2
by @halimahz
*(2)*
kusan daƙiƙa huɗu kaina na juyawa kafin na iya sakin hannunsa na ɗan matsa gefe da shi na dafa jikin gini. Sama-sama na ke jiyo muryan Furhana na faɗin,"wai Sabina kin san shi ne?".
Ta faɗa tana ƙarasowa inda na ke. na buɗe idona da ƙyar na dubeta ina cewa,"A'a ban san shi ba, ban ma san waye ba".
Cikin ƙarfin hali nayi magana ina daɗa dafe kaina, ta matso kusa gare ni da tashin hankali tana dafa kan nawa ta shiga jera min tambayoyin,"lafiya?".
A wannan lokacin babu abinda na ke so irin a cire min kaina a dire shi a gefe, in yaso a barni naci gaba da rayuwa a haka idan da yiwuwa kenan, idan kuma har cire kan zai zama silar rasa raina to tabbas zaifi min sauƙi a cire shi dan na rabu da wannan tsananin sarawar da yake min, da kuma amsakuwar kukan jaririn da har yanzu ban bar jinsa ba.
"Na shiga uku menene naga kina dafe kai? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...kinga abinda kike neman jawa kanki ko Sabina, ni uban me ma kika gani da kika yo cikin bola sai kace wata mahaukaciya".
Muryar Farhana na fita ne cikin faɗa sosai da kuma tsananin nuna kulawa gami da matuƙar nuna damuwa akaina. magana na ke so nayi amma na kasa, sai laɓɓana da ke aikin yin rawa, ko idona da ke buɗe kaɗan dishi-dishi na ke gani da su, jiri ya ɗebeni na nemi na zube a wajen, tayi azamar riƙe ni ta zaunar akan bulo ɗin da Yaya ya tashi.
Hawayen azaba ya shiga min sintiri a saman fuskata, Farhana kuwa bana kallonta amma a yanda muryarta ke fita da rawa na san kuka ta ke na kiɗima, ta kama kaina tayi min adu'a, sannan ina jinta ta miƙe tana surfa zagi da bala'i ga bawan Allah'n da na san ba shi da hannu a wannan halin da na shiga.
Ta dage akan sai ya faɗa mata abunda yayi min ko kuma ta kira masa ƴan sanda yanzun nan, shi dai bai saurareta ba dan banji yayi mata magana ba.
Kuma haka ta ƙyale shi ta dawo kaina duk a ruɗe tana ƙara faɗa masa wallahi komai ya same ni sai inda ƙarfin shari'arsu ya ƙare ita da shi, dan ba zata ƙyale shi ba. Da ace ta san irin azabar da na ke ji acikin kaina, da kuma hoton da ke haskawa cikin duhun idona, da bata tsaya tana wannan jarabar ba, kamani kawai zata yi mu tafi gida a sama min lafiyar ciwon da nake ji.
"Na banu ni Farhana, ban san me kika shigo yi wajen nan ba, yanzu duba matsalar da kika jawa kanki...yanzu me zan faɗawa Gwaggo?".
Kuka ta ke yi sosai a sa'ilin, kuma har ga Allah maganartata na ƙara ƙarfin iskar guguwar da ke wucewa ta cikin ƙoƙon kaina ne. sai dai cikin lokacin da ba zai haura sakanni takwas ba na manta da halin da na ke ciki da duk wani abu da naji yana damuna, hatta hanzarin miƙewar da nayi ban san nayi ba dalilin jin Farhana tana cewa da shi.
"Ina zaka je? ina zaka tafi? kasan Allah ka ƙara ɗaga ƙafarka daga nan sai na yi maka ihu, ka zo ka sakar min ƴar'uwa dan na san koma menene kai ne sila,, kai maye ne ka kamata mugu".
Duk da cewar ba sosai na ke gani ba, amma a taku biyu na cimma inda yake tsaye, a haka na ƙara damƙe hannunsa gudun kar ya tafi ya kai kansa wajen da zai ci gaba da cutuwa, hakan zuciyata ke ce min,"Barinsa nan wurin zai kai kansa ne inda yafi nan muni".
