TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

4

by @nanadiso10

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)


NA

NANA DISO

&

ASMY B ALIYU




4..

Sai wajejen ƙarfe 10 sannan yasamu kansa yau ma haka ya wuni baici abinci ba saboda mutanen dake zuwa gaisuwa daga abokanan kasuwancin su harma na iyaye. Bangarensa ya Nufa bayan yaraka mahaifin fa'iza har motarsa sukayi sallama suka fita. Da ɗan hanzari yakarasa bangarensa sai da yayi Sallama ya bude yashiga kawataccen palonsa da ko ba'ayi maka bayani ba kasan anzuba kudi aciki bai tsaya anan ba har sai da yakarasa ciƙin daƙinsa Nan yashiga cire kayansa bakinsa dauke da bismillah sai da yacire komai ya ɗauki karamin towel yashiga bandaki yayi wanka yafito yana kallon yadda mazan takarsa ke wani Nuni dan ambaton Allah yayi haɗe da faɗin "Subhanallahi Allah kawomin sassauci." lamarin karfin jikinsa tun baya damunsa har yafara damunsa yanzu Allah yataimkeshi ma biƙin nasu bai wuce watanni   suka rage ko dazu da faiza ta rike hannunsa sai da yaji jiƙinsa ya mimmike duba da ba yanayin farin ciki yake ba ya hanashi shiga yanayi. Har sai da ya kwanta ya tuna da fatimatul batool hakan yabashi damar karasawa cike da ɗan hanzari sallama yayi agurin kamin ya nufi ciƙin dakin hajja yana sallama. " Dan Albarka. " hajja tafada tana kallonsa." " Hajjata yafaɗa idonsa na kokarin kawo ruwa." " DanAllah kabar kukan nan haka sadauki Addu'a zakayiwa innarka banason kukan nan naka." Sai da yayi shiru nadan lokaci sannan yace " Ina batool ?" " Gatacan acikin gadonta gaskiya Allah yawadaran malam kabiru wallahi Nayi danasanin auransa da ƴar'uwata inbanda babu kyau a musulunci da sai Nace Allah ya'isa wannan cin mutunci har ina komai yafaru tunda ansamu karuwa dashi ai ya ajiye yazo mana ko dan wannan baiwar Allah." Batare da yace mata komai ba ya'isa bakin gadon yana ganin kyakyawar fuskar yarinyar dake kama da yayarsa wato Aunty maimuna ganin yadda ta kaikaice kamar tasansa tashiga murmushi sai yasakashi murmushi atake yana fadin " Allah yayimiki albarka ya rayamun ke Ya omri." Kamar tasan me yake fada sai tashiga murmushi. " Wai badakai nake magana ba SADAUKI kayimun banza kamar bakasan me nake faɗi ba." Sai da ya dakkota daga cikin gadonta sannan yajiyo kusa da hajja  yace " Ayimun afuwa hajja wani abun yasake faruwa ne?" " Kai dai wallahi matarka ta Bani  da halinnan naka na Shariya yanzu duk bayanin da nake maka bakajina saboda Allah To malam lawan yasamu uban yarinyar nan yake gayamasa rasuwa shine yace  Ai shine budar  bakinsa yace bashi yayi cikin ba wai bayan yasaketa cikin yabayyana narantse da Allah dan baffanka ya hana fidda maganar nan da na tabbatar muku sai na makashi kotu dan bazan yadda ya shegantamin diyaba hajja tafaɗa kuka na kokarin kufce mata." Aunty maimuna da shigowarta kenan tace " Ai wallahi inna baikamata abar kabiru haka ba bayan tozarci harda jaririya." Ko da yadago idonsa sun canza daga kalar dasuke zuwa wata kalar sosai bacin rai ya sauka a fuskarsa amma ganin yarinyar tasaka kuka yasashi kokarin kallonta yaga metakiyiwa kuka, aunty maimuna ce ta mika masa madarar yarinyar tana fadin wallahi tausayi take ban saboda rashin ruwan nono gashi ni ban iya bata kasan yarancan dana yaye suma basu samu ba sai madarar Na basu gashi mutane basusan shayar da yara nono yanzu dazarar kabata kamin lokaci kaɗan taji yunwa. " Ina rokon Alfarma gareku DanAllah kubar maganar kabiru a ajiyeta agefe tunda ya nuna bashida imani da mutunci to sai abarshi da halinsa yarinya kuma inshaa Allahu sai nazame mata duk wani gata arayuwarta Ni nan nazama ubanta kuma uwarta danHaka hajja kidaina daga hankali akansa wallahi bakusan komai akan malam kabiru ba shine yayi sanadiyar mutuwar innata dan kuwa zuwa... nan yabasu labarin dukan da ya samu anayiwa innarsa. Hajja ce tasaka tafi tana fadin Innalillahi wa'inna illahirrajiun DanAllah Sadauki wannan satin ka shiryamana tafiya muje muyiwa ƴar'uwata addu'a." " Tohm hajja amma zan shiga china thursday sai dai ko idan nadawo ko?" Badamuwa  bari nakoma palour din.


