Na Ashirin
by @maikosai53
ƘADDARATA CE A HAKA
©Maryam Abdulaziz_Maiƙosai(Matar Abdul)
P_20
A yadda yake sanarwa da ummin nasa daddaɗan labarin da ya auko garesu sosai ta nuna murnarta. Ba sai ka tambaya ba domin labarin zuciya a tambayi fuska dan ƙarara fuskarta ta bayyanar da tsantsan farincikin jin labarin.
"Gaskiya na yi matuƙar farinciki da jin haka Nasir, na ji daɗi sosai. Kuma haƙiƙa ina so ka riƙe mini Nuriyya tsakani da Allah, kamar yadda mhaifinta ya roƙeka ni ma zan roƙeka bana so ka sake bari ta zubar da hawaye don Allah. Idan har ka zalunceta ban yafe maka ba, domin ina jinta a raina da zuciyata sosai fiye da kai."
"In sha Allahu babu abin da zai sameta, wannan alƙwari ne na ɗaukar muku."
"To Allah ya yi muku albarka" Cewar Ummi.
"Amin Ummina" faɗin Nasir ke nan.
"Yaushe ne za ta tare Ummi?" ya yi tambayar yana sosa ƙeyarsa.
Yadda ta fahimci maganar ta sa da gaske ya yi ta, ya sanyata itama haɗe fuska domin ya ɗauki maganar da za ta yi masan da gaske take yi ita ma ta ce,
"Sai nan da wata huɗu, na za ta ita Nuriyyan ta sanar maka ai?"
A firgice ya ɗako ya kalli Ummin, yana son yin magana amma ya gaza domin yadda ta tsare shi da idanuwanta sam ba zai iya yin musu da ita ba. Tamkar ɓarawo haka ya miƙe saɗaf-saɗaf ya fice daga falon. Shi kam har ga Allah Umminsa ta zo masa da wani abu wanda zai iya cewa babban cikas ne a wajensa. Allah ya gani a matse yake da yaga ya zauna a Nuriyyansa waje guda.
Har ga Allah umminsa ta matsa masa sosai, don dai kawai babu yadda zai yi ne, ba kuma zai iya musanta mata ba ko har ya sa ya yi jayayya da ita a matsayinta na wacca ta kawo shi wannan duniyar. Sai tabbas dole ta sa ya ɗau mataki kan Nuriyya tunda har ba ta tausaya masa ba ta amince da batun ummin tasa. Kai tsaye wajen Ahmad ya wuce zuciyarsa a matukar kuntatace.
Ganin irin yadda yanayin fuskarsa ta sauya ya sanya Ahmad tuntsirewa da maɗaukakiyar dariya, cike da tsokana ya soma furta. “Ango ka sha kamshi” wani takaici ne ya kume Nasir, cikin ƙanƙanin lokacin ya jefa mi shi wani irin kallo tare da jan yauƙaƙƙen tsaki.
Ahmad ya ɗan dafa kafadar shi tare da sake furta. “Sorry aboki yaya dai? Me ke faruwa?”
Al’amarin da ya sanya Nasir wurga mi shi wata uwar harara kafin ya kai ga cewa.” To mene ne ma bai faru ba? Wallahi matsawar ta yi haka ne domin cutar da zuciyata ni ma sai na rama, sai na ɗau babban matakin da za ta gane cewa akwai bambanci tsakanin maɗi da zuma.”
“Wai me ya faru ne? Ka sanar da ni ba wai ka tsaya kana yi mini kwanakwana ba.” Cewar Ahmad.
Tsaf ya kwashe klomai tsakaninsa da ummi ya sanar masa. Abin da ya haifarwa da Ahmad kwashewa da dariya ke nan.
“Na wawo! To me ya yi zafi haka? Ita fa ba ita takai zomon ba rataya aka ba ta me ye kuma za ka ce za ka ɗau mataki a kanta? Ni a ganina ummi ta yi daidai, domin ka san dai gaba take da mu, kuma duk abin da yaro yake hange bai kai na babba ba. Ka yi hakuri da sannu komai zai wuce, wane irin ƙalubale ne baka shanye ba sai wannan kuma?”
