TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

8

by @nanadiso10

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)


DAGA ALKALUMAN ƳAN TAGWAYE BIYAR


AREWABOOK@Nanadiso10



NA

NANA DISO

&

ASMY B ALIYU


8..


A kwana biyu da maganar fasa auren sadauki bakaramin ciwo yayi ba dan tun yana kiran likita har takai takawo baffa da kansa ya kaisa asibiti suka bashi kwanciya wanda hakan bakaramin daga hankalin hajja yayi ba da Aunty maimuna dan su yadda suke ganin yana tada jijiyoyin wuya akan yafasa auren basu taba tunanin hakan zai haifar masa da ciwo ba ko kuma ya firgitasa, Yanzu ma yana kwance akan gadon asibitin hannunsa akan cikinsa yaɗan rike yana ciza baki ga kuma mararsa dake faman ciwo kamar tacire " Yaa Allah!!!" hajjata kiyimun addu'a. " dayake itama duk afirgice take ta kallesa cike da tausayin yaron nata abunka da mai farar fata fuskar tayi jajir ga idonsa dake bata tsoro duk da uwace amma zargin data keyi akan ɗan nata " Sadauki me isa bazaka janye batun batool ba kayi Aurenka ina tunanin haka shine mafi Alkhairi. " baice mata komai ba har ta dafa cikin nasa tashiga yimasa addu'a tana gamawa yasamu bacci ya ɗaukesa.


   Aunty maimuna dake zaune dakin maigidanta tana bawa batool madara atake yarinya ta shiga raira kuka har mai gidan nata dayake dattijone yana jijjiga batool din alamun tayi shiru amma kamar zugata sukeyi. " Maimunatu yakamata yarinyar nan tafara cin abinci kinga madarar nan bata isarta fa." " Nafara bata Alhaji." Baikara cewa komai ba yana jijjigata amma kwatakwata kamar ba lallashinta akeyi ba. Daya daga cikin matarsa wacce ta kasance uwargida ce tashigo tana fadin " saboda Allah alhaji Ankawo yarinya duk ta addabi mutane da kuka babu na dare babu na rana sai tayita cillarawa mutane kuka." Babu wanda ya kulata har aunty maimuna ta karbeta tafita daga nan ne mai gidan nasu ya hau yimata fada sosai har taji haushi tabar masa dakin nasa.


  Yanzu ke fa'iza kinason sadauki kika tsaya wata can ta zugaki gashi hatta kudin aure an mayar me yashiga kanki? " Nifa bana sonsa ko kinji nacemiki ina kaunarsa ne? Ki kyaleni da sha'anin wahalalle." " Dallah yimun shiru wallahi kina kaunarsa ko kinzata dazu banga hotunansa kike kallo ba nidai babu abunda zance miki sai dai nace kinyi asarar nagartaccen namiji." " Allah zai bani wanda yafisa fa'iza tafada tana barin gurin." Ko data dawo gidama kusan  maganarce  da mumy take ta  fada sosai yau kamar an zuga mumy din " Ke ba'a riko aka rike miki taki uwar kinsan ladan rikon maraya kuwa tun ina tsumma baffa ya rikeni har nayi aure har duniya ta Nade banida uban da yafisa wallahi akan shirmenku na kawaye.." dady da shigowarsa kenan yace " Dan Allah karki yimata baki mana itafa zata zauna dashi tunda ta nuna batason zaman ai Alhamdulillah sai takawo wanda takeso ba shikenan ba Amma kwanakki sunja magana taki cinyeewa kullum abu daya kike repeating ki kyalemun diyata please."  batace komai ba ta basu gurin.


  Tun likitocin suna tunanin sallamarsa har takai andaina maganar dan da safe zaka ganshi ras har su sha hira da mutane Amma da zarar dare yayi lafiyar sai anemeta arasa wannan shine abunda yasa hajja dawowa asibitin dan ko ta koma gidan batada nutsuwa Akan yaron nata. Yanzu ma kwance yake ya danna azkar awayarsa yanayi duba da yamma ce sai da yagama sannan ya karbi carbin hajja yashiga tasbihi wannan kadai hajja tagani akansa ta godewa Allah dangane da sha'anin yaron nata da sallah da azkar basa wucesa. Haka kwanakin suka riqa tafia  kamin Allah yabasa lafiya Aka sallamesa a ranar  da yakoma yana isa wanka kawai yayi ya wuce zuwa shagunansa dan yasan dole akwai bukatar zuwa. Hajja dake zaune a palour Aunty maimuna da kullum gida take yini saboda tun tana amarya haka takeyi gidan nasu zaman sai addu'a duk da uwargidan itace mai fitana kuma kowa part dinsa yake amma kananun maganganu da munafurci abun har yