UWANI 'YAR ƘASHIN

2

by @ameeraadam

*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*


      ©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.


  

 SHAFI NA BIYU



 Uwani da ke laɓe tana jin su sai da ta saki murmushi sannan ta wuce ɗakin da Lami da Goggo Sala suke kwana, tana shiga ta samu mai sunan malam yana kwance yana bacci. A hankali ta ɗauko shi sai da ta zo tsakar gida, ta saka shi a cikin ƙatuwar tukunyar da ake dafa wa Lami ruwan wanka amma babu ruwa a ciki. Ta saka hannu ta ɗan jijjiga shi don ya tashi, saboda dama ta jima da sanin Baba Isuhu matsoraci ne na bugawa a jarida, don haka ta gano lagonsa.


 Baba Isuhu ba ƙaramin ɗacin kalaman Goggo Sala ya ji ba, ya saci kallonta rai a ɓace ya ce.


  "Allah Ya kwashe mana dai, ni allan-musuru ne na san ke ce a wurin? Wallahi ni da na ji na ɗebo abu a kaina na ɗauka hannuwan Lami ne." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar yana fitowa falo. Ya bar Goggo Sala a tsaye cike da takaicin abin ya faɗa.


 "Tsabar iskanci da wulaƙanci har ƙirjina ya yi lalacewar da za a ɗebo su aka a ɗauka hannuwa ne?"

  Goggo Sala ta ayyana a ranta.


 Yana zuwa ya ji mai sunan malam ya tsanyare da kuka. Kusan tare suka kalli juna shi da Lami, sai dai jin shiru babu kukan uwar garken ya sa suka ɗan saki jikinsu. Cikin sanɗa suka fara takawa a hankali har suka fita tsakar gida, suna yunƙurin tafiya ɗaki suka ji kukan mai sunan malam a cikin tukunya ga shi kuma tukunyar a rufe. Lami ce ta yi ƙarfin halin buɗewa nan take ta yi tozali da shi.


 "Isuhu akwai abin da yake shirin faruwa wallahi." Lami ta faɗa murya na rawa.

"Lami ko dai a garin ɗaukar uwar garke ne na tako aljanu? Na shiga uku kada su taɓa mini mai sunan malam." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar cikin kuka, Goggo Sala na ƙarasowa suka wassafa mata abin da yake faruwa. 


"An ya kuwa Isuhu uwar garken ka ɗauka ba aljanu ba kuwa? Gaskiya ruwa ba ya taɓa tsami banza." 

 Cikin Baba Isuhu ya sake ɗurar ruwa, ya waiga a hankali yana kalle-kalle daga can kusurwar bango ya hango kamar mutum a tsaye, Uwani da ke raɓe ganin kar ya gano ta ya sa ta yi wata girgiza haɗe da cewa.


  "Meeeeesuuuuhuuuu zaaaaan cinyeeeeee idoooonnnnkaaaaa." 


 Jin abin da aka faɗa ya sa Baba Isuhu da su Lami suka faɗa ɗakin da su Lami suke jego. Uwani ta samu ta saɗaɗa sannan ta wuce sashen Dada tana sakin murmushi, ko ba komai ta gano lagwansu da yadda za ta dafa su a ruwan sanyi.


 Su Baba Isuhu gabaɗayansu babu wanda ya samu sukunin rintsawa, don Baba Isuhu ko sallar asuba bai samu ya fita ba. Sai da gari ya yi haske tarwai sannan suka fito suka yi alwala suka yi sallah, Goggo Sala ta ɗora ruwan wankan mai jego. Ita ma Uwani idonta biyu har aka yi sallar asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita.


 Ko da gari ya waye babu wata damuwa a tattare da Uwani don ba ƙaramin jin daɗin mafitar da ta samu ta yi ba, ita kanta Dada ta yi mamakin ganin Uwani tana harkokinta. Sai dai a lokacin da ta ƙarasa garken awakinta sun ba ta tausayi musamman da ta ga tagwayen uwar garke sai koke-koke suke alamun suna neman ta, tana zuba musu abinci suka daina kuka sai tagwayen uwar garke da har lokacin ba su daina kuka ba.