Shi yasa komai zai ƙara faruwa da ni ba zan sakesa ba, ko da ace zan dawwama anan babu lafiya kuma babu tafiya. amma ga wani maɗaukakin mamakin da al'ajabi, damƙar hannunsa da nayi sai kawai naji komai na washewa, ciwon yana tafiya, komai na janyewa, kuma a hankali komai ɗin ya tsaya cak, kamin ya tafi gaba ɗaya in dawo daidai da yanda na ke.
Sai naji nayi sanyi ƙalau, haka kuma wani abu da ban san menene ba na tsargawa a jikina. na buɗe ido ina dubansa, yana nan dai tsaye a wurin, kenan tun a ɗazun bai motsa ba, sai dai wannan karan hannayensa duka biyun na zuɓe ne cikin aljihun wandonsa.
Sai kawai na ƙara kamo hannun nasa a haka naci gaba da jansa, kuma a yanzu bai min gardama ba, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, kawai bina yake kaman yaron da ke bin mahaifiyarsa. ni kuwa ƙara saurin tafiyarmu na ke dan mu bar cikin bolar da wuri, saboda zuciyata faɗa min kawai ta ke karki tafi ki barshi a nan, sai dai komai zai faru ya faru da ke.
Gaba ɗaya na manta ma da wata Farhana sai da na jiyota tana faɗin, "Allah kayi min maganin abunda ke neman yafi ƙarfina...yanzu da kike janshi ina za ki da shi? Kin manta halin tsananin da kika shiga ne yanzu?".
Ba tare da na tsaya daga tafiyar ba ko kuma na juyo nace da ita. "Tare zamu tafi. ba na son zamansa anan".
"Allah uwar da ta haife shi". Ta faɗa tana jefan mugun kallo.
Sai kuma ta ƙara da cewa,"Amma dai kin yi hauka ko Sabina? ba ki san mutum ba, ba ki san shi ɗin ko aljani ne ba, ko kuma macuci kawai dan ɗebarwa kai masifa da nemarwa kai jaraba shine kika wani kama zuwa inda yake harda ƙarfin halin ruƙo hannunsa za ki tafi da shi, to ki kai shi gidan uban wa uwar masu taimako ta duniya...yanzu wannan ɗan wiwin har ina dalilin da za'a taimake shi?".
"Kenan Farhana kawai idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan halin sai aƙi danganta hakan da jarabawar rayuwa? saboda hakan kuma sai aƙi taimakonsa?".
Na faɗa ina tsareta da ido a sanda na tsaya da tafiyar.
"Oho ni bance haka ba amma wannan dai ai bai yi kama da wanda za'a ce ƙaddara ce tasa shi shiga wannan yanayin ba...dan haka kawai ki sake shi mu tafi, kar ki so ki tona zuciyata kiga takaicin da ke ciki".
"Ohhh Farhana ki fahimce ni mana, duk abinda zaka yi kayi shi don Allah kuma zuciya a tsarkake, wataran baka san ta inda za'a taimake ka ba kaima. Nifa kawai na tausaya masa ne, naga kuma bai dace muna ganin halin da yake ciki ba mu tafi mu barshi a haka, ni kaina mamakin kaina na ke yi na tunkarar mutum irin wannan ba tare da wani tsoro ko shayi ba, amma a hakan dai zuciyata ke ƙara karfafa min gwiwa akan abinda ta raya min akansa. Yanzu tafiya zamu yi da shi sai mu sauke shi a gidansu".
Ta galla min harara tana faɗin,"mtswww ƴan wiwi nawa ki kai arba da su ba ki taɓa yunƙurin taimaka musu ba sai akan wannan mahaukacin".
Kuma furucinta na ƙarshe ya tsaida ƙafafuna, na rufe ido kaɗan sannan na buɗe, magana na ke so na yaɓa mata, amma ba zan iya ba, bata cancanci hakan daga gare ni ba, kuma hakan ba halina ba ne sam. sai kawai na kaɗa kai da cewar,"Su sauran ba su yi kama da waɗanda suke biɗar a taimaki rayuwarsu ba ne shiyasa kika kalla banyi hakan ba. shi kuwa sai dai idan idon mara imani ne ya sauka akansa, amma a hoton fuskarsa na farko da ka kalla zaka shaida ɗan Adam ne da yake cikin wata jarabawar rayuwa, ki kalla ƙwayar idonsa da kyau ki gani, ita kaɗai me shaida miki halin ƙuncin da yake ciki ne, balle shi yanda ba ki ɗaya abunda ke zuciyarsa ya bayyana a saman fuskarsa...Farhana ko kaffara ba zanyi miki ba mutumin nan yana da ciwo a tare da shi, wannan ciwon na damuwa da yake roƙon Allah dare da rana ya magance mishi, kuma wataƙila Allah ya sakoni cikin rayuwarsa dan na zama sila...shi yasa ko da na ganshi naji ba zan iya yin yanda kike so ba...so please lets go, i beg you kar ki ƙara faɗin magana mara daɗi".
