TA ƘI ZAMAN AURE

Chapter 13

by @khadeejacandy

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: ***


*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*



✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧



𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆



 *Talla👇👇👇* 


***

*INA MATAN DA SUKASAN DARAJAR GYARA❓DAKU NAKE MACE MAI GYARAN BATA ZAMA BORA❌*


*KUZO GA INGANTATTUN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI💪BA MUNA KAYABA❌ HAJIYA KIZO KISAI KAYAN MATA WURIN DA BAZAKIYI ASARAR KUDIN KI BA*


*INA MASU CEWA NI KO NASHA KAYAN MATA BASAMIN AIKI HMMM HAJIYA BAKIDAI SIYA KAYA MASU INGANCI BANE, KAYANMU SUNA KARA NI'IMA, TAYARDA SHA'AWA, DADI, TIGHTENING (MATSI), CIKO DA GABAN MACE (DUK BUDEWAR SA), DUMIN GABA GA, KAMSHIN GABA GA KUMA NA KARA DANDANO OVER 💃💃💃💃💃👉 GA KUMA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI DAGARGAZA SANYI KODA YA SHEKARA 10 A JIKINKI* ***


*A DAYA BANGAREN KUMA MUNADA SABAYA MAI GYARAN NONO DUK LALACEWAR SA KO KIN HAIHU GOMA SABAYAR MU ZATA CIKO MAKI DA BREAST SUYI GIRMA SOSAI MADAME*


*GA KUMA TA HIPS (MAZAUNAI)SU CIKO SUYI BULBUL NONO YA CIKO SOSAI HJY KIYI KIBA YAR DAIDAI SKIN DINKI YAYI KYAU KI KOMA TAMKAR TARWADA*

 

AKWAI KUMA NA GYARAN NONO WANDA BAYA SAKA KIBA💃💃💃 


GASKIYA NA YARDA DA INGANCIN KAYANTA👆👆👆





*Chapter - 13*


Babu kowa a tsakar gidan balle na ce wani ne ya rika ni ya isa da ni kofar dakinmu, haka kuma ba zan iya fadar cewar kafafuwana sun kawo ni ba, domin samun kaina na yi tsaye a tsakiyar dakinmu ina kallon hudun daren da ya cika daki. Can ka na ji an dafa ni muryar Hana ta fara isa kunnena. 


“Da ni ce ke, zan auri mutumen nan ko dan na samu rabuwa da Baba lafiya, kuma zaki huta da duk wata masifa tashi da tashin hankali ko fada, idan kika yi aure zaki huta Noor”


Na juyo na kalli ta saitin inda take tsaye. Amman na kasa ce mata komai sai hawaye ne suke min zuba, a rayuwa ban tana jin wani abu tashin hankali ba irin wadda na ji a yau din nan. Sai na ke jin kamar sanarwar mutuwa aka min cewar Zafeer ya mutu ya bar ni a raye. 


“Noor ki yi addu'a kawai, kuma karki bari so ko shashancin da ake ganinki da shi ya zama silar lalacewarki saboda bakin da Baba yayi cewar be yafe ba idan kika kula Zafeer”


Na sulale kasa a hankali na zauna a gurin, na rasa me zan yi ko na ce, kalamaina kamar sun kare, duk wani kuzari a yau ba ni da shi. Me yasa Baba zai min haka? Anya ya san yadda nake son Zafeer kuwa ko kuma yadda shi Zafeer din yake so na? Mama ta yi gaskiya tace ni ce na janyowa kaina kuma haka din ne, domin ni na yi silar zuwan Kareem da abokinsa a gidanmu gashi sun lalata baiko ba tare da na san waye mai so na a cikinsu ba, ba ma nuna suna so na ba, kuma ba su furta ba ban taba ganin wata alama dake nuna soyayyata a garesu ba. Gaba daya sai na ji kamar mafarki nake wunin ranar sai ya zame min kamar ba gaske ba, ni dai na san ina matukar kaunar Zafeer irin kaunar da nake jin idan ba shi ba ba zan iya zaman aure ba. A inda na zauna ban tashi ba har garin Allah ya waye kuma bachi be kusanci idona ba, haka kuma ban bude baki na ce da kowa komai ba ban kuma ihu ko kururuwa ba, saboda ina jina a wani yanayi na dabam da ban saba jina ba. 