  Bayan Sati biyu.


    GIDAN MALAM KABIRU


  Dariya matarsa sahura takeyi tana faɗin amma malam kayimun daidai wallahi. " Ni za'a bari da wahala kina kallo gidannan abinci na dakyar muke ci shikenan naje nadakko jaririya in kawota nan taci me?" " Ai gwara dakace musu shegiya ce." Uwrgidansa ce tace " Amma malam kaji tsoron Allah wallhi bandaina magana bandaina gayamaka gaskiya yarinyar nan hakkinka ce naje naganta wallahi kamar an yanka kara hancin ka sak fa idonka dan daima tabiyo yayar uwarta." " au Hansai sai da kikaje bayan nahanaki zuwa." " Sai naje idan da abunda zakayi sai kayi ni zaman amana mukayi da baiwar Allah kuma bayan ta mutu ace bamuje gaisuwa ba dan mune masu bakar zuciya ni nakasa sanin halinka wallahi anya kanada imani." Ƙau kakeji an wanketa da mari." " wallahi zan sakike kije can ki koma kauye mara mutunci." " Ai dukan mata da bakin hali ba yanzu kafara ba dan haka dan ka dakeni ba abu bani ba tausayi ko imani ne dakanka ba inshaa Allahu diyar binta sai ta zamar muku MURUCIN ƘAN DUTSE.." " Gaskiya yaya ina tantama anya kina kaunar malam kuwa wannan shegiyar jaririyar kikewa fata nagari? Wai yaya kanki ɗaya kuwa." Harararta matar tayi tace " Haka zaki kare kuma haihuwa kema kinyi tashege daƙin nan malam yashiga zaginta ta uwa ta uba har yana cewa sai yasaketa bata kulashi ba haka yaranta sukayi masa banza suma." " Gaskiya nidai ina dana sanin samun uba daya daga cikin yaranta tafada tana jan tsaki." " Addu'a zakuyitayi masa." " Ai wallahi yadda yake wulakantamu babu abunda zan masa yarinyar tafaɗa tana barin gurin.


