TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

3

by @nanadiso10

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)





NA

NANA DISO

&

ASMY B ALIYU


3...


Anan cikin karamin parlon Hajja,yayi zamansa ya ɗora Fatima batool a kirjinsa da ta lafe sosai cikin natsuwa da kwanciyar hankali take baccinta a natse.ko dogon motsi kasayi yayi ganin yake idan ya motsa zata iya tashi.jin yake kamar kansa zai rabe gida biyu saboda tsananin ciwon da yake.sai da baccin nata yayi nisa Aunty maimuna ta fito ta karbeta .ta ɗan kallesa tana faɗin.'Ya kamata kaima kaje ka samu kayi bacci ,gyada kai Kurum yayi tayi masa sai da safe ta juya ta koma cikin daki.

Ajiyar xuciya ya sauke jiki sanyayyen ya koma bangarensa yana zuwa ya cire jallabiyyar jikinsa ya nufi closet dinsa ya dauko kayan bacci masu tsantsi ya saka riga da wando farare tas a hankali ya hau kan bed dinsa

Ya kwanta lumshe ido yayi yana tunanin yadda rayuwar Fatima batool zata koma,a gefe ɗaya yana tunanin yadda zai yiwa su hajja bayanin da zarar anyi aurensa zai mayar da batool din gidansa .ta zamana karkashin kulawarsa ko kaɗan baya son tayi wani maraici.a gefe ɗaya yana tunanin yadda zaiyiwa Faiza bayani ,yasan halin Faiza duk da tsananin soyayyar da take yi masa zaiyi matuqar wahala ta yadda da riqon Fatima batool.saboda Faiza irin yaran nanne ya'yan Hutu da ko kaɗan basa son wahala.baso ɗaya ba ba sau biyu ba ta sha faɗa masu bata fatar da sunyi aure su fara tara ya'ya ya'ya basa gabanta tana so su mori amarcinsu kafin xuwa ƴa'yansu.shi dai duk abunda zai faru bazai taɓa barin batool a hannun kowa ba idan Faiza taji zata iya rayuwa dashi a haka shikenan idan taji bazata iya ba kowa ya kama gabansa.daman shi bawai matsuwa yayi da yin aure yanzu ba daman hajja ce ta matsa da kuma gidansu faiza.da wannan tunanin da ya matsawa kansa ya tashi da ciwon kai mai tsanani sallar asuba ma lattin tashi yayi dakyar ya tashi yayi sallah ya koma ya kwanta jin ko dogon motsi yayi sai kansa yayi wani irin sara masa.waya ya dauka ya kira Aunty maimuna akan ta saka yar aiki ta kawo masa tea.yana buqatar cin wani abu kafin yasha magani ,duk da lokacin karfe bakwai na safe dan takwas batayi ba yanayin muryarsa cikin kulawa Aunty maimuna ke tambayarsa ko bayada Lafia ne?"sai da a dafe kansa kafin ya bata amsa da kansa ne ke ciwo zai sha magani ya kwanta.kafin rana tayi.ko magana mai tsayi baya sonyi.sannu tayi masa tana sauke wayar,shima jifa da wayar yayi akan bed dakyar ya koma parlor dan jiran a kawo masa tea .dan ba kowa yake bari ya shigar masa cikin master bedroom ba mai aikinsa ɗaya ne namiji shike masa gyaran bedroom.baa jima ba yaji ana knocking kofar falon dakyar ya miqe tsaye ya nufi kofa ya buɗe cikin girmamawa ta saukar da kanta kasa ta gaishesa ciki ya amsa ya juya yabar bakin kofa ta shigo cikin falon ta nufi Centre table din dake cikin parlor ta aza madaidaicin tray da ta shigo dashi.juyawa tayi ta fice daga sashen nata.jingina bayansa yayi da kujerun da suka kawata falon.ya kai minti goma a haka dakyar ya tashi ya haɗa tea.rabin cup kawai ya sha ya aje

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa jin zafi ma taso masa.jallabiyyar dake jikinsa ya cire jin zafi na fita ajikinsa

Saboda ruwan tea da ya sha masu

Zafi kai tsaye toilet ya nufa ya sakarwa kansa shower.wanka yayi ya fito daure da babban towel sama sama ya shafa cream din da yake amfani dasu masu tsadar gaske.wani dogon wandon bacci ya dauko har kasa ya saka ya ɓalle magani ya sha da ruwa marar sanyi kai tsaye kan bed ya nufa daidai nan wayarsa ta soma ring.kallon wayar yayi ganin Faiza ce ta kira yasa ya dauka .Ashe rasuwa akayi maku shine ka kasa sanar dani?"jin yayi shiru yasa ta manta batayi masa sallama ba Tasan kuma ya tsani haka,dole sallamar tayi tana gaishesa da Respect ya amsa

Cikin muryarsa mai cike da izza da wani irin class wanda shike saka mata mutuwa akansa.gaisuwa Faiza tayi masa ,tana faɗin."anjima zata zo da mumynta suyi gaisuwa ya amsa da Allah ya kaisu.kokarin jansa take da hira ya katseta da sauri yana faɗin."Faiza muyi magana zuwa anjima kaina na ciwo bacci zanyi.

Cike da kulawa tayi masa fatan idan ya tashi Allah yasa kan ya daina ciwo.

Kafin ta sauke wayar.kashe wayar yayi duka dan yana bukatar yin Bacci.

