TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

TSOKACI

by @nanadiso10


Cikin Nuna tsantsar bacin ranta ta ƙalleta haɗe da riko hannayenta tana mai goge mata hawayen dake bin fuskarta tace " Kina ɗiya mace amma ace babu abunda kikasani sai shirme da korafi baki iya tarairayar mijinki ba sai faman kuka da saƙin magana?

Haba ɗiyata Kasancewarki ta diyar mace dolene kikasance macce mai sanin yakamata mai hakuri mai kuma iya fuskantar kalubalanta iya ƙula da mijinta haɗe da kissa tamu ta mata da kisissina Amma da anyi magana ƙice baidamu dake ba!!!


soyayya da ƙauna suna ginuwa ne aciƙin zuciyar mu idan da kyautatawa da kuma girmamawa ga junanmi amma babu lafazi mai dadi babu kyautatawa ba babu jan hankali babu komai sai korafi gaki nan har mace agaban mijinta Amma baki iya tafiya ba baki iya rangwada ba, sai ki tsaya kamar iccen da baya tankwaruwa.


Dole ne ki miƙe ki iya salon jan hankali mijinki rausaya da rangwada ki iya kisisina kulawa girmamashi haɗe da lafazi masu dadi da taushi..kikasance ma'abociyar turare wacce ta iya shagwaba da fari da idanuwanta da rangwada haɗe da karya murya kada kisake kizama daga ciƙin ballagazayan mata ita diya macce ai ƴar ado da kwalliya ce...