Chapter 3
by @matardear1
💫💫💫💫
*UNCLE J*
💫💫💫💫
[ Labari ne mai sarƙakiya ban tausai' munafunci zallar ƙauna da kuma romantic]
*Littafin Uncle j na kuɗi ne kar ku manta regular ₦ 500 vip group ₦ 1000 special payment₦ 1500 via *** maryam Ahmad opoy ko katin mtn ko aitel ta wannan number ***.*.
*...sannan free page ba mai yawa zanyi ba only* *10 page in sha Allah ki hanzarta kisanaki*
Episode 5&6
Jin yara na hayaniya yasa anty Hadiza fitowa ganin ƙanwar tata itama da farin ciki ta iso gareta ta riƙe mata hannu ta ce" antyn yara daga ina haka?'"
Murmushi jannat tai tare da faɗin walllahi daga gida nake, mutanen gidan suna gaida ki ma ita dai anty Hadiza tasan faɗi take tasan ba wanda zai ce saboda ta nuna tana san su mama ita da jannat suka shige cikin ɗaki inda yarinyar anty Hadiza ta kawo Mata ruwa da tsobon da take sai dawa suna sha suna fira' wani yaro ne ya yi sallama cikin gidan ya ce wai ana kiran haske.......... Gabanta ne ya faɗi ta nuna kamar ba ita ba, ita anty Hadiza bata san wacece haske ba ta ce ma yaran kaje ka ce gidan nan babu mai irin wannan sunan yaran ma duk ƙanana ne!
Yana fita kuwa ya faɗi sakon da aka ce mashi..... murmushi Waheed ya yi tare da ƙara ce ma yaron kaje ka ce wadda ta shigo yanzu ake sallama da ita, ko da jannat taji wai ita sai kunya ta kamata gaban anty Hadiza sai taji duk ba daɗi' anty Hadiza ta buɗe baki zatai magana jannat ta riga tada da cewa walllahi ban san shi ba anty Hadiza....
Duk abinda suke yaron na tsaye bai tai ba, ta ce'' jannat kije kiga waye mai Maganar nifa bana san wannan tsoron da kike nunawa; ta ce ma yaro ya tafi yana fita ya ce ance tana nan zuwa duk ya kwashe Abinda jannat ta faÉ—a ya faÉ—i ma Waheed shine dai murmushi yake saboda yaji rikincin nata yaro ya ida sa dacewa haka dai antyn ta ta tace mata wai jannat kije kiga waye ne bana san rigima!"
Ya ji daɗi har cikin ran shi don yau ya san sunan hasken shi, lalle dole zatai jan aji wai zullaziya kenan🤣🤣. Tana fitowa ko kallon kirki bai ishe ta ba, ta yuya mai baya tare da faɗin gani malam wai bashi ko tara sai bina kaje kullum haba nifa nagaji........ita ala dole faɗa take mai nan amma bakin ta kamar tana nomal magana ne ba faɗa ba sai yaji ta ƙara shiga ran kamar mai ya ce jannat layin mune nan fa.
Ware fararen idon...ta tai kamar zatai kuka ta ce'' to ni gidan anty Hadiza nazo ai ba wai layin ku ba"
Harara ya wulla mata tare da faÉ—in yanzu dai Kinga gidan mu can, yana faÉ—a tare da nuna mata wani plat din gida ya sha fenti sai kofar gidan akwai shagon É—inki, a sama an rubuta Waheed fashion cikin zuciyar ta ta ce ko shine mai É—in ki su anty Hadiza ne, ya ce mai kike tunani haka Haske?
ÆŠan girgiza kai tai tare da faÉ—in bakomi, ni kabarni na tafi saboda musha fira dani da ita bata bari ya bata amsa ba ta shigo gida' ko da ta shiga sai ta cigaba da firar ta saboda kada anty Hadiza ta ce waye ne...
******************
Suna isa gida kai tsaye palorn dady suka nufa inda ta ce'' Jalal kaje darling table Ina zuwa bari na haÉ—a mai ruwan wanka, tana gama fadar haka ta barshi Nam ta wuce ciki don haÉ—a ma Alhaji ruwan wanka, tana shiga tafara taya shi cire kayan ta shiga cikin bayin ta haÉ—a mai ruwan can bangan Jalal kuwa wayar ce ya É—auka ya kira budurwar sa don kwana É—aya da bai yi abinda ya saba ba sai jin shi yake kamar bai da lafiya"!
Kusan minti 40 sannan dady ya fito wanka, mummy ce ta dauko mai jallabiya ash color tai matuƙar amsar jikin shi suka fito tare da mummy lokacin har jalal ya gama cin abincin shi yana dai zaune nane bai tashi ba, haka mummy ta iso tana mai gyara mai inda zai zauna...