   BEIJING CAPITAL INTERNATIONAL AIRPORT CHINA


  Babban filin saukar jirgi ne faɗar haduwarsa da kawatuwarsa sai wanda yagani Alhamdulillah yafada ayayin da yake karasowa sanye yake da ash colour na kananan kaya sunyi masifar kyau da karbar jikinsa mamakine yakusan kasheshi ganin wanda baiyi tsammani ba yazo tarar sa cikin girmamawa yace " Welcome sir yana karbar jakarsa dake hannunsa. " Thank you sadauki yace  yana shiga motar yaja suka tafi. Wani kayataccen hotel suka shiga fadar haduwarsa ko kawatuwarsa sai Allah dakine suka shiga babba akawai babban palour sai dakuna guda uku da kitchen da toilet. " Do you need anything sir." " No let meet tomorrow please." " Already sir take care yafaɗa yana barin daƙin.  Agogonsu yaƙallah yana tunani Nan yacire komai najikinsa da addua sannan yashiga bandaki sai da yawatsa ruwa yayi wanka sannan yafito yagabatar da sallolin da baiyiba yanajin door bell ya bude dakansa yana karbar abincin sannan yashige ciki, Sai da yaci sannan ya samu ya dan zauna kan kujerar yana duba sakwanni wayarsa ce tayi ringing da ɗan mamakinsa ya kalli mai kira sai data  kusa katsewa yadaga yana fadin " Kamar jira kikeyi in saka line din baki barin in huta fa'iza." Cike da damuwa tace " Wallahi hankalina duk baya jikina fatana kawai naji muryarka kuma nakiraka kanamin faɗa." " Sorry yafada da ɗan shafa sajen fuskarsa kamin kuma yace yakike?" " Ni wallahi baka sona nike kiranka  amma baka kirana yanzu yaushe rabon naganka? Saboda Allah?." Murmushi yayi yace " Matar sadauki da yardar Allah." Indi yafadi haka tasan karshen nuna soyayya kenan sai tasaka dariya. Nan tashiga bashi labari yana jinta duk da aikin dake gabansa sai datagama sannan yace " inafata hakan ya sakaki farin ciki matar sadauki da yardar Allah." " Inasonka SADAUKI NA." " Thank you yafada yana kashe wayar saboda maganar tata bakaramin hargitsa masa tunani yakeyi ba duk wata gaba dake jikinsa sai da ta amsa dan dafe ƙansa yayi yana faɗin Subhanallahi yaa Allah wannan fitina kasa nafi ƙarfinta yafada yana ganin yadda tsigar jiķinsa take mimmikewa. Shayin dake gabansa ya dauka yana sha wanda yakara tayar masa da wata fitinar a hankali yace " I can't wait for 5month komai adaddafe nake in komawa za'ayi komai agama tunda yana daf da gama hada lefe kuma gidansa is ready yanzu dan shine yake kallon gidan mahaifinsa duk da babu wanda yasan nasane sai shi da yar uwarsa da hajja, yanason faiza matsalar sa daya da'ita kyamar mutane kuma yasan wannan bazai dameshi ba tunda shima bawai mai saƙin jiki da kowa baniba dan idan baya kasar to tabbas yana tare da hajja ko kasuwa."


   Gaskiya mumyn ina son SADAUKI wallahi nifa dama an dawo da bikin nan kusa" Mumy ce ta kalli fa'iza tace " Allah dai ya shiryaki wallahi ke kin maidani kamar kakarki." " To wai mumy idan banyi hira daku ba da wa zanyi nifa wayayyiyace." " Bani guri ne dan Wallahi sadauki zaisha fama." Kalmar fama kaɗai da tafada yasata murmushi tana shigewa daki.


  Sannu da kokari hajjata yau ban shigo da wuri ba so nakeyi SADAUKI yadawo sai na tafi daita hajja ni zan riketa." " Banki taki ba Amma nasan ɗan uwanki bazai yarda ba." " To hajja saboda Allah shifa aure zaiyi ina ke ina wata wahala yanzu?" " To Allah yakiyaye fitina ai gobe zai dawo kusan kullum sai anyi video call kusan sau uku maimuna Lalliah kenan baya barin wani dan wani yaji dadi kinga ydda sadauki yake kula daita." ai dole akula da zuri'arta inna , hajja Allah yayi mata albarka yarayaman ita bari nayi mata wanka." " ai nayi mata tun dazu sai dai kara hadamata madarar ko. Sai data gama komai sannan driver ya maidata gidanta hajja kuma ta cigaba da kula da batool da yanzu kana daukarta zata sakar maka murmushi.


#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#HOT LOVE/ROMANTIC