SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

.

by @nkds

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*




A can ɓangaren kuwa


Zama Dr_Salahah tayi kana suma suka zazzauna a kujerun dake Kallon wanda ta zauna shiru office É—in ya É—auka gaba É—aya sun zuba ma ta ido suna jira suji abin da zata faÉ—a, a kalla sunkai mintuna biyar a haka.


Sannan Dr_Salahah ta É—ago daga rubuce rubucen da take yi tana kallon su, ta cire farin glass dake saÆ™ale a fuskar ta fararen idanunta suka bayyana kana ta fara magana cikin harshen hausa yadda gaba É—aya zasu fahimci abinda takeson faÉ—a musu da kyau.


"Wato Abin da Rahoton binkciken da muka gabatar akan Dr Haleesat Rashid Rayyan shi ne, akalla an ɗauki tsawon kwanaki biyar ana gana ma ta a zaba sannan binkciken mu ya nuna cewa an ɗauki tsawon kwanaki goma a kullum sai anyi Raping ɗinta sau biyu, bayan an gama kuma ana saka wani abu mai tsatsa kodai sanda ko ƙarfe ana goge duk wata alama ko hujja wacca zata nuna anyi ma ta fyaɗe.😭


Daɗin daɗawa kuma binkcike ya nuna ba iya maza ne kawai suka yi amfani da ita ba hadda ma mata sannan ta ƙarfi suke yi wanda hakan ne yasa duk taji ciwuka a jikinta da bakinta sai kuma hannunta da aka Rubuta wasu alphabet guda biyar.


"M_M_R_D_L."


Sune abin da aka Rubuta a hannun daman ta sai kuma tsakiyar hannun hagunta nan ma aka Rubuta "X" da alama É—aukar fansa ne yasa aka sace ta ba wai saboda kuÉ—i ko wani abun ba."


Tana faÉ—in haka tayi shiru tana kallon su.


Tun lokacin da Dr Salahah ta fara magana gaba ɗaya shiru suka yi suna kallon ta Alhaji Rafiq ashe suma ya yi ma lokacin da Dr ta ce anyiwa Haleesat ɗiyar ɗan uwanshi fyaɗe, shi kuwa Alhaji Riyaz ba abin da yake iya furtawa sai kalmar inna lil lahi har ƙarshe.


Abubakar ne kawai ya yi ƙarfin halin yin magana cikin murya wacca alƙalamin 'Nainarh Kd' bazai iya bayyana yanayin da yake ba.


"Yanzu Dr Salahah kina ganin Haleesat zata iya ci gaba da Rayuwa kuwa?...'


Shiru Dr Salahah tayi sannan ta bashi amsa da


"Gaskiya bani da amsar wannan tambayar naka Mister Mai Kyau sai dai kawai abin da na sani shi ne bamu da kayan aikin da zasu taimaka wajen kulawa da Lafiyar ta yadda ya kamata, sai dai akwai wani Babban Likita da muke buƙatar taimakon sa amma a halin yanzu baya ƙasan nan."


"Za'a iya fita da ita Abroad kuwa wannan taƙin da ake ciki?.''


Abubakar ya tambaya a dabke, Dr Salahah ta ce 


"Mister Mai Kyau ke nan wannan ai ba'a ridaga anzo maganar fita da ita Abroad ba tukunna, saboda Yanzu abu É—aya muke tsoron faruwar sa."


"Menene shi wannan abun?.''


Abubakar ya kuma tambaya, Dr Salahah ta ci gaba da cewa 


"Wannan abu É—ayan shi ne, muna tsoron kar ta sama Abrogating, ko kuma mental illness, da sauran su saboda abin da ya same ta."


Abubakar har ya buÉ—e baki zayyi magana ke nan aka banko Æ™ofar aka shigo, Sailuba ce hankalin ta a Mugun tashe da alama taji abin da suke tattaunawa ne, Æ™arisowa wurin su tayi cikin kuka take faÉ—in 


"Auntie Haleesat ce take buƙatar ganin ku dukan ku hadda Yaya mai kyau...''


Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Dr da Abubakar suka sauke fahimtar da suka yi bataji komai daga abin da suke tattaunawa ba.


Da sauri Abubakar ya miƙe tsaye ya fice daga office ɗin a 360 ita ma Sailuba tabi bayan shi, hannun Alhaji Rafiq, Uncle Riyaz ya kamo ganin yaƙi tashi amma sai ji ya yi hannun ya biyo shi. Da sauri ya juyo yana kallon shi a mugun tsora ce.


Kallon Dr Salahah ya yi a tsorace yake tambayarta. 


" Dr duba min ya mutu ko?.."


Ya yi ma ta Tambayar Like a Little kid sannan kuma hawaye yake yi.


Da sauri Dr Salahah ta Æ™arisa wurin ta shiga duba Alhaji Rafiq bayan tayi abin da zata iya ta É—ago tana kallon Alhaji Riyaz da ya zuba mata ido sannan cikin hawaye da murmushi ta ce 


"Bai mutu ba ya dai faÉ—a doguwar suma ne."


Wani wawan burki yaja daga ƙofar ɗakin yana hango yadda Haleesat Rashid Rayyan ta koma wata abun tausayi.

A hankali kamar kazar da kwai ya fashe ma a ciki ya fara taku a hankali yana ƙarisawa wurin gadon da take kwance.


Durƙusawa ya yi da duka ƙafafunsa yana kallon ta yayin da yake tariyo abubuwan da suka taɓa faruwa tsananin sa da ita, tun farkon ganin ta da ya yi a gidan su, da son ta da ya ke ma ta daga kallon farko, da ma yadda ya bayyana ma ta soyayyar sa a gare ta, amma saboda wani dalili nata tayi rejection nasa, da kuma yadda tasa ya ɗauka ma ta alƙawarin dashi kansa yasan bazai yuwu ba.

Na ya taimaka ya cire ta daga zuciyar sa domin kuwa ita É—in ba wani tsawon rayuwa ne zatayi ba a doron duniya.


Komai dawo masa yake sabo fil a zuciyar sa, bai san kuka yake yi ba, har sai da yaga tana girgiza masa kai, alamar a'a sannan yasa hannunsa wanda yake faman rawa saboda tsananin tausayinta da ƙaunarta dake zagaye dukanin ilahirin jikinsa da ruhin sa.


Ya share hawayen fuskarsa amma wasu ƙara zubowa suke hannun damansa yakai ya kamo nata hannun yana kallon ta cike da tausayawa game da tsananin ƙaunarta.


Zayyi magana, tayi saurin girgiza masa kai tana murmushin ƙarfin hali.


Sannan ta kalla su Hajiya Zinaru da Sailuba dake tsaye gefe sunyi curko curko sai share hawaye suke yi, murmushi tayi kana ta mayar da kallonta kan Rafi'at dake durƙushe can jikin gadon tana hawayen tausayin Ƴar uwan nata, da hannu Haleesat Rashid Rayyan tayima Rafi'at alama da ta ƙariso wurin, ko damuwa da cikin jikinta Rafi'at batayi ba ta ƙarisa wurin da sauri.


Har yanzu murmushin dake saman fuskar ta bai gushe ba, ga fuskar nan tata tayi wani haske na musamman sai faman shaining take yi, ga wani kyau na musamman da ta ƙara, amma kana ma ta kallon gurilla komai Rashin imanin ka saika tausaya ma ta wata ƙilama saika zubar da hawaye saboda Abin bakyan gani, tana jin jiki sosai sosai. 😭


Kamo hannun Rafi'at tayi sannan ta kamo hannun Abubakar tana murmushi ta haɗa wuri ɗaya kana cikin murya irin wanda daga ji kasan mai ita ba ƙaramin jin jiki yake ba ta fara magana.


"Kamar ko yaushe anaso mutum ɗan adam ya kasance mai kyautatawa ɗan uwansa zato ko ya ya ne, amma wannan zamani mutane masu kyautata zato sunyi ƙaranci a wannan Rayuwa...

