chapter 27&28
_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*
*_Wattpad:Rabiatu333_*
*_𝘼rewabooks:Rabiattu0444_*
*Ummu maher collection*
***
com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C
*Sirrinmu➡️*
ƴar uwa kina ganin yi wa miji biyayya,ƙauyanci ne? to wallahi shi ne ribarki duniya da lahira.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️27 & 28
........Alhaji Badamasi ya ce"wallahi Hajiya Khaltume ko kaɗan ba kida kirki, yanzu sai da kika sanya yaron nan ya saki wannan yarinyar? Saboda kin tsane ta? to wannan wacce irin tsana ce haka? kada ki manta fa kina da ƴaƴa mata har guda biyu, ɗaya agidan miji ɗaya agabanki idan akayi musu haka za kiji daɗi?"...........
Da saurin gaske ta cafe tare da ce wa"a ah fa Alhaji, ka dena yiwa yarana fatan tsiya ta yaya ma za a haɗa yarana da waccan baragurbin yarinyar? ni ƴaƴana suna da tarbiyya, in sha Allahu babu abinda zai faru dasu sai alheri tunda alherin suka shirya kuwa".
Gyaɗa kai ya yi cike da takaici sannan ya kalleta kallon yaro bai san wuta ba sai ya taka, sannan ya ce"to lokacin da hakan zai faru sai ki hana, sannan kuma gargaɗin da zanyi miki shi ne, ki tabbatar daga nan zuwa gobe yaron nan yaje gidan aminina don ya ɗauki matarsa, idan ba haka ba wallahi kema hanyar naku gidan zaki yi, don ba zan zauna da baragurbi ba ina can ina wahala kan neman halak a kullum ke kuma abinda kika sani shi ne mugunta da son rai, to wallahi ba zai yiwu a agina gidana da haram ba, idan kunne yaji jiki ya tsira".
tunda ya fara maganar ta kafesa da fici ficin idanunta sannan ta kai bango asan sanin dalilin mijinta na wannan maganar? saboda haka ta fara magana cikin fushi.
"Alhaji kana cikin hankalinka kuwa? ni zaka saka akan waccan shegiyar yarinyar? mayya wacce tasha a nonon uwarta? shi ne tsabar mugunta akeson tazo tayi ta lashemu, kamar yadda uwarta ke lashe mutanen gidansu? to wallahi ba zata saɓuba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shekarata nawa da kai baka taɓa ce min ko da jeki zanzo ba, shekara 35 kenan da aurenmu amman shi ne yau akan wannan yarinyar kake min kuri da zaka sakeni saboda ita? to wallahi ga fili ga me doki saura sukuwa, ni kuma zanga ta inda Ahmad zai dawo da wannan mayyar yarinyar"...................
Cafka ya kaiwa bakinta, har sai da tayi ihu sannan ya saketa gefe ta faɗi tana kuka, ya nuna ta da manuniyarsa ya ce " inajin mantani kika yi ko? ko don bakya ganina da kayan soji shi ne duk maganar da tazo bakinki zaki dinga faɗamin? to wallahi yanzu da kuma baya duk ɗaya ne awaje na, zan iya rufe ɗakin nan inyi miki mugun duka sannan kuma in horaki irin horon sojin da yayi lefi, kuma dolenki kibi abinda nake so ko kina so ko bakya so".
yana faɗar hakan ya fice yana huci tamkar ƙububuwa, tana zaune zaman ƴan bori har ya ida ficewa baki ɗaya, wani kukan baƙin ciki ya turniƙe ta wato asirin da ta yiwa mijinta ya karye kenan? Ai da ko musu da ita bai isa yayi ba, amman yau gashi akan wata tsinanniyar yarinya yana zaginta da kuma ci mata mutunci.
a haukace ta tashi ta ɗakko wayarta, ta rasa wa ma zata kira? Sai ta danna lambar ƙanwarta Asabe.
kiran farko ta ɗaga tana mata kirari "kaga mata agidan tsohon soja mazan fama Allah dai ya ƴara miki lafiya da nisan ƙwana". ........
Tun kafin ta ƙarasa maganarta ta ce"ke! Asabe nifa ina cikin matsala ne, saboda haka bana son wani habaici ke ba matar sojan bace da zaki cikani da maganganu".
Asabe ta haɗiye dariyarta, domin tasan duk yadda akayi yau an ɓata da tsohon soja ne.
ta ce"yi haƙuri yaya, ba ni nakar zomon ba....."
tayi ƙwafa sannan ta ce"Asabe yau Alhaji ni ya kalla ya ce wai akan wannan mayyar yarinyar zai iya rabuwa dani? anya kuwa ba asiri suka yiwa Alhaji ba? to wallahi dama wajen da kika je ɗinnan nake son ki rakani, ayi abinda za a lalata rayuwarta kamar yadda ta lalata rayuwarmu".
