NI DA YAYA ARMAN

29-30

by @autarmama

๐Ÿ *NI DA YAYA ARMAN* ๐Ÿ

Hot love storyโ™ฅ๏ธ๐Ÿ”


```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*


๐Ÿ“š *JARUMAI WRITERโ€™S ASSOCIATION* ๐Ÿ“š


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู†


*BOOK ONE*๐Ÿ“”

๐Ÿ…ฟ๏ธ...............29&30



" Mamy na rabu dashi Shima kuma nasan Daddynshi ya rabashi dani tunda bakusan mu amulata dashi"Yawwa ko kefa Aira ki taimakamun ki fiddani kunya ki rabu dashi sannan ki daina abunda zaidinga jamun Zagi kinji"Gyada kai tayi tace "Insha Allahu Mamy Na daina" Allah sa da gaske kike na yafe maki duniya da Lahira Allah maki Albarka "




"Sosai Aira taji sanyi a ranta tace " Ameen Mamy nagode sosai"sosai Mamy ta saki jiki da Aira ta dinga janta cikin dabara ta Tambayeta ta ce " ranar da kuka tafi ina kikaje kuka kwana badai abunda yayi maki ko idan da Abunda ya faru fad'amun wlh ba maiji kuma bazan dake kiba kinji na rantse "





Nan Aira ta bawa Mamy Labarin komai Da ya faru daga karshe ta ce " Allah Mamy Gaskiya na fad'a maki ba abunda yamun ni yaya baitab'amun maganar banza ba kawai zargine kuke amma shi ba haka yake ba"wata nauyayyar Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta tabbata Aira idan ta fad'i magana haka take Dan bata karya





Sai sannan taji sanyi a ranta ta cire zargin dake ranta daman duk wannan Abun da tayiwa Abba itama akwai zargin a ranta kawai Dai abunka ga d'a da uwa ne "to yanzu shikenan komai ya wuce na yarda ki kiyaye nan gaba Dan Allah" to Mamy "sannan tace " Mamy banishi na rik'e maki ta fad'a tana mik'a hannu ta amshi Ameer tare da pidarshi ta sab'eshi a kafad'a ta fito palour Sai murna take yanzu Hankalinta kwance ta sasinta da Iyayenta.




Haka rayuwa taci gaba Aira na shan wayarta da Arman a b'oye babu Wanda ya fahimta Kullum idan Sadiq ya kira Aysha idan ta bata wayar kin amsa take ba yanda Aysha batayi da itaba amma saita k'iya tun yana kira har ya hakura ya daina kira Wanda hakan sosai yayiwa Aira dad'i.



Amma ta koma bangaren Inna kullum Inna da kewar Aira take kwana take yini Dan tayi mugun Shak'uwa da ita gashi taga Airar tayi zuciya ko bangarenta bata k'ara shigowa dak'yal a daddafe Inna ta daure tayi sati biyu ba Aira sosai kewarta ta dameta gashi Shima Arman bai sake zuwaba duk Abu ya dameta.




Yau Aira y'an gidan su duk suna zaune a palour ana hira da misalin Tara na dare har Abba da su Mamy Amer na Bayan Aysha ta goyashi Inna ta shigo Aira na ganin shigowarta ta kauda kai Wajenta Inna ta nufa ta ce "Haba y'ar lelena daman zaki iya fushi dani Duka ina duniyar take bare mu dake cikinta biko nazo ki taho mu koma gidan duk bayamun dad'i da kika tafi" Turo baki Aira tana zunbura Baki ta ce




"Keda kika koreni ni ba Inda zani kije Chan takwarartaki ta dinga tayaki kwanan ni bazan koma ba"Inna ta Goge hawaye ta ce " Haba Hajara Dan Kinga ina sonki shiyasa kikemun wulakanci to wai ba na baki hakuri ba ki taho mu tafi "ba Inda zani ni ki tafi " Sudai su Mama suna gefe suna Dariya kasa kasa Dan Inna da Aira sai Allah haka zasuyi fad'an kuma inna tadawo tana bata hakuri"cike da Masifa Inna ta juya ta kalli su Mamy ta ce





"ku yanzu cikinku ba mai bata hakuri Kunajina kukayi banza dani Dan kun rainani ke Rahama ba y'arki bace Baki isa kice tayi hakuri kodan daman Nasan ai ke kike zugata shiyasa yanzu ta gujeni kiwon d'an makwarwa ne nayi " tafada tana Goge hawaye "Cikin ladabi Mamy ta ce " kiyi hakuri Inna ni wlh banzugata ba Dan kar nayi magana kuma kice ina ruwana shiyasa amma kiyi hakuri sannan ta harari Aira ta ce "Tashi ku tafi" Turo baki Aira tayi ta ce "Mamy itafa da kanta ta koreni har cewa tayi karna k'ara zuwan mata" Inna tace