 "Kai Talle asirinmu fa ya kusa tonuwa, kai Allah ne kaɗai ya tarfa wa garinmu nono." 

 Baba Isuhu ya faɗa yana yin ƙasa da murya.


 "Ai na san za ka gyara komai, kai ma fa shaiɗanin kanka ne. Yanzu dai ya za a yi da kai da ƙafafuwan? Kuma cinyoyin baya ka san na ce maka ni zan ɗauke su." Mai gari Talle ya furta.

"Ni yanzu kai da ƙafar 'yar akuya nake so ka samo mini, saboda zan kai wa Dada don na badda idonsu a kaina, cinyoyi dai gaskiya na gaba za ka ɗauka. Kuma sai yamma liƙis za ka aiko min, ka tabbatar an daddatsa komai don kada a fahimci naman babbar tinkiya ne." 

 Mai gari Talle ya gyaɗa kai yana shirin magana ya hango Uwani a ɗan nesa da su tana haɗa tukwanen taɓo, idan ka ga yadda ta mayar da hankali tana wasa sai ka rantse da Allah ba ta san wainar da suke toyawa ba. Ganin ta ya sa Talle Mai gari ya ce.


 "Abokina ma yi magana anjima kawai, yanzu dai gaskiya sauri nake." Daga haka suka wuce, don shi kansa Baba Isuhu ya lura da Uwani duk da ta yi kamar ba ta san suna yi ba.


 Uwani na ganin Talle mai gari ya tafi gida ta watsar da kayan ƙasar hannunta, ta sake ɗaure ɗamarar da ta yi da ɗankwali wacce cike take da jelolin raguna da tumakai, da ta shiga kasuwar awaki ta samo. Tana daga jikin katangar ƙofar gidansa ta ga ya shiga soron gidan, da yake turakarsa a soro take don haka a kan idonta ya faɗa ɗakinsa. Tana nan tsaye ta ji ya sake fitowa a tsammaninta fitowa waje zai yi sai ta ji ya shiga cikin gida yana faɗin.


 "Amarsu ta ango mai daɗin tuwo da miya, wannan ɗan waken da kika shanana mini man ƙuli ai dole na bada tukwici." Da sauri Uwani ta faɗa ɗakin tana shiga ta samu sabuwar langar Zuwaira amaryar mai gari cike da ɗan wake, da sauri ta cakuɗa ta hau ci saboda tsabar ƙeta ta dinga haɗa uku-uku huɗu-huɗu tana ci, cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye ɗan waken tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha, ta zaro jelar tumaki biyu ta saka a ciki.


 Tana shirin miƙewa ta ji alamar tahowar mai gari shi da Zuwaira yana faɗin.

  "Haba wane mutum ki dinga haɗa kanki da waccen ballagazar. Ke fa komai na ki na daban ne Zuwairatuna." 

 Uwani da ke ɗakin cikin matsananciyar faɗuwar gaba ta shige uwar ɗakinsa, can bayan ƙofa ta ɓuya don ta tabbata matuƙar mai gari ya kamata sai ranta ya yi mummunan ɓaci.


 Zuwaira cikin kwarkwasa ta zauna tana fari da idanu, hannunta ɗauke da mufici tana yi masa firfita. Mai gari da ƙarfinsa ya ɗauko langa amma jin ta fayau ya sa shi mamaki don ɗan waken da ya gani cike da langa yake, yana ɗaga murfin ya ganshi fayau sai jelar tinkiyoyi a ciki. Wani abu ne ya tsarga masa tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, cikin faɗuwar gaba ya furta.

  "Zuwaira kina ganin abin da nake gani kuwa?" Zuwaira da mamaki ya sa ta hangame baki ta ce. "Mai gida me ye wannan kamar jelar tumaki? Ina ɗanwaken da na zuba maka?" Mai gari ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana shirin magana daga can uwar ɗakinsa ya ji an ce.

   

"Taaaaalleeeeeeeeeh."

  Zuwaira ta waiga cike da tsoro ta ce, "Kamar kukan tinkiya kamar kuma cewa aka yi Talleh." Kafin ta gama magana tuni gumi ya gama wanke Mai gari, Zuwaira na shirin sake magana suka ji ƙarar buhu sai kuma Uwani ta sake maƙe murya ta ce.


