Chapter 14
Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: ***
*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*
✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧
𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
*Chapter 14*
“Kasan halinta ai da shirme da ma dai baka bata wayar ba”
Mama ta fada sai ya juya ya kalleta.
“Na dauka magana zata yi masa ta hankali amman meye na fada masa magana haka gatsai, babban mutum ne fa Mama kawai yana da saukin kai ne shiyasa Noor ta same a ruwan sanyi”
“Yanzu aikin gama ai ya gama, sai a tari gaba, ka je ka bashi hakuri kace baka sani ba ta dauki wayarka ta kira shi”
“Haka zan yi”
Ya juya ya fita Mama ta bi bayansa ni kuma na zauna ina ta aikin kuka. Yadda na kwana banci ba haka na wuni haka wani daren ya sake tararda ni na kasa cin komai sai ruwa kawai nake iya sha...
A daren ma sai na kasa bachi saboda tunanin Zafeer ko ya dawo ko kuma yana can, a wane hali yake a can? Wace kalar azaba suke gana masa? Me zai saka ma su kama shi? Na ji yayi abun da be dace ba amman ai taba shi aka yi domin be taba zuwa haka nan kawai ya ci mutuncin Kareem ko ya masa wani abun ba sai yanzu.
Mama ce ta shigo har cikin damunmu a lokacin da Hana take shirin makarantar Islamiya kasancewar yau assabar ba kamar sauran ranakun da take zuwa makarantar boko ba. Ta zauna kusa da ni ta aje min kunun.
“Noor daure ki sha idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zata wahalar da ke, kuma ita kaddara ba a kauce mata komai wayon mutum, idan Allah ya kaddara Zafeer mijinki ne zai aureki babu wadda ya isaya hana, idan kuma Allah yayi shi ne mijin ba ko an taru an hadu za a daura muku aure ba zai dauru ba, kalli yadda kika rame cikin kwana daya da rabi, kin koma kamar ba ke ba, ki yi hakuri kinji ƴata”
Ta kwanto da ni jikinta sai na ji sanyi a raina na lallabar da ta yi min da kuma kokarin kwantar min da hankali. Na bude bakin a hankali ta fara ba ni kunun ina sha har na sha rabin kofin sannan na ji na koshi.
“Na koshi Mama”
Hana ta kalli kunun ta kalleni.
“Lallai na yarda kina son Zafeer kalli yadda kika natsu kika koma kamar ba ke ba, kuma yadda kike fushi ko kuka baki rabuwa da abinci amman yau dubi yadda kika ki cin abinci”
Na kalleta kawai na dauke kai domin ni kadai na san yadda nake ji a raina ni kadai na san halin rayuwar da bake ciki
“Ni ma dai na yi mamakin yadda noor ta natsu kamar ba ita ba”
Mama ta fada kamin ta yunkura ta tashi tsaye ta dauke kunun ta fice daga dakin. Hana kuma ta gama shirinta ta kama hanyar makaranta, aka bar ni a dakin ni kadai ina jin jikina babu karfi tunani ne ko kuma dai yunwar da bana ji ce take karya garkuwar jikina. Ina daga kwance na ji sallamar kawata Zainab, na tabbatar a lokacin Mama bachi take domin ban ji ta amsa mata ba, wata kila kuma tana bandakin ne ko kuma ta fita ba tare da na sani ba. Cikin dakinmu ta shigo ganinta ya saka na tashi zaune domin na san ba zan rasa labarin Zafeer a bakinta ba.
“Noor amman dai baki da lafiya ko?”
Na daga mata kai.
“Me yake damunki?”
“Ni ma ban sani ba”
Ta yi shiru tana kallona kamin ta kawar da kai ta ce.
“Wata magana na ji ana ta yi Noor, ko da yake dai ba zan boye miki komai ba gaskiya Zafeer ma ya fada min kuma ya aiko ni gurinki na kawo miki wannan takardar, amman ina son na san me ya hada ku Noor?”
“Ba abin da ya hada mu, me kika ji?”
