Chapter -9
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: ***
*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*
✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧
𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
*Talla👇👇👇*
KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN ❓👇👇👇
To kiyi saving numba ta ki danna wannan link👇 *** Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI😍ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI👇👇
1.INFECTION CIWON SANYI 👉LALACEWAR BREAST👉RASHIN HIPS & BUTT👉KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING👉TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?👉 AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only 👌
KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA 👉 KIYI SAVING NUMBER TA DM ME ***
Chapter - 9
KAREEM POV.
8:19am ya nade sallayar da yayi sallah ya aje, sannan ya dauki wayarsa dake ringing ya duba. Ganin number mahaifiyarsa ya saka shi farinciki.
“Hello Momy”
“Ashe zaka dauka, ai na dauka idan an kira ka ma ba zaka dauka ba”
“Haba Hajiya me ya kawo wannan maganar kuma?”
“Yaushe rabon da ka kira ni?”
Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna gefen gadonsa.
“Na kira sai Baba Karami ya dauka ya ce min kina bachi kuma likitocin sun ce a barki ki huta na kwana biyu kar a takura miki, ana son ki samu bachi”
“Wannan ba hujja bace, hakan ai be hana matarka kirana safe da rana da dare ba, kullum sai ta kira ni sau uku ko da ban amsa wayar ba zata ce idan na farka a sanar min ta kira waya, haka ma mahaifinku kullum sai ya kira ta gaishe shi”
Yayi shiru for few seconds sannan ya ce.
“Yi hakuri Momy, Wallahi saboda likita yace a barki ki huta ne yasa ban takura da kira ba, Daddy kuma ina son na shiga this Saturday na gaishe shi”
“To ya dai kamata dai, ina yaran?”
“Suna lafiya Momy, ya karfin jiki”
“Alhamdullahi ina samun sauki, yanzu dai suna gasa min kafafuwan ne, sun ce jinin ya sauka”
“Maa Shaa Allah haka nake son ji, Allah kara sauki ya dawo mana dake lafiya”
“Ameen, Allah ya muku albarka kai da yaranka, Yusura ma Allah ya mata albarka mace ce mai mutumci samun mace irinta akwai wahala yanzu, yarinya ce mai kirki da biyayya duk da kasancewar ta yar'uwa ta kara karfafa zumuncin, bata taba nuna min cewar ba ni na haifeta ba, shiyasa ko da yaushe nake jan kunnenka akan riketa amana, duk da na san kai ma yaro ne mai biyayya da kulawa, Allah dai ya muku albarka”
Sai da Kareem ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya sannan ya amsa da Ameen yayi mata sallama ya sauke wayar. Sannan ya mike tsaye ya aje wayar ya nufi kofar dakin ya bude ya fita, sai da ya fara leka dakin Tine ya duba bata cikin sannan ya rufe kofar ya sauko kasa.
“Ina kwana?q”
Ya gaishe da Yusura dake jera kuloli a dinning. A madadin ta amsa sai ta tambaye shi domin shi da ita ba al'adarsu ba ce gaisawa da juna da safe, kara ma shi ya kan fada mata wani sa'in idan zai fita, ko kuma gaisheta musamman idan yaransa suna nan.
“Wani abu kake bukata ne”
Ya kalli tv domin shi ma ba son kallonta yake ba, yana daga cikin dalilin da ya saka duk yadda yake son tsara gidansa ko tsara zama fa matarsa wannan rashin son, da kuma rashin ba shi hadin kai sai ya wargaza tsarinsa. Ya dauke ba tare da ya kalleta ba ya ce.
“Momy ta fada min kina kiranta kullum ki ji ya jikinta”
“Ba saboda kai nake yi ba, bana bukatar godiyarka, ina yi ne saboda kulawa da ita da girmamata wani abu ne da na saba da shi tun kamin na aureta, aurenka ba shi da tasiri a gurina baka da kimar da zan maka alfarma”
Ya zuba hannayensa a jallabiyarsa ya daga kai ya kalli yadda Allah ya wadata da mazaunai da shape kamar wadda ta yi surgery.