"Kai Hajara banda sharri a ina na koreki " Abba ne ya ce "Mamana tashi ku tafi banson doguwar magana" Tashi Aira tayi ta ce "To Abba a ranta sosai taji dad'i Dan daman kamar a k'aya take bata samun damar shan waya da Arman Yanzo ko gidan Inna ko kwana zatayi tana waya dashi ba mai sani d'akinta ita kad'aice kawai ta gwada batasone Dan inna tasan Taji Haushi Akwatinta ta d'auko wayoyinta daman suna ciki ta fito ta harari Inna ta ce .




" To muje kuma wlh kika k'ara korata ko kika zagi Mamy na taho har abada bazan koma ba"To y'ar lelena Inani ina Kara korarki ni daman Chan ban zagar maki uwa ba Rahama ai y'ar kirkice bakiji sunan ba Rahama duk Inda kikaji an ambaci Rahama ai andace bakiga ba ko mutum mutuwa yayi ba Rahama ake nema mashi "Dariya Aira tayi sosai hada rik'e cike tace " To shikenan My Inna muje suma su Abba Dariya sukayi sosai Har Mamy wai yau itace Inna ke yabo .



Su Aira na fita Mamy ta tashi ta cewa Mama"Yaya saida safe "To Auntynsu Allah tasheni lafiya Mama ta fad'a " Mamy ta kalli Aysha da murmushi fuskarta ta ce "Yau ko tayin bacci zai miki" Dariya Aysha tayi ta ce "Mamy muje saina kwantar dashi Dan karya tashi suna zuwa d'akin Aysha kwantar da Amer Sannan ta kalli Mamy ta na Sosa kai ta ce " Uhm Mamy Dan Allah wani taimako zakiyimun"Mamy tace "inajinki Aysha fad'a kai tsaye insha Allahu indai zan iya zan maki shi"




Cike da kunya Aysha ta bawa Mamy labarin Saurayinta Abdulkharim da hadu Airport daga karshe ta ce "Shine yanzu yace yanason yazo ya gaishe da Abba shine nake tsoron yiwa Abba magana Dan Allah Mamy ko zaki fad'a masa nasan ke zai fahimce ki " Murmushi d'auke da fuskar Mamy ta ce "Ah masha Allah kice munkusa shan biki amma gsky Naji dadi karki damu Insha Allahu zanyi mashi magana ba matsala" Godiya sosai Aysha tayiwa Mamy Dan tasan daman itace zata fad'awa Abba direct yayi na'am.




Mamy Bayan ta fito daga wanka jikinta daure ta towel ta dauki amer tana cikin sauyamai kaya Abba ya shigo kauda kai tayi kamar batasan yashigo ba Dan tun sanda sukayi rigima ta ke fushi dashi cikin kwantar da murya Abba ya ce "Haba sarauniyar mata Farar mace alkyabbar mata wai har yanzu baki huce ba Fushin nan ya isa Haka kinsan bazan jureba Airar ma data had'amu na yafe mata".





" hmmm kawai mamy tace taci gaba da abunda Take Abba ya ce "To wai ba nace kiyi hakuri ba Haba my rahama bansanki da rashin yafiya ba "cike da kissa Mamy ta ce "hmm ya wuce Abban Aira amma karka sake irin haka gaskiya" Cike da farinciki Abba ya ce "Bazan sakeba Amma kema ki daina fad'amun magana son ranki gaban kowa"




Murmushi kawai tayi a take suka shirya kamar basu tab'a fadaba(Su Abba da Mamy Daman ba a hakura da love ba๐Ÿ˜‚๐Ÿ™ˆ) cikin hikima Mamy ta fad'awa Abba sak'on Aysha sosai yayi farinciki daman yanzu kuma burinshi tunda ta gama karatu Aure kuma alhmdllh tunda ta samu cikin Sauk'i.




Haka rayuwa taci gaba Aira komawarta gidan Inna sosai tayi mata dadi Dan tana samun damar shan wayarta da Arman da vedio call tarayyarsu taci gaba saima shakuwa da suka k'ara An sanya bikin Aysha Da Abdulkharim wata hud'u masu zuwa Wanda aka had'e da na Ummy itama Bayan gama karatunta Saurayinta ya turo Wanda dukansu cikin garin suke sosai hakan yayiwa iyayensu dadi.



Su Abba ganin Aira ta nutsu ya sanya suka saki jiki da ita suke hamdalar ta rabu da Arman musamman mamy


Arman saida Yayi wata biyu baizo garin ba Dan tunda Abba ya dakeshin nan bai sake zuwaba kullum Mummy cikin lallabashi take akan yazo tayi kewarshi Dan Arman ko sati biyu bayayi baizoba amma wannan tafiyar har wata biyu baizo tasan fushi yayi dak'yal ta samu ta shawo kanshi ya ce zaizo.



Ranar da zaizo Aira sai Farinciki take Dan ya sanar mata ji take kamar ran sallah Tunaninta d'aya Inda zasu had'u Dan yace mata ko gidan Inna bazai dinga zuwa ba Dan kar a dinga samun matsala tana cikin tunani Dan tun d'azu yace mata jirginsu zai tashi wata dabara ce ta fad'o murmushin jin dad'i tayi Tabbas wannan shawarar ita ce kawai mafita cikin Sauk'i...........โœ๐Ÿฟ



๐Ÿ˜ฑtofa wata shawara ce Aira ta yanke ?????



_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