19
by @azizat
*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)
Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat
*MMG'S*
_Chilli powder_
Tasty Yaji... *kin kuwa san sirrin haɗa yaji da garin ɗanwake mai kyau ko kuma dai a bar maganar kar ayi tone-tone?. To! matso Hajiyata ba sai kin wahalar da kanki ba, MMG's Tasty Yaji sun zo muku da sauƙi, ba ruwanki da jan hanci ko tari wajen dakan yaji. Kawai order za ki yi a kawo miki yaji mai kyau har gida. Ga kuma garin ɗanwake mai danƙo suɓul-suɓul Malamata . Domin gwada yajin mu da garin danwaken zaku iya tuntubar mu ta wannan lambar. *** ko ta wannan number ***.* Sayan na gari mai da kudi gida, sai an gwada akan san na kwarai, sayan daya-daya ko sari akan furashi me rahusa.
Page 019
***
*2014, KADUNA*
Wayoyi guda biyu ne a gabanta ga ɗaya da ta riƙe tanata dannawa.
Yanayin yadda ta nitsu tana bin hirar da ake a tashar BBC Hausa zai tabbatar maka hiran na da mahimmanci a gareta. Jiya aka sake hirar kuma daga jiyan zuwa yau a ƙalla sama da mutane dubu hamsin sun kalli hirar.
Maimaita kallon take saboda ta tabbatar babu inda ta yi kwaɓa ko kuma ta manta da mahimmin abu da bata faɗa ba.
Komai ya mata a kwalliyarta amma ta ɗan lura kamar wacce ta mata zanen gira ta yi ɗaya ya fi ɗaya girma. Bata da gashin gira sai 'yan tsilli-tsillin gashi da ba su fi a irga ba, wannan yasa in dai za ta fita koda ba zata yi kwalliya ba to dole ne ta zana giranta. Sau da dama idan ta tashi a barci ta kalli fiskarta a madubi giranta take fara dubawa. Ba kalar mayukan ƙara gashi da bata shafa a giran ba amma gashin ya ƙi tohowa, kuma kaman shafe-shafen mai da ta yi a baya ya sake soye giran nata.
Hajiya Munira Bawa kenan wacce duniya ta fi saninta da Hajiya MoBaby. Babbar Producer ce kuma Director a masana'antar Kannywood. Sannan mata a wajen Colonel Naseer Muhammad Zaki.
Duk da shekaru bakwai kenan da ta dena fitowa a fina-finai har yanzu tauraronta bai dena haskawa ba dan duk inda za a kira Producers na Kannywood guda biyar to dole a tsinci sunan kamfaninta a ciki.
MoBaby ta zamo ɗaya daga cikin iyayen Kannywood. Su ne ke juya masana'antar. Sune masu faɗa aji.
Tana da jarumai dayawa da ta shigo da su cikin masana'antar ta koya musu aiki har ta yaye su.
Bata shiga film amma tana aikin bayan fage. Tana da ɗimbin mabiya a shafukan Instagram da Facebook.
Bayan harkar film tana da business ɗinta na skincare products. Inda take da mayuka da kayan kwalliya da ta fitar duka ƙarƙashin kamfanin MoBaby Cosmetics.
A shekaru bakwai da aure Allah ya albarkaceta da 'ya'ya biyu. Babban Ibrahim Khalil yanzu shekaransa shida sai ƙaramar 'yar shekara biyu, Zainab da suke kira da Zee ko Baby saboda sunan Iya da ta ci.
Akwai yaron mijinta Al'amin da ta riƙe amma yanzu yana boarding school inda yake JSS 2.
Zahra ƙanwar Al'amin har yanzu tana hannun Iya ita kam ko a hutu bata son zuwa Kaduna dan bata shiri da Munira. Tsakaninta da Babanta sai dai idan ya zo duba su a Azare ko kuma dukka gidan sun zo hutu Azare. Tana gaban Iya tana shan gata, ba wanda ya isa ya taɓa Zahra idan ka ce zaka taɓa Zahra yanzu zaku ɓata da Iya.
Shigowar Mukhtar ya sa Munira ta kashe video'n da ta ke kallo ta fuskance shi.
"ƙaramin Soja" ta faɗa tana dariya. Duk cikin 'yan'uwan mijinta babu wanda tasu ta zo ɗaya irin Mukhtar ɗan gidan Indo. Shekarar da ta wuce ya fara karatu a NDA Kaduna. Shima ɗin sahun Kawunsa yake son bi.