“Me yasa tun farko baki fada mata baki son danta ba, wannan soyayyar karya kike nuna mata”
Ya juyo ta kalleshi.
“Danta ya kasa fuskarta ya fada mata be son matar da ta zaba masa sai ni? Dukan abun da na ke yi ma Momy ina yi saboda Allah kuma saboda ita din uwace a gareni, ta rike ni a lokacin da uwata ta tafi ta bar ni, ta rike ni a lokacin da yan'uwan mahaifina suna wofintar da ni, ta rike ni a lokacin da ban san komai ba, tun bana iya cin komai sai madara har na mallaki hankalin kaina, a hannunta na yi ilmi a hannunta na girma ita nake kallo a matsayin uwa, da Momy zata ce Yusura dauki wuka ki dabawa kanki Wallahi zan daba. Na fada maka duk wannan ne saboda ka san ba saboda kai nake yi ba”
“Ni ma bana fatan shiga alfarma, bana fatan kasancewa a karkashin inuwar alfarmarki, ina jin fiye da abun da kike ji game da auren nan”
Ta tintsire da dariya.
“Na nawa kuma? Ai na gama yi maka alfarma Kareem tun da har ka kasa rike kanka ka keta rigar mutuncina, kuma ka yi nasara har na haifa maka yaya biyu, ka gama cin alfarmata, sai kuma me?”
Ta daga masa gira tana jiran amsarsa. Baya jin zai biye mata su fara abun da suka dauki lokaci ba su yi ba, ta saba fada masa magana marar dadi amman a haka yake hadewa ya danne saboda yana jin shi namiji ne ya fita hankali da tunani, and wani lokacin yana jin kamar ta ci albarka cin yaransa. Yayi murmushi ya sake kallonta ya dauke kai ya juya ba tare da yace komai ba ya nufi stairs.
“Ga breakfast dinka nan”
“Ba a gida zan ci abincin safe ba”
Ta tabe baki ta ja kujera ta zauna tana magana a hankali da muryar da ba zai ji ba.
“Ni dai kawai ina ibada, kuma ina jiran ranar takaba”
Kareem ya shiga dakinsa ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya fara murza jikinsa har yayi wankan ya gama maganar da Yusura ta jefeshi da ita cewar ta gama yi masa alfarma tun da har ya kasa rike kansa har sai da ya kai ga jikinta tana cin ransa. The part that ita bata san duk kokarin kai kansa da yake gurinta yana yi saboda ya bata hakkinta ba is more painful sama da aurenta. Yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya saka hula ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya saka talkaminsa ya fice daga gidan. Ko da ya sauko tana zaune a dinning din tana cin abinci. Be kulata ba ya fice daga falon motarsa ya shiga ya murza key mai gadin ya bude masa yana mika masa gaisuwar barka da safiya. Hannu kawai Kareem ya daga masa sannan ya kama hanyar da zata kai shi gidan abokinsa. Yana kan hanya kiran Safeena ya shigo wayarsa, duba wayar kawai yayi ya aje be sake daukarta ba sai da ya isa gidan Hafiz sannan ya kira ya sanar masa yana waje.
“Shigo ciki mana”
Kareem ya bude motar ya fito ya rike da wayarsa da Safeena ke kara kira. Iskar bakinsa ya busar sannan ya amsa wayar.
“Hello”
“Baka kira ka ce ya jikina ba? Baka yi tunanin ko bana jindadi ba? Miscarriage na yi ba jiya, yanzu baka ma damu da lafiyata ba Kareem?”
“Safeena ina son za mu yi magana da ke face to face amman bana son mu yi magana yanzu sai idan mijinki baya gari”
“Na ji muryarka wani iri, matarka ce ta bata maka rai?”
“Me zai saka matata ta bata min rai?”
“Ban sani ba, amman dai na san nice mai faranta maka a kodayaushe ba tare da gajiyawa ba”
“Ya jikinki.?”