Bayan na yi sallah asuba na nemi gurin kwanciyata na kwanta sai idona suka ce firr ba dai bachi ba Nooriyya, karyarki ba a wannan wunin ba, haka na tashi zaune na kurawa kofar wajen ido, na dade a zaune kamin na iya bude baki na fara ambaton Allah, Ban yi wani kwakwaran motsi ba har Hana ta gama shirinta na makaranta ta fita ta zuba kunu sannan ta kawo min nawa har inda nake kallo daya ta yi min ta fahimci a tsorace nake ga idona yayi wani Ja kamar wadda ta shekara bata yi bachi ba. 


“Ga kununki in ji Mama...”


Na kalli kunun na dauke kai ina jin ba zan iya kai komai a cikina ba yanzu. Ni dai ba wani sanin damuwa na yi ba amman ina jin dakinta na daf da ni domin kokarin rabani da Zafeer da Baba yake ko ma yayi wani abu da ban taba mafarkin faruwarsa ba. 


“Wa'alaikusalam”


Muka ji Mama ta amsa sallamar Zainab dake sanye da uniform din makaranta, Hana ta jiya ta fice daga dakin kamar dai babu wadda ya damu da halin da nake ciki, wata kila ba su yi zaton soyayya ta ta kai haka ba, ko kuma ganin suke wani abu ne da zan iya mantawa a take. Ko kuma dai saboda ni na janyowa kaina ne shiyasa lamarin ya zo min ta haka. 


“Noor... Lafiya kike kuwa?”


Kamar an bude min kofar sassauci tana tambayar haka sai na fashe da kuka na kwanta jikinta amman na kasa fada mata damuwata har ta gaji da tambayata ta koma rarrashina. 


“Allah dai yasa lafiya, Zafeer ya je gidanmu shi ma cikin damuwa yace na fada miki ya zo jiya amman be samu ganinki wai yana son ku hadu a gurin aikinsa ko kuma kwanar dan musa mai itace anjima da karfe goma”


A sirrance take fada min sakon na Zafeer, abun da hausawa ke cewa ga bikin zuwa babu zanen daurawa, domin ban isa na tsallake umarni da furucin mahaifina na je na ganshi ba, kuma a yau bana jin zan iya budewa kawata cikina balle na fada mata damuwata da babu mai min maganinta sai Allah.


“Noor akwai wata matsala ne? Fada min ko minene dan Allah”


Na girgiza mata kai na matsa baya na kwanta ina maida numfashi daker. 


“Wai fada kuka yi da shi ne ko kuma me?”


Nan ma dai ban ce mata komai ba. Har ta gaji ta tashi ta fita ta barni rumgume da bakincikina. Ban iya fitowa na yi komai ba har Mama ta gama aikinta na gida, Yaya ya dauko ruwa sannan yayi wanka ya fita, a nan na samu mikewa tsaye ina jin kaina na masifar ciwo ga wani jiri jiri da nake ji yana dibata yana yawo da ni. Ruwa na zuba na shiga bandaki wai saboda na samu na yi wanka amman sai na saka yin wanka na zauna a bandakin ina ta kuka. Hankali be kara tashi ba sai da wani almajiri ya shigo ya ce Zafeer na sallama da Noor Mama tace masa yaje yace bana gidan. Rumgume kaina na yi ina ta kukana babu mai rarrashina har sai da na gaji na tashi na daura zanena na fito ba tare da na yi wanka ba na aje ruwan a waje sannan na nufi dakin Mama na zauna daga bakin kofar dakin ina kuka na ce. 


“Mama Wallahi duk na daina abun da nake, ba zan sake kin jin maganar kowa ba, Mama ki yafe min kuskurena, kuma dan Allah ki roka min Baba yace ya yafe min yayi hakuri ya bar ni na auri Zafeer dan Allah Mama”


Kaya take ninka amman haka be hana ta kalleni ba ta ce. 


“Kin fi kowa sanin halin Babanki ai, yanzu ya ga mai kudi ba zai yarda da soyayyarki da yaron nan ba, kuma ni ban ga laifin ubanki ba, daman tsuntsu da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka, tun abun nan be yi nisa ba ya kamata ki gane gadar zare kike yi ma kanki amman ina, hankali yayi yamma ke kin yi gabas, idan kika ga Babanki be hada aurenki da wannan mutumen ba to sai idan shi din ne yace baya sonki ko kuma wani ya gani wadda ya fishi”


“Ba so na yake ba Mama Wallahi wata kalmar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi ba”


Na fada da muryar kuka wani kukan na cin karfina. 