  "Ga uwar garke ta dawo ba ta mutu ba, na zo tafiya da talleh a cikin buhun mutuwa." Zuwaira da mai gari nan take suka shiga rige-rigen guduwa, Uwani da ta saka kanta a cikin wani ƙaton buhun gero ta biyo su buguzum-buguzum da gudu tana fisgar malun-malun ɗin mai gari. Mai gari kafin ya shiga cikin gida ya kifa ya kai sau uku, da ya tashi malun-malun sai ta sake harɗe shi.


 Ladiyo da ke tsakar gida sai ganinsu ta yi a guje. Zuwaira ta shige ɗakinta ta banke ƙofa, yayin da Mai gari ya faɗa ɗakin Ladiyo, yana tafe fitsari da zawo na bin wandonsa.


 Waige-waige Ladiyo ta fara yi don ita ba ta san gudun da suke yi ba, ganin haka ya sa ta shiga ɗakinta, a can ƙasan gado ta hango Mai gari gumi na yanko masa ta ce.

  "Mai gida wai me yake faruwa ne?" Mai gari ya sake jan zanin gado don ya rife kansa ya ce. "Ladiyo gamo muka yi a ɗakina, wallahi aljanu ne a ciki." 


 Wani wari ne ya ziyarci hancinta, ta kai kallonta wurin ƙafar wandonsa ta ce. "Mai gida me nake gani kamar zawayi?" 


 "Idan zawayin ne akwai uban da ya yi mini shi? Ba abina ba ne ki bar ni mana Ladiyo." Mai gari ya faɗa yana muzurai.


"Don Allah ka taso mu je ka sauya kaya kafin yara su dawo gida." Shiru mai gari ya yi sannan ya ce. "Amma za ki tsaya a ƙofar banɗaki ko?" Ladiyo ta gyaɗa masa kai cike da mamakin wai yau ita Mai gari yake ce wa ta yi masa rakiya banɗaki. Da ƙyar da suɗin goshi Ladiyo ta samu kan Mai gari ya fito, Uwani da ke ɗakin Mai gari har ta fito za ta tafi gida ta ji suna maganar shiga banɗaki. Da sauri ta saki murmushi ta ɗauko buhun ta zagaya ta bayan gidan Mai gari, zuciyarta fes don babu mutane sosai sai waɗansu ƙananan yara da ba su wuce shekara uku ba suna wasa.


 Kasancewar banɗakin karkara a buɗe yake ta sama ya sa duk abin da Mai gari yake faɗa tana ji, sai da ta tabbata da Mai gari ya tuɓe sannan ta tsugunna ta saitin rariyar ta ce.

  

 "Shi kenan ma Talle ya zo masarautarmu da ƙafafuwansa yana wanka, buhun mutuwa zo ka kai Telle inda ya kai shugabarmu wato Uwar garke." Uwani na gama maganar ta watsa masa jelar tumaki biyu ta saman banɗakin, sannan ta wurga ƙaton buhun geron da ta fito da shi. Tana daga nan wurin ta ji Mai gari ya zuba ihu ya fice a guje yana faɗin.


 "Wayyo Allah! Za su tafi dani, wayyo Ladiyo ki taimaka mini buhun mutuwa ya biyo ni." Garin gudun da Mai gari yake yi ne ta ga takalminsa wari ɗaya ya faɗo ta bayan katanga. Dariya Uwani take yi kamar mahaukaciya sabon kamu, sai da ta yi mai isarta sannan ta ɗauki takalmin mai gari wari ɗayan ta ɗaure shi a cikin ɗankwalin da ke ƙugunta kai tsaye ta wuce gida.


 Yamma ta yi liƙis a lokacin tana tafe tana waƙoƙinta, da mamaki take bin galleliyar motar da ke ƙofar gidansu. A gaban motar ta tsaya ta isa gaban mudubin motar tana kallon kanta tana yatsine-yatsine, ta mudubin ta hango Salele hannunsa ɗauke da tulu ya ɗebo ruwa. Uwani ta ƙwalla masa kira, nan take jikinsa ya fara rawa, "Yar ƙashin gwiwa don girman Allah ki bari na kai wa Innata ruwan nan." Uwani ta tsuke fuska sannan ta ce. 