“Baki ji an kama Zafeer ba? Jiya misalin sha daya na dare ya dawo gida, kuma kamin a kama shi ina ta jin magana sama sama cewar ke da mahaifinki kun bi kudi wai ana son a aura miki wani ba Zafeer ba, ance har da gida ya siyawa Babanki kuma yana kawo muku kayan dadi a gida”
Mamankin jin cewar ya siyawa Babana gida ba abu ne na mamaki ba, wata kila Baba ne ya fada wata kila kuma abokansa. Amman zancen yana kawo mana kayan dadi wani zance ne da ban san da zamansa ba. Kuma ban san wata rana da Kareem ya kawo mana kayan dadi haka nan siddan ba, har sai idan ni na shigo da su, jin cewar mahaifina da ni kaina mun karkarta ga mai arziki wani abu ne da ya fi ko wane yi min daci, domin idan har abun da Baba yake kudiri ya tabbata mutane za su yi mana kallon maciya amana ne. Musamma ni babu ta inda zan iya wanke kaina. Ta damka min takardar dake hannunta.
“Gashi Zafeer yace na kawo miki, kuma Noor da gaske ne Babanki yace kar Zafeer ya sake zuwa kofar gidanku?”
Hawaye na amsar tambayarta domin su suka fara fita madadin kalma a bakina.
“Ina ganin kamar da akwai matsala a kasa Noor baki son fada ne kawai, ko dai dole ake son yi miki?”
Nan ma bance mata komai ba, zata sake yin wata maganar ta ji muryar Mama da ta fito daga bandaki.
“Zainab ce”
Sai ta tashi da sauri ta fita daga dakin tana gaisawa da Mama. Ban bude takardar ba sai da ta fice gaba daya daga cikin gidan, ina warwarewa gabana yana faduwa kamar ance zan karanta sakon mutuwarsa ne a ciki.
“Noor... Me yake faruwa? Nace ki zo ki same ina son magana da ke kin ki, na hadu dake na miki magana kin ki ki amsa ni, an kama ni jiya na yi tunanin zaki zo ko da gidanmu ne ki tambaya ko ki kira wayata, amman na tambaya baki yi ko daya ba, why? Da farko na dauka ko Baba ne kawai aka yi nasarar sauya masa ra'ayi kaina, amman jikina yayi sanyi a lokacin da na ji baki neme ni ba, ko dai ke ma ya sauya miki ra'ayi akaina ne Noor? Shekara uku da muka yi a tare kike son batawa saboda kudi? Kina son ki manta da ni ki rayuwa da wani saboda kudi? Haba Noor kin san fa ina sonki, jiya da na dawo gida ke na fara tambayar kin zo, Inna ta yi kamar zata kashe ni saboda haushi, amman hakan be hana ni rubuto miki wannan wasikar ba a yau kuma zan sake rokokin ki a karo na karshe... Ina son ki fito mu hadu a bayan islamiyarku, zan jira ki a gurin daga yanzu har zuwa azahar, ina son mu yi magana ne Noor bana nufin cutar dake, kuma hakan zai karyata abun da zuciyata take hararon game dake, na san ke karamar yarinya ce kuma kina son rayuwar jindadi, amman hakan be isa ya saka ki yi watsi da ni ba ki kama wani da baki da tabbacin ko zai iya rike ki... Noor in har baki fito ba to ni ma zan hakura dake har abada kuma hakan yana nufin ya sauya miki ra'ayi akaina kenan!”
Ina karatun hawayena na jika takardar, Zafeer ya zo min da wani abu mai nauyi da ba zan aikatawa a yanzu ba, domin ba zan tsallake maganar mahaifina kuma na yi silar mutuwar auren mahaifiyata a yanzu ba. Ina sonsa amman Baba ya shata liyi a tsakaninmu. A nan wata zuciyar ke ce min na fita naje na dawo ai Baba baya gidan kuma be san an yi ba, wata kuma na ce min na lallaba Mama na ce ta roki Baba naje an ga Zafeer ko da na iya yau ne kawai. A cikin duka shawarwarin ban dauki ko daya ba, A kowane sakon da minti idan na tuna Zafeer yana can yana jirana sai na ji hankalina ya tashi, a haka na wuni a dakin ina kuka har na ji kiran sallah Azahar.
Shinkafa da miya na daga cikin favorite food dina amman ranar sai na kasa cin wadda Mama ta girka. Da dare ina jin lokacin da take labartawa Mama cewar tun ranar ban sake cin komai ba har yanzu, a madadin Baba ya ji tausayina sai ya rufe ta fada wai ita take goya min baya nake wannan iskanci. Tashi na yi zan fita sai Hana ta fara kokarin hana ni.
