1
by @halimahz
*Ina farawa da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Ƙai.*
_______________________________
*ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....kazalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai da ke cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana ya ke tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shi ne; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine me cece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!...*
*Kano, ƙarfe uku na Yamma.*
Sanye na ke da maroon hijab wanda ya ɗauki kyawuna matuƙa, a yayinda Farhana ke yafe da ƙaramin gyalenta wanda itama yay ma ta kyau sosai. Cikin takun natsuwa da hankali muke fitowa daga cikin Sahad Store da ke nan anguwar zoo road. Ledar hannun Farhana kawai zaka kalla ka gane cewa ba ƙaramar siyayya ce muka yi ba. muna tafe muna magana a cikin nishaɗi, duka idanuwanmu kewaye da gilashi, sai dai akwai banbanci a tsakanin gilashina da nata, domin nawa na magani ne wanda ake kira da medical glass, ciwon idon da na gada a wurin Kakata mahaifiyar Abbana, ita kuma Farhana na gayu ne, wanda bata rabo da shi a kullu yaumin.
Zuwanmu bakin jar motar da ta ke mallakin Farhana ce muka tsaya, sannan Farhana ta buɗe booth ta sanya ledar kayan hannunta, tukunna na buɗe gaban motar na shiga, bayan Farhana ta rufe booth sannan itama ta zagayo ɓangaren mazaunin driver ta shigo ta zauna tana yiwa motar key.
"Wash Sister wallahi na gaji da yawa yau, kai ni kam sai na kwan biyu ban kuma zuwa wani biki ba". na faɗa a sa'ilin da na ke kunna Ac'n motar.
"Yanzu ai zamu ƙarasa gida, nima da kika ganni duk a gajiya na ke, buƙatata kawai na jini cikin shower".
Cewar Farhana tana karya kan motar zuwa kan titin da zamu hau. na ƙara cewa,"ke kin san ma za ki samu ruwa a gida, ni yanzu na koma da wuya idan ba sai na fita neman mai ruwa ba, saboda anguwar mu muna cikin matsalar ruwa...Gwamnati gaba ɗaya bata tausayin rayuwar talaka, ba wuta ba ruwa a inda talaka bawan Allah ke rayuwa, kai Allah kayi mana magani".
Na numfasa kamin na ƙara cewa,"Allah sarki Gwaggona na san yanzu tana can tana tsumayin dawowa ta, kuma kin san fa sai da ta ce ka da na jima".
Farhana ta ce,"kinga ba wannan ba ma, ni damuwar ma Allah yasa mu tarar da telan nan yana shago, kar musha wuyar banza ga wannan uban go slow ɗin, kalla fa tun ɗazu danja ta ɗaga amma har yanzu motoci sun gagara wucewa".
"To amin dai, Allah ya nufemu da rutsa shi".
Na faɗa ina yatsine fuska alamar gajiya sosai a tare da ni.
Direct sharaɗa muka wuce shagon da Momin Farhana ta aikemu amso ma ta ɗinki.
Ba ƙaramin takaici muka ƙunsa ba da muka je ba mu samu me ɗinkin ba, tsabar haushi ma ko jiran yaron shagonsa da ke mana bayani bamu yi ba muka fice dukkanmu rai a ɓace, dan ni har ji nai kaman na gwaɓe bakin saurayin da na san ƙarya ce kawai yake gilla mana.
Tun fitowarmu daga shagon na ke ta duban jefi-jefin jama'ar da ke layin, kasancewarsa layi ne da bai tara mutane ba, sai ƴan tsirarru haka, unguwa ce bata masu kuɗi ba amma kamar wata babbar estate shiru kake ji.
Nace da Farhana,"Ni kam ki yi sauri mu bar layin nan ina tsoronsa, kin san yanzu kidnappers sun yi yawa a gari, mutane ba tsoron Allah".
Itama tace,"hmmm sauri ai ke ce zance ki yi, kina tafiya kamar ba za ki taka ƙasa ba, kee ni ko dai kina da matsalar ƙafa ne?".
Nayi mata hararan wasa sannan nayi murmushina mai sanyi ba tare da na ce ma ta komai ba, muka ci gaba da tafiya hannunmu riƙe da na juna kace mu tagwaye ne, sai dai muna gab da ƙarasawa inda mu kai fakin naji ƙafafuna sun tsaya cak daga tafiyar, yayinda hannuna ya zame daga cikin na Farhana, na bi gefen haguna da kallo kafin naji ƙafafuna na jana suna tafiya da ni zuwa wani wuri, wani wuri da ban san me zai iya faruwa ba idan na riske shi, na bar Farhana naci gaba da tafiya tana ta maganarta ita ɗaya duk tunaninta tare muke.