Mister Mai Kyau ga Ƴar uwata kuma Auntie ta Rafi'at Rafiq Rayyan please ka taimaka ka riƙe ta da amana, ka sota ka ƙaunace ta kamar yadda na tabbatar da cewa ita ma tana ƙaunar ka fiye da Rayuwarta please Mai kyau ka taimaka ka riƙe mana ita amana. ir vosotros oír mí u cuál ?.. { did you hear me or what ? }...."


Tayi maganar tana dariya duk da cewa cikin ciwo take, murmushin yaÆ™e kawai Abubakar yake yi yama kasa magana sai faman girgiza ma ta kai yake yi alamar yaji kuma ya yadda zai riÆ™e alÆ™awari, kallon Rafi'at tayi kana cikin murmushi ta ce 


"Auntie Rafi'at please ga your lawful naki ki riƙe shi amana kin san fa yana ƙaunar ki ko?, dan Allah zaki riƙe shi da amana tunda kin san yana ƙaunar ki."


Cikin hawaye da murmushi Rafi'at ta shiga girgiza kai kana ta ce 


"Nasani Haleesat nasani sister..."


Kallon su Hajiya Zinaru da Sailuba tayi kana tayi musu alama dasu ƙariso da saurin su suka ƙariso wurin gadon har rige rigen riqe hannunta sukeyi.


Murmushi Sailuba tayi kana cikin hawaye da dariya ta ce 


"Auntie Haleesat kin warke zaki tashi mu ci-gaba da girka abinci tare muna wasanni kuma, Daddynmu yace za'a kama mutanen da suka miki wannan ba za'a gyalesu ba har sai sun faÉ—a Wanda ya saka su kinji ko?."


Tayi maganar tana kuma kamo hannun Haleesat dake cikin nata, dariyar ƙarfin hali Haleesat Rashid Rayyan tayi kana cikin muryar marasa lafiya ta fara magana.


"Sailuba kinji ki rabu da mutanen da suka min haka kinji?."


"Saboda mene Auntie Haleesat?."


Sailuba ta tambaya cikin sauri hawaye na zuba, Haleesat ta bata amsa da "Saboda Allah ya fisu, kuma Allah yana tare da masu Haƙuri."


Mai da kallonta kan Hajiya Zinaru tayi kana ta fara magana bayan ta kamo hannunta.


"Hajiya! please! Yau ɗaya dai zan iya kiranki da wannan Babban suna wato Mahaifiya?, domin kuwa kin cancanta da na kiraki da wannan suna, a dalilin kin riƙe ni da amana da gaskiya kinyi min riƙon da ko iyayena sai haka, amma ni kuma ina ganin baki kai na kiraki da wannan suna ba, dan Allah Hajiya zaki iya yafewa wannan Ɗiyar taki sannan ki bata damar kiranki da wannan sunan Mahaifiya?..."


Hawaye Hajiya Zinaru take amma hakan bai hanata murmushin farin ciki ba, jin yau Ɗiyar da ta Raina da hannunta wacca tsawon shekarun da suka yi tare bata taɓa kiranta ko tayi ma ta kallon uwa Mahaifiya ba sai yau gashi tana roƙon ta.


Da kyar ta iya buÉ—e bakinta dake tsananin rawa ta ce 


"Eh na yadda Haleesat ɗita kullum kiyita kirana da sunan mahaifiya domin hakan ba ƙaramin farantamin raina zaiyi ba kinji?."


Cikin kuka da dariya Haleesat Rashid Rayyan ta buɗe bakinta a hankali kana cikin dabara ta furta a saman laɓɓanta


"UMMA NA, MAMA NA, MAMY NA..

 Hakan ya yi daga yau zan dinga kiran ki da UMMATA...''


Da sauri Hajiya Zinaru ta amsa ma ta da sosai ma hakan Ya yi tana maganar ne kamar bata cikin hayyacinta tsoro take karta rasa Haleesat kamar yadda suka rasa iyayenta Sanadin hatsari mota.