.....................................
Bayan kwana biyu yaron "anty Hadiza ne ya kai É—inkin kayan makarantar su na islamiyya shagon waheed yaje an sane ya tadda ana ida sawa, Waheed ya kalle shi ya ce kai salim wai daman jannat Æ´ar uwar ku ce"?
Murmushi salim din ya yi tare da faɗin "anty jannat "ita ma ƙanwar ummana ce fa gidan su ɗaya baba ɗaya uwa kowa da tashi, haka dai yaro ya kama surutu Waheed ya tsaida shi ta hanyar miƙa mashi kaya ya ce'' to antyn ka bata da wayane?"
Salim ya ce" ehh bata da ita sai dai ta mama take kiran mu mugaisa"
Tunani ya kama yi ashe daman ƴar uwane,lalle da ita zai kama ƙafa saboda ya tsunduma cikin san jannat kamar mai ba zai iya misaltuwa...
.........."jannat Kinga tunda yanzu kun kusa gama makaranta ya kamata ace kin fidda miji duba da Æ´an uwanki suma da sungama makaranta ake zancen biki Kinga dai su samira suma suna da nasu samarin duk lokaci É—aya mama ke wannan maganar"
Gabanta ne ya faɗi jin mai mama take cewa ganin ita ko kare bata kulawa' sai dai ma wannan natattacen yaron ya tukura mata; duƙar da kanta tai ta ce'' mama in sha Allah zan yi abinda kika ce amma don Allah abar zancen sai nan gaba!"
Sai mama tai shiru ganin ta ce'' haka don ita jannat macece mai hakuri da juriya don duk abinda zai girgiza ta bata iya nunawa a fuska,ita É—in mai tarin biyayya ce ga duk abinda mama ta furta mata tana aikawata!!!!!!!!!!!!
Warar ce aka dafa ta gyara ta, tana shirin fita ne sai ga sallamar yaro wai ana kiran jannat inji wani mai mashin a kofar gida; kafin su jannat su ce komi mutanen gidan suka amsa da bata nan yaro dai ya tsaya kalli inda jannat take tsaye tana kallon ikon Allah mama ta yafoto yaron da aka aiko ta ce" kaje ka ce tana zuwa kaji"
ta kalli ''mama tare da faÉ—in haba mama daga zuwa Sai kice ina zuwa ni walllahi bance ma kowa yazo ba ban tsaya da wani balle nace mashi yazo"
Kallon ƴar tata dai ta ce'' jannat kije idan kika fita zaki ga komaye ke kiran ki ' kinsan dai ba ƙyau ka wulakanci ga ɗan Adam Allah ya daraja ji kin kuma sani"
Jin kalaman da mama ke mata ne tasa hijabin ta, zata fita ne innar su samira ta ce Allah yasa wani mai kwasar kashine walllahi da sai nai ruwa nayi tsaki kin aure shin ta idasa Maganar tare da bangaje jannat ɗin ta wuce dakin ta; ita dai ba abinda take tunani irin wanene zai zo mata a cikin wannan halin sai dai in da wata manufa ya zo ta ida sa wajen," tana fita wannan dai natattacen ne tagani zaune saman mashin ɗin shi yasa farar riga tishet sai ɓakin wando ya yi matuƙar kyau sosai ta matso inda yake haɗi da mai sallama..
Wow ya furta cikin ranshi don jin zazzaƙar Muryar ta, mai daɗin sauraro har bai so ta daina sallamar bai gani tai ya na kallon ta tai saurin sadda kanta ƙasa don bata iya haɗa ido dashi nauyi take ji ka tse shirun tai tare da faɗin ina wuni?
Sai a lokacin ya amsa mata sallamar hadi da gaisuwar da ta mai ya ce'' sunana Waheed ina zaune a layin su anty Hadiza ne nasan Kinga shagon ɗinki na wanda yake kusa da gidan mu, ina da ƙanwa mu biyu ne iyayen mu su ka haifa nazo da babban zance ne gunki ki bani dama na furta maki"....
Kallon shi tai cikin zuciyar ta kuwa cewa take yanzu waye ya baka damar yin wannan labarin naka? A fili kuwa murmushi tai tare da faÉ—in yanzu dai kaga yamma tayi ina san fito da sana'a tane in badamuwa!
"Jannat ki daure kiban ko minti 30 ne nasan zai isheni na faÉ—i sako na"
Hakan kuwa a kayi ta ce'' mu koma daga dakalin ƙofar gidan mu kaga nan, mutane na wucewa hanya ne!"