Bai dade da kwanciyar ba ya samu baccin ya d'aukesa.acan cikin gida kuwa su hajja tunda sukayi sallar asuba basu koma ba saboda wanda suke zuwa amsar gaisuwa kuma hankalinta na akan Sadauki da har kusan qarfe goma da rabi na safe bai shigo ba sai tambayarsa akeyi ,kasa daurewa hajja tayi tana tunanin ko ciwon kan nasa ne yayi tsanani.ta faɗawa Aunty maimuna taje ta dubasa ko kan ne.idan baiji sauqi ba

A kira family doctor dinsu kawai ya Dubasa.knocking kofar parlor Aunty maimuna tayi jin shiru yasa ta kama handling din tana addu'ar Allah yasa a buɗe take babu key.tana turawa ta buɗe,saka kanta tayi cikin baban parlor nasa banda karar AC da kamshin room freshener da ya gama gauraye ko'ina babu abunda ke tashi a parlor kai tsaye master bedroom dinsa ta nufa.tsayawa taya a bakin kofa tana knocking kofar.daidai lokacin da Sadauki ya fito daga wanka tashinsa kenan,rigar wanka ce ajikinsa ya bada umurnin a shigo kai tsaye dan yasan bazai wuce Aunty maimuna ba ko hajja.su kaɗai ke shigowa har cikin bedroom dinsa.

ɗan tsayawa Aunty maimuna tayi daga bakin kofar tana kallon rigar wankar dake jikinsa wacce ta rufe ko'ina ajikinsa.ka tashi kenan ?"ya ciwon kan."Aunty maimuna ta jero masa tambayoyi lokaci ɗaya,na samu sauqi ya batool ?"me take ko kwana take?"ya faɗa yana kallon Aunty maimuna jin amsar da zata bada.

Tana hannun murjana ta goyata bacci take.da sauri ya buɗe ido cike da tsoro a Muryarsa yake faɗin."Haba Aunty maimuna taya zaki baiwa murjana goyon batool idan ta qaryata fa.?"ya faɗa cike da tsoro a Muryarsa,girgiza kai Aunty maimuna din tayi mamakin Sadauki na kasheta murjana Babbar yarta ce a kalla yanzu shekarar ta kusan goma sha huɗu,basar da zancen tayi tana faɗin."a kawo maka break fast anan kayi a bangaren hajja akwai mutane.da haka ta juya tabar kofar dakin nasa daman kuma bata shiga ba.cikin natsuwa ya shirya

Anan bangarensa yayi break fast

Kafin ya nufi bangaren hajja da manyyan kaya ajikinsa tun kafin ya karaso kowa yasan Sadauki ne saboda sabon da kowa yayi da turarensa mai matuqar tsada da kamshi mai kamewa a koina.sama-sama ya gaisa da bakin dake bangaren hajja kai tsaye ya wuce main parlor hajja Acan ya tarar da Aunty maimuna xaune tana amsa waya murjana ce har lokacin goye da batool a bayanta tana ɗan xagaye da falon da sauri ya nufeta.yana faɗin.'murjana ta kwanceta haka kar ta jimata ciwo

Faɗa ya hauyi akan kar a kara baiwa murjana goyon batool din."haɗe rai murjana tayi tana kallon uncle din nata ,nafa iya goyo Lafia lau Uncle

Ka tambayi mami Kaji nike goya sadiq lokacin da yana karami.tana nufi Kaninta din da Aunty maimuna ta yaye tuntuni.zama yayi yana qarewa kyakkyawar fuskar batool din kallo batareda ya qara bi ta kan surutun murjana ba.ta dade a hannunsa kafin ya miqawa Aunty maimuna din ita

Ficewa yayi daga falon ya nufi can babbar harabar gidan inda baki maza ke zaune.baa jima ba baffansa watau yayan mahaifinsa ya iso da ya'yansa manyya maza biyu da kuma matansa

Kai tsaye cikin gida suka nufa suka qara yiwa hajja gaisuwa kafin su dawo harabar gidan acigaba da zama dasu.sai bayan sallar la'asar baffansa ya wuce bai jima da tafia ba Faiza ta iso cikin mota Tareda mahaifiyarta wacce ita ke jan motar kai tsaye maigadi ya buɗe masu get har cikin babban parking lot sukayi parking.

Mahaifiyarta ta fara fitowa kafin itama ta fito kowane da mayafi akansa.na mahaifiyarta yana da ɗan girma nata ne dai bayada girma ko kaɗan tamkar ba gidan gaisuwa Tazo ba ko aikinta ganin yadda mutane keta kallonta,hangosu Sadauki ya qaraso cikin girmamawa yana gaisheda maman faiza.cike da kulawa ta amsa tana masa gaisuwa.kallonsa kawai Faiza keyi tamkar zata haɗesa dan so bata damu da jama'ar dake harabar wurin ba ta riqo hannunsa da sauri tana ɗan narke masa.tuni mummy ta wuce bangaren hajja ,how are you?"ta faɗa tana ɗan matse hannunta dake cikin nasa.zare hannunsa yayi a hankali cikin nata suka jera zuwa cikin gidan.da Faiza da mahaifiyarta sukayiwa hajja,gaisuwa da duka mutanen dake cikin parlor,itadai Aunty maimuna kallon faizar kawai take ganin irin shigar da Tazo gidan ta'aziyya dashi

Ta lura budewar idon Faiza tayi yawa sosai.haka taga babu abunda ya shafi Sadauki kamar ya fison haka kasancewar ya saba da rayuwar Turai ganin yake hakan ba komai bane rayuwarsa yake kai tsaye irin ta turawa.sun jima sosai a gidan kafin suyiwa su hajja sai da safe akan gobe zasu dawo wannan karon ma Sadauki har bakin mota ya rakasu sai da yaga fitarsu ya koma wurin zamansa.




#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#HOT LOVE AND ROMANTIC

#TSARIN ALLAH

#YAN TAGWAYE NOVELS.