Page 11
by @oumamani20
🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎
Free page 11
Written by
Mrs A.M
Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*
Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.
Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
***
*BABY BEAUTY LOUNGE*
*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*
*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*
PHONE NUMBER *** OR ***
*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*
Da sallama na shiga gida baba kuma ya tsaya shigar da Machine dinsa garejin makocin mu, su Umma suna zaune ita da Inna fure sai hajjo da ke gefen Umma tana yanke farce.
Dukan su ido suka zubo min suna kallona, ban tsaya ko gaishe da su ba na shige dakin mu da dan sauri ina fadin "Mamana Mamana mai share hawaye na..."
Murmushi Mama dake zaune tana gyara wake tai kawai yana gyada kai, da sallama na shigo dakin ina fadin "Mamana ni kadai".
Bata dago ta kalle ni ba hakan yasa na matsa jikinta kawai na shige jikinta na rungume ina sakin ajiyar zuciya.
Kasa hana ni kwanciya a jikin ta tai sai cigaba da gyara waken ta kawai tai, ganin ta min shiru batai magana ba na dago na kalle ta cike da shagwaba nace "Mama kina kallo fa na shigo baki min magana ba".
Ba tare data kalle ta ba tace "ke da kika shigo kin gaishe ni ne Dije?".
Turo baki nai ina dirza kafa a kasa cike da shagwaba nace "Mama ina wuni toh, kuma da dana shigo waka nake miki fah Mama ina wake ki kamata yai kina tafa hannu kina cewa lale lale Dijen gala ta mai gari ba auran talaka ba.."
Mama bata san lokacin da ta fashe da dariya ba tace "sannu Dije, Allah ya nuna min ranar da zaki yi hankali".
Turo baki nai ina cigaba da dirzar kafata a kasa sai kukan shagwaba nake da ba hawaye.
Ganin abin nawa bana kare bane Mama tace "zaki min Shiru ko sai na make ki anan kuwa".
Shiru nai ina janyo jakata fito da ledar nai na bude takeaway din ciki, a jiye wa nai a gaban Mama nace "Mama gashi kinga MD ne ya bani amma na kasa ci duk yunwar da nake ji nace tare zamu ci nida ke".
Mama da tunda Dije ta fito da abincin gabanta yake faduwa ganin lafiyayyan abinci ga kaji zuku-zuku.
Zuba wa Dije ido tai taga idonta na Kan abincin sai hadiyar yawu take, hade rai tai sosai tace "Khadija.."
Wani irin bugawa kirjina yai Jin sunan da Mama ta kira ni dashi Wanda ban taba jin ta kira ni da wannan sunan ba.
Ganin irin kallon da take min yasa ni saurin sunkuyar da kai na kasa gabana yana faduwa sosai.
Murya a kausashe Mama ta sake cewa "Khadija".
Kawai sai na fashe da kuka ina fadin "Mama don Allah kiyi hakuri baxan sake ba wallahi.."
Zuba min ido Mama tai gabanta Yana faduwa, cikin sanyin murya tace "waye ya baki wannan abincin?".
Kai na a kasa nace "MD ne ya bani Mama, mai companyn kuma shine nake yi wa gyaran office din".
Har ynxu nazartar ta Mama take, a nutse tace "ki fada min gaskia Dije, baki yai ko tambayar sa kikai".
Gaba daya tsoron Mama ya kamani jiki na har wani rawa yake sbd tsoro, hawaye na zuba a idona nace "Mama kar ki dake ni don Allah baxan sake ba wallahi".
Wani irin tsinkewa Zuciyar Mama take tsoron ta daya kar aje MD dinnan latsa Mata yarinya yai shine ya bata abinci, tabbas ta yadda da tarbiyya Dije amma dan yau ne fah.
Kara tartaro nutsuwa Mama tai tace "baxan dake kiba inhar baki yi abin dukan ba Dije, fada min yadda akai ya baki abincin nan".
Kai na a kasa na fadawa Mama dukkan abinda ya faru a office din, da kuma Yasir da muka sha hira da shi hadda Salim din da ya ke ta min ihu..
In banda bugawa ba abinda zuciyar Mama take, tabbas yar t ta shiga cikin jarrabawa ta sabuwar rayuwa, addu'ar ta kawai Allah ya tsare Mata ita a duk inda take.
Ajiyar zuciya ta sauke murya a sanyaye tace "Dije irin tarbiyyar da nai miki kenan?".
Kuka na sa kawai ina girgiza Mata kai jikina a sanyaye.
Girgiza kai tai tace "wannan ba tarbiyya ta bace Dije, ban miki tarbiyya don ki dinga rokon abu a hannun wani ba, kina kallo ko a cikin gidan nan bana yadda ki karbi abu sbd bana son ki tashi da kwadayi amma daga zuwan ki company yau har kin fara roko Dije".
