General NASEER Zaki

20

by @azizat

*GENERAL NASEER ZAKI*

(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03

Arewabooks: Azizat


                          Page 020

*2014*


*SOMEWHERE AROUND GULAK, MADAGALI, ADAMAWA STATE*




Sanyin Asubahi ne ya fargar da Colonel Naseer Zaki daga dogon suman da ya yi.

Hannunsa ya fara motsawa sannan ya buɗe idanunsa, tsilli-tsillin ciyayi da yake gani dishi-dishi shi ya tabbatar masa da cewa ba mutuwa yayi ba. Yunƙurin miƙewa yayi amma hakan ya gagare shi. Rufe idanunsa yayi a karo na biyu yana ƙoƙarin tattaro ƙarfinsa.

Bayan tsawon lokaci ya sake buɗe ido, wannan karan yunƙurawa yayi da duk iya ƙarfinsa ya motsa daga inda yake kwance ya mirgina gefe.

Jan jiki ya fara yana ƙoƙarin kaiwa gindin wata ƙatuwar bishiyar da yake hangowa ko zai samu ya dafa bishiyar ya miƙe.

Yana jan jiki yana hutawa har ya kai jikin ƙatuwar bishiyan kuka.

Ya yunƙura ya tashi zaune ya jingina bayansa da bishiyar.

Tari ne ya kufce masa wanda ya sa shi bezar da jini ta bakinsa.

Idan bai samu taimako ba babu yadda za a yi ya iya tsira da rayuwarsa.

Gari ya ɗan fara haske amma bai ga alamar akwai mutane a kusa da inda yake ba.

Nishi yake, yayinda duk lokacin da ya yi yunƙurin miƙewa sai ya kasa. Ƙarfinsa ya ƙare.

Ya rufe ido yana kiran sunan Allah...

***

"Kyauta, ki fito mu wuce fa"

Abubakar Sɗang ne a tsakar gidansu yana ɗauke da fartanya da kuma wata jaka da ya goya a baya.

Tun bayan rasuwan Babansu da rikicin Boko Haram ya ɓarke suke rayuwan taka-tsantsan.

An rufe makarantu dan haka ko result ɗinsa na gama HND bai samu ya karɓo ba. Makarantun Sakandare kam ba a san yaushe za a buɗe su ba. Kyauta har ta sallama da yiwuwar komawa makaranta nan kusa.

Babu abinda suke sai aikin gona dan ruwan bana ya zo da wuri, ana shiga watan August kuma ruwan ya fara yawa.

Kaka Medugu dai tun mutuwar ɗansa hankalinsa ya gushe. Wani lokaci mantawa yake cewa ɗansa ya mutu sai ya kira Kyauta ya fara tambayarta "Adarju bai dawo bane?" Ko kuma yace "Babanku na gida kuwa?, na ga bai shigo ya gaishe ni ba"

Idan yana irin haka Kyauta kuka take sakawa saboda tuno mata da babban rashin da tayi ya ke. Wani lokaci kuma sai ta biye masa da cewa Babanta ya kusa dawowa.

Fitowar Kyauta daga ɗaki sai Sɗang ya sakawa tsohuwar machine ɗin Baba ƙirar Jincheng key ya fara burgata, sai da ya burga sau uku kafin ta tashi.

"Kaka mun tafi gona" Kyauta ta faɗa duk da ta san ba lallai ya tashi daga bacci ba.

A ƙofar gida ta tadda Sɗang yana jiranta. Ta hau machine suka wuce gona.

Tsoron hare-haren Boko Haram yasa mutane da dama basa iya fita gonakinsu dake wajen gari.

Duk da dai har yanzu babu wani hari da aka kawo kusa da su, amma suna da labarin nesa da su ana ta kai musu hare-hare.

Sai da suka sha aiki rana ta fito sannan suka ɗan tsaya dan su huta.

Cikin Kyauta ne ya juya ta miƙe da sauri tace wa Sɗang za ta ɗan kewaya.

"Ngwatam kar ki yi nisa, it's not safe"

Gyaɗa kai ta yi ta ɗau goran ruwa ta fara tafiya.

Duk inda ta duba sai data ga bai mata ba sai da ta hango wata ƙatuwar bishiyar kuka, ta ƙarisa wajen da sauri ta tsugunna lokaci guda kuma ta sake zawo. Idan ya saura kwana ɗaya ko biyu ta fara al'ada to a lokacin take fara ciwon ciki, wani lokaci har da gudawa.

Tana tsugunne ta rufe idonta tana ɗan fitar da nishi a hankali, sai kuma ta ji wani gurnani a bayanta. Tsoro ne ya shigeta ta haɗiye yawu da ƙyar ta kasa kunne tana jin kamar gurnanin a kusa da ita ne. Hannu na rawa ta jawo goran ruwa ta yi tsarki a gaggauce ta miƙe.

