ELHAJJ

Page 10

by @oumamani20

🤎🤎🤎🤎

          *ELHAJJ*

                 🤎🤎🤎🤎


Free page 10

   

  Written by

    Mrs A.M


Marubuciyar 

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*


Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.


Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

***



*BABY BEAUTY LOUNGE*


*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*


*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*


PHONE NUMBER *** OR ***


*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*



  Ware idon sa yake kawai yana kallon ta yana jinjina wa karfin halin ta.


Ganin yadda yake kallona yasa ni kara shagwabe fuska nace "plz Ya Ustazu nasan ustazai basu da rowa, kar Ka cemin kwadayayyiya ni bana kwadayi sha'awa kawai ta ban Ka taimako".


Dan kure ta yai da ido kafin yace "Ke baki tsoron na sa Miki wani abu a cikin abincin, baki sanni ba kawai kice na baki kaza, baki san ana tsafi da nama ba?".


Zaro ido nai sai kuma na kyalkyale da dariya, wani kallo na masa irin ni zaka yiwa wayo dinnan.


Lumshe idonsa yai ya bude yace "baki yadda ba koh?".


Turo karamin bakina nai gaba nace "ai nasan ustazai basu tsafi, kuma ni na yadda da kai ai nasan ba abinda zaka sa min".


Tsigar jikinsa ce ta tashi haka kurin bai san dalili ba amma sai ya samu kansa da jin dadin yadda ta nuna ta yadda da shi.


Tabe baki yai ya tura mata takeaway din fried rice din duka roba biyun da KFC din sai ruwa roba daya.


Kallon sa nai da murna nace "Ya Ustaz duka ni zan cinye su".


Fuska a hade yace "dauki ki fita plz, kin cika min kunne da surutu".


Yar gajeriyar dariya nai na dauki duka takeaway din nace "angode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya raba Ka da iyayen ka lafia, Allah ya kare Ka daga sharrin masu sharri.. daga haka na fice daga office din ina murna sosai".


Tun da ta fara masa addu'a ya lumshe idonsa, yana amsawa a ran sa. Addu'ar daya rasa daga gun matar sa kenan, ko mai zai bata kuwa sai dai tace tnx shikenan.


Haka kurin yake jin wani yanayi a zuciyar sa dan gane da wannan Yarinyar, daga zuwan ta yau ta sashi yai magana sosai abinda bai taba faruwa da shi ba kenan ya tsaya Yana magana da wani.


Ina fitowa Yasir dake danne danne a system dinsa yace "Khadija abinci MD ya baki".


Kallon sa nai ina rike ledar da kyau nace "eh, ko bakin ciki kake min ne daga zuwana Ya Yasir?".


Dariya ya kyalkyale da ita yace "oh Khadija! Ba bakin cikin da nake Miki kawai dai ina tausayin kai na kinga da duk abinda MD yaci yana rage min amma ynxu ke xai dinga bawa na sani".


Gwalo na masa nace "ohoo dai kuma fa ba shine ya bani ba kaza na gani zubu zubu manya, yawuna ya tsinke shine nace ya taimako ya bani to kaga ai baxan cuci kai na ba".


Dariya kawai yake yace "ynxu dai Khadija je ki ci abincin kizo muyi hira anan, don gaskia ina son hira da ke kina sani nishadi".


Farr nai da idona nace "a nawa, kasan buhari ya hana aikin banxa".


Girgiza kai yake kawai yana dariya yace "haba kanwata, so nake fa kizo muna hira ina aikina, kinga lokacin da na gama sai na zaga da ke kiga ko ina a company din".


Murmushi nai nace "kuma haka ne bara nai sauri na dawo toh".


Cikin palourn naje na zauna, har na bude fried rice din Zan ci sai na tuna da Mama, shiru nai kawai cikina sai kukan yunwa yake amma bana Jin zan iya cin wannan cimar dadin ba tare da Mama ba.


Rufewa nai na dauko ledar kawai, gurin Yasir na dawo nace Ya Yasir ina zan ajiye wannan ledar, na fasa cin abincin sai anjima ynxu bana Jin yunwa.


Dan shiru yai yana tunani kafin yace gaskia ban san inda zaki sa ba Khadija, kinga nan gurin kowa yana iya zuwa sai dai office din MD shi kuma wannan baxai taba ma yiwu wa ba.


