ALƘALAMIN SO

Page 7

by @dijaham20

ALƘALAMIN SO




DIJAH(AM)OUM AMANI



PAGE 7



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




🎤🎤🎤🎺 ALBISHIRINKU


Amarya da💃💃💃💃uwar gida da masu taron biki ko suna ko taron birthday, basai kin wahalar d kanku wajen siyan kayan fitar bikiba kizo UMMU SUDAIS tashare muku hawaye. Zatabaku hayar duk abunda kuke bukata akan farashi me sauki


i€¥^


Muna bada wedding gowns, alkebbar kai amarya, kayan Fulani nayara d manya farare dakuma blue black,, Muna d abun dauri head & shoulders, Muna d kayan kamshi kala kala sai Wanda kikeso,sai angwada akansan na kwarai💃💃



********


Slm jama a Muna d Zumar nono d kibbah da duwawo jadidan inkikasha Bata Mikiba kizo abaki kudinki,

Kiyi kyau kalar Yan gayu,kiba maikyau ba da kwayaba


Haba hajiyata kina zaune 

Oga najin haushinki jiki duk kasusuwa Dan Allah kidaure kisiya ki gwada kigani batada Wani side effects. Sai angwada akansan na kwarai


Muna da Sabulun tsarki (liquid soap) inganttacce yana mgnin kyakayin gaba zafin saduwa yana ciko d mace ga kuma y matseta yana Kara dadi d gardi,yana Kara ni’ima yana dauke warin gaba, dade sauran matsalolin mu na mata 


Munada turaren tsugono 

Dakuma na kaya

Muna bada renting duka a wajen Ummu SUDAIS


Zaku iya tuntubar mu ta wannan numbern

*** 





  Ya Haidar mai zai yi in ba dariya ba, shi kan sa Abba juyar da kan sa yayi yana kokarin hana kan sa dariya, da ƙyar ya samu ya ɗan gyara yanayin fuskar sa kafin ya juyo ya kalle su fuskar sa a dan haɗe ya ce "zaku saki juna ko sai na zo nan na wanke ko wannen ku da mari, ban da rashin ji ku ɗin muharraman juna ne da zaku wani rungume juna".


Jin muryar Abba a dan fusace yasa muka saki juna kowa na share hawaye.


Girgiza kai kawai Abba yayi ya riƙo hannu na muka wuce part din mu, sai juya wa nake Ina daga wa Sultan hannun shima yana daga mun hannu a haka har muka shige part ɗin mu.


Da sallama na shiga palon har lokacin hannu na yana cikin na Abba, Mami ce kawai a palon da bowl na fruit salad tana ci a nutse, ɗagowa tayi ta kalle mu gani na a bayan Abba ya sata murmushi cikin tsokana ta ce "wa nake gani kamar yan makaranta?"


Rau_rau nayi da ido na alamun kukan zan sake, dole ta shiga lallashi na da bani haƙuri.

  Ni dai duka rai na a bace yake gashi da Ya Kausar ta dawo daga school ma tsokana ta kawai ta dinga yi ni dai ban kula ta ba don haushin kowa nake ji a gidan.


Shirye_shirye ake mana sosai gashi wani abin baƙin cikin wai makarantar baa zuwa da provisions sai dai a school fees din har da pocket money ake biya, a sati sau biyu zaku dinga zuwa school shop kuna shopping din abubuwan da kuke so.


Haka aka gama haɗa min kayana a sabuwar akwati ta da Abba ya siyo min babba mai kyau da daukar ido, saboda rashin ji irin nawa ranar da naje yiwa Hajja sallama sai da na taho da yajin data daka min mai dan yawa. Sam ban bari Mami ko Ya Kausar sun gani ba don fada kawai zasu min.


  Yau Sunday tun asuba ban koma bacci ba saboda yau ne ranar tafiyar mu gashi kuma Baaba ya ce mu shirya karfe 9 zamu tafi saboda nisan makarantar.