“Noor karki fita”
“Magana kawai zan yi da Baba”
Na amsa ta sannan na fita na isa har gurin da Baba yake na risina kasa ina kuka.
“Baba dan Allah dan Allah Baba ka yi hakuri karka aura min wani idan ba Zafeer ba, Wallahi Zafeer nake so Baba shi kadai nake so, idan na auri wani ba shi ba mutuwa zan yi Wallahi”
Ya haska ni da fitilarsa mai haske...
“Eyyyyyyeeee lallai duniya ta miki dadi, tabbas kin samu yadda kike so Noor, yanzu har abun ya kai ki dubi idona ki fada min ga wadda kike so ki aura? Duka nawa kike? Ke har wata soyayya kika sani ma? Dan uwarki can da da ake aure wata soyayya aka sani amman yanzu saboda zamani ya lalace duniya ta bude muku ido kuma uwarki ta saka kin raina ni shiyasa kika zo kika zame ni kina fadar zaki mutu idan ba Zafeer ba?”
Ya juya gurin Mama ya rufe da fada tana amsa masa sai ya rufe ta da duka ni kuma na yi hanzari tashi cikin karfi hali da rashin karfin jiki na tare Mama sai ya hada ni da ita yayi mana duka kamar be san inda muka fito ba. Dukan Mama a gaban idonmu wani abu ne da yake saka mana tsanar mahaifinmu kullum kuma wani abu ne da Baba yake jin dadi aikatashi, wata kila yana tunanin hakan zai saka mu kara tsoronsa ne abun da be sani ba hakan yana saka sanar kiyayyarsa a zuciyarmu ne kawai kuma ya kan saka mu yi masa kallon wani azzalumin mutun tsabanin Uba da kowa wane yaya suke yi ma iyayensu.
“Dacan ina cewa Haihuwar Noor ce ta kawo min kariyar arziki, ashe ke ma baki so na da arziki duba abun da yaron nan yayi mana daga zuwansa, kuma inda zata huta ne ba gidan wahala ba amman kin bi rana da safiya idan na fita kina hore mata kunne kar ta saurare shi idan ya zo ko? To ni zan kira shi zan bashi ita sadaka na ga uban da zai hana auren idan akwai wadda ya haifa min Noor din, gaba daya baki iya ba su tarbiya ta kwarai saboda baki san zafin haihuwa ba”
Haka Mama ta mike tsaye tana kuka tana fadin.
“Malam idan har ka aikata hakan ni kuwa zamana a gidanka ya kare, ba ta yadda zan zauna ka wulakanta ni kuma ka aurar da yata a inda za a wulakanta, babu yadda za'ayi wadda ka aura mata ya ga dararja ko taka, babu ta inda zata yi kima a gurinsa, mutumen da be bude baki yace yana sonta ba saboda ya siya maka gida zaka ce ka dauki Noor ka bashi sadaka bayan kuma yarinyar nan ba shi take so? Wannan abun kunyar har ina?”
Baba ya dan matsa baya ya ce.
“Ni kike fadawa Haka Hajara?”
“Na fada maka Malam Naziru, ka yanka ni yau ka ci, na gaji da kai na gaji da halinka...”
Baba ya nufi i da fitilarsa take ya duka ya dauka ya haska fuskar Mama da kyau.
“Hajara yau ni kike fadawa haka? Idan kika sake fadar wata kalamar a gareni marar dadi to a bakin aurenki...”
Wani irin karfi da kuzari da ban san Mama da shi ba, ta yi sufa ta isa gurin da Baba yake tsaye ta saka hannayenta biyu ta tureshi da karfi sai da ya fadi kasa.
“Na aikata wanda ya fi wannan ka kashe ni yau karka bar ni na kwana da rai... Tun da na aureka ban huta, yara har sun girma su ba su huta ba ni ban huta ba, cin mutunci babu kalar wadda baka min ba, to na gaji aure kuma na hakura da shi na fi sha'awar na mutu a haka”
Ni da Hana muka nufi Mama muka rike ta da karfi muka kuka domin ba halinta ba ne, macen dake tsoron daga kai ma ta kalli Baba yau ita ce ta saka hannu ta ture shi a kasa.
“Kalu Innalillahi.... Wa'Inna..... Ilaihirraji'un.... Hajara... Ba ke bace, Wallahi ba ke bace..”