Ya sani har ga Allah Ahmad ya fi shi gaskiya, to amma shi fa sam baya jin zai iya haƙurin kin kasancewa da Nuriyya ba.
“Ta shi muje” ya ji ya yi furucin.
“Zuwa ina fa?” Ahmad ya jefa masa tambaya.
“Wajen Nuriyya” ya ba shi amsa da haka.
Dariya Ahmad ya saki, ba tare da ya musanta mi shi ba, mota suka faɗa tare da wuce gidansu Nuriyya kamar yadda Nasir ya bukata.
A falon gidan suka sami masauki, Nuriyya ta shigo hannunta ɗauke da matsakaicin faranti mai ɗauke da kofuna guda biyun da ke zube da ruwan lemon tsami. Ta ajjiye gabansu yana mai matswa gefe tare da gaisar da su.
Ko kallon inda take Nasir bai yi ba, shi ala dole fushi yake yi da ita. Ahmad na kallon shi ta wutsiyar ido, dariya ya yi mai kama da murmushi.
"Na ce ko na tafi ne? Na ga kamar ba a yin maraba da zuwana." Nuriyya ta ce cike da tsokana.
Abin nema ya samu, matar falke ta haifi jaki! Tuni Ahmad ya yi katsalan ya ce.
"Kin ga yi tafiyarki Nuriyya don da alama wannan zuwan bana ki ba ne." ya ƙarasa yana kallon Nasir.
Wani wawan kallo Nasir ya aikawa Ahmad shi, yana mai taɓe baki kafin ya karkace baki ya ce.
"Jeki ɗin, wallahi na lahira sai ya fi ki jin daɗi" ya ƙarasa yana yin ƙwafa.
Kusan a tare suka kwashe da dariya tsakanin Ahmad da Nuriyya.
Fuskarsa a murtuke tamkar damammiyar fura ya sake kai dubansa gareta ya ce.
"Shin da saninki Ummi ta ce ba yanzu za ki tare ba?"
Ta yi ɗan guntun murmushi kafin ta ce. "I mene ne?"
A matuƙar bazata ya sake kai ganinsa gareta, yana mai mamakin yadda ta ba shi amsa kai tsaye, lallai ma wato sam ba ta tausayinsa. Ganin irin kalon da yake bin ta da shi ya sakata saurin faɗin.
"A ganina iyaye sun fi mu sanin abin da yafi dacewa da mu, don haka bai kyautu mu ƙi amsar abin da suka zo da shi ba, idon mun yi haƙuri lokacin ba mai tsawo ba ne, ka yi haƙuri kada ka ce za ka yi jayayya da mahaifiyarka."
Ji yake zuciyarsa na yi masa suya, yana jin kalamanta tamkar garwashin da ke ƙona masa farfajiyar zuciyarsa, sai dai tabbas ya san tafi shi gaskiya domin maganar iyaye ba abar banzatarwa ba ce ba. To amma me ya sa kai tsaye ummin za ta zartar masa da wannan tsattsauran hukuncin?.
"Ka ga ka yi haƙuri ka sakawa ranka salama, kamar yau ne fa." Ahmad ya ce yana mai dafa kan kafaɗarsa.
Ture hannun ya yi haɗi da jan tsaki A ƙufule ya miƙe ya fice daga falon zuciyarsa a cunkushe.
Yana fita Ahmad ya kalli Nuriyya ya ce. "Kada ki damu na san zai sakko, duk cikin ɗoki ne. Yauwa don Allah ni kam so nake a yi mini iso wajsn Munira domin yasin zuciyata na gab da fashewa."
Nuriyya ta ɗan yi murmushi kafin ta kai ga cewa. "A'a babu ruwana, ka tafi kai tsaye gareta kawai." Tana gama faɗin haka ta miƙe tare da ficewa daga falon, Ahmad ya saki wani guntun murmushi tare da bawa falon baya shi ma.
"Munira kin san me?" Nuriyya ta katse Munira daga kan karatun littafin da take yi. Ta ɗago da kanta ta kalleta tare da ba ta amsa da. "A'a sai kin faɗa."
Nuriyya ta ɗan saki wani guntun murmushi kafin ta kai ga cewa."Hm! Kin san wai fushi yake yi da ni saboda Ummi ta ce ba yanzu zan tare ba kuma na amsa mata."