Duk yadda zan fada muku irin baƙin cikin da nake ciki baza ku fahimta ba, makarantar shegen tsirfa gare su, bedsheet biyu kadai suka ce mu dauka daya fari sai navy blue, hijab shima guda biyu kaɗai fari sai baƙi ko mai dai sun rubuta abin nasu abin haushi.


Sai karfe 8:30 na shiga wanka shima sai da naga Maryam ta shigo a shirye tana ce min ban shirya ba dama sannan na tafi wanka, a gurguje na fito bayan na boye yaji na sosai a jiki na.


Da Mami da Umma zamu sai Ya Hamza da Ya Haidar sai kuma Sultan, tun da muka dauki hanyar nayi shiru naki ce wa komai sai dai na bude ido na sosai Ina kallon hanya, tafiyar fiye da awa daya muka yi kafin mu iso katon gate din makarantar, shima bayan an bude mana sai da muka yi tafiyar 10mins a mota bamu hadu da komai ba bayan manyan duwatsun da suke mana oyoyo, tuni jikina ya gama sanyi.


Mun hadu da students da suka fara dawowa suma ni dai sai rau rau nake da ido amma naki yadda nayi kuka don kar ma wasu students din su gani su rai na ni, Maryam dai sai kukan ta take yi bama da aka raka mu hostel din mu taga an raba mana daki ni Ina room 1 ita tana room 8.


Ni dai ajiye kaya na kawai nayi a room din da aka bani mai ɗauke da gado biyu sama da kasa ya kama ta mutane hudu kenan, bin Maryam nayi zuwa ɗakin ta wacce har lokacin take sharar hawaye duk kuwa da cewa ita dakin nasu ma kowa ya hallara da alama tun da ragowar students din sai shirya Kayan su suke a wardrobe.


Zama nayi a gadon ta dake kasa na shiga shirya mata kayan don ita da dukkan alamu in aka bar ta ba abinda zata yi, tun da su Mami suka tafi take kuka ni kai na dauriya kawai nake yi amma kukan nake matukar so nayi.


 Gaisawa nayi da ƴan ɗakin suka fada min sunan su da class din su, yar SS3 ce sai yan Js 2 su biyu, muna ɗan hira sama sama har na gama shirya mata komai din ta hatta gado kuwa sai da na gyara mata. 

 Sallama nayi mata na wuce room din da aka bani don shine na farko kana shigowa New hostel din, ɗakin na same sa da mutane uku, kallon su nake kamar yadda suma suke kallo na don ganin su, yaran biyu baza su wuce shekara 11 ba sai dayar da nake tunanin zata iya 14 amma zan iya girmar ta da kaɗan tun da ni ma har ynxu ko 15 ɗin ban karasa ba.


Kallona suke sai dai ganin yadda duka suke kallona kamar a dan tsure yasa ni sakar musu Murmushi Ina cewa "ya kuke?"


A tare suka ce "lafiya qalau".


Murmushi na sake yi mai faɗi na ce "suna na Aisha Muhammad Gamba Ina SS2 new comer ce ni", na karashe ina kara faɗaɗa fuska ta.


Wacce zata kai 14 din ce ta ce "suna na Karima Mahmud a Js 3 nake ni tun Js 1 nake man" ta fada ita ma tana murmushin.


Dayar ce ta ce "suna na Amina Abubakar Js 1 nake".


Dukkan mu sai muka mayar da kan mu kan ɗayar wacce tun da na shigo haka kurin naji yarinyar ta burge ni ban sani na ko dan ganin ta da nayi fara mai ɗan kyau ne oho.


Murmushi tayi daya sa kumatun ta duka biyun lotsa wa ta ce "suna na Zarah Aminu Js 1 nima nake, kuma ni ce a saman gadon ki".


Murmushi nayi musu gaba daya na ce "Allah ya saba halayen mu"


Duka suka amsa da "Ameen", ban tsaya gyara kaya na ba na shiga taya Amina da Zarah jera Kayan, ita Amina a saman gadon Karima take, ita Karima tun da ta gama gyara kayan ta a wardrobe ta fice tare da friends din ta su kuwa basu San kowa ba kamar yadda nima ban sani ba din.


