FACALA

Chapter 5&6

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_Wattpad✅_*

***


*_𝘼rewabooks✅_* https://arewabooks.com/user/rabiattu0444


*Sirrinmu➡️*

ƳAR UWATA ANASO BAYAN KIN GAMA AL'ADA KIDINGA TSARKI DA GANYEN MAGARYA,YANA CIRE INFECTION DA SAURAN ƘARNIN JINI👏🏻.


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼


➡️5 & 6

…………………da sauri ya fice,duk da saurin ba wai ɗabi'arsa bace autar Momma ce kawai ta kula da saurin da yake amman iyayensa duk basu kula ba,sam bata son ganin yayanta cikin matsala shiyasa kowani takunta acikin idonta yake,saboda haka itama sai ta zama me bin ƙwaƙƙwafinsa da son ta san inda yake zuwa yake sauri haka.


yana fitowa cikin takunsa na alfarma ya shiga mota,bai bari kowa ya buɗe masa murfin motar kamar yadda ake masa ba.

sai ya zama wajen ma kamar anyi yasar bayi don baby kowa awajen,Aamiru dake cikin motar ya ce"shegen kaya daɗina da kai baka sanya akan komi,yanzu ta yaya ka fito ba tare dasu Momma ko me martaba yasan inda za kaje ba"?.


Har lokacin Galadima bai ce komi ba,bai kuma juya ya kalli Aamiru yasan hakan zata iya faruwa dama don yasan halin mutumin na sa da shegiyar tambaya? saboda haka sai yayi masa shiru wato shiru ma magana ce.

shi kuwa sai yaja bakinsa yayi shiru bai ƙara tambayar aminin nasa ba,don daman yasan ba lallai ne ya amsa masa ba don kaf duniyar nan bayan Momma da me martaba sai Allah, babu wani mahauluƙin daya san kafatanin halin galadima wanda ya wuce Aamiru.

tare suka tashi tun daga haihuwarsu har zuwa karatu,kai ƙarshe ma rana ɗaya aka haifesu Galadima Aliyu da safe shi kuma Aamiru da yamma,saboda haka komi na ƙuruciya tare sukayi daga baya ne suka rabu shima don wani babban shingine daya zagaye ahalin na su,wanda yayi musu mugun dabaibayin da har yanzu aka kasa ƙwancesa acikin BABBAR MASARAUTA.

tafiya sukayi me ɗan nisa sannan suka isa wani ɗan ƙaramin gida,wanda ba yake ɗauke da ɗakuna biyu da kuma banɗaki ko kitchen ma babu aciki,sai ɗan ƙaramin tsakar gida wanda bama zai yiwu mutum huɗu su ƙwanta ba.


daga ƙofar gida Aamiru ya tsaya ya ƙwanƙwasa,Galadima yana kallonsa wanda idanuwansa suka kaɗa sukayi jazur tamkar garwashi,yana son yayi hawaye ko da kaɗan ne amma ya kasa yi,don yana da wata irin zuciya me mugun tauri da kuma kafiyar hawaye,ko mutuwa akayi sai dai kaga idanuwansa sun kaɗa sunyi jawur,amman baya iya yin kuka bai san dalilin hakan ba,sai dalilin ba zai wuce irin yadda yayi gumurzu arayuwarsa ba,yana tuna wani abu da ba zai taɓa goge masa ba,wanda yake ganinsa kamar ayanzu yake faruwa.


Daga can ɓangaren kuwa Aamiru sai buga gidan yake,amman ba'azo anbuɗe masa ba can ya hango wasu samari acan suna zaune ya ƙarasa kusa dasu sukayi hannu sannan ya ce"don Allah guys ina tambaya?Don Allah su Ahmad sun tashi ne daga can gidan"?.

samarin suka baza idanu a inda yake nuna musu ɗin.

ɗaya daga cikinsu ya ce"eh gaskiya sun tashi kusan shekara biyu kenan".

Aamiru ya tsaye,ya kasa ko da juyawa don bai san ma abinda zai tarar gun abokin na sa ba,dama shi ajikinsa yana ji kamar ba zasu samu abinda sukazo nema ba,can wata dabara ta faɗo masa ya ce"don Allah ko zaku iya ƙwatanta mana inda suka koma"?.