Ban bari ya sake magana ba kawai na nufi office din MD din, a hankali na bude na shiga na tare da nayi knocking ba.


Cikin fada fada naji yana fadin sa'an "kine ni Saudat, mai yasa kika rai na nine wai? Kodan kinga ina Shiru da duk abinda kike yi ne".


Daga dayan bangaren Saudat ta Kara marairaice wa tace "plz Dear kayi hakuri don Allah, har na shirya fah kawai sai aka gayyace mu bikin yar aminiyar Umman su Nabila ne fah dear baxan iya cewa baxan je ba".


Ran sa ya gama baci a harzuke yace "wato bani da muhimmancn da zaki iya kirana kice min kin tafi wani gari har Abuja daga lagos bayan kwanakin da kika kara akan Wanda na baki koh Sauda".


Kukan kissa ta sakar masa har da shessheka don tasan baya son kukan mace ko kadan.


Ai kuwa tayi nasara don shiru yai kawai yana sauraran ta ya daina fadan da yake, ganin taki daina kukan kawai ya kashe wayar sa ran sa a bace.


Sati daya tace zata yi sbd bikin kanwar aminiyar ta da za'ai a Lagos amma sai da ta kara kwana uku akai, ynxu kuma tana ce masa wai tana Abuja ana bikin yar aminiyar Umman Nabila din kuma sai tayi kwana har hudu.


Ni dai tun da na shigo naga yadda yake fada hankali a waya jikina yai sanyi, na takure a jikin kofa ina mar-mar da ido, a rai na fadi nake ashe ya iya fada haka.


Taba handle din kofar da ake yine yasa na matsa baya kadan aka shigo, Salim ne ya shigo yana rike da wasu takaddu.


Mai da kofar yai ya rufe sannan ya juyo cikin office din, idon mu ne ya hade da juna, a tare gaban mu yai wani irin bugawa da karfi...


Kallon sa nake kawai gabana yana faduwa haka kurin naji wani abu yana yawo a cikin kai na.


Shima a bangaren Salim din cikin bugawar kirjin da bai san dalili ba ya zuba mata ido yana hasaso irin kyaun ta, duk da tana cikin hijab amma hakan bai hana sa kissima irin yadda surar ta take ba, lokaci daya yaji sonta da kaunar ta sun mamaye zuciyar sa abinda bai taba ji ba kenan, yaji yana son mace tsakani da Allah haka....


Ni kam ganin kallon da yake min yayi yawa yasa ni turo baki, a shagwabe nace "badai kyau kallon haram toh".


Dariya yai yace "ni nake miki kallon haram din?".


Shiru nai kawai ina kauda kai na gefe haka kurin bai kwanta min a rai ba, kawai sai naji bana son sa.


Elhajj daya zuba musu ido yana kallonsu mai da idon sa yai ya lumshe ransa yana kara baci, duk ransa a jagule yake game da abinda Saudat ta masa.


Daga kafa nai a hankali duk a rude nake sbd yadda Salim ya ke bina da kallo, karasa wa nai gaban table dinsa nace "Ya Ustaz ga ledar abincin nawa na koshi na ynxu xan ci ba, don Allah zan iya ajiye wa a office dinka?".


Hade rai yai sosai yace "waye Ya Ustaz din wai?".


Turo baki nai nace "kai mana..."


Zuba mata ido yai kafin yace "me yasa kika rai na ni wai?".


Zaro idona nai nace "ni din kuma? Mai nayi maka fisabilliahi".


Kara hade ran sa yai yace "ki daina ce min ya Ustaz bana so, aiki kike min call me MD.."


Turo baki nai nace "toh Ya Ustaz...." Da sauri na sa hannu na kame baki na ina zaro ido nace "sorry MD".


Kada kai kawai yai yace "ajiye a gefen resting chair din can"


Sum sum na tafi na ajiye a gefen ta har da dan turawa yadda ba za'a gan ta ba sannan na wuce na fita daga dakin.


Kallon bayanta Salim yai yana sauke ajiyar zuciya, ran sa adan bace yadda suke magana da Elhajj ya karaso gurin Elhajj din.


Zama yai yana Mika masa hannu sukai musabaha, kafin Elhajj yace wani abu salim yace "wace wannan wai".


Tabe baki Elhajj yai yace "yarinyar Baba Auwal ce, shine ya kawo ta tana son aiki ne so zata dinga gyara min office".