“Wannan kuma ke kika jiyo, ga dubu biyu nan tashi ki kai gidan mai adashe, bashin da kika ci ne ban gama biya ba”


Ta jego min kudin ni kuma sai na kai hannu na dauka, na kalleta sannan na tashi na fice daga dakin ina hawaye. Dakinmu na koma na zauna gaba daya sai na rasa abun da ke mini dadi. Na kusan minti talatin a dakin ina kuka har sai da Mama ta yi magana sannan na yunkura na tashi idona a kumbure na saka rigata da hijab na riko kudin na fito na saka talkamina na fice daga gidan. Kamar wata marar lafiya haka nake tafiya har na isa gidan mai adashen na bata kudin na juyo na fito ta babu wani kuzari a tare da ni. Daf da zan isa gida na ji muryar Zafeer yana kiran sunana amman na kasa waigawa saboda bana son na yi arba da fuskarsa kar rauni ya saka ni karya doka da mahaifina ya saka min, amman hakan be hana shi shan gabana ba. 


“Noor magana fa nake miki kina tafiya kamar baki gan ni ba, me ke faruwa ne?”


Na dauke kai na kauce daga gabansa na cigaba da tafiyata. 


“Noor... Noor.. Ni ne fa, Noor”


Na kasa juyawa kuma na kasa amsa masa sai hawaye suka zubo min. Ya sake shan gabana. 


“Jiya na tafi gidanku ban samu ganinki ba, idan har Baba zai juya min baya ya ki sauraren uzurina ban yi zaton haka daga gareki ba Noor, kin san ina sonki sosai zan iya jure komai ban da rashinki Noor, na roki Baba jiya na ce ya yi hakuri ya ba ni wata biyu zuwa uku zan yi na yi duk yadda zan iya, zan aureki Noor ko haya ce zan kama mu zauna kamin na samu aiki, amman me yasa kike kokarin canja min? Ko wani abu aka ce na miki? Ko kuma an fada miki wani aibuna ne...?”


“Babu wani aibunka da za a fada min da zai saka na tsane ka Zafeer, babu wadda zai iya shiga tsakanina da kai, babu wani laifi da zaka aikata a duniyar da zai saka na juya maka baya”


Magana nake masa a zuciyata amman a zahiri na kasa furta komai sai kallonsa nake. 


“Noor...”


Ya sake kiran sunana muryarsa a sanyaye, nan din ma ban amsa ba sai ma kauce da nake kokarin yi daga gabansa na cigaba da tafiyata. 


“Baby Noor Noor yau ni nake miki magana kina tafiya? Ina kiranki kin ki amsa min? Me yake faruwa? Fushi kika yi? Saboda na ce ba ni halin aurenki a yanzu? Zan aureki Noor ko ta halin Yaya na miki alkawari hakan yayi miki?”


Nan ma ban juyo ba shi kuma be fasa bin bayana yana bayyana min kalaman da suke kara tsuma zuciyata ba. 


“Noor please, ina binki a baya kina tafiya kamar wani bakonki miye haka?.... Nooorr!”


Daga karshe ya kira sunana a tsawace har sai da na tsaya cak daga tafiyar da nake. 


“Ko dai mutumen nan ne ya fada miki wani abu a kaina? Ko kuma Baba ya fada miki wani abun ne dabam da ba shi na fada ba, me yasa kike min haka? Why?”


Na hade yawu na cigaba da tafiya da sauri na barshi a gurin tsaye, ina shiga gidan na samu Mama sanye da hijab ta nufo kofar fita.


“Alhamdullahi, daman bayanki zan bi saboda na san halinki zaki iya satar kafa ki tafi gurin Zafeer din nan”


Ni dai ban ce komai na nufi dakinmu na kwanta ina ta gurzar kuka kamar babu gobe. A haka Hana ta dawo daga makaranta ta same ni har na yi rama tsabar kuka da tashin hankalin da na samu kaina a ciki. 


“Noor dan Allah ki ba kanki lafiya, ki yi ta addu'a idan Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isa ya hana”


A nan na samu damar amsa mata da toh sannan na tashi zaune ina kallon kunun da ya aje min tun safe. 


“Baki sha kunun ba?”


“Ba zan iya cin komai ba, Hana”


Na kira sunanta sai ta amsa min ta duko. 


“Dan Allah ki roka min Baba yayi hakuri Zafeer yace zai nemo kudi nan da wata uku zai aureni, ki ce yayi hakuri ya bar ni na yi magana da shi, hukuncin yayi min tsauri...”