Kuka na kara saki mai dan karfi duk na rude, so nake na matsa kusa da ita amma na kasa sbd tsoro, da kyar na bude baki nace "Mama don girman Allah kiyi hakuri kuskure ne wallahi Mama baxan sake ba, sha'awa kazar ta bani amma na tsane ta ma ynxu kwata kwata".
Murmushin takaici Mama tai tace "Dije kazar ce ta burge ki shine xaki karba, mai yasa baxa kiyi hakuri ba tunda kin san bamu da shi, irin wannan halin dashi samari suke amfani in sun gane yarinya Mai kwadayi ce suke cutar ta Dije, irin wannan dabi'ar ita Maza suke so suga ni Mata suna marmarin abin hannun su suku ma sai su fanshe a jikin ki".
Rintse ido na mai nadama na baibaye ni, tabbas sai ynxu ma nake Jin kunyar abin da nai, roko ba dabi'a ta bace kawai dai kazar ce data burgeni da kuma yunwar da nake ji.
Ganin yadda jikina yai sanyi yasa Mama cewa "toh shikenn kar ki sake kinji, yarinyar kirki ina alfahari da ke sbd nasan ko Mai kike yi kina yi ne sbd ni Amma don Allah ki sake kiyaye wa kinji.."
Daga mata kai nace nace "Ngd Mama insha Allah baxan sake ba Mama".
Murmushi tai tace "dauki abincn kici nasan yunwa kike ki".
Turo baki nai nace "Mama nidai baxan ci ba gaskia, haushin abincin nake ji akan sa kike fushi dani".
Murmushi Mama tai tace "ai ba fushi nake na Dije, kawai ban ji dadin yadda daga fara aiki kika soma watsi da tarbiyya taba ne".
Marairaice wa nai nace "ai baxan sake ba Mama".
"Allah yasa" ta fada tana mike wa ta shige daki...
Shiru nai kawai ina tunanin wautar da nayi na rokar abinci a gun MD ko wani irin kallo zai min ynxu oho ga karin haushi na yadda ya ce min wai ina wanka, gaskia ya kamata na fara wanka akai akai ko tsallaken kwana daya ne nayi na daina barin ina kwana uku ban yi wankan ba.
Duk yadda Mama tai tai naci abincin nan kasa ci nayi sai hakura tai kawai ta fita da kanta ta bawa almajirai abincin har robobin.
Kwanciya nai bayan na yi addu'ar kwanciya bacci, wayar mama ce a hannu na ina game din snake, game din nake amma ban san mai yasa ba hankali na gaba daya yana Kan MD.
Haka kurin nake Jin a jikina kamar yana cikin damuwa, kallo daya na masa naji tausayin sa kawai ya kamani.
Kallon agogo nai naga har 1 ina tunanin da ban san ko na meye na, mike wa nai na fita zuwa tsakar gida nayi alwala.
Dawowa nai hau Kan sallaya na fara sallah, kawai sai na samu kai na da yiwa MD addu'ar Allah ya yaye masa dukkan abinda yake damun sa, na dade sosai ina addu'ar kafin na mike na koma Kan gado gefen Mama na kwanta.......
********
Kwance yake akan gado ba abinda yake tunani sai yadda Dije take dariya tana hira da Yasir.
Lumshe idon sai yana Jin wani kaunar ta yana Kara ratsa jini da vein dinsa, ba abinda yake kara hangowa sai yadda take magana bakin ta yana motsi dan karamin bakin ta kawai yake hangowa.
Murmushi yai yana shafa saitin zuciyar sa bai taba jin haka ake soyyaba Ashe, matar sa auren saurayi da budurwa sukai kuma yana son ta a lokacin amma Jin yadda yake kaunar Dije sai yaji Ashe ma ita ba wani son ya yake ba.
Yana cikin wannan tunanin Mariya ta shigo cikin shigar bacci, tana da kyau sosai duk da kasancewar ta ba'ka, za tayi sa'a da Saudat shekara 30 amma tana da kyaun jiki
Tun da ta shigo ya zuba mata ido tana kallon ta, ji yake ina ma ace Dije ce ta shigo dakin sa ynxu, shifa baya ma Jin sha'awar matar tasa gaskia ynxu don shi Kam Dije tayi kane kane a zuciyar sa.
Tsaki yai kawai yana mikewa ya hau Kan gado.
Da mamaki Mariya ta kalle sa, cikin sanyin jiki ganin yadda yai mata tace "lafia Daddyn Junior, mai ya faru".
A hasale ya dago ya kalle ta yace "ni don Allah ki kyale ni, ki fita ma daga dakin bana son ganin ki gaba daya".
Da mamaki tace "kamar ya Daddyn Junior, taya zaka ce min na fita daga dakin Ka".
Mikewa yai yace "dallah malama wuce ki fita tun kafin na tsinka Miki Mari, haba nace bana son ganin fuskar ki dole ne?".