Ta gefen ido ta ga kamar akwai wani abu a bayan bishiyar da ta ke. Ta yi ta maza ta leƙa bayan bishiyan. Ai kuwa ta saki ihu ta yi baya zata gudu sai ta faɗi.

Kamar a mafarki ya ji ihun mutum a bayansa. Kamar ihun mace yake ji.

Yunƙurin tashi yayi da dukkan sauran ƙarfinsa.

Kyauta ta fara ja da baya-baya ganin mutumin dake bayan bishiyar na shirin tashi. Yau dai kwananta ya ƙare ta yi gamo da 'yan bindigar Boko Haram.

Dan Allah...kar...." ya furzar da jini. Kyauta ta ƙura masa ido jikinta na kakkarwa. Ita bata gudu ba, ita bata motsa ba. Gaba ɗaya ji tayi kamar an ɗaure ƙafafuwanta.

"Kar ki... gudu" ya ƙarisa maganar da ƙyar.

Ta ji me ya faɗa. Tana jin Hausa. Yaruka huɗu ta iya Hausa, Marghi, Turanci da kuma Fulatanci kaɗan-kaɗan.

"Ki taimaka min" ya faɗa bayan ya miƙe tsaye yana dafa bishiyar.

Tsoro da ya gani a tattare da ita ya sa shi faɗin " ni soja ne. Ba zan cutar dake ba"

Kyauta ta yi shiru tana kallonsa. Tabbas kayan sojoji ne a tattare da shi. Amma a yadda mutane ke bada labari suma 'yan bindigar sukan saka kayan sojoji.

Idanunsa ta cigaba da kallo tana tunanin miye abin yi.

Miƙewa ta yi a hankali daga inda ta faɗi.

Bakinta yayi nauyi, tana son cewa zata je ta kira yayanta amma ta kasa magana.

Ta juya baya ta kwasa da gudu tana kiran Sɗang!, Sɗang!, Sɗang!.

A hanya ta haɗu da Sɗang wanda shima jin shirunta ya sa shi biyo bayanta. Yana jin tana kiransa sai kuma hankalinsa ya tashi.

"Lafiya? Bana ce kar kiyi nisa ba"

Bayanta ta fara nuna masa tana haki saboda gudu da ta yi.

"Menene?"

"Soja. Soja na gani bashi da lafiya"

"Soja kuma?. A ina?"

"A can kusa da rafi"

"Nace miki ki tsaya kusa, idan wani abu ya sameki fa"

"Zo mu tafi" ya jata

Tirjewa ta yi tace " Sɗang zai mutu idan bamu taimaka masa ba"

Sɗang ya dubi inda take nuna masa. Ba dai 'yan bindiga ta gani ba?

"Sɗang ka je ka duba shi"

Sɗang yai ta maza riƙe da fartanya a hannunsa yai gaba Kyauta ta bi bayansa tana nuna masa hanya.

Tun daga nesa Sɗang ya hango mutumin da Kyauta ta gani.

Daga nesa suka tsaya suna kallonsa har lokacin yana zaune gindin bishiyar da Kyauta ta ganshi.

Sɗang ya ɗan matso kusa da shi yaiwa fartanyansa riƙon maƙami.

"Sɗang soja ne" Kyauta ta sake faɗa da yaƙinin da bata san daga ina ta samo ba.

Tausayin mutumin da yake a galabaice ne ya kamata.

"Kai waye?. Daga ina ka fito? " Sɗang ya tambaya yana tsaye a kansa.

Tari Colonel Naseer yayi ya sa hannu ya goge jinin daya ɓata masa baki yace "Colonel Zzaki" Yai shiru yana nishi.

"Ka nuna min shaidar da zai tabbatar kai soja ne"

Colonel ya sa hannu da ƙyar ya ciro tag ɗinsa daga aljihun wandonsa. Sɗang ya karɓa ya duba ya ga an rubuta N. M. Zaki, sannan serial numbarsa, da kuma blood group ɗinsa (O+).

(Da addininsa, wanda ake sawa saboda idan soja ya mutu a san ya za a yi da gawarsa).

"ruwa" Colonel Naseer ya faɗa lokacin da Sɗang ya mayar masa da tag ɗin.

Da yare yai wa Kyauta magana akan ta je ta kawo ruwa. Da gudu ta fetta a guje tana jin tausayin mutumin.

Sɗang ya tsaya kusa da Colonel yana tunanin abin yi.

Lokacin da Kyauta ta kawo ruwan suka bashi yana shan kaɗan sai ya fara amai saboda ya kwana biyu babu komai a cikinsa.

Kyauta ta ƙanƙame Sɗang tana tausayin Colonel.