Ya tambaya domin ko da yace be damu da Safeena ba ko lafiyatarta ko kuma yace baya sonta yayi karya.
“Da sauki, ina asibiti yanzu haka”
“Idan kin dawo zamu yi magana”
“Okay i love you”
Ba tare da ya amsa mata da i love you too ba ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sannan ya doshi kofar shiga yayi knocking. Hafiz ya bude masa kofar.
“Shigo mana”
Ya shiga falon kamar marar lafiya.
“Bismillah ga breakfast na san baka karya ba”
Hafiz ya fada yana nuna masa dinning, Kareem ya karasa daman gidan ba bakonsa ba ne. Ya zauna a kujera Hafiz ma yaja kujera ya zauna.
“Yanzu nan ni ma na dawo gida, na sauke madan a gurin aiki”
Kareem ya sauke ajiyar zuciyar dakw bayyana damuwarsa sannan ya ce.
“Hafiz ina cikin matsala, ina jin kamar ina daure da sarka, ina jina kamar ina a tsakiyar hanya da ta kasu na rasa wacce zan bi?”
“Me ya faru bayan abun da na sani?”
Tambayar da Hafiz yayi masa kenan yana zuba madara a cikin tea da already ya saka sugar. Kareem ya fara masa samun cikin Safeena da kuma zubewar wadda shi ya fi damunsa a yanzu. Hafiz ya aje tea cup din dake hannunsa yana kallon abokinsa da mamaki.
“Yanzu abun ya kai jar ciki ya shiga tsakaninku Kareem kuma har ta yi alfahari da haka? Subhanallahi abun ya munana ya kazanta”
Kareem ya dauke idonsa daga barin kallon abokinsa saboda kunyarsa da yake ji.
“Baka ji tsoro ba ace cikin ya zube saboda kishina?”
“Hakan ya ba ni tsoro sosai kuwa, kuma hakan yana nufin idan baka shata line tun da yanzu ba, Safeena zata wuce gona da iri, kuma zata jan yo maka matsaloli da yawa, a cikin idon yarinyar nan na hango rashin kunya da rashin imani, matukar baka takawa lamarinta burki ba zata janyo maka matsalar da baka isa ka fitar da kanka ba, kuma zata jefa duk wadda yake tare da kai a matsala”
Kareem ya sauke ajiyar zuciya.
“Zuciyata na raya min wani abu akan son haihuwa da take da ni, na san tana sona, amman na tsorata da wannan son, idonta yana kokarin rufewa akaina ina jin kamar tana son ta haihu da ni ne a yanzu, saboda a gaba mu kasance tare, ni kuma babu wannan a tsarina ba zan iya auren Safeena ba”
“Idan kuma ta gane haka ba karamar illa zata maka ba, shiyasa nake son ka rabu da ita tun yanzu ka tuba ya canja Kareem, karshen cin amanar da zaka yi shi ne ka bari matar nan ta dauki cikin da bana mijinta ba kuma ta haifa masa yaron yayi hidima da shi, kuma da zarar ta haihuwa zata bukaci ka aureta ne ko kuma wani abun dabam, a yadda na lura bata da kunya zata iya lalata rayuwarka saboda idonta a rufe suke, zata iya maka illar da zaka rasa aikinka ka rasa matarka ka rasa girmamawa daga yayanka kuma ka rasa kima a idon mahaifiyarka da yan'uwanka, duk wata kima da martaba da ake ganinka da ita zata iya zubar da ita”
Kareem ya dauki tea ya sha yana nazarin kalaman Hafiz. Sai da Hafiz ya motsa tea ya sha ta gutsira biredi sannan ya ce.
“Ina yarinyar nan? Ya hannunta Noor ko?”
A take murmushi ya cika fuskar Kareem kamar ba shi ba.
“Ka ma tuna min ya kamata na kira na ji ya jikinta, jiya ta dawo bayan na kaita gida...”