Yana fada yana girgiza kai, sai kuma aka yi sa'a nepa ta dawo a lokacin, daga ni har Hana muna kallon yadda yake yunkurin tashi ya kasa domin ba karamar faduwa yayi ba. Na saki Mama na nufi inda Baba yake na rika shi ya mike tsaye sai dai be tsaya daidai ba hannunsa daya yana rike da kunkurunsa, na nufi inda fitilarsa take na dauko na kawo masa sai ya karba ya nufi kofar gidan ya fIce ba tare da ya sake cewa komai ba. Ni kuma na gurin ina jin kamar an dora wano nauyi a kai saboda na zama silar fadan iyayena a yau ma, gashi an doki Mama kuma Baba yayi rauni. Na dade a haka ina hawaye sannan na nufi kofar dakin Mama na zauna na fara rusa kuka kamar ba ni ba, Mama da kanwata Hana kuma suna cikin daki suna na su. Shigowar Baba ne ya saka na tashi tsaye da sauri kuma na yi hanzarin yanke kukan da nake ina kallonsa tare da wasu abokansa biyu.
“Ina take?”
Suka tambaya bayan sun yi sallamar da ban samu amsa musu ba saboda kuka da nake ta kokarin ganin na ci karfinsa.
“Tana can ciki ko ta fita Noor?”
Baba ya fada yana tsaya daga can baya su kuma suka shigo cikin gidan suka isa gurin kofar Musamman ma Malam Isuhu da ya kasance Malamin Addini.
“To wai magana suka yi ne ko me? Ke Noor Mamanku tana ina ne?”
Na nuna masa kofar daki. Baba kuma ya ce.
“Ai na san ba ita bace yadda ta tureni din nan ba karfinta ba ne, kuma duk zamana da ita bata taba nuna min yatsa ba, amman yau tureni ta yi a gaban yara, yanzu haka bana iya tsayawa daidai, ai ba ita ba ce shiyasa ban sake ce mata komai ba, na fita na kira ku ayi abun da ya dace idan karatu za a mata ko addu'a sai ayi”
Baba na rufe baki Mama ta taso ta fito daga dakin a fusace.
“Babu wasu aljannu Malam Isuhu kar ya wahalar da ku, azaba ce da zaman auren na ukuba na ganshi a gidan har na gaji, yace idan na sake yi masa masifa a bakin aurena to na yi aure ya kare, ka aurawa Noor wadda duk ranka yake so amma zamana a gidanka ya kare, yara ba kanana ba ne da wayonsu ranar da duk suka so ganina sai su tararda ni inda nake”
Malam Umar da Malam Isuhu suka juya suna kallon Baba cike da takaici da mamaki.
“To wai miye silar wannan abun ne?”
Baba ya nuno ni da fitila ya karaso cikin gidan yana kashe min ido.
“Ka ga yar iskar yarinyar da ta assasa komai nan, ita ce silar komai ita ta lalata lamarin nan”
Mama ta shiga tsakani ta tare ni.
“Babu ruwan Noor a ciki, ni ka saba yi da ni ka yi da ni, yarinyar da abinci ma ya gagareta ci saboda mugun bakin halinka ita kake dorawa laifi, daman kullum cewa kake saboda na haifo maka ita rayuwarka take cikin matsala, saboda baka yarda da kaddara ba”
A take masifar ta koma gurin Mama ya koma yana haskata da fitila yana tafiya a karkace ka ganinsa ka san kunkurunsa ya bugu.
“Toh... Wai da kike wannan hakilon kina hauka kin isa ki hana ni aikata abun da na yi niya ne? Ai daman na fada miki idan kika sake magana a bakin aurenki to ki je na sake ki saki uku Hajara na gaji da ke na gaji da halinki, kije kya gani Noor kuma sai na aura mata yaron nan mai mutunci mai karamci sai dai ki hadi zuciya ki mutu, ita kuma idan ta haihu ta bijire min na gani...”
Ban san lokacin da na dora hannu a kai na kwala ihu ba, domin na san miye saki na kuma san abun da saki uku yake nufi babu sauran zama a tsakanin iyayena kenan. Kuma duk ni ce sila. Malam isuhu ya rufe Baba da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Malam Umar ma fadan yake yana Allah wadai da abun da Baba ya aikata a gabansu. Hana kuma ta shiga zubewa kasa tana tashi tana ihu.
“Mun shiga uku mun lalace, Mama idan kika tafi mun shiga uku Innalillahi...”
