Chapter 1
by @nanahbenz
KANON DABO
Aunty hafsat kinji dadi abinki kinyi dacen namiji,
wacce aka kira da aunty hafsat dariya tayi sanna ta wuce kitchen dan saman ma yan uwan nata abunsha cike da fara’a da karamci da karramawa na bafulatana,daga kitchen ta jiyo karar wayarta wanda daga ringing tone din tasan burin zuciyantane ke kira kuma uba ga yayanta,sosai tayi murmushi ganin yanda yaran nata ke kokawa wajen rigerigen daukan wayan, da gudu maisun ta bata wayan tare da daga mata kiran,daga yanayin fiskanta zaka gane abun ba me dadi bane,a sanyaye ta amsa da “toh daddy”a yanda take kiran mijin nata kaman yanda yaran ke kira .
Ta kawo musu dauke da murmushi sanna take sanar dasu zataje Tasha dan dauko kannen mijinta wanda sukazo daga maiduguri,batajira amsan su ba ta dauki hijab dakuma kudin mashin wanda alokaci shi ake hawa babu napep,tana zuwa Tasha ta gane kannen mijin nata duk da ba wani sani ta musuba,zainab ita ta fara gaisheta sanna da yayyinta maza guda biyu najeebu da kuma sule,babu wani jimawa suka Isa gida inda kannenta ummi da mami suka zuba ido dan ganin masu shigowa babu wanda yayi magana cikinsu se ido da sukabi yar Uwar tasu dashi,bayan takai mazan masaukinsu ta umarci me aiki ta gyara musu,anan ta umarci zainab taje dayan dakin wanda anan ne ta sauki kannenta da sukazo daga jalingo.
Wannan kenan……
TARIHIN ALHAJI SAFWAN DA IYALANSA
Alhaji safwan ya kasance matashi me Neman na kansa tun Yana ne karami, mahaifiyarsa su 3 ta haifa sai kuma kishiyan mamanshi da takeda guda 2, Jamila , safwan, da kuma najeebu, inda sule da zainabu kuma dakinsu daban,bayan rasuwar mahaifinshine ya tafi jos dan Neman kudi,ananne ya kama Gida yake zaune inda duk wani dan kauyensu daga maiduguri idan yazo wajenshi yake sauka kowa yayi yanda yaso, inda shi yake ciyardasu ya tufatar dasu yakuma musu makaranta, inda najeebu shima yazo bashida aiki se bacci da safwan yaga hakane ya nema mishi aikin company karshede aka koreshi haka ya ci gaba da rayuwa da tallafar rayuwar mutanen garinsu inda su duk basa gani, a inda har waenda yasaka makaranta duk sun kammala,amma shi Sam kasuwanci ya hanashi,bayan kammalawarsu wasu sun samu aiki wasu sun kara gaba inda shima ya samu ci gaba zuwa kanon dabo