Sɗang ne ya taimaka masa har ya kuskure bakinsa sannan ya sake gwada shan ruwan aka ci sa'a bai amayar ba.

Sɗang da Kyauta suka ja gefe suna maganan yadda zasu taimaka wa Colonel. Idan suka barshi a nan ba su masa adalci ba. Amma ya za a yi su kai shi gida ba tareda mutane sun gane ba.

Ƙarshe dai Sɗang ya yanke shawaran su je gida su ɗauko masa kaya ya saka su samu su shigo da shi gari.

Duk da Kyauta ta nuna Sɗang ya je za ta tsaya tareda Colonel amma bai yarda ba. Su biyun duka suka taimaka masa ya dafa su suka taka zuwa cikin gonansu.

Jikin bishiyar giginya da ke gonansu suka jingine shi.

Sɗang yace "za mu je mu taho maka da wasu kayan, ba za mu iya shiga da kai cikin gari a haka ba mutane za su tsorata"

Colonel ya gyaɗa kai. Tunda suka ce za su dawo ya yarda cewa za su dawo ɗin.

Kyauta ta rinƙa juyawa tana duba Colonel har suka kai wajen da Sɗang ya ajiye machine ɗinsa ya burga ta hau suka tafi. Gudu sosai suke kamar za su tashi sama duk da hanyar gonan nasu babu kyau.

Suna isa gida Sɗang yace Kyauta ta shiga maƙotansu ta kira masa Joseph. Ta fita daga gidan da gudu.

Sɗang ya sa key ya buɗe ɗakin Baba. Akwatin kayan Baban ya jawo ya ciro riga da wando da wata coat ɗinsa.

Ya fito ya nemi leda ya saka kayan a ciki.

Ya jiyo muryan Kaka yana tambayar Adarju ne ya dawo. Sɗang yace bai dawo ba.

Yana fitowa Kyauta da Joseph suka ɓullo. Sɗang yace Joseph ya hau machine ya bi shi. Kyauta ta ce " ni fa?"

"Ki zauna a gida"

Ta ɓata fuska ta koma gefe tana addu'ar Allah yasa kada wani abu ya samu Colonel kafin su Sɗang su ɗauko shi.

A hanya Sɗang yake faɗawa Joseph abinda ya faru tareda ja masa kunne akan kada ya ji maganar a bakin wani.

Lokacin da suka isa gonar Colonel na nan a inda suka bar shi ya rufe ido kamar mai barci, motsinsu da ya ji ya sa shi buɗe ido a firgice.

Sɗang da Joseph suka taimaka suka cire masa kayansa suka saka masa kayan da suka taho da shi suka maida Khakinsa cikin leda.

"Anya zai iya hawa machine?" Joseph ya faɗa cike da fargaba. Yanayin yadda yake ganin Colonel kamar ba zai kai labari ba.

Sai da suka sha fama kafin suka iya ɗaura Colonel akan machine, Sɗang ne yake tuƙa machine ɗin sai Colonel a tsakiya sai Joseph da ya tare bayansa.

Kyauta na can gida sai sintiri take a tsakar gida tana ganin kaman su Sɗang sun jima sosai, ya kamata ace sun iso gida.

"Męnagkur" Kaka ya kira sunanta daga ɗaki amma hankalinta yayi gaba

"Ngwatam" ya sake kira ya ji shiru. Hakan yasa ya ɗau sandarsa ya fito waje.

"Ngwatam" ya kira da ɗan ƙarfi

"Na'am Kaka" ta juyo a ɗan firgice

"Ki zo ki dafa min magani"

Ta amsa da to.

Kaka ya zauna a kujerar zamansa dake ƙofar ɗakinsa yana cin namijin goro.

Kyauta ta shiga ɗakinsa ta ɗauko tukunyar magani ta fito still hankalinta na kan hanya tana jimirin dawowan su Sɗang.

Ko dai Sojan ya mutu ne?

Ko kuma dai wasu sun zo sun ganshi a gonar sun tafi da shi?

Ko 'yan'uwansa sojoji ne suka ɗauke shi?

Tambayoyin da take yiwa kanta kenan.

Tana cikin tsiyayawa Kaka maganinsa a ƙwarya ta ji ƙaran machine. Da sauri ta miƙe ta bar abinda take.

Har tsakar gidan Sɗang ya shigo da machine Kyauta ta washe baki ganin su uku ne akan machine ɗin ba su biyu ba.

Sai dai Joseph na sauka daga machine yana ƙoƙarin riƙe Colonel machine ɗin ta yi gefe za ta faɗi, Sɗang na ƙoƙarin saitata amma sai da suka wuntsila dukkansu.

Sɗang da Joseph suka miƙe yayinda Colonel ke kwance a ƙasa kamar gawa...