Kafin ya tafi makarantar ma sai da yayi zaman watanni a gidansu bayan ya gama Sakandare. Yaron bashi da girman kai haka zai zage yayi ta mata aikace-aikace irinsu wanke mota da kuma kai ɗanta Khalil makaranta.
Yaranta ma gaba ɗaya sun saba da shi, da ya zo zaka ga suna ta ihun Uncle Mukhtar. Hatta Baby Zee tun ba a yayeta ba ta ke maƙale masa. Yanzu ma da ta ganshi zata fara Uncle babu me. Wato ya goyeta.
Yadda jinin Mukhtar da Munira ya haɗu ba haka abin yake tsakanin Munira da mahaifiyar Mukhtar ɗin ba. Indo da Munira basa ga maciji. Ba dan ma Mukhtar ɗin ya nace yana son zama Soja ba babu abinda zai sa ta yarje mishi ya je kusa da Munira.
Duk da dai yanayin rayuwa wasu daga cikin 'yan'uwan Naseer suna gindin Munira amma Indo kam ko inuwa ɗaya basa iya zama tare.
Wannan rashin shiga jikintan ya siya mata mutunci dan kuwa bata shakkar gayawa Munira magana idan wani abu ya faru.
Idan ka cire Indo, Dr Aminatu da Hadiza duk sauran sun zamo 'yan amshin shatan Munira. Da siyasa da kuɗi ta siye bakin sauran 'yan'uwan Naseer.
Yanzu duk abinda za a kitsa a familyn su Naseer kafin aje ko'ina maganar zai dawo kunnen Munira. Ita kuma idan ta samu ta hure kunnen Sojanta shikenan ta toshe duk wata ƙofa da za su samu su ci galaba akanta. Ta san kan Sojanta, ta san wasu notina za ta taɓa ta samu kansa, ta kuma san ina za ta murɗa ya mata abinda take so.
"Allah ya ja kwanan matar Colonel" Mukhtar ya faɗa yana sara mata.
Munira ta yi murmushi tace " ba dai tafiyar za ka yi ba?"
"Ai na haɗa komai sai tafiya. Ina ga Colonel fa ba zai samu shigowa ba sai dare"
"Ai kam tunda muka ji shiru har yanzu to sai can dare"
"Madam ni zan wuce, idan Colonel ya dawo a faɗa masa na wuce"
"To Allah ya bada sa'a ƙaramin soja"
"Amin Madam ɗin Colonel, daga ke kaɗai babu ƙari"
Kalamansa suka saka Munira washe baki. Ai ko bai faɗa ba daga ita ɗin babu ƙari. Babu macen da ta isa ta shigo gidanta, ba ayita ba kuma ba za a yi tan ba. Lion ai nata ne ita kaɗai.
"Mukhtar, maiaiki ta baka kayan da nace ta haɗa maka kuwa?"
"Eh, suna cikin mota. Ina godiya Hajiyar Colonel. Thank you so much"
"Haba kai"
"Su Khalil ba sa gida ko?"
"Zee ta yi bacci, Khalil yana wajen lesson"
Mukhtar ya ce "barin yi maza na tafi kafin su zo su hana ni tafiya"
"Ai kai da yaranka sai a hankali"...
*
Tunda ƙarfe goma shaɗaya ta yi Munira ta cire rai da dawowar Zaki a ranan. Kwansa uku kenan a Abuja kuma yau da rana yace mata suna hanya zai dawo.
Wani cream color nightie ta saka mai tsantsi tana kwance akan gado tana bibiyar abinda ke faruwa a Instagram. Koyaushe tana cikin yawon bibiyar shafukan bloggers tana neman me ake faɗa akanta. Wani lokaci har comment take da fake account ɗinta da ta buɗe kawai saboda bibiyar abinda ke faruwa.
Lokacin da kiran Colonel ya shigo wayarta da sauri ta ɗauka dan ta matsu ta ji ko lafiya dan tun da yamma numbarsa bata shiga.
"My Lion"
"Gamu nan isowa"
"Yanzu???"
Kashe wayar ke da wuya ta ji ƙaran buɗe gate. Ajiye wayarta ta yi ta sauko daga kan gado. Room slippers ɗinta ta saka ta fito falo.
"My Lion lafiya kuka yi dare?"
Bai amsa mata ba ya wuceta ya shige ciki.
Yanayin fuskarsa ya shaida mata ba lafiya ba. Ta saba ganin irin wannan fiskar shiyasa bata firgita da komai ba.