Ganinta nayi kawai ta wuce ta gabanmu bakinta na faɗin,"tabɗijam, ko duniya za'a tasa tafiya da wannan ɗan wiwin ba'a motata ba, don babu abinda zai sanya ni yayibar mahaukaci na kama tafiya da shi, shi ɗin ai yasan da gidan nasu amma yazo ya zauna anan....mtswww ina wani alaman tausayawa a tare da shi balle a taimaka masa, saboda haka kinga tafiyata ƴar jawa kai jafa'i, Yo duk inda marar lafiyar ƙwaƙwalwa yake ai zaka shaida".
"Ke ce ki ke masa kallon mara lafiya amma ƙalau ya ke kamar yanda muke".
"A'a ba dai kamar ni ba kam, me lafiya dai ba zai zo kusa da bola ya zauna ba har yana shan sigari. Ai da gani kin san waye, cikin biyun dole ɗaya, mahaukaci ko kuma riƙaƙƙen ɗan daba, ki sake kallonsa da nazari tukunna ki dubi yanayinsa da idon fahimta".
Ta ƙarasa faɗa tana nuna shi da baki a yatsine. Kallon Farhana kawai yake yana ganin yanda ta ke banka masa wata uwar harara ta ƙyama, na san yaji rashin daɗin abinda tace, amma gani na ke kamar nafi shi jin rashin daɗin hakan.
"Haba don Allah Farhana, ya za ki dinga aibata ɗan'uwanki musulmi da irin waɗannan kalmomi marasa daɗi, bayan ba ki da masaniyar komai a kansa. Ki tuna fa addininmu ya yi hani da tozarta musulmi".
"Hmmm! lallai har yanzu ba ki da wayo Sabina, kuma indai za ki ci gaba da biyewa wannan zuciyar taki zata kai ki ta baroki akan saurin taimako da kuma tausayi. kuma ina mai gaya miki tun wuri ki bar wannan ɗan shaye-shayen kizo mu tafi, don wallahi irinsu ne tantiran ƴan iska masu lalata ƴaƴan mutane, waɗanda bakin uwa ya gama binsu har suka rasa matsuguni sai bola".
Maganarta ta ƙarshe tayi wani dukan ganga a zuciyar Alhussain, dan haka yay saurin rumtse ido da gaggawa ko ya samu sassaucin raɗadin da maganarta ta haifar masa. yau rana ɗaya kuma rana ta farko da aka taɓa faɗa masa kalma mafi muni da ɗaci a rayuwarsa. lalata! bakin uwa!, to shi da bai taɓa ma yin gaba da gaba da wata ƴa mace ba ta ina zai lalatata? wama ke raɓarsa daga maza har Mata? Babu! Shi ɗaya ne a rayuwarsa, kuma ba shi da iyaye balle yace yana da uwar da bakinta yabi shi...amma sai gashi yau har ana kiransa da ɗan daba, zai iya rantsewa a iya tsayin rayuwarsa ba ya tunanin ya taɓa riƙe wuƙa ko makami, yaji yana shan sigari amma ba ya taɓa ɗarawa daga kanta, itan ma dan ya kanji sauƙin ciwon zuciya ne idan yasha...amma sai ga shi yau ƙanƙanuwar yarinya na gaya masa son ranta ba tare da ta san shi ɗin waye ba kamar yanda shima bai san kowaye shi ba. ƙwayar idonsa tayi masa nauyi kamar an baɗa masa ƙasa a ciki, buɗe su yayi da matsananciyar damuwa gami da ɓacin rai, bai da ikon yi mata komai saboda ya cancanci a faɗa masa dukkan wasu kalmomi masu muni.