Sai da na tabbatar komai nasu ya kimtsu sannan nima na shiga jera abubuwana a wardrobe, books din da aka bamu kuma na saka a study table din dake gefen gado na wanda yake mallaki na kenan duk da ma dai study table din huɗu ne ko wanne da kujerar sa kawai na zabi wannan din ne don shine a jikin gado na.


Toilet na shiga na duba na gani kana shiga sink ne guda biyu sai kofofi uku biyu a jere daya daga lungu, na jeran wajen wanka ne sai toilet kuma dake lungun ko Ina fes hadda kayan wankin toilet din da za’a buka ta.


Alwala kawai nayi na fito, ganin Amina da Zarah kowa a zaune a kan kujerar table ɗin sa sun yi shiru sai suka bani tausayi matuka, Murmushi na musu na ce "ku tashi kuyi alwala mu fita naga masallaci ɗazu da muke shigo wa acan ake sallah kuma gashi an kira sallar".


Duk mike wa suka yi suka shiga toilet yin alwalar, Ina tsaye jiran su sai ga Karima ta dawo, Murmushi ta min tface"Sister Aisha an Kira sallah kuzo mu tafi masallaci kafin a tTara .


Kafin na bata amsa su Zarah sun fito kowa Hijab din house wear din sa kawai yasa muka fito, Karima ke min bayanin masu sanye da house wear ash seniors ne su juniors nasu light brown ne.


Ko a masallaci sai manne min su Zarah suke da alama a tsorace suke har lokacin.


Bayan idar da sallar mun fito na hadu da Maryam, murmushi nayi sosai Ina dafa kafadar ta na ce"Maryama ya kadaici?"


Bata bani amsa ba sai bayana data kalla tana kallon su Zarah wadanda suka gaishe ta, mai da kallon ta kai na tayi alamar tambaya, kafada na daga mata na ce "a room din mu suke Js 1 suke sai Karima a Js 3".


Cikin wani yanayi ta ce "ke ce kaɗai a Ss kenan kuma kece shugabar dakin?"


Taɓe baki nayi na ce "to gashi nan kuwa kina gani ni ma nayi mamaki dai".


Bata sake cewa komai ba nima ban sake magana ba sai tasa keyar su Zarah da nayi muka shiga zagaye school din, ba inda bamu je ba ban da classes area da ke kulle.


Sai bayan magriba aka bamu abinci mai rai da lafiya, na kuwa ci abinci na sosai don ni ko breakfast ban yi ba..




*********

Cikin sati uku da zuwa na makarantar zan iya cewa ɗai_ɗai kune basu san Aisha Gamba ba, ba wai wani abun ne yasa aka sanni ba face abubuwa kalilan, na farko yawan merits din da nake samu a wajen teachers saboda amsa questions a class gashi duk Friday a assembly ana fadar wacce tafi kowa merits, sati uku kenan a jere ko yaushe ni ce dai nake fin kowa samu, sai kuma dalilin su Zarah wadan da suka zama kamar jela ta bama su kadai ba kusan gaba daya Js 1 din da wasu a Js 2 saboda assignment din da nake koya musu in basu gane ba.


Babban abinda kuma ya sake sani farin jini a gurin juniors shine yadda ko kaɗan bana yadda Ina kallo a musu mugunta. 


Na mai da hankali na sosai wajen karatu tun da duk sati ana bamu waya mu kira gıda yasa na rage damuwa, Ita Maryma dama ban san mai yake damun ta ba niɗai a sanin da nayi mata tun kuruciya bata da tara kawaye amma zuwan mu makarantar nan ta shige cikin wasu mara sa Jin maganar SS 2 da nayi mata magana sai ce min tayi so nake tayi ta zaman kadaici har ciwo ya kama ta? Dole na rabu da ita kawai na kawo ido na saka mata amma kam in har naga tayi wani abun da bai dace ba zama nake nayi mata masifa da nasiha sannan nayi wuce wa ta.