Kallon kallo suka shigayi a tsakaninsu,alamar kamar dai basa son nuna gidan,ganin kamar zasu ɓata masa lokaci yasa ya ce"ok ga check nan na kuɗi ga duk wanda ya faɗa mana gidan".

da sauri samarin ƴan zaman banza suka kawo hannu su duka kamar zasu haɗa da hannun Aamiru ɗin.

ya ɗanyi dariya ya ce azuciyarsa oh kuɗi me canja ɗan adam daga me amana zuwa akasin haka.

da sauri wani acikinsu ya fara ƙwatanta musu unguwar,har da haɗawa da bada number waya don idan ma anje baya nan a nemeshi ta waya.

yayi murmushi wanda har wushiryarsa ta bayyana,ya yi musu godiya sannan ya taho wajen abokin sa yana murmushi don yasan dai ba zaiji zafi kamar idan ya dawo masa babu wani labari ba,hausawa sukace da babu ƙwara ba daɗi.


yana shigowa cikin motar,ya ɗan yarfe gumin da ya fara jiƙa masa riga sanyin AC na ratsa cikin ɓargo da gashin jikinsa,anan yake ƙara godewa Allah daya yo sa acikin masu hannu da shunu,agaskiya talakawa ba ƙaramar shan azaba suke yi ba,shi de yasan ba zai iya rayuwa acikin wannan azabar ba zai iya mutuwa baki ɗaya,amman ahaka amininsa yayi har shekara guda dasu acikin wannan azabar.


bai ce masa komi ba,don daman yasan halinsa indai har suka fito Aamiru ya shiga cikin rana to tabbas idan ya shigo gida ko mota ko iya magana baya yi sai ya samu damar shan iska sannan yake iya magana ma.

Kaɗan ya rage yayi masa dariya,sai dai ba zai iya hakan ba saboda yadda jikinsa da zuciyarsa suka yi masa zafi kamar garwashi sakamakon ganin gidansu Ahmad ɗin arufe.


sai da yasha iskar sosai sannan ya iya buɗe bakinsa ya ce"kasan da ƙer matasan can suka bani address ɗinsa ma? gaskiya ni aganina aminina gwara ka haƙura ka sare,kabar abinda ya wuce ya zama tamkar ruwa ko wani kogi me wucewa,ta inda duk wanda ya sanka ma ba zai gasgata abinda kake shirin yi yanzu ba".

wani wawan kallo ya yi masa,tare da ɗauke kansa tamkar ma bai san yana magana ba,atake kuma jijiyoyin kansa suka ƙara tsayi da kauri,farar fatarsa ta ƙara wani irin jazur tamkar wanda aka yiwa aman wuta,yana son yayi magana tabbas amman kuma sai yake jin kamar ba zai iya yin maganar ba,hankalinsa da nutsuwarsa yaji yana neman barin gangar jikinsa.

shi kuwa Aamiru kasaƙe yayi yana kallonsa,ya kasa gaba balle baya da motar suna de ciki ne tamkar waɗanda suka mutu duka amotar,hatta jan numfashi ma da ƙer suke yi,don agaskiya ya tsani yaga aminin na sa acikin matsala don shi kaɗai yasan faman da sukayi dashi abaya kafin ya koma yadda yake ayanzu.


Aamiru ya buɗe baki zaiyi magana da sauri ya ɗaga masa hannu tare da daka masa wata wawiyar tsawa,wacce ke tafe da ɓacin rai da kuma amon wuta.

da sauri yaja bakinsa ya kame,don har ga Allah ya tsorata sosai kuma shi sam ma baya son tsawa don da wani ne yayi masa to wallahi ko ɗan uban waye shi sai ya ƙwana agidan duhu.


To fa ko menene gidan duhu oho?😥💃🏼to nima anan zan face kada a cillani gidan duhu😂➡️.




***       ***        ***


Kuka Balaraba take tana ce wa"shikkenan an kashemin ƴar tawa da maita tsiya,don anga ba a haifa ba Allah bazan yarda ba yau ko ni ki ita".