"Ummata ina Abbana Yake da Uncle Riyaz bangansu ba wai suna ina ne?."


Haleesat Rashid Rayyan tayima Hajiya Zinaru tambayar tana Ƴan waige waige, murmushi Hajiya Zinaru tayi kana cike da zaulaya take faÉ—in 


"Yau wannan nema neman haka sekace kina mana bankwana kodai kinaso Dr Salahah tayi sauri tayi Discharged namu tunda kin warke ne?..."


Murmushi Haleesat Rashid Rayyan tayi Yayin da fuskar ta take Æ™ara wani haske da shaining gunin burgewa kana ta ce 


"Ummata ba bazaki fahimci abin da nake ji bane, ina kallonsu cikin fararen kaya sunayi min murmushi Yayin da wasu suke miƙo min hannu, kin san miye kuwa?."


Bata jira Hajiya Zinaru ta amsa ma ta ba ta ci-gaba da cewa.


"Ummata dan Allah keda Abban mu dasu Rafi'at da Sailuba da kowa duk Wanda nayi wa wani laifi a Rashin sani kuya femmm..."


Tarin da ya taho ma ta ne yasa ta kasa ƙarishe maganar da zatayi nan ta shiga tayi ɓaɓɓaka tarin tambar kayan cikin ta zasu yo waje.😞


Tana mai furta kalmar shahada su duka suna tayata sun ɗauki lokaci a haka kana can suka ji tayi tsit hannunta dake sarƙe cikin nasu ya sage ga fuskar ta ɗauke da qayataccen murmushi.😓


Ganin tayi shiru yasa Rafi'at ƙara kamo hannunta tana mai kiran sunanta amma ina rai ya yi halin sa Wanda yafi su ƙaunar ta ya amshi abin sa.


Ganin da gaske dai batayi magana ba yasa Abubakar dake gefe ƙarisowa wurin cikin sauri ya shiga duba ta, duk da cewa shin ɗin ba Likita bane amma kuma yasan cewa Haleesat Rashid Rayyan bawai tayi bacci ba ko kuma zata farka zuwa anjima ba, a'a bata duniyar gaba ɗaya shikenan TAFARU TAƘARE Haleesat Rashid Rayyan ta tafi inda muma muna nan ƙarisawa idan lokaci ya yi domin kuwa kowa lokacin sa yake jira, lokaci nayi ba jira za'a tafi tafiyar da babu dawowa har abada har duniya ta naɗe shikenan kuma.😭😭😭


Ja! da baya ya farayi cike da matsanancin tashin hankali babu abin da yake iya furtawa sai kalmar inna lil lahi har ƙarshe yana mai rumshe idanunsa Yayin da wasu siraran hawaye suke zubowa akan kyakyawar fuskar sa.


Fahimtar abin da yake faruwa wai Haleesat ta tafi, tafiya na har abada yasa Rafi'at ta yanke jiki ta faÉ—i a wurin sumammiya.


Ita kuwa Sailuba kusan zaucewa za'a iya cewa tayi saboda tsananin tashin hankali, Yayin da Hajiya Zinaru ta koma Tamkar mutum mutumi.


/Yau abin dai Alƙalamin Nainarh kd bazai iya rubutawa Yanda yake ba saboda is very vThither Ban tausayi over 😭😭😭....Kuyimin Afuwa....😓😓😓/


Gaza jurewa Abubakar ya yi domin kuwa zai iya cewa tunda yake a tsayin Rayuwar sa bai taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba.


Fita ya yi daga É—akin kai tsaye office na Dr Salahah Gashwa ya wuce ashe camma wani tashin hankalin zai kuma tarar wa domin kuwa Alhaji Rafiq Rayyan ne ciwon zuciyar sa ya tashi Ashe ma har gado aka bashi anan Asibitin.


Tashin sense.!😫


Tashin Hankalin Wanda ba'a saka masa Rana zuwa Yammacin Ranar gaba É—aya dangin Alhaji Rafiq Rayyan suka hallara a wannan Asibitin zuwa lokacin kuma Sailuba ta fara dawowa hayyacinta amma ba gaba É—aya ba.