Asabe ta ce" kinji ko yaya ? wallahi wannan yarinyar ba zata taɓa barinki ki zauna lafiya ba,yo ai daman Yaya tun tuni ke kika ƙi bada haɗin kai, amman yanzu tunda ke kika yi magana gobe da sassafe kizo mu tafi".
hajiya ta ce"Allah ya kaimu Asabe".
ta kashe wayar tana jin zuciyarta wasai, don ko babu komi yarinyar ta shigar mata hanci da ƙudundune, ta hanata gaba ta hanata baya.
*** *** ***
"Malam don Allah ina neman gafararka, abisa son zuciyar da ɗana Ahmad ya aikata akanku, na ɗaukar maka alƙawari in sha Allah komi zai zo ƙarshe daga yanzu zansan ta yadda zan ɓullowa shi Ahmad ɗin"....
tun kafin ya ƙarasa Malam ya tare shi da ce wa"haba Badamasi, wani kuma bada haƙuri? ai ni aganina duk mun riga da mun zama ɗaya, ko da babu wata alaƙa tsakanina da kai ai kai maƙocina ne, saboda haka ka daina ce wa komi kan wannan maganar, ita kuma mamana ya zama dole ta koma gidan Ahmad, tunda dai haryanzun da muke maganar nan ba ce wa yayi ya sake taba, saboda haka ka faɗa masa an jima yazo ya ɗauke ta su tafi".
da sauri ya ce"a ah haba aminina, ya yaya zakace haka? bayan duk Zubairu ya faɗamin cin kashin da yake mata? sai kuma ace ta koma tun yanzu? Ai kaga ba a nuna masa yayi laifi ba kenan? saboda haka yanzu inason a kiramun ita ta faɗamin duk abinda ke faruwa, shima yanzu zan kirasa duk ayi ta ta ƙare idan ma ya gaji da zama da itane sai ya sake ta, don bazan yarda da wulaƙanci ba".
Malam ya murmusa cike da taƙaicin abinda ke faruwa, yadda yake jin Adawiyya aransa abin babu abin ƙwatance aciki, yana son yarinyar ne sosai saboda kaf yaransa babu wacce tayi kama da mahaifiyarsa sai ita, kai hatta maganarsu ma iri ɗaya ce, yana roƙon ubangiji ya fidda ta acikin wannan matsalar.
da kansa ya shigo muna zaune a falon Ammi, tana kallon series ɗin labarina a sabuwar tv ɗin da Abba ya siyo musu, ni kuma ina cin abinci alokacin.yana shigowa na tashi da sauri ina gaidashi, ya amsa min cikin fara'a sannan ya ce"yauwa mamana, ni da babanki Alhaji Badamasi muna son ganinki a babban falo na".
sosai gabana ya yanke ya faɗi, ya fara bugawa da ƙarfi har sai dana sanya hannuna dai dau saitin zuciyata ina kiran sunan Allah. hankulan iyayena ya dawo kai na, Ammi ta girgiza kai cikin tausayawa ta ce" wai ni malam ana aure dole ne? yaron nan ya saki yarinyar nan mana? ko maƙiyana ba zanso ya auri miji irin Ahmad ba, amman tsakani da Allah an hana yarinya sakat, gaskiya ni dai ba zata koma gidansa ba, yaje can ya nemi wata yarinyara ɗaya tilo an sanya min ita agaba , kalli yadda ta zuƙe ta rame ta fita a hayyacinta duk da tana cikin rayuwar ƙuruciyarta ne, shekara 17 ko ashirin ma bata kai ba, a kyale ta haka mana ba sai ya kashemin ita ya bugo yace azo a ɗauke ta ba".
ta faɗi hakan tana furzar da huci, tausayinta ya kamani sosai don tunda nake da ita ban taɓa jinta tayi sa'insa da Mahaifina ba, sai yau da ta gaza ɓoye kunyarta akaina don ba ƙaramin kunyar ƴar fari take dani ba.
Malam ya kalle ta cikin ƙwantar da murya da damuwa ya ce"kiyi haƙuri Zulaiha, ki kuma sanyawa zuciyarki salama akan wannan batun, shi fa aure rai ne dashi sai kiga ke kina nan kina huci da tada jijiyar wuya, ita kuma yarinyar ta ce xata komawa mijinta, to kinga kinji kunya anan ko? saboda haka ina me baku haƙuri da ki cire bakinki cikin wannan maganar".