Hafiz ya girgiza kai bayan ya gama sauraren labarin da Kareem ya ba shi na abun da ya faru tsakaninsa da Noor da iyayenta a jiya.
“Mahaifinta yana son abun duniya sosai kuma baya tunanin abun da ya dace, miye abun sadaka a nan?”
Kareem ya tabe baki.
“Ba dan na bashi kudi ba babu abun da zai hana shi dukanta, yarinyar tana ba ni tausayi ga mahaifiyarta ta kai ga nuna mata wuka”
“Kawai tana nuna musu real her ne, su kuma sun ki fahimta”
“Shi kansa saurayin da wahala ya iya handling dinta, yana zuwa ya rufe ta ta fada duk sai na ji babu dadi, shiyasa ma na riga su isa na yi magana da Babanta, sun kasa fahimtarta but with time zata daina, yanayin rayuwa ne kowa da yadda yake tashi”
Hafiz ya kalleshi yana murmushi.
“She's sweet”
“Yeah she's so friendly tana da shiga rai”
“More especially when she meet someone like you, kana son wasa da kiriniya a yadda na sanka Kareem kai mutum ne mai son rayuwar aure da nishadi, kai mutum ne mai son shakuwa da mace, kana yawan ba ni labarin yadda kake son ka yi rayuwar aure da matarka irin na soyayya da kaunar juna da taimakona, idan ban manta ba yana daga cikin dalilin da ya saka kake son Safeena sosai”
Kareem yayi murmushi ya girgiza kai.
“Wannan duk da ne Hafiz, ban da yanzu”
Hafiz ya sake yin murmushi ya cigaba da karyawarsa har sai da Kareem ya ciro wayarsa yana fadin
“Ka tuna min ma, bari na kira Yayanta na ce ya bata na yi mata ya jiki ba mamaki kuma ban siya mata magani ba na manta sam”
“Karka kira, tashi muje mu duba ta kawai zai fi mutunci, kuma sai ka rubuta mata maganin nan daga nan ko ba siya ba sai ka bada kudin maganin”
Kareem ya kalleshi ba dan yana jin son tafiyar ba.
“Why?”
“Zata ta maka complain ne idan baka je ba ai, na lura ita ma tana son kasancewa da kai if not ba zata yi karya tace kai saurayinta ba ne”
Kareem yayi dariya.
“Wato wannan yarinyar ko? Idan baka fahimce ba zaka hau sama ka fado ne ka ji rauni, babu wani son kasancewa kawai tsabar iskanci ne da son nuna ita wata ce ai ta fada min gaskiya”
Hafiz ya aje cup din ya Mike tsaye.
“Ba mamaki abun da muke fata ya kasance ai, shiyasa na kirata da Amaryarmu a gaban Safeena, kuma na san ba zaka kunyata ni ba, ba za ka zabi bangaren Safeena ka bar bangarena ba, ko ba Noor ba dole zaka yi aure Kareem, saboda ka samu gurin da zaka rika jin sanyi, kuma karin sauren zai nesanta ka da wannan zunubin da kake diba, ina fatar dai Momy ba zata ba mu matsala ba”
“Momy bata da matsala da karin aurena, ni din ne dai bana ra'ayin mace fiye da daya”
“Ai shi ya cutar da kai har kuka fada tarko kai da Safeena, auren fari baka auri wadda kake so take sonka ba, yanzu zamu nemi mai sonka mu aura maka”
“Indai dan haka ne, kar muje gidansu Noor yarinyar nan tana da wadda take so, ba kuma zan sake kuskuren auren macen dake son wani ba, na yi na farko saboda biyayya ba zan yi na biyu ba”
“Take so ko dai yake sonta, ai ita bata san so ba a yanzu, kai ka fada min shekarunta fa, kuma kaga yadda rayuwarta take, shi kuma ba lallai yana sonta ba ko kuma zai iya zama da ita, and ba dan wannan zamu je ba, zamu je ne saboda mahaifinta ya maka alfarma idan muka yi haka next time idan ta sake laifi ta gudo gurinka zamu iya ba shi hakuri kuma ya hakura”
Kareem ya bishi fa kallo, ya fi gamsuwa da reasons dinsa na karshe dan haka ya mike tsaye ya bi bayansa. A motar Kareem suka dauki hanya, kamin su isa Kareem ya bi ta wani pharmacy ya siya mata magani ciki har da na zafin kafa saboda tafiyar da tace masa ta yi a jiya.