“A ina kika ga Zafeer din?”


“Dazun da Mama tace na kai kudin adashe...”


“Amman dai ke kam Noor baki jin magan yanzu duk bayan gargadin da Baba yayi miki yace miki be yafe ba idan kika sake magana da Zafeer sai da kika yi? Kin san abun da tsinuwar iyaye take nufi kuwa...”


Na girgiza mata kai da sauri. 


“Ban yi magana da shi ba, shi ne yake bibiyata yana fada min haka, ransa ya bace da ban yi magana da shi ba, ni ma na ji kamar na mutu saboda yayi min magana ban amsa masa ba, Hana babu dadi dan Allah ku yi magana da Baba ko zai ji, ni na san haushina yake ji amman ke zai iya saurarenki saboda ya san kina da hankali”


“Aa Mama ma bana jin zata iya tunkararsa da wannan maganar balle kuma ni, indai ba son kike ya tsine min albarka ba ni ma, ki dai ta addu'a ni ma zan taya ki”


“Na gode”


Na fada mata sannan na tashi kamar yakusasshen lawashi na fita daga dakin, alwala na yi na dawo dakin na yi sallah azahar na yi ta addu'a. Misalin karfe hudu na yamma Yaya Nabil ya shigo gidan da ledarsa kamar yadda ya saba, ko da an yi girki balle yau da ba a girka komai a gidan ba. Awaje ya zauna gurin da Mama take zaune domin kusa da kofar dakinmu ne, ina jinsa yana ta fada da alama ransa a bace yake ban fuskanci me yake magana akai ba, amman na ji sunan Zafeer da Oga Kareem kuma na ji zancen yan sanda. Hakan ya saka na mike tsaye ina jin jiri na taka na isa kofar na rike kofar na tsaya ina kallonsa. 


“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un abu be yi dadi ba, yaushe wai?”


Na ji mama ta fada sai Yaya yace. 


“Yanzu nan ba a dade ba Wallahi, kuma duk Baba ne sila, shi ai yana da gaskiya ko nine zan aikata fiye da haka, me yasa Baba zai yi halin karanta miye amfanin haka? Fisabillilahi haka ake yi, ni gaba daya bana jindadin yadda Baba yake tafiyar da rayuwar gidan nan, ban taba ganin uba irin na mu ba”


Mama ta juyo ta kalleni sai ta miko min hannu. 


“Zo nan ki zauna”


Na isa kusa da ita na zauna sai ta saka ni a jikinta ta rumgume ni. 


“Wai an kama Zafeer”


Na daga kai da sauri na kalleta. 


“Me yayi?”


“Wai ya tafi gurin aikin Ogansu Yayanki yayi masa cin mutunci a cikin mutane shi ne shi kuma ya saka aka kama shi yana can rufe”


Na fashe da kuka ina jin kamar na tashi na tafi amman babu dama. Yaya ya kalleni a tausaye ya ce. 


“Ni na rasa gane wane irin kalar uba Allah ya ba mu, gaba daya babu ruwansa da damuwarmu, yanzu mutumen ko auri Noor Wallahi ba zai ga mutuncinta ba saboda ya san yadda aka yi ya aureta...”


“Jarabawa ce ta rayuwa, sai hakuri Nabil duk yadda zaku ji be kai yadda ni nake ji ba, ku ai ubanku ne ni ko mijina ne, duk jarabawar da za'ayi mace ko yaya ko wace iri ce mai sauki ce idan ba a gidan aurenta ba ne, idan mace tana shan wahalar rayuwa akan ce idan kika yi aure kin huta, amman idan ta tararda kaddarar a gidan aure, to wannan ita ce jarabawa mai girma, domin shi aure yana nufin rayuwa ne ko mutuwa, babu yadda zaka yi, duk yadda kuke jin bakincikin ubanku be kai yadda ni nake ji ba, yara biyu na rasa kamin na haife ku, shekara shirin da uku da aure babu ranar da bana kwana da bakincikin ubanku”


Ta karashe zancen cikin kuka Ya Nabil ya sauke kansa kasa rai a bace nikam kuka kawai nake ina jin bana da makiyi a duniyar kamar Kareem, sai kuma mahaifina da nake jin na tsane shi a yanzu. Na dago daga jikin Mama na kalli Ya Nabil 


“Yaya dan Allah ko zaka kira min Kareem a wayarka na yi magana da shi please? Dan Allah?”