 Da sauri ta tashi tsaye har tana haɗawa da tuntuɓe,ga kuma ƴarta na ƙwance shame shame tamkar gawa da sauri Xubair yasha gabanta,ya haɗe girar sama da ta ƙasa duk abinta tana tsoronsa idan ya canja kala irin haka.

ya ce"wai ke Balaraba wacce irin mahaukaciya ce ne? wajen wa xakije da daddaran nan? kuma sannan wacece mayyar"?.


wani irin kallo ta watsa masa duk da tana jin tsoronsa ta ce"wajen Rabiatu zani ta fito min da kuruwar ƴata da ta cinyemin,Allah wannan karon bazan yarda ba sai ta zo ta tsallakamin ƴata,don na gaji da wannan iskancin ai babu wanda bai san su mayu bane wannan kyaun na su ai ba na ƙarya bane,na cin mutanene don dama ance duk masu cin mutane kyawawane".

tana faɗar hakan tayi gaba fuu,da mugun sauri ya janyota ta faɗa kan kujera,ta fashe da kuka tana ce wa"ai dama nasan kaima an gama da kai sai abinda akace kayi shi kake aikatawa,wato an kasa gamawa da ƙaninka shine aka dawo kanka ko? to wallahi ko zaka kashe ni yau ko ni ko Rabiatu".


 ganin da gaske take kamar mahaukaciya sabon kamu yasa yasha gabanta,gami da damƙo hannunta ya dinga janta tamkar shara har sai daya kawota cikin ɗakinta,sannan ya cillata ya sanya mukulli ya rufe ruf yana jinta tana ihu tana zaginsa iya ƙarfinta,amman bai bi takanta ba ya ɗakko ƴarsa ya fita da ita ya shiga mota,kao tsaye ya kaita asibitin daya ke kaita akoda yaushe don duba lafiyarta.

da gaggawa suka shiga da ita wani ɗaki.

ya zauna yayi jugum,takaici fal zuciyarsa shin wai wata irin mace yake aure ne? tunda ya auri Balaraba har zuwa rana ta yau bai taɓa farin ciki da aurenta ba,sai dau baƙin cikin dake nuƙurƙusar zuciyarsa,dako kai ƙararta yayi wajen iyayenta sai su goyi bayanta,dama ubanta mijin tace ne sai abinda mahaifiyarta ta tsara shi akeyi agidan.

idan ta cewa uban kar kaje ko nan da can to fa bai isa ya shallake wannan shingin ba tare da sanin uwar ta sa ba.


  ya sharce gumin daya jiƙa masa jiki,ko shafa jikinsa yayi yasan ya rame sosai shiyasa yanzu ko kallon mudubi baya sob ya yi,don yasan ba alkhairi zai gani ba.


yana cikin wannan tunanin wani siririn likita ya fito,ya ce"kai ne mahaifin Khadija ko?".

da sauri ya ce"eh ni ne".

likitan yace"muna buƙatar jini don jinin jikinta ya ƙone baki ɗaya,saboda haka sai ka siya jini anan hospital ko kuma ka kirawo ƴan uwanka don asamu jinin wanda zaiyi dai dai da na ta".

tsabar firgici kasa magana ya yi,da ƙer ya iya juyawa ya fito waje ya rasa me ma zaiyi yaji daɗi,yana cikin wannan tunanin ne wayarsa ta fara ƙara,ya cirota ahankali tamkar wanda ƙwai ya fashe wa aciki.

Muryar Umma yaji tana sababi"wai kai Xubairu wani irin mutum ne? anya ma bakayi hauka ba kuwa? ka kulle yarinyar mutane acikin ɗaki? alhali kuma akan gaskiyarta take".


bai san lokacin da ya ce"akan gaskiyarta fa kika ce Umma? mecece gaskiyarta anan? tana son jawomim masifa ne? saboda son zuciyarta da haukanta,Allah Umma zan iya sakin Balaraba akoda yaushe don dama ba sonta nake ba".


Daga can ɓangaren Umma ta ce"inye ɗan kuka me jawa uwa tasa zagi,yanzu kai Zubairu bakaji kunyar maganar ka ba?,matarka uwar ƴaƴanka kake so ka saka? saboda wata banza wacce ma ko ƙuda bata ajje mana ba? juyar yarinya wacce sai dai taci ta ƙwanta? akanta ne kake wannan haƙilon saboda an taɓani? ko an taɓa Bilkisu da Aisha ƙannenka"?.



ya ce"to Umma ni de indai akan wannan maganar ce gwara in kashe wayata,don ga Nana can ba lafiya yanzu ma ƙara mata jini za'ayi don babu jini jikinta ya ƙone".