NOOR POV.
Ban kwanta ba sai da na rama sallah magariba da ban samu yi ba saboda tafiyar da na yi a kafa zuwa gidan Kareem sannan na kwanta a dakinmu tare da Hana, washe gari na farka da asuba, da kaina na warware hannuna saboda alwalar da zan yi na ji azaba sosai amman a haka na daure daman karfin hali rayuwata ce, Hana ce dai da bata saba da wahala ba ta tashi da zazzabi saboda dukan da Baba yayi mata. Mama ita ta yi shararta da safe bayan ta gama hada mana abun karyawa. Ina zaune dakinmu ina ji sallamar yaro Mama ta amsa Baba dake daki kwance yana sauraren redio kuma ya kashe radio yana sauraren abun da yaron yana fada.
“Wai Zafeer ya ce a ga sako a abawa Noor kuma yace yana waje yana sallama da ita”
“Toh shiga ga dakinta can ka kai mata”
Na ji Mama ta fada, sai yaron ya iso bakin kofar dakinmu yayi sallama, na mike tsaye na amsa sai ya shigo rike da katon kwando ya aje min.
“Gashi Wai Zafeer yace a kawo Miki kuma yace yana waje yana sallama”
“Toh”
Yaron ya juya ya fita ni kuma na dauki hijab dina na saka sannan ya bude kular dake cikin kwandon na duba kwai ne soyayye da plantain sai kamshi suke. Na rufe na fita ina jindadi na nufi waje cikin natsuwa, tsaye na same shi rike da wata ledar da ban san meye a ciki ba.
“Baby Noor ya jikin?”
“Alhamdullahi, kai ka aiko min da sako?”
“Eh na yi tunanin ko ba zaki iya cin abun da aka girka ba a gidan na saka aka shirya miki wannan”
“Na gade”
“Never mind, jiya na kwana da tunaninki a raina, na zo Mama tace kin kwanta, jiya ya bani kamar wani abu ya faru dake, sai na kasa natsuwa”
“Lafiya Kalau”
“Kin ji sauki? Ya hannu mu gani”
Na bude masa ya duba cike da tausayawa.
“Noor dan Allah ki daina wannan rashin jin nan bana jindadi yadda abubuwa suke faruwa dake, kuma bana son yadda Mama ko Baba suke miki hukunci, kuma Noor please bana son na sake ganinki da mutumen nan, bana son na sake jin wata alaka tsakaninki da shi”
“Bafa komai tsakanina da shi, kawai shi yace abokina ne wai, na fada masa ina da saurayi ina da wadda zan aura”
Ya daka min tsawa.
“Wane irin aboki? Abota ake mace da namiji ne? Kar na sake jin sunansa ma na fada miki ko?”
“Eh na daina”
“Good karbi wannan magani ne na siyo miki na sha da shafa”
“Toh na gode Sosai Zafeer ina sonka sosai”
“Ina sonki Noor, ina sonki irin son da baki taba tunani ba, irin son da idan na rasa ban san wane hali zan shiga ba”
“Ni ma idan ba kai ba ba zan auri kowa ba”
“Ko ma kin yi auren ba zaki zauna ba, babu wadda zai iya dawainiya dake Noor sai ni kadai, da zaki auri maza dari Noor ba za su iya dake ba sai Zafeer ke tawa ce har abada!!!”
Na yi murmushi ina jindadi shi kuma ya mika min ledar na karba yayi min murmushi sannan yace.