Da sauri ta ce" in bar maganar ko? tunda bata shafe ni ba ko me? ai wallahi idan kaga na cire bakina a maganar ƴata sai dai idan mutuwa na yi".
Malam ya fara harzuƙa, abinda bai taɓayi ba kula mace idan tana huci sai naga yana ta bala'i har yana maganar indai taƙi yarda na koma to ta shirya bar masa gidansa don ba zai zauna da marajin magana ba.
da sauri na tashi na shiga tsakaninsu, don har mutanen gidanmu sun fara jin komi, don tuni har mama uwar gida ta hallara awajen, tana wani mugun murmushi me cike da fassarori da dama.
na ce"don Allah kuyi haƙuri ku bar maganar nan, duk akai nane iyaye na ke faɗa? duk akan aure na ne kuka samu wannan gagarumar matsalar? don Allah ku yafemin iyaye na ku sasanta kanku, indai kiranka ne Abba zanje amman bana son ganinku cikin wani hali".
Na faɗi hakan ina me fashewa da tausayin kaina dana iyayena.
Malam ya fita cikin matsanancin fushi, har yana tuntuɓe Mama uwar gida ta gama shigowa ɗakinmu, ta ce"Zulaiha wai me ya ke faruwa ne? amman sai naji kamar magana kuke akan komawar ta gidan wannan banzan yaron Ahmad ko? to wallahi kada ki bari ƴarki ta koma masa, don ba dena halinsa zaiyi ba don naji ance ma abin gaba yake don har neman mata ya ke.........."
wata tsawa Ammi ta daka mata, har sai da na tsorata itama maman ta tsorata sosai.
"ke! Jamila, kar nake ganinki munafuka me fuska biyu, wato kinzo kima dariya kina murna nayi faɗa da Malam, to ai ni kinsan a tarihin rayuwata ban taɓa yi ba, ke kuwa wani irin rashin arziƙine bakya masa agidan nan, saboda haka kada ki ƙara sanyamin baki akan auren ƴata, kije kiji da matsalar taki yaran da suka yi miki ƙwantai a ɗaki".
Sosai mama tayi mamakin jin wannan furucin daga bakin Ammi, ta kama kukan munafurci tana ce wa"yanzu ni Zulaiha kika zaga agidan nan? don kina ganin yanzu kin dafa ƙasa da hannayenki? to wallah sai kinsan kin faɗamin magana".
Ammi tayi mugun tsaki ta juya mata baya, ganin taƙi fita ne yasa ta taso da sauri tamkar zata rufe ta da duka, sai ta fita da sauri tana zagin Ammi ni kuwa kallonsu kawai nake, don Ammi ta bani mamaki sosai dama ance me haƙuri bai iya harzuƙa ba, ganin Maman ta fita Ammi ta juyo gare ni tana nuna ni da manuniyarta ta ce"to saura kuma idan sun tambaye ki zaki koma ki ce eh, wallahi daga ranar na raba gari dake kada kiga malam ya ce inbar masa gidansa, kiji tausayina to a halin yanzu ina da gidan da zan zauna idan ya sake ni, daga ni har ke ba zamu tagayyara ba, tunda ina da aiki na saboda haka ki tashi kibi umarninsa kije idan kuma kinje ki buɗe bakinki kiyi magana don kada a ƙara cutarki, don na lura har da sakacinki ma komi ke faruwa".
na tashi na fita duk jikina babu ƙwari, na shiga babban falon Malam na sunkuyar da kaina ina gaida Baba ya amsa yana ce wa"zo kusa dani ɗiyata ki zauna".
Na zauna cikin jin kunyarsa, amman duk kana kallona za kasan ina cikin matsala sai kuwa na jiyo maganar Baba yana ce wa"ƴata daman inason ki faɗamin gaskiyar abinda ya ke tsakaninki dashi, don Zubairu ya faɗamin wasu amman ba lallai yasan wasu ba".
bakina yana kakkarwa na ce"Baba don Allah abar maganar baki ɗaya, bana son tuno abinda ya wuce amman idan hakan ya ɓata maka rai kayi haƙuri".
ya kalleni cikin nutsuwa, don ya gane ina son kare mijina ne bana son faɗin sirrinsa, ya ɗauki wayarsa ya fara kiransa kiran farko ba shi ne ya ɗaga ba, macece ta ɗags ta ce"hello wai waye ne haka ya damu mutane da kira"?.