Ni a mate din mu Fatima Haruna kawai nake kula wa ita ma sbd naga yarinyar tana da brain ne shiyasa nake dan biye mata, nifa haka nake kun ganni sam bana tara kawaye nafi gane ko ma maye nayi da amini na Sultan.


Zauna nake akan gado Ina cin daya daga cikin snacks din dana siyo a shop, sanye nake da rigar house wear dita kai na sanye da hula baka, weekend ne kuma tun jiya da daddare na gama duk assignment dina gashi da asuba nayi wanki shiyasa nake huta wa ta, bamu dade da dawowa daga islamiyya ba wacce muke zuwa duk weekends da safe sai bayan azahar zamu dawo.


Shigowar su Amina ne yasa ni daga kai na kalle su, da mamaki na ajiye ledar snack din Ina mike wa tsaye ganin Karima da Amina sun rike Zarah wacce keta kuka hannun ta dafe da duka fuskar ta.


Mike wa nayi Ina karasa wa gurin su, hannu nasa na dago fuskar ta Ina cire hannayen ta da ta rufe fuskar da su, bude manyan ido na nayi da mamakin ganin shatin hannu a duka fuskar tata.


Kallon Amina nayi da take kuka ita ma na ce “me ya faru?”


Cikin kuka tace “Sister Aisha, Sister Nana ce ta saka ta wanki dazu da safe shine ynxu ta ce mata ta kwaso kayan ta kawo, kuma fa wankin har taya ta nayi don kar a samu matsala ma amma muna kai mata sai tace bata wanke ba jika sa kawai nayi ya shanya shine ya mammare ta kuma ta ce ta sake wanke mata”.


Ido na daya kada yayi jajir cikin masifa na ce “ta sake wanke war ko bata yi ba?”


A dan tsorace ta ce “ai Sister Nanan da friends din ta suna tsaye sai da ta sake wanke wa sannan suka ce ta tafi”.


A tsawace na ce “ban ce duk shegen daya saku aiki kuzo ku fada min ba?”.


Duk shiru suka yi har Zarah din, Karima ce tayi karfin halin cewa “Sister Aisha tsoro ne zai hana su zuwa fada miki tun da ba wanda bai san muguntar yan SS 3 din set dinnan ba”


Kara kallon fuskar Zarah nayi wacce har ta dan kumbara abin ka da farar fata, hannun ta na Kama na zaunar da ita akan gado na, cikin bada umarni na ce wa Karima ta dauko towel da ruwan zafi ta dan daddanna mata fuskar.


Mai da kallona nayi kan Amina na ce wuce ki kai ni in da shegun suke


Dan bude ido tayi zata yi magana sai dai yadda na mugun hade fuska yasa ta yin shiru kawai tayi gaba.

 

Fita muka yi daga hostel din namu zuwa babbar compound din hostel din, tafiya muka yi mai dan tsayi zuwa inda suke zaune a kan kujeru suna hira kamar ba sune suka gama cin zalin yarinya ba.


Duk da nasan gang din su amma sai da na sake kare musu kallo Ina gyada kai a rai na na ce (yan iska da an musu auren wuri da tuni sun haifi wacce ta kusa kai Zarah sun wani saki nonuwa ruguza ruguza a gaba)


Kallon keyar Nanan nayi kafin na dage da iya karfi na na sakar mata wani bahagon mari a keyar sai da tayi gaba ta kifa a kasa.


Dukan su mike wa tsaye sukai a dan razane, har ita Nanan daya mike tana shafa keyar ta dake mata wani mugun zugi.


Kallona tayi ta ce “wace ke dan uban ki?”


A fusace na ce “uwar kice Gamba don kut***** ubanki”




(Yarinyar Uncle ta ballo mana ruwa Jama’a nidai nayi ta kai na🫣😂)





DijahAM

***