɗang yayi rarrashin yayi faɗan amma Kyauta ta ƙi komawa makaranta.
Sati uku da rasuwan Babanta aka fara exams ɗin second term a makarantarsu.
Da fushi da kuka ta tafi makarantar dan ta rubuta jarrabawar bayan Sɗang ya korata.
Sai ga shi a washegari aka bada sanarwar an rufe makarantu saboda hare-haren 'yan Boko Haram da kuma sace ɗalibai da suka yi.
Wannan yasa Kyauta ta koma zaman gida, har yanzu dai bata gama farfaɗowa daga mutuwar Babanta ba.
***