Sosai abin ya bawa Baba mamaki ya ce"ke ɗin wacece da kike tambaya?".
sai kuwa ta ce"ah kaji min ɗan rainin hankali? kira wayar mutane sannan ka ɓige da tambaya? saboda haka kada ka kuma kiran wannan wayar".
sai kuwa yaji an kashe wayar, da sauri ya kallemu ni da Malam bai san tun tuni naji komi ba, na sunkuyar da kaina wani abu na yimin yawo a ƙirjina, yanzu ace mijina shi ne ya ke neman mata? mijin dana bashi dukkanin yarda ta? na bashi komi na rayuwata? na sadaukar da farin cikina akan na sa? amman yau shi ne ya ke gutsira rayuwata zuwa gunduwa gunduwa?.sai na fashe da kuka me tsanani, don ba zan iya barin arai na ba tunda ina da raguwar zuciya.
Baba ya ce"Adawiyya, ina son ki share hawayenki in sha Allah zan tsaya miki baxan bari ya ƙara damar cutar da rayuwarki ba, tabbas zargin dana ke masa ya zama gaske zan kuwa nuna masa ni ɗin nine ubansa shi kuma ɗana".
dai dai lokacin kira ya shigo wayarsa, ya ɗaga kiran yana me gimtse fuska ya ce"wato Ahmada halin daka faɗa kenan? to babu laifi amman ka sani yau ba sai gobe ba zaka bawa Adawiyya takardarta, sannan duk inda kake kazo yanzu muna nan muna jiranka gidan Malam".
Bai bari ya yi magana ba ya kashe wayar, cike da haushi da kuma nadamar ɗaukar Ahmad a mutum, ashe rayuwar dabbobi ya ke gudanarwa.
*** *** ***
"haba gwaggo, babu wani asirin da ake masa don kuwa da kansa ya shaidamin komi saboda haka ni na yanke shawarar ciresa daga cikin ƴaƴana, don wallahi ganinsa cikinsu zai sa naji na ƙara tsanarsa".
ya faɗi hakan cikin ɓacin rai marar misaltuwa.
gwaggwala ta ce"la ha ila ha ilallahu mahammada rasulillahi, yau naga abinda ya isheni? Au kai yanzu har ka yarda ce wa shi ɗin zai aikata hakan yana cikin hayyacinsa? To wallahi aƙwai wata ƙasa, don duk yadda akayi waɗannan mugayen matan naka biyu su suka shirya komi, amman zan shayar dasu baƙin cikin da suka sanyamu aciki, tabbas wannan mummunan abune ya faru a masarautar nan, sai dai duk da ahalin yanzu wasu sunsan wannan maganar, to ba kowa ne ya sani ba kuma inason ta tsaya anan. amman tabbas yaron nan aƙwai abinda ke bin rayuwarsa wanda mu bamu sani ba, abu ɗaya zan faɗa maka shi ne ka janye wannan mummunan furucin naka akansa, sannan kada ka yarda wannan lamarin ya haifar maka wata matsalar? kai dai abinda zanja hankalinka shi ne ka tsaya da bautar ubangiji, tare da sadaka da nafilfilu idan ma wani ne yayi wannan abin ya koma kansa, idan kuma ba wanine yayi ba Allahu yasa shi ne mafi alkhairi arayuwarsa, kada kuma ka fasa yi masa addu'ah kada kuma ka manta shi kaɗai ne ɗanka namiji, ko don haka za a iya shiga tsakaninku, sannan nan da sati ɗaya ma za a ɗaura masa aure da Amira, ƴar wajen ɗanka don yarinyar da kukanta tazo tana sonsa idan ma rashin aure ke damunsa kaga sai a samu ayi masa, yo daman kun kai yaro lafiyayye ƙasar turawa ta yaya za'ayi ba zaiji sha'awar zama kusa da mace ba, bana mantawa da muka taɓa zuwa dubasa wata yarinya har gida ta biyo sa, amman abinda zai baka mamaki ko kallonta baiyi ba, ƙarshe ma yajawa masu gadin kunne daga baya ma ta dena zuwa, saboda haka bikinsa da Amira nan da sati kuje ku fara shirye shirye".
hankalinsa ya ɗan ƙwanta, don daman shi ajikinsa yana jin anya kuwa babu lauje cikin naɗi? amman shi sam baya san munana kowa zato, saboda haka yasa bai kawo komi ba, don duk mumuni na gari ba zai ɗaukarwa kansa gammon zunubin wani ba........soon➡️
FACCALA NOVELS FANS
***
com/L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA
*NABIHA DATA SERVICE*
kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.
MTN
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
3GB. 900
_____
GLO
500MB. 150
1GB. 300
2GB. 5,50
3GB. 850
_________
AIRTEL
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
5GB 1,200
__________
9MOBILE
500MB
500MB 150
1GB. 250
2GB. 450
3GB. 600
Via:-
5458227606
Nabiyyah Aminu
Moniepoint
my no
***
*MRS GREEN CE*