Idonsa yana bin Farhana da kallo da saƙa wasu abubuwa cikin ransa, yana jin tsakin da ta ke taja acikin kansa.
Sai ya cire hannunsa daga nawa, na dube shi da rashin jin daɗin abinda Farhana tayi, tausayinsa naji ya daɗa kamani, ko da wannan ɗaga ƙafar kaɗai da yayi mata zan iya shaida na rantse yana cikin wannan halin ne kawai dan ba shi da yanda iya, amma ba da son ransa ba.
Muryarta a sanyaye nace da shi,"Don Allah Yaya kayi haƙuri da abinda ƙawata tayi maka, rashin fahimta ne ya janyo hakan, amma a madadinta ina mai baka haƙuri, na san kowa ne aka yi masa ba zai ji daɗi ba, kar da ka sanya ɓacin ran hakan a ranka ya kuma haddasa maka damuwa".
Sai kawai naji ya buɗi baki yana cewa,"Kema kar da ki damu, dama na shirya fuskantar wannan ƙalubalen, irin wannan kalaman ba za su dame ni ba, ko da finsu ne ma ba zanji ciwo ba...da sannu kema za ki faɗa min su ne, wataƙila yanzu, wataƙila zuwa wani lokaci".
"Allah ya kiyaye bana fatan hakan ko da ba akanka ba". Sautin muryarsa ya washe da ce min,"Ke kam wai ba kya da tsoro ne?". Ya faɗa murya da ɗan ƙarfi.
Sai nace,"Allah shine abin tsoro ai, kuma kai ɗin ai ba kayi kama da mugu ba da har zan tsorata da kai. Yanzu dai kazo mu tafi kaga magriba na gabatowa kuma Gwaggona zata mani faɗan ban dawo da wuri ba".
"Ba ki sanni ba, ba ki san wane ni ba amma kina nema na raɓe ki, nace miki bani da gida, anan wurin na ke rayuwa ta. Shin wai ba ki gudun na cutar da ke ne ke kam?".
Na marairaice idanuwa ina dubansa da rashin jin daɗi nace,"Annabi S.W.A yace *KAMATUDINI TUDAN* (duk abunda kayi sai anyi maka). kai ɗin kana da Mama, kana da Ƙanwa, ƙilan ma kana da Yaya mace, nan gaba zaka auri mace, kuma ta iya yiwuwa ka haifi ƴa mace. Kaga kuwa nayi amanna da cewar ba zaka cutar da ni ba saboda ba zaka so wani ya cutar da naka ba".
Sai yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace min,"Ki dinga kiyayewa, ba kowanne kalar tausayi ba ne abun yarda, ba kowa ake gani a tsanani a taimaka masa ba, Yanzu ki bi bayanta ku tafi gida, kar Gwaggon ki tayi miki faɗa".
Maganarsa ta haddasa jikina yin sanyi, naji raina fayau, nayi ƙasa da idona ina kallon yatsun ƙafata nace,"To idan na tafi kai fa? Zaka tafi gida?".
"So na ke ki yarda da ni, bana magana balle har ta kai ga nayi ƙarya. inda kika ganni anan na ke rayuwata tsayin shekarun da na faɗa miki, idan har na biki bani da wani gida da zan nuna miki nace ina da alaƙa da shi, babu wani halitta na bil'adama da zan kalla na ce miki jinina ne, don haka ki tafi kawai ki ƙyaleni".
"To amma ka yi alƙawari idan na tafi na barka ba zaka kuma shan wannan abar me cutarwa ba?".
Sai ya rufe ido ya ɗan kauda kai gefe, ba zata taɓa fahimtarsa ba, ba zata taɓa ganewa ba.
"Akan mene zan ɗauki alƙawarin da ba zan iya cika shi ba? Kawai ni dai ki tafi kuma kar ki kuma dawowa inda na ke".
"Kana nufin ba zaka iya daina shanta ba kenan? Na faɗa maka fa shanta haramunne, ko ka fi so ka aikata abunda Allah ya haramta? Ina tauhidinka yake?.
Idonsa a kulle ya shiga girgiza min kansa alaman A'a.