"My Lion ina aka tura ka?"
"Kawo mun ruwa"
Miƙewa ta yi ta wuce kitchen ta ɗebo masa ruwa a glass cup ta kawo.
Sai da ya sha rabi sannan ya ajiye ya kalleta yace " Khalil da Zee sun yi bacci?"
Munira ta gyaɗa kai.
"My Lion baka ce komai ba. Maiduguri aka tura ka ne?"
Hare-haren 'yan Boko Haram yayi ƙamari a wajajen Maiduguri, Yobe, Adamawa, Katsina. Kwanan nan jahohin da ake tura sojoji kenan. Watanni biyu da suka wuce aka tura mijin wata ƙawarta matar wani Captain da suka taɓa zaman barracks a Jos. Kuma tunda ya tafi sau ɗaya aka ji daga gareshi basu sake sanin halin da yake ciki ba. Ko jiya sai da Abida ta kirata tana kukan har yanzu fa babu labarin mijinta.
"Adamawa" Colonel Naseer ya faɗa a hankali.
"Ran Monday zamu wuce"
Munira ta ja dogon numfashi. Ya za ta yi tunda soja take aure.
Duk lokacin da tafiya irin wannan ta tashi dole ne su yi haƙuri. Cikin shekaru bakwai da suka yi tare sau biyu yayi irin wannan tafiyar, sauran tafiye-tafiyensa courses kawai ake tura su, cikin ikon Allah kuwa da jajircewarsa har gashi ya kawo wannan matsayi na Colonel.
"Zan wuce Azare gobe, zan je na yiwa Iya sallama. Zan dawo a goben saboda jibi zamu wuce Abuja Monday kuma zamu ƙarisa Adamawa"
"My Lion har ka sa jikina yayi sanyi. Kai!" Ta riƙe kanta.
"Ki yi haƙuri My Darling. You have to be brave. Ance wata uku zamu yi, but zamu iya fin haka"
"Hmmm" Munira ta fara girgiza kai tunani kala-kala na zuwa mata.
Ko da Naseer ya samu Iya da batun tafiyar itama gaba ɗaya hankalinta tashi yayi. Abubuwan da ke faruwa a yankin da zai je bai ɓoyu mata ba. Kullum tana riƙe da rediyonta tana sauraren labaru, kusan kullum sai ta ji ance an kai hari waje kaza ko kuma bomb ya tashi a waje kaza.
"Iya dan Allah a cigaba da saka mu a addu'a"
"Ai tunda ka fara aikin nan bakina bai dena maka addu'a ba Nasiru. Allah ya tsare min kai ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya."
Naseer ya amsa da Amin.
"Zahra tana makaranta ko?"
"Ai bamu san zaka zo ba dana ce ta zauna a gida"
"Zan je makarantar na dubata kafin na wuce"
"Da wurwuri ne zaka tafi?"
"Akwai shirye-shirye da zan yi" ya faɗa yana duba agogon hannunsa.
Iya ta taɓe baki tana girgiza kai. Duk lokacin da Naseer ya zo da maganar za su je aiki sai hankalinta ya tashi, har sai ya dawo kafin hankalinta yake kwantawa.
Lokacin da Naseer ya wuce Kaduna, Iya da kanta ta shiga store ta auno shinkafar tuwo, so take da an sauko sallar jummu'ah ta sa a mata sadakar masa.
Al'ada ce in dai Naseer zai tafi aiki irin wannan to kullum sai ta sa an yi sadaka saboda Allah ya tsare shi.
Lokacin da Naseer ya tafi jihar Adamawa aka ji shiru daga wajenshi bayan sati biyu da tafiyar sai hankalinsu ya fara tashi.
Da aka yi wata ɗaya da tafiyar Iya da kanta ta kira Munira tana tambayar ko ta ji daga wajen Nasiru. Munira tace mata ai inda suka je jeji ne babu network.
Iya ta sake tsorata da lamarin tana tuno shekarun baya da yai irin wannan tafiyar aka dena jinsa tsawon watanni lokacin yana tareda marigayiya Fatima.
Shiru-shiru fa watannin suka shafe biyu, uku, huɗu. Iya labarin da ake ji shine yana nan da rai amma a jeji suke dan haka babu network ɗin da za su iya magana da shi...
A kullum addu'ar Iya shine Allah ya cigaba da tsare mata Nasirunta a duk inda yake.
***