Na yi zaton Mama zata tausaya mana ko ta tausaya ma kanta amman ban ga alamar hakan a tare da ita ba, domin babu hawaye ko daya a idonta. Sai ma juyawa da ta yi ta shiga dakin ta fara hada kayanta. Malam Umar yana bata hakuri sai abokinsa da suka zo tare wato Malam Isuhu ya ce.
“Hakuri me zata yi lamari ya lalace ya sake ta har saki uku? ABu dai kamar wadda aka jefa, baka dubi yaranka ba baka kalli kai kanka ba ka saki mace da girma ya fara kama ku a tare, har ina aka taba haka?”
Baba ya fara kokarin kare kansa.
“Baka san halin matar nan ba, Wallahi hakuri kawai nake da ita, yanzu ai sai ta koma can ta zauna cikin dangi ta ji idan akwai mai iya daukar abun da nake dauka, wulakanci take min kala kala duk ita ce silar lalacewar yarinyar nan Noor, ga bakinciki kamar ba mijinta ba, bata kaunar wani abun farinciki ya same ni, na gaji....”
Takaici ya saka Malam Isuhu ficewa daga gidan, Mal Umar ne kadai ya tsaya ya fitar da Baba yana masa fada abun da yake be kamata ba. Na taka na isa cikin dakin na tsaya ina kallonta.
“Mama tafiya zaki yi?”
“To zama zan yi? Auren ubanku har aure ne? Ku dai da yake ubanku dole ku yi hakuri ku zauna a haka amman ni yanzu kam Allah ya sama min yanci, kuma kin fi kowa zama sakarya wawuya a gidan nan, idan zaki canja hali ki canja idan kuma ba zaki canja ba, to zaki sha wahala rayuwa ba yanzu ba har nan gaba”
Na matsa baya na jingina jikin kofa ina kallon Mama har ta gama hada kayanta.
“Kar wadda ya bini yana min ihu kuma kar wadda ya sake min kuka, kukan be hana ni tafiya, kuma ni da mahaifinku zama ya kare har a bada....!”
Haka ta saka kai ta fice a fusace ko kadan kuka be ziyarci idon Mama ba, ni yau sai ta canja min ma kamar ba ita ba. A dakin muka zauna na tsawon lokaci muna kuka ni da Hana dake ta dora min laifi.
“Sai da na ce kar ki fita amman baki ji ba, gashi nan kin yi sanadin da Mama ta tafi, jindadi da sanyi da muke ji ta bangarenta kin yi sanadin da muka rasa shi, kuma duk saboda Zafeer din nan ne, kamar kanki farau soyayya, yanzu kuma sauran ki yi sanadin da Baba zai tsine miki sai kiji sanyi, kullum ke kike janyo mana matsala a gidan nan kullum da ke ake kuka...”
“Babu wadda zai sake kuka da ni Hana ba zan sake aikata abun da wani zai yi kuka da ni ba”
Na tashi ina jin jikin babu karfi, gurin da Yaya yayi min wacan dukan yana taso min da ciwo. Na koma dakinmu na kwanta hankali be kara tashi ba sai da na ji shigowar Yaya Nabil domin na san ba zai min da sauki ba, a take na tashi zaune na zubawa kofar dakin ido ina jiran shigowarsa. Shiru shiru ban ji ya shigo ba, hakan ya saka na tashi tsaye na isa gurin kofar sai na hango shi zaune bakin kofar Mama rike da yar leda ya kifa kai da guiwa a kasa...
*** **** ***
GAM..... ya rufe motar ya saka key din a aljihunsa sannan ya fara waigewaige inda zai samu yaron da zai aika. Daga karshe sai ya nufi kofar gidan ya kwankwasa yaja baya ya tsaya yana kallon agogon hannunsa da ya nuna karfe goma sha daya da rabi. Nabil ya fito yana murza ido da alama a lokacin ne ya farka daga bachi.
“Nabil kana ciki...”
Sanin cewar abokin ogansa ya saka Nabil ya mika masa hannu da sauri suka gaisa.
“Ina Baba fa yana ciki?”
“Aa magana zaka yi da shi? Allah yasa ba wata matsalar bace?”
“Aa babu wata matsala na zo ne kawai na yi magana da mahaifinka?”
“A game da ni ne? Ko oga ya kore ni ne? Saboda Noor ta ari wayata ta yi masa maganganu marasa dadi”
Hafiz ya girgiza kai.