“Me zaki ce masa?”


“Magana kawai zan yi da shi dan Allah Yaya, kar yaje yayi ma Zafeer wani abu dan Allah Yaya”


Rokonsa nake da muryar kuka hawaye na min zuba, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kama number sai da ya kira sannan ya mika min. Ni kuma na karba na mike tsaye na shiga dakinmu. 


“Assalamu Alaikum”


Ban amsa sallamar ba na yi shiru kamar wadda ta rasa abun cewa. Hakan sai ya fahimtar da shi ni ce a waya ba Yayana ba. 


“Noor me ya faru...?”


“Komai ma ya faru Kareem, na yi dana sanin saninka a rayuwata, sanadinka Baba ya raba ni da Zafeer ni shi kadai nake so ba zan taba son kowa ba, saboda me zaka kama shi?”


“Ba a fada miki abun da yayi ba? Planning ma fa nake na yadda zan taimaka masa ya aureki, tun jiya da na fahimci abun da Babanki yake kokarin aikatawa, amman sai gashi yau a restaurant a gaban jama'a yana ci min mutunci yana kira da sunaye kala kala, shiyasa ai na rufe shi sai yayi hankali tukuna”


“Kana takama da kudi ne kawai Kareem, shiyasa ka siye Babana kuma yanzu ka kulle saurayina, to ni ba zan siyu ba, ba zan taba sonka ba, kuma na tsane ka da na san bakincikin da zaka haifar min kenan ba zan yarda ko magana ta shiga tsakanina da kai ba...Ka sake shi Wallahi saboda ka ga shi ba shi da kudi ka yi masa haka...”


Ban gama fadar Abun da nake son fada ba Yaya ya fisge wayar ya kashe. 


“Shi ke nan na rasa aikina...”







KAREEM POV. 


Sai da kiran ya katse sannan ya kalli Hafiz dake zaune a gabansa. 


“Ka ji da kunnenka ko? Shiyasa na saka hands-free ai saboda ka ji”


Hafiz ya dauke idonsa daga wayar ta Kareem dake aje a kan teburin ya kalli Kareem. 


“Kurciya ce fa kawai take damun yarinyar nan, ai kai baka fito ka fada mata cewar kana sonta ba ko? In ba shi ba miye na wani kiranka ta fada maka magana haka? Wallahi bata da wayo”


“Ko ma dai minene yanzu ta fadi mind dinta, tun farko na fada maka yaron nan take so, ko na rasa matar aure a duniya ba zan taba auren matar da bata so na ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin masoya ba, so ka sake tunani Hafiz ka je ka gyara lamarin yarinyar da saurayinta kuma ka nunawa mahaifinta gaskiya, karka cutar da ita ka cutar da saurayinta”


“Amman baka ga abun da ya zo mana ba dazun nan”


“Abun da yayi be kyauta ba, abu ne da kowa ya sani, shiyasa har na saka aka kama shi, kuma yanzu za a sake shi, amman kokarin ganin ka shiga tsakaninsa da Noor daukar alhaki ne, indai saboda ni kake yi ka daina ni dai ba zan auri yarinyar nan”


“Ni fa alheri kawai nake kokarin kullawa, kuma ni ban cewa mahaifinta ya rabata da saurayinta ba, kuma ban cewa saurayinta ko ita su rabu da juna ba, ni dai ina kokarin sama maka mafita ne Allah ya san manufata shiyasa nake ganin zaka iya koya mata sonka cikin kankanen lokaci, amman zan gyara komai kuma na maka alkawari daga yau ba zan sake rokon ka auri Noor ba, kuma zan je na samu mahaifinta zan gyara duk inda kake tunanin na lalata, daga nan har zuwa nadewar duniya Kareem ka cigaba da zama a haka ba zan sake maka magana ba”


“Hakan ya fi ba, na san yadda kiyayya take ba zan yarda na sake aikata kuskure a karo na biyu ba, kuma ba zan yarda na shiga tsakanin soyayyar kowa ba, yadda rayuwar Noor take ba zan yi mata sha'awar ta zauna da wadda bata so ba”


Ya dauki wayarsa ya mike tsaye ya fice a office din a fusace. Hafiz ya bishi da kallo yana murmushin takaici. 


“Ba laifinka ba ne laifina ne, kuma zaka gane ka yi da ďan halak...”


Ya fada sannan ya cije bakinsa ya hade rai.