Sai da tayi gaba sosai sannan ta fahimci tafiyar tamu ba tare muke ba, ta waigo da kanta sai kawai taga babu ɓurɓushina ma a wajen, kuma a wannan lokacin ɗaga idon da za tai can gefe ta hangeni ina tafiya cikin sauri-sauri har ina harɗewa, saurin da a duniyarta zata rantsewa duk wani mahaluƙi bata taɓa ganin nayi shi ba tun yarintarmu.
Tsananin mamaki sai yasa ta riƙe haɓa.
"Sabina! Sabina!! ke Sabina wai ina ki ke neman zuwa haka? bola fa naga kina neman shiga, wai kin yi hauka ne? Keee!!".
Zan iya cewa a sama-sama naji abunda ta ke cewa, dan haka hannu na ɗaga mata ta baya kawai ba tare da na yi yunƙurin tsayawa ba, kuma zagin da ta ƙunduma ta wurgo min shi yasa ni ɗaga ƴar muryata ina cewa da ita,"Farhana ba fa bolar zan shiga ba, ki biyo ni ko ki jira ni yanzu zan dawo".
Farhana ta sauke numfashi tana zubawa sarautar Allah ido, tabbas banda ta san wace ƙawarta lallai zata iya cewa aljanu ne da ita ko kuma tana da ciwon hauka ne, amma a yanzun ma ba zata ƙi cewa Sabina ta samu matsala ba. Gani tayi sam ba zata iya barinta ita ɗaya ta shiga cikin wannan bolar da shigarta babu abinda mutum zai kwasowa kansa fa ce musiba, hakan yasa ta bi bayanta itama cikin sauri, abunda ya ƙara bata mamaki kuma hangenta da tayi ta tsaya gaban wani mutumi da ke zaune saman bulon wani kango a jikin bolar.
Farhana tayi turus ta tsaya domin ita kuwa al'amarin ya fara bata tsoro, gwara ta tsaya daga nan ɗin idan taga abin bana tsayuwa bane sai ta arta ana kare, domin ta fara tantama da lafiyar ƙwaƙwalwar Sabina.
Saurayi ne kyakykyawa na ajin ƙarshe zaune saman bulo a bakin wani kango, shekarunsa za su kai ashirin da bakwai zuwa da takwas, shi ba fari ba kuma shi ba baƙi ba, haskensa dai-dai misali, jikinsa sanye da yadi me arha ruwan madara wanda ya amshi jikinsa, a kallo ɗaya zaka yiwa kayan jikinsa ko da ace daga nesa ne ka gane cewar yadin a koɗe yake, irin koɗewa da jemewarsa su ka gaji da duniya, duk ya farfashe ya yayyage, koren silifa ne ɗan madina wanda duk ya suɗe sanye a doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu, Kansa a ƙasa yake hannunsa riƙe da taba sigari, cikin ƙwarancewa ya ke zuƙa yana fesar da hayaƙin ta gefensa. zai kuma zuƙa kenan yaji an ƙarɓe ta daga hannunsa, ya ɗago jajayen idanunsa domin ganin mahaluƙin da ke da ikon karɓe masa abokiyar rayuwarsa.
Idonsa ne yay tozali da ƴar kyakykyawar budurwa tsugune gabansa, tana sauke masa kyakykyawan murmushi, da wannan idanun nata masu zurfi, kallo ɗaya yay mata yayi saurin ɗauke idonsa saboda faɗuwar gaban da ya tsinci kansa a ciki, ba tare da sanin dalilin hakan ba, kuma haka kawai sai yaji ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri abinda bai taɓa riska ba tsawon shekarun rayuwarsa.
Ina lure da shi da yanda yake bina da kallo ta ƙasan ido, wucewar sakan ɗaya, biyu, uku, ya ɗago da kansa gaba ɗaya yana sauke kallonsa dukka akaina, har yanzu ban bar yi masa murmushi ba, hakana ban ɗauke idona daga ƙwayar idonsa ba da ke haskawa da ƙyallin mamakina ba, kuma zan iya rantsewa a wannan lokacin abinda yake rayawa acikin ransa shine _ko dai ni mahaukaciya ce? Ko kuma ba mutum ba ce? Ko kuma nima irinsa ce?._
Na gyara zaman glass ɗina sannan nace da shi,"Hy Mr Man".
Na faɗa ina ɗaga masa gira sama, sai dai shi idonsa na kan sigarin da ke hannuna da ban yar da ita ba, sai na kalli sigarin tukunna na maida kallona kansa kamin na shiga ce masa.