 Ai kuwa sai cewa Umma tayi"uhm kaji ko? ai daman bazasu barta da jini ba,Allah kaji ko? ko Balaraba bata ɗauki mataki ba Allah ni sai na ɗauka don idan kai baka san mutuncin kanka da darajarkanka ba to mu munsani,ta inda ƙaninka ya fika kenan? Ahmad bai taɓa bijirewa magana ta,amman kai babu abinda ka sani sai ƙuntatawa waɗanda suke sonka,kake son waɗanda suke cinye muku kuruwa".


 bai kashe wayar ba har ta gama sababinta,don kanta tayi shiru shi kuwa ya fito don siyan jinin sai dai duk jinin da aka gwada babu irin na ta,haka ya haƙura ya koma gida kai tsaye ya ƙwanƙwasa ɓangaren ɗan uwansa.


kamar daga sama naji ana buga sashen mu,nima alokacin na kasa barci na tashi ina sallah ina kaiwa Allah kuka na,ga bakina daya kumbura sosai sai dana ɗan gasa shi da ruwan zafi sannan ya koma normal amman ba kamar yadda yake da ba.


Shi kuwa sai barcinsa yake,na tashi ahankali naje bakin ƙofar tsoro ya ɗan ɗarsu araina na fara magana ahankali"waye anan".

Kamar daga sama na jiyo muryar Yaya Xubair,da sauri na buɗe masa ina ce wa"sannu Yaya Zubair,Allah de yasa lafiya"?.

Ya ce"to lafiyar de ba lafiya ba don Nana ce a asibiti kuma ayanzu haka tana buƙatar jini kuma an gwada na can yaƙi yi,shine na dawo muje da Ahmad ko zaiyi dai dai tunda jininsa O  ne.


da sauri na ce"subhanalillahi,ai ba muga ta zama ba muje har dani sai a gwada don nima O ɗin ne dani banbancin nasa dana wa shi Nagetive ni kuma positive".

ya ce"a a baza ayi haka ba je ki faɗa masa tukunna ya taso".

Nasan zan iya janyowa kaina zagi don haka nace"ba komi muje kawai don yanzu tunda ya fara barcin nan ba tashi zaiyi ba".


  Bai ce komi ba ya wuce muka tafi,duk jikina amatuƙar sanyaye zuciyata cike da tausayin Nana Khadija,don tunda aka haifeta yarinyar har yau bata yi lafiya ba,batz cikakkun ƙwana biyar ba tare da ciwon ya tashi ba.kuma har da sakacin mahaifiyarta don haryanzu bata dena yi wa yarinyar wanka da ruwan sanyi ba,sannan kuma maganinta ma sai taga dama take ba ta,abinci ma sau biyu yarinyar ke ci arana,don dama tuni ta yaye yarinyar wai ita ba tasan yawan takura,uban baya so amman ahaka ta yaye ta babu yadda zaiyi tunda abin a jikinta yake.


 Ashe Hajiya ta fito acikin wannan daren,tazo ta buɗe Balaraba sai kuka take ta faɗo kan Hajiya tana ce wa"ina ya kai min ƴata Hajiya"?.

Hajiya ta ce"yace min suna asibitin da ake kaita wai ba tada jini".

da sauri suka tafi asibitim Balaraba sai kuka take.

Muma alokacin muka shiga asibitin,Balaraba na gani na ta........Soon➡️✍🏽


ga link na facala game nema,bana son maza a grp da ƴan iska ehe😎😂.

***

DFeZycAMeQZ09jYzYRWCX0


#YARIMA

#RABIATU

#AHMAD

#BALARABA

#ZUBAIR


MRS GREEN CE.


SHARE

COMMENTS.


TALLAH TALLAH TALLAH


MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.


Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾


Haɗin Dilka

Haɗin man gyaran gashi

Haɗin sabulun gyaran jiki

Haɗin ƙugu(hips)

Haɗin gyaran (Breast)

Haɗin maganin infection

Haɗin furen zogale

Haɗin tsumin tabaje

Haɗin Kaza 

Haɗin tantabara

Haɗin ƙamshin jiki

Haɗin ƙamshin baki

Ingantattun maganin mata

 

     Bonus

Sirrin riɗi

Sirrin magarya

Sirri magaruwa

Sirrinmu(Addu'oi)


Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga

Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani *** SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.