 "Don uwarka wani abin na ce maka ne, kawai ka zo na ce ko." Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa idonsa na zubar da ƙwallah don ya san yau kwanan tulun Innarsa ya ƙare. 


 Duk abin da yake faruwa Jafar na daga cikin motarsa yana kallonsu, kamar ya yi mata magana sai kuma ya ce bari ya tsaya ya ga iya gudun ruwanta. Don ko ba a ce masa Uwani ba ce, kamaninta da na mahaifinsa ya alamta masa.


 "Sauke ruwan tulun nan." Ta furta fuska a haɗe. Babu musu Salele ya sauke, Uwani ta fara ɗiban ƙasa tana ƙwaɓawa a saman gilashin motar Jafar, domin baƙin gilas ne kuma ba ta taɓa tsammanin da mutum a ciki ba. A hankali ta fara zuba ruwan tulun tana wanke ƙasar wani wurin ya yi jurwaye wani ya wanku, ta ɗora tulun a saman motar sannan ta ce. 


 "Salele tulun Innarku yau shi zai tuƙa mu zuwa garin Kano, ka san fa sabuwar motata ce da Dada ta sayo mini jiya." Uwani na sakin tulu ya faɗo ƙasa tush! Salele ya wage baki ya saki ihu cikin ɗacin zuciya.


 A hankali Jafar ya fara zuge gilashin motarsa, Uwani da ke gefe ta yi mutuwar tsaye saboda tsoro don ba ta taɓa tsammanin da mutum a ciki ba. Sai kuma ta maze ta fara harare-harare don kar ya raina ta, ta kalli wurin da Salele yake ihu ta buga masa tsawa. 


"Za ka yi mini shiru ko sai na mayar da bakinka ƙeya." Tamkar an yi ruwa an ɗauke haka Salele ya yi tsit yana goge ƙwallah.


 "Uban wa ya ce ki jiƙa mini mota." 

 Uwani ta ji saukar maganar Jafar a kunnenta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi saboda tsoro amma don kada ya gano ta sai ta haɗe fuska ta ce.


 "Ka ga malam bar ganinka da wasu kayan 'yan sanda ka ɗauka za ka tsorata ni, babana ma babban ɗan sanda ne. Wallahi yanzu ihu ɗaya zan yi ya kai ka caji ofis ya sa a kulle ka." Uwani ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki, sannan ta yamutsa fuska ganin Jafar ya kafe ta da ido yana kallo ya sa ta ci gaba.


 "Kai ni fa ban ma yarda da kai ba wallahi, an ya ma kai ba ɗan sandan bogi ba ne? Dubi yadda kake raba idanu kamar shege a rabon gado. Wai ma uban wa ya ce ka jiye mota a ƙofar gidanmu..." Uwani ta haɗiye ragowar kalamanta sakamakon ganin Jafar ya buɗe mota ya fito, ba Uwani ba hatta Salele sai da ya tsorata da yanayin da ya ga Jafar. Uwani a dole don kar ta kunyata kanta ya sa ta cigaba da tsaiwa ta ce. "Ka ga malam tun kashinka bai bushe a hannuna ba ka..." 


 Ta sake haɗiye ragowar kalamanta sakamakon jin Jafar ya damƙi hannunta da ƙarfin gaske.


"Yeeeh Uwani ta shiga hannun ɗan sanda." Salele ya faɗa da ƙarfi cikin murna yana tsalle, tuni cikin Uwani ya kaɗa. Salele ya ja baki ya rufe sakamakon ganin bindiga saƙale a gefen aljihun Jafar. 


Da ƙarfin gaske Jafar ya fisgi hannun Uwani kai tsaye ya wuce cikin gida da ita. Tamkar raƙumi da akala haka Uwani take bin Jafar ƙirjinta na bugawa, zuciyarta na shelar neman agajin gaggawa. Don duk iskancin Uwani tana tsoron bindiga ɗari bisa ɗari.