"Wannan tana cutarwa, ba ta amfanar da mai shanta, Almubazzaranci ce, tana cutar da na kusa da kai. a bisa haka Malamai suka ce tunda duk abinda ta ke haddasawa haramun ne to itama ta zama haramun".
Ina gama faɗa na jefar da sigarin a ƙasa, na ta ke da takalmina, sannan na maida glass ɗina da na cire bayan na goge shi. yaji sanda iska ta ɗebo abunda tace ta shigar cikin kunnensa, kuma yaji yanda kalaman na ta suka samu zama a cikin kansa, ya tantance maganartata cikin kowanne futar harafi, sai dai ya kasa tantance zaƙin sautin da ya fita a cikin amon muryartata, ba sau ɗaya ba ba sau biyu yana jin maganganun aljanu a cikin wannan bolar, sai dai tunda yake ji bai taɓa jin sautin murya me zurfi da daɗin saurare irinta ba.
Ni kuwa ƙura masa ido sosai nayi ko tsoronsa ma banji, kuma shi ma sosai yake kallon ƙwayar idona, sai dai Allah masanin gaibu, dan ban san me zuciyarsa ke karanta masa ba akaina.
Sai kawai na ƙara murmusa kuncina a karo na babu adadi, tare da harɗe hannayena a ƙirji ina faɗa masa abunda bai tambayeni ba, haka kuma babu nuni na yana baƙatar sanin hakan.
"Sunana Sabina Auwal, anan garin kano nake. And you?".
Awannan lokacin abinda Sabina bata sa ni ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewar_Ba Mutum ba ce._
Bai bani amsa ba, babu kuma yunƙurin hakan a tare da shi, abu ɗaya ne kawai ke ɗawainiya da ni, aiwatar da wasu abubuwa da ba na sanin lokacin da na ke yinsu...matsowa kusa da fuskarsa nayi, na ɗaga masa kai alamar ina jiran cewarsa akan tambayar sunansa da nayi.
Ssai naji shi da saɓanin abunda na tambaye shi ɗin.
"Me yasa ki ka faɗa min sunanki bayan ban tambaye ki ba?".
"ka fara bani amsar tambayata tunda ni na fara".
Na faɗa ina ɗan karayar da wuyana. A hankali naji muryarsa na fita, kuma a lokacin so nake na toshe hancina saboda warin sigarin da ke fita a bakinsa, amma na kasa saboda bana so na nuna masa ƙyama.
"Duk da bana jin yaren da kika yi min tambayar, amma zai iya yiwuwa na fahimta. in dai yanda na fahimci tambayar taki ne to ni ba ni da suna, kuma ba ni da sunan Baba, ban san kuma garin da na ke ba, abinda kawai na sa ni bani da Asali kuma ba me Asali ba ne sannan bana buƙatar shigowar kowa cikin rayuwata".
Kawai na saki baki galala ina ƙare masa kallo da maɗaukakin mamaki, kuma ƙwayar idona na haska masa da cewar ban yarda da abunda ya faɗa ba.
"Tun ina ƙarama kamin Mama nah ta rasu, ina tunawa kamin ta rasu ta gaya mun babu kyau ƙarya, don haka kar na yi kuma kar na koyi yinta, kuma kar nayi tarayya da me yinta. Sannan da na girma, Gwaggo nah wata rana ta yiwa Yaya nah faɗa cewar ba'a so Babba yana ƙarya, ƙarya na zubar da girma da darajar mutum. Dan haka kaima kar ka yi ƙarya kaga babba ne kai, kuma ni yarinya ce, idan kayi zan koya a wurinka, kuma na san ai ba zaka so hakan ba ko Yaya?".
Ina masa maganar ne da yanayi irin na yara shawagaɓaɓɓu.
"Me ya kawo ki nan wurin?". Ya tambayeni yana mai tsare ni da ido da alamu na tuhuma.
Na tsarota sosai, tsoro ainun da amon muryarsa da kuma kallonsa, haka kuma tsoron bai sa na yi masa ƙarya ba, na faɗa masa ainihin abunda ya kawo ni. "Na zo ne domin na hanaka shan sigarin da ta ke haramtacciya a addininmu".
"To ki tashi ki tafi, ni ɗin ba na son kowa a kusa da ni, ki tafi kar naji miki rauni,babu ruwanki da abar da na ke sha".
Yanayin da yay maganar kuma ya ke dubana ba ƙaramin kaɗa ƴaƴan cikina yay ba, ina kallo ya zura hannu a aljihu ya ɗakko kwalin sigari ya buɗe ya ɗauki ɗaya, sannan ya ƙyasta laita ya kunna, zai kai baki kenan na miƙe da zafin nama na ƙwace ina yin jifa da ita. kamar zan fashe da kuka nace,"Don Allah kar kasha, ba zan iya ganinka kana shan abunda zai cutar da kai ba, ni bana son ma ganinka anan, kazo mu bar nan wurin don Allah".