“Aa ba haka ba ne, wannan abun ai be kai a koreka ba, ni kaina na san halin Noor a yanzu balle kuma shi Kareem da ya fi kowa fahimtar ta, ba mamaki ace baka sani ba ta ari wayarka ta kira ko?”
Ya daga kansa da sauri.
“Eh ba da sanina ba ne”
“Ba matsalar ce ta kawo ni ba, wata maganar ce dai mai muhimmanci, kuma bana tunanin Kareem zai koreka gaskiya saboda ya san hanyar cin abinci ka a nan take, Kareem yana da kirki sosai fiye da yadda kake tunani, kuma yana da saukin kai amman be san ma na zo nan ba ”
Nabil ya ji hankalinsa ya dan kwanta kadan, sai dai tashin hankali rashin mahaifiyarsu yana nan a cikin ransa. Ya juya zai koma cikin gidan.
“Bari na sallamo maka shi”
Hafiz yaja ya matsa baya ya jingina da motarsa yana kallon yanayin unguwar, ta dayan bangaren kuma yana jin bakinciki yadda Kareem ya watsa masa kasa a ido. Babu bata lokaci Baba ya fito yana gyara hula, ganin Hafiz ya saka shi murmushi ya karasa da kansa ya mikawa Hafiz hannu suka gaisa cikin girmamawa.
“Yanzu ake tafe?”
“Eh Wallahi wani abun ne ya kawo ni, na yi tunanin za a fi samunka da safe ne shiyasa na zo kamar yanzu...”
“Maa Shaa Allah aiko na jidadin zuwanka, daman ina nemamka har ina shirin fadawa Nabil ya kira min kai”
Hafiz yayi fuskar mamaki tare da murmushi a fuskarsa.
“Ikon Allah toh Allah yasa lafiya dai?”
Baba yayi dariya.
“Lafiya kalau, sai alheri a game da Noor ne amman dai bari na fara jin abun da ke tafe da kai tukuna”
“Aa Baba a sawun giwa ya take na rakumi, fada min na ji dalilin neman tukuna”
Baba ya gyara tsayuwarsa ya jingina da motar Hafiz tare da sauke ajiyar zuciya.
“Watooo ka san lamarin mace, ko da babba ce balle karama kamar Nooriyya, ni abun ma sai yayi min wani iri Wallahi, ina ce yaron nan yaje yayi muku tashin hankali jiya?”
Hafiz ya daga kai sama.
“Eh haka ne, shi ne ma dalilin zuwa na bada hakuri kuma na bada shawara....”
“Toh ai saboda kai ne yaje yayi wannan tashin hankalin”
“Saboda ni kuma Baba?”
“Kwarai kuwa, ai yarinya buga kafa ta yi a kasa tace kai take so, saboda na yi masa maganar idan be shirya ba to fa ya kauce saboda ina son na aurar da ita, shi ne ya zo yana rokonta yana rokona sai na sake zaunar da su na fada musu dalilina na son aurar da ita, sai ya tashi yana zage zage kasan abun ka da marar tarbiya, ita kuma ta fusata tace ba zata ma sake kula shi ba, to in takaice maka da magana uwar ta saka ta a gaba da masifa tace to idan ta juya masa baya sai ta fitar da wadda take so, ita kuma tace kai take so...!”
Da mugun mamaki Hafiz ya nuna kansa.
“Ni kuma Baba? Ni ko dai abokina Kareem?”
Baba yayi dariya kamar gaske.
“Kai din dai, sanadin haka uwarta ta yi fushi yanzu haka bata cikin gidan ma, amman waka a bakin mai ita tafi dadi bari na kira maka ita Nooriya sai ka yi magana da ita ka ji”
Kamin Hafiz yayi wani yunkuri Baba ya nufi cikin gidan ya shiga. Hafiz ya nuna kansa har lokacin mamaki yake.
“Ni...? Baba dai ba fahimta da kyau ba”
Ya furta yana kallon kofar gidan zuciyarsa na bugawa da karfi...
____________
Toh fa ana zaton wuta a makera....
Anya ana samun uba irin Baba Naziru kuwa?
Auren Mama dai ya kare amman an bar baya da kura.
Nikam na tambaye ku mana, Zafeer be baku tausayi ba?
Hafiz na kokarin kulla alheri reshe na shirin juyewa da mujiya yaya kenan?