 Lokacin da Jafar ya shiga ɗakin Dada babu kowa a ciki, don haka ya wurgar da Uwani gefe fuska a haɗe ya ce.

  "Maza tashi ki fara tsallen kwaɗo." Uwani jiki na rawa ta fara tsallen kwaɗo sai dai ba ta kai ko ina ba, ta fara hawaye shaɓe-shaɓe. Belt ɗinsa ya ciro yake lafta mata idan ta tsaya, don haka lokaci ɗaya Uwani ta fara fita a hayyacinta. Bayan ta gama tsallen kwaɗo ya saka ta tuƙin babur, da kansa ya gwada mata yadda za ta yi, tana daga tsaye ban da numfarfashin kukan Uwani babu abin da yake ta shi.


 "Allah mai yau da gobe, wato yau kukan Uwani nake ji a gidan nan? Tabbas gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, Uwani yau wa kika taɓo wanda ya fi ƙarfinki haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon ganin Uwani a ƙobare da ƙafafuwa tana tuƙin mashin. Baki a sake Dada ta ce. 

 "Ke Uwani wane sabon iskanci ne kuma haka? 'Ya mace da ke ki hau wani ƙobare ƙafafu kuma kina kuka." Uwani jin abin da Dada ta faɗa ya sa ta faɗi ƙasa ta sake fashe wa da kuka.


"Wallahi idan na ƙirga uku ba ki tashi ba sai kin maimaita har da tsallen kwaɗo." Jafar da ke zaune a gadon ƙarfen Dada ya furta fuska a haɗe. A yatsine Dada take kallon wurin ta ce.


 "Waye haka kuma da baƙaƙen kaya? Na san dai na ba wa Mamman tarbiyya ba zai yi wannan rashin imanin ba, domin ni musulma ce kuma ina sallah a ɗakina amma dubi garsameman ƙato ya shigo mini da waɗannan takalman kalar na arnan Lagas har cikin ɗakina. Wai Jafaru za ka fito ka cire mini takalmi a waje ko sai na kira ubanka mamman ya fitar da kai?" 


"Dada kada ki sake ɓata mini rai!" Jafar ya furta a takaice.

"Ran naka ya fi na ran ƙuda ɓaci, ke Uwani ta shi ki tafi wannan zalinci ba za a yi shi a ɗakina ba. Ni kam wallahi Sa'idu ya gama cutata da ya haɗa mini zuri'a da aikin kaki." Dada ta furta ƙwalla na zuba.


 Bindigar aljihunsa ya zaro yana juya ta, ganin bindigar ya sa daga Uwani har Dada suka zabura. Hawaye bibbiyu na bin fuskar Dada ta ce, "Yanzu harbe mu za ka yi Jafaru? Ni kam ko ana sauya muku zuciya daga ta musulmai zuwa ta kafirai a wurin tirenin ne?" Jafar ya sake haɗe fuska ya ce. 

 "Ta kanki zan fara ma, Dada sai yau kika san ana sauya mana zuciya?" 


 Ganin yadda ya sha kunu ya sa jikin Dada ya fara karkarwa, Jafar ya fara takowa a hankali kafin ya ƙarasa sai gani ya yi Dada ta zube ƙasa a sume. Murmushin gefen baki ya saki, Uwani na ganin haka ta wage baki ta ƙwalla ihu, a daidai lokacin Malam na madina ya kawo kai yana faɗin. 


 "Wallahi Uwani sai Allah ya yi mana hisabin wannan ihun da kike yi mana babu ji babu gani." Jafar ya hango a tsaye ya mayar da bindigarsa aljihu, yana shirin magana ya hango Dada a yashe a ƙasa.


 "Na Madina wallahi Jafaru ne ya sa bindiga zai harbe mu shi ne Dada ta faɗi." Uwani ta faɗa fuska da hawaye shaɓe-shaɓe don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya yi wani irin ihun da jaruman indiya suke yi, cikin kukan kura ya yi wata irin sufa ya cukumi wuya Jafar haɗe da maƙale shi yana faɗin.


 "Wiiiiihuuuuuuhuuuu gafara ga maza nan bisa kanka."




***

#Ummou Aslam Bint Adam🌚