“Allah ya baki lafiya, shiga ciki kar ace kin jima a waje”
“Toh”
Na masa waving na dawo cikin gidan, a tsawon shekara uku da muka yi tare da Zafeer ba zan iya fadar ranar da kaunarsa bata karuwa a zuciyata ba, kamar yadda ba zan iya bayyana yadda yake kaunata ba. Soyayyarmu da shi wani abu mai rikitarwa, duk yadda iyaye suke gajiya da ni shi be taba gajiya da ni ba. Ko da na shiga dakin na samu Hana ya bude wasu abubuwa tana ci, ban ce mata komai ba na dauka ka kasa na cirewa Mama da Baba na su sannan na zubawa Hana na ta na fara cin biredin kamin na fita waje na dauko kofi na zuba tea dake cikin karamin flask na fara tsomawa kamar mai cin tuwo da miya. Ina gama cinyewa wani yaron ya shigo yana sallama da Baba, ina jin lokacin da ya fita be dade ba na ji ya shigo da baki yana kiran a dauko tabarma. Tashi na yi na fara lekawa waje a hankali ashe sara na yi kan gaba, idona ya sauka akan na Kareem dake kallon kofar dakinmu kamar ya san a nan nake rayuwa. Murmushi ya sako min sai na yi saurin komawa na zauna gudun kar Mama ko Baba su ce na yi laifi.
“Noor... Fito ga Alhaji ya zo ganinki”
Na dauki Hijab dina na saka na fito waje n zauna. Na gaishe su cikin natsuwa suka amsa mutumen da ya kira ni da Amarya a office din Kareem ya amsa yana murmushi kamar ya san ni.
“Lafiya Kalau Noor ya jikin?”
“Lfy kalau”
“Waya ce ki warware?”
Kareem ya tambaya cike da kulawa yana kallon hannun nawa kamin ya koma kallon fuskata.
“Idan zan yi sallah ruwa be tabawa”
“Noor..”
Sai yayi shiru wata kila yana gudun Baba yayi min fada ne. Murmushi yayi min sai na sauke kaina kasa ina murmushi.
“Noor me kika ci haka bakinki duk maiko”
Abokinsa ya tambaya sai na kai hannu na taba bakin cike da kunya domin ban san maikon ya bata min baki ba.
“Ai kazamar Budurwa ce nan”
Cewar Baba yana kokarin kunyata ni. Abokin da ban san sunansa ba yayi dariya ya ce.
“Aa Baba mantawa ta yi dai da alama, gashi nan ta gyara muku gida ko'ina an share fes”
A nan kam na yi sa'a Baba be tona min asiri ba, yayi dariya kawai yayi shiru.
“Ni sai nake ganin kamar na sanka, amman dai ba zan iya tunawa ba ashe nan ne gidanka”
“Ikon Allah zai iya yiyuwa ka san ni Wallahi, ai da yake ku masu arziki ba tuna talaka kuke ba, amman na yi mamaki”
Mutumen yayi murmushi yana cigaba da fadar.
“Haba Baba wadda ke da irin wannan gidan za a cewa talaka sai dai mai rufin asiri”
“Yaro ai haya nake a nan ba gidana ba ne, tukuna na dai”
Mamaki ya saka na kalli Baba da sauri jin yana fadar gidan da muke ciki ba gidansa ba ne.
“Allah yayi budi, yanzu kuna biyan nawa a wata kamar wannan?”
“Toh da dai talatin ne, amman wannan shekarar na ji yana fadar zai maida shi dubun hansi, saboda halin rayuwa”
“Allah ya bada yadda za'ayi”
Baba ya amsa da Ameen, duk abub da ake idon Kareem yana kaina, idan muka hada ido sai ya sakar min murmushi. Sai daf da za su tafi sannan ya ba ni ledar magani ya bude ya nuna min yadda komai yake.
“Baba ka bincika, mu ji gidan idan be fi karfinmu ba sai mu siya zai fi biyan haya”
Cewar Abokin yayin da ya kai tsaye, Kareem ya kalleshi da sauri ni ma na kalleshi baki sake ina mamaki Baba kuma ya mike tsaye.