Da mamaki Salim yace "but she's young bai kamata ta dinga irin wannan aikin ba".


Cikin ko in Kula yace "ita taga tana so ai koh, I don't care".


Shiru Salim yai yana son ya cewa Elhajj ya bashi ita ta dinga gyara masa office amma kuma bai san wani fassara Elhajj din zai masa ba dole yaja bakin sa yai shiru kawai suka shiga tattauna wa akan abinda ya kawo sa....


Ni kuwa ina fita gurin Yasir na nufa muka shiga Hira Yana aikin sa, da yake shima mai surutun ne cikin lokaci kan kani muka Saba sai hira muke yana bani labarin yan matan da yai.


Muna cikin hirar Salim ya fito daga office din, kallon ta yake yadda take dariya tare da Yasir nan da nan yaji ransa yayi mugun baci.


Cikin bacin rai ya karaso inda suke, kallon ta yai yace "mai kike yi anan?".


Kallon sa nai da mamaki nace "kamar ya? Hira muke yi mana nida Yaya Yasir".


Tsaki yai yace "tashi ki koma can ki zauna bana son ganin ki anan gurin".


Wani kallo na masa fuskata a hade nace "sannu MD".


Da mamaki ya zaro idon sa yace "Ke ni kike fadawa magana haka".


Nima ran nawa a bace nace "toh ai gani nai company din na MD ne kuma shi nake yi wa aiki, shi Mai yasa bai hanani magana da Ya Yasir din ba sai Kai".


Shiru yai kawai bai sake magana ba takaici kamar zai sashi fashewa da kuka, kawai ya juya ya fice daga palourn.


Yana fita naja tsaki ina fadin "aikin banxa kawai, wallahi anji kunya dai".


Yasir da ya sandare a tsaye yace "kin san waye shi kuwa kikai masa rashin kunya?'.


A fusace nace "ko waye shi in dai na MD bane ban damu ba".


"Tab toh in fada miki dan uwan sane kuma aminin sa sannan daga MD sai Shi a companyn nan tsaf zai sa a kore ki don ma shi mutumin kirki ne bashi da damuwa Sam ga fara'a, ban san Mai ya ke damun sa ba da har ya miki magana ma, Yasir ya fada yana Zama akan kujerar sa".


Tabe baki nai nace "oho koma dai meye ni bai min na wallahi, haka kurin naji bana son sa".


"To wallahi ki kiyaye don bashi da damuwa amma baya daukar raini"


Banza na masa har sai da ya gama aikin sa sannan muka fita tare ya shiga nuna min companyn ko ina in muka je sai na gabatar musu da kai na a matsayin Dije mai gyara office din MD.


Sai da aka shiga masallaci sallar la'asar sannan na koma floor din mu nayi tawa sallar, har wani jiri jiri nake ji sbd yunwa amma bana jin zan iya cin abincin.


Biscuit din da Yasir ya siyo ya bani shi naci nasha ruwan Despenser din dake palourn, sai karfe shida aka tashi.


Office din MD na shiga na dauki ledata ban gansa ba da alama Yana cikin dakin nan, ban kuma damu dana tsaya ba kawai na fito.


Sallama nai wa Yasir na sauka ina boye ledata a cikin katuwar jakata, a raina ina fadin yau ga ranar manyan jakunkuna.


Bayan machine din Baba na hau muna tafe ina basa labarin yadda yau din ta kasance min, sai Kara bani shawara yake.


Na kuma fada masa MD din ya bani abinci amma ban ci zan kai wa Mama muci tare.


Murmushi Baba yai yace "ban dani za'a ci Kenan Dije".


A kunyace nace "A'a Baba tare zamu ci ai shiyasa ma na fada maka, kaga sai Mama ta dibar na".


Dariya yai yace "A'a kuci abin ku na koshi ma ni, fatan ba rokar sa kikai ba dai koh?".


Tsifi tsifi nai da idanu a dake nace "ba rokar sa nai ba Baba, shine kawai ya bani".


Gyada kai Baba yai yace "Madallah don yana da kirki sosai nasan kika rokesa zai baki amma don Allah kar ki rokesan kar ya dauka kwadayayyiya ce keh".


Daga kai nai nace "toh Baba, Zan kiyaye".


A haka har muka karasa gida.........





*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*


***



Comments Nd share plz





Mrs A.M🥰