Na faɗa ina kamo hannunsa don mu tafi. a tsawace yace da ni,"kar ki ƙara cemin Yaya, ni ba Yayanki ba ne, kuma kar ki ƙara taɓa ni tunda kin san halak da haram".
"Shikenan ba zan kuma ba. Amma sai ka faɗa min sunanka idan ba haka ba ni kuma ba zan daina ce maka Yaya ba, tunda kai ɗin ka girme ni ka yi sa'a da Yaya Abba, tarbiyar gidanmu bata koyar damu faɗan sunan na gaba damu ba gatsal".
Ƙwace hannunsa yay anawa yana doka min tsawar da tasa naja baya babu shiri, yana faɗin,"ki tafi ki barni ko. Nace miki bana da suna bana kuma da sunan Baba, banda kowa, na tsinci kaina ina rayuwa ne ni ɗaya kawai, ba na so kowa ya raɓe ni...dan haka bana son kuma jin maganarki anan wurin ki wuce ki bar nan".
Ni ban sani ba, kuma ban ta ya ba, amma haka kawai na ke jin hannuna na kaiwa ga nasa. Na kawar da tsoronsa ina kuma kamo hannunsa da yake ɓoyewa ta bayansa, roƙonsa na ke kamar sabuwar mayya, kai kace na san shi ina da wata alaƙa babba da shi, sai ce masa na ke,"Yaya kar kayi fushi ka duke ni, na maka alƙawarin ba zan kuma tambayan sunanka ba tunda baka so. Amma yanzu ka zo mu tafi gida, zamanka anan zai cutar da kai, ga warin bola ga sigarin da kake sha, abun yayi yawa".
Cikin wata razananniyar murya ya ƙara ce min. "Shekaruna goma sha biyar ina rayuwa anan Wurin, anan na ke yini na ke kwana, sigari ita ce abincina kuma ita ce abokiyar rayuwata, Allah shi ke tallafe da rayuwata, maƙociyata da nake jin daɗin mu'amala da ita wannan bolar, warinta shi na ke shaƙa naji daɗi. Duk tsawon wannan shekarun ban cutu ba sai a yau da kika zo?, to wace ke? me kika isa ki sauya a rayuwar da Allah ya tsarata a haka tuntuni?...kinga ki shige ki tafi ki bani wuri tun ban maki rauni ba".
Tsantsar tausayinsa naji ya kamani, da wani firgici da kalamansa suka haifar min, saboda ganin yanda damuwa ta daɗa bijirowa a saman fuskarsa, har yana maganar tana rawa kamar zai fashe da kuka saboda ƙuncin rai. sai na sauke kaina ƙasa ina goge ƙwallar da ta tarar min, wucewar sakanni uku na ƙara kamo hannunsa naja shi da ƙarfin da Ƙafafunsa ba su iya yin gardama ba. Yayinda a lokaci ɗaya naji ihun kukan jariri na ƙwala ƙara a cikin kunnena, ƙarar kukan da ya sani saurin gimtse ido, tare da damƙe hannunsa da ƙarfi babu shiri, inda hasken hoton wani jariri ke giftawa a cikin duhun idanuna, sai naji kaina na wani mugun sarawa da wannan tsala kukan da jaririn yake yi.
Wani abu da ban fahimta ba a lokacin shi ne; wataƙila anyi amfani da gatari ne wajen sara shi a tsakiyar kaina ya rabe gida biyu, ta yanda yin gaba da komawa baya zasu gagara a tare da ni, ta yanda zuƙar numfashi da fitarsa ba za su ƙara wanzuwa a tare da ni ba.
___________________________________
_Hey Guyz how are you doing? Hope you are all doing fine. how was the first charpter? loving the story already bah? encourage me by comments and voting, thats the only way i will know my effort is beaing appreciated...it's not a new story buh an old story am updating, i just changed the story title da sabunta labarin, kuma no disappointment a wajen posting in sha Allahu☺....ina fatan zan samu haɗin kanku daga farko har zuwa ƙarshe. Allah ya bani ikon gamawa lafiya, amin Ya Rahman...As i Promise you ba zan yi delaying ma ku posting ba, so you people ma kar ku ji ƙyashin yin react, vote da comment.👏👏_
#React,Vote,Comment
#Al-hussainBook1
#Gamjiwriter's
#Teamfitattubiyar
#2024
#February
#Share
#***
#Halimahz
#Purchase₦300