Munira ta muskuta kafin ta kai ga cewa."Karki da mu, da sannu zai fahimceki kuma ya sakko, ai ya san dai babu wanda a isa ya ja da umarnin iyaye!"
Nuriyya ta ɗan sauki ajjuyar zuciya, kafin ta furta. "Haka ne. Allah ya sa ya sakko da wuri."
Ta ɗan numfasa kafin ta sake furta. "Ke! An ba ni saƙo fa, amma na ce ya zo kai tsaye gareki." ta ƙarasa tana sakin dariya.
Yayin da Munira ta gyara zamanta sosai tana kallon Nuriyya ta ce. "Bangane ba, ki yi mini bayani dalla-dalla malama"
"Dalla! Ba fa wani dogon abu ba ne ba, saƙon dakon soyayyarki aka ba ni, aka ce na gaya miki wai zuciyar na daf da fashewa."
"Waye?" Munira ta yi tambayar.
"Waye kuwa ban da Ahmad" Nuriyya ta ba ta amsa tana mai shigewa uwar ɗaka, tare da sakin dariyar shaƙiyanci. Ita kuwa Munira sakoko ta yi tana bin Nuriyya da kallo.
***
Cikin shiga ta riga da wando take, rigar babu maraba da ba a sakata ba, ta yane kanta da wani ɗan guntun gyale, bakinta kuwa cingum ne sai tauna shi take yi ƙaras-ƙaras! A wani irin babake ta kalli Idris kana ta ce.
"Wai kana nufin ka ce mini kai ba ka san abin da ke faruwa ba?"
"Me ya faru?" ya jefa mata tambaya madadin ya ba ta amsa.
"Ba ka da labarin auren Nasir da Nuriyya? Ba ka da labarin sake mayar da Baffanta koto don sake wata shari'ar kuma duk Nasir ne ya shirya haka?"
A matuƙar firgice ya ɗako ya kalleta kafim ya kai ga furta. "What? Garin yaya haka duk ta faru ban sani ba? Wane irin sake na yi haka? Lallai ya kamata na tashi tsaye domin yanzu ne wasan zai fara, idon sun san wata ai ba su san wata ba"
"Calm down! Kada ka damu komai zai yi normal. Yanzu zan je Abuja zan yi mako biyu amma da na dawo sai mu fara aiwatar da ƙudurinmu, ko ya ka ce?" ta ƙarasa cike da tambaya.
"It's normal! Ni bawai akan shari'arsu nake fifiƙa ba, ina so ne ko ta halin ƙaƙa naga sun rabu, me ya kamata na yi?"
Wani irin kallo ta jefe shi da shi kana ta ce. "Ni da kake gani na fi ka kaiwa ƙolokuwar damuwa da kasancewarsu abu guda, ba kuma za ka fini sanin abin da zan yi ba, na nemi haɗin kanka ne domin don dai kai kawai namiji ne. Kamar yadda na ce ka bari ɗin na dawo"
"Shi ke nan, sai dai ba na fata ki yi daɗewar kiwo a can."
"In sha Allah! " ta ce da shi tana mai faɗawa cikin motarta.
***
Yau kimanin kwana biyu shiru Nasir babu alamunsa balle aga ko da inuwarsa ce. Al'amarin da ya yi matuƙar tashin hankalin mutane biyu wato Ummi da Nuriyya Idan an kira wayarsa ma a kashe. Gaba ɗaya Nuriyya ta susuce ta burkice ta zama wata iriya.
Kiran Ahmad Ummi ta yi akan yazo tana son ganin shi. Ko da yazo bayan sun gaisa tambayarsa ta shiga yi kan Nasir. Sai dai sosai ya cika da mamaki jin bayanin Ummin, ke nan fushi ya yi? To ina yaje? Ya shiga jerantawa kansa mabambanta tambayoyi.
Wasa-wasa har aka yi kwana uku babu alamun Nasir, al'amarin da ya sake ɗimauta Nuriyya ke nan. Ummi kuwa tuni ta sake shiga cikin damuwa da tunanin abin da ya sama ɗan nata.
Maiƙosai