Hakan kuwa da tafaɗa ba ƙaramin burgeshi, tai ba lalle ya tabbata ya samai ta ya yi mata mai tarbiyya....daga can dakalin suka koma ya fara zaiyana mata sirrin da ke cikin ranshi; ita wasu maganganun ma kunya suke bata daga ehh sai a'a shine kalmar da take furta mai ta ce nidai ina so kaban kwana biyu idan nai tunani sai in faɗa maka na amince ko ban amince ba!
************
Bayan kwana biyu da isowar dady duk wani rashin ji "Jalal ya maida shi gefe ya aje inda mummy take jin daɗi dama haka yake kullum da ta godewa Allah ™ yanzu yana ganin ya dage ya tafi zai koma ruwa🥲. haka yake yi ita dai mummy addu'a take Allah ka shirya mata Jalal din ta yau ya kama juma'a ne ƙurarran lokaci ne mummy sai da tasa masu aiki suka taya ta aikin gashi ranar suna abincin sadaka wa almajirai............Jalal ne ya fito cikin blue ɗin shadda sai hula mai ƙobe, da ya daura da ita riƙe yake da dadduma kamar bashi bane mai zuwa club ɗin nan yadawo musulmin shi🤣🤣. Ya ce'' mummy zamu tafi masallaci ai mana addu'a"..
Shafa kan shi tai tare da faɗin my lovely son Allah Ubangiji yasa adawo lafiya' ina mai roƙon Allah da ya shirya min kai Allah yasa a hanyar ku tadawowa ko zuwa a ga matar aure ai min surika; a mota ma shine yake driver ɗin dady na gefen zaman banza shima nan dady ɗin ɗaura mashi ya yi daga inda mummy ta tsaya ya ce'' wai dady kungaji dani ne da kuke ta faman nai aure?"
Kallon shi dady ya yi ya ce'' a'a abdul jalal shi ana gane mutumin kirki ne ta hanyar aure idan ya kai Lokacin sai dai idan babu halin yin auren ne shine mutum zai hakura amma kaifa son mai karasa a ciki? Kana da kuÉ—i kana da sana'a ga gidan ka da ka gina mai kake jira yanzu to sai aure ai!!!"
Uhmm dady in sha Allah na kusa kamar yadda kuke so inyi zanyi in sha Allah "dady fatana ku tayani addu'a" haka dai suka isa ana firar uba É—a gwanin sha'awa har suka dawo gida, inda dady ya raba ma mabukata kuÉ—i saboda duk ranar Friday yake ranar laraba yake dawowa ya koma Lahadi duk lokacin da zai dawo zai raba masu kudine su ta samai albarka...
............... bayan kwana biyu da zuwan Waheed gidan su jannat, tana ta jiran shi ranar amma bai zoba saboda ya ƙara bata lokaci tai tunani mai zurfi hakan ko a kai mama ta bata shawara mai ƙyau ta ce'' jannat idan kin amince da shi to kada ki bata mai lokaci ki faɗa mai in kuma kina san shi sai ki faɗa mai shima, jannat da taji mama ta ce wai in tana San shi duk abin sai ya bata kunya ta sun ne kai mama ta ce ja'ira ashe kina so da baki fita ba ai da naga yadda zaki kifara san nashi"
Da sauri tafito ta cigaba da aikin ta na mai tuna maganganun shi tana jin wani sanyi cikin ranta ji take daman tai tsuntsuwa taganshi a gabanta don ita macece wacce bata iya san abu ba idan tana san abu tsakani da Allah yake san wannnan abu, ko habaicin da suke yaɓa mata tana jin su sai dai ta share kawai ba wai don bata jin haushi ba a'a bata nuna masu ne!
Washe gari tunda ta dawo makarantar yamma ma take jin gabanta na faduwa, gashi kwana biyu tunda Waheed ya san gidan su ya daina zuwa ƙofar islamiyar tasu, ƙarfe 6:00 ta fidda warar ta duka a waya ɗaya take tadawo gida saboda sun gyara warar su ga yajin tafarnuwa mai daɗi wanda yaji magi: samun wata kula tai ta zuba warar ɗari biyu ta aje cikin ɗakin su ita dai mama bata ce komi ba illa idanu.......karfe 8:30 dai-dai akai sallama wai ana kiran jannat, wannan karon bata jira maganar mana ba tai gaba don ganin ko Waheed din ne tana zuwa kuwa taganshi kan dakalin ƙofar gidan nasu ta gaida shi ta ce bari indawo......tana shiga ta ce mama shine kular da ta aje wara ta ɗauka Hadi da ruwa a kofi sai dadduma tafito
Shin wacece jannat?
Wanene Abdul Jalal?
Wanene Waheed?