Tsaki taja ta juya ta fice tana cewa "Allah ya kyauta".
Yana kallon ta kamar zai bita ya mammake ta yace "aikin banxa kawai, mace gidahuma bata iya komai ba wai Daddyn Junior" ya fada yana kokayar maganar ta.
Cikin takaicin ya koma kan gadon Yana jin haushi, amma daya tuna da Dije sai ya lumshe ido yana fatan yai mafarkin ta......
*******
Zagaye makeken dakin ta take duk da sanyin AC dake tashi amma gumi take yi ko ta ina.
Ita taya ma zata fara wannan abin, ta nemin dan cikin ta, toh dan cikin ta mana haba, mahaifin sa take aure kuma babarsa yayar tace.
Goge gumi tai kawai yana yarfe hannu ta, gashi fa na Kan dutse ya ce Mata dole wannan ne matakin karshe akan wannan cikar burin ta da take so.
Ita da namiji ma ba sha'awar sa take ba, ita fa don dole take zuwa shinfidar Papa amma sam baya burge ta tana da matan ta tsala tsala har guda biyu(Wa'iya zubillah innanillaihi wa innanillaihir raji'un, Allah Ka tsare mana imanin mu Ka sa mufi karfin zuciyar mu).
Ita sam bata san ya zatai ba gashi bata da abokin shawara, ko aminiyar ta bata taba nuna mata cewa tana zuwa gun boka ba sbd a tunanin ta matukar Ka bari sirrin Ka ya fito daga cikin Ka, Ka fada wa wani toh ba shakka ya tashi daga sirri don dole wata ran sai ya bayyana, ko neman matan da take ba Wanda ya sani sai isu isu kungiyar su.
Ajiya zuciya ta sauke tana fadin dole na yadda da wannan abin, amma kafin nan sai na fara sa masa maganin nan tukun don bana son a samu matsala, amma kam wajibi ne ma na sadu da Elhajj in har hakan na nufin cikar burina..
Murmushi tai tana samun nutsuwa ta zauna akan kujera sai kuma maganar na kan dutse ya dawo mata akan cewa ba ita kadai bace take son ganin bayan Elhajj, da akwai masu yin shirin da yafi nata ma.
Tana mamakin ko su waye haka suke son ganin bayan sa kuma bayan ita, ya kamata ya dage sosai ta yi abinda na kan dutse ya umarta gudin kar wasu can suyi shirin su tana zaune su kwace komai.
Da haka ta dan samu nutsuwa ta kwanta akan gado tana sauke ajiyar zuciya.
*****"*
Washe gari da safe wanka nai na shirya a nutse har da turaren Mama na fesa, sai murna Mama take ganin yadda na nutsu nayi wanka cikin nutsuwa.
Kayan makaranta nasa na fita hannuna rike da Humaira autar mu yarinyar Inna fure, jini na ya hadu da nata sosai, matsalar kawai iya da take Hana ta min magana.
Tare muka je makarantar har aji na kai ta kafin Nima shiga.
Sai tsokana ta ake wai na fara aikin goge goge a wani company na Sama maid, amma ko a jikina ni ba Wanda ma na tsaya kulawa don kar na biye musu su bata min jiki, jina nake a Sama nayi wanka.
Sai karfe 3 na koma gida, a gurguje naci abinci na sa Kaya da hijab kudin motar da Baba ya bawa Mama ta bani na karba na fita.
Ban sha wahalar samun adaidai ta ba, shiga nai muka tafi.
A kofar companyn ya ajiye ni na biya sa kudin sa na shiga, tun daga bakin gate duk Wanda na gani sai mun gaisa in ya nuna bai gane niba na tsaya na masa bayanin nice Dije mai yiwa MD aiki.
Sai da na biya gurin Baba na gaishe sa sannan na wuce floor din MD.
Ina zuwa na samu Yasir a tsaye da alama fitowar sa kenan daga office din MD din.
Kallona yai yace idon ki Kenan Khadija, tun dazu nake zuba ido baki zo ba.
Dariya nai nace ina wuni Ya Yasir.
Fuskar sa dauke da murmushi yace lafia qalau Dijen Mama.
Murmushi nai nace Ka manta jiya na fada ma ina zuwa makaranta, ban dade da tashi ba na biyo, don ma nayi sauka asabar da lahadi kawai nake zuwa.
Daga kai ya yace haka fah, na manta shaf wallahi, ki shiga ki gaida MD toh.
Daga kai kawai nai na tura handle din kofar na shiga.
Idona ne ya sauka akan abinda yake ci, paper children ne daya ji Hadi a foil paper ga kifi lafiyayye shima a gefe, sai sakwara da miya.
Ban san lokacin dana hadiyi yawu ba ina fadin "daure daure Dije".
Dagowa yai ya kalle ta da mamakin abinda yaji tana fadaaa.......
*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*
***
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