Yayin da ita kuma Rafi'at abin yazo da sauki ta farfaɗo shima dai Alhaji Rafiq Rayyan abin sai godiyar Allah sai dai shi Asibitin sun riƙe sa saboda tsaron lafiyar sa.


Saboda haka bai sama damar Raka maragayya Haleesat Rashid Rayyan izuwa makwancinta ba.


Da yake a wancan lokacin waya tayi ƙaranci yasa ba kowa ya sama damar zuwa ba cikin Ahali wa'inda suke da nisa, sai washe gari suma mutanen Jigawa State suka ƙariso.


Rafi'at gaba ɗaya ta ɗauki damuwar duniya ta sakawa kanta domin kuwa koda abinci bata iya ci sosai ta saba kafin suyi aure da Abubakar Mai Kyau a kullum tare suke da Haleesat Rashid Rayyan koda wani wuri zasuje to tare suke zuwa, bama ita kaɗai ba gaba ɗaya ɓangarorin abin sai a hankali.


Satin Haleesat Rashid Rayyan biyu da Rasuwa Rafi'at ta koma gidan mijinta Abubakar zuwa lokacin kuma an sallami Alhaji Rafiq Rayyan daga Asibitin.


/RAYUWA KE NAN😭/


_*BAYAN_WANNI_BIYU*_


Rayuwa ta ci gaba da tafiya sumuluquii ta wasu ɓangarorin amma banda ɓangaren Rafi'at da mijinta Abubakar domin kuwa zama suke zaman doya da manja tun rasuwar Haleesat Rashid Rayyan komai ya taɓarɓare tsakanin su ko ɗan kulawar da Abubakar yake bata a Sanadin cikin jikinta Yanzu babu, domin kuwa wani miskilanci Yake ji dashi haka suke zaman abin sai addu'a.


Ranar wata litina Rafi'at ta tashi da naƙuda ba'a ja lokaci ba da yake da wata tsohuwa Babah Ladii ƙanwar Kakansu a gidan saita taimaka ma ta zuwa Yamma lokacin Abubakar ya dawo ya tarar da halin da ake ciki, bai ɓata lokaci ba, ya kira Hajiya Zinaru ta waya ya sanar da ita abin da ke faruwa.


Ko kafin Hajiya Zinaru ta ƙariso Rafi'at ta haifo kyakyawan Jaririn ta ƙato mai kama da ubansa kamar an tsaga kara komai iri ɗaya sak, Like father Like son 🤓


Koda suka ƙariso ita da wata ƙanwar ta sai kuma Sailuba nan suka haɗu da Babah Ladii suka shiga kula da mai jego da kuma Jaririnta.


Zuwa kwana uku da haihuwa gaba É—aya Ahalin Alhaji Sameer LamiÉ—o dana Alhaji Rafiq Rayyan ba Wanda baizo duba lafiyar mai jego da kuma Jaririn da ta haifa ba, kowa yazo sai ya yaba da kyau irin na wannan jariri.


Ranar suna Yaro Yaci suna


ABDUL'MALEEK.!


/THE KING/


Mutane na kiran sa da Maleek Yayin da iyayen sa suke kiran shi da


BUDDY


Wato Aboki

Duniya sabuwa fil a wurin Rafi'at da Jaririn ta Abdulmaleek domin kuwa tun a Ranar da ta haihu wani kulawa na musamman Abubakar Yake bata ita da Jaririn su sunyi ƙiba sunyi ɓulɓul abinsu.


ABDUL'MALEEK Ya taso Yaro ne shi mai ƙiriniya sosai da sosai domin ko Asibiti Rafi'at ta tafi dashi tofa Ya dingi dukan Yaran mutane ke nan gashi ita kuma Likitar Yara ce, gashi daga ita har uban sa suna ƙaunar shi sosai ƙaunar da ta sa basa ganin laifin sa koya yake.