"To in dai haka ne, don Allah kar ka kuma shanta daga yanzun nan. Kaga shi yasa ma mutane ke maka kallon ɗan iska, kuma alhalin kai ɗin ba shi bane. Wannan ba zata yi maka maganin damuwa ba sai dai ta cutar da kai, ka miƙa lamuranka ga ubangiji sai kaga ya yaye maka damuwar da ke tare da kai. Ƙilan mu kuma haɗuwa ƙilan ba zamu kuma haɗuwa ba, amma ina roƙonka da Allah kar ka kuma shan sigari, ka nisance ta nisa na har abada kaji Yaya".
Kawai sai na kalla ya runtse ido yana jijjiga min kansa alaman yaji kuma zai yi yanda nace. har cikin raina sai naji daɗi, duk wani abun ma ban san ina yi ba, na saki Murmushi kana nace masa,"Na gode Yayana. Kuma ka sani idan ni bana ganinka Allah yana kallonka, dan haka ka riƙe alƙawarin da ka ɗauka...alƙawari yana da girma, kayana ne kar ka manta da wannan".
Na juya cikin rashin kuzarin jiki na barshi a tsaye, yayin da na ke jin tasirin kallonsa da yake bina da shi ajikina, kuma har sanda na shiga mota na zauna idonsa na kaina, zuwa lokacin da Farhana ta yiwa motar key sannan naga ya juya ya koma inda muka fito.
Kuma tun bayan zaman Alhussain da kuma bayan tafiyar Sabina, tunaninsa guda ɗaya ne yake yi, _Dama akwai ranar da zata zo wani ya kusance shi da nuna kulawa gami da tausayawa irin haka? Dama a cikin Mata akwai masu uzuri da kirki irin haka?_
Tambayoyin da yay ma kansa kenan, a yayin da hoton Sabina ke haska mishi a ido da amsar tambayar tasa. ta kasance a tare da shi alhalin bata san shi ba, bata san waye shi ba, ba zagi, babu ƙyama, babu walaƙanci, babu tozarci, sai ƙoƙarin janyo shi a jikinta domin ta nuna masa illar halin da ya jefa kansa ciki, halin da ya na zaune a cikinsa ne ta dole bisa ƙaddara. ayau kuma sanadinta yaji yana bala'in son kasancewa da ahalinsa, ya gansu ko da ace ba za su kalle shi ba, ko da ba zasu karɓe shi ba, ko da za su wulaƙanta shi.
Wani abu mai zafin gaske yaji ya taɓa zuciyarsa, *SHIN WANENE SHI?*, *SU WAYE IYAYESA?*, *MENE SILAR KASANCEWARSA A WANNAN HALIN*, *YAUSHE ZAI FITA DAGA WANNAN ƘANGIN RAYUWAR?*, *HAR TSAWON WANNE LOKACI ZA'A ƊAUKA KAMIN ƘADDARARSA TA SAUYA FUSKA?*.
Duk sai yaji zuciyarsa ta matse sosai, ta yi rauni, ya dafe goshinsa ya kuma runtse idonsa da ƙarfin gaske, ya cije leɓensa na ƙasa hawaye masu zafin gaske suka shiga malala a fuskarsa, sai kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi tare da kifa kansa a saman cinyarsa yana riƙe da kansa da ke mugun sara mishi tamkar zai bar jikinsa. wannan yanayin, wani yanayi ne da yake tsintar kansa a duk sanda ya rasa amsar waɗancan tambayoyin, ya ɗau tsawon lokaci a haka cikin rera wannan kukan mai ƙaramin sauti tamkar ba namiji ba, kukan da babu saukar hawaye. Daga bisani ya miƙe ya tafi masallaci dalilin kiran sallar da ya ji ana yi, bai baro cikin masallaci ba har sai da akayi sallar isha'i kana, nan ma sai da za'a rufe masallacin sannan ya fito.
A dawowarsa ya tsaya a dai-dai inda motar su Sabina tayi parking ɗazu, kallon wajen yake da haskawar hoton abunda ya faru a ɗazu, bai san dalili ba, amma haka kawai yaji yana so yarinyar ta ƙara kasancewa da shi. sai yasa hannu ya matse idanunsa da ke rufe, ƙasan zuciyarsa na raya masa da cewar _ko zata sake dawowa?._
#React,Vote,Comment
#Al-hussainBook1
#Gamjiwriter's
#Teamfitattubiyar
#2024
#February
#Share
#***
#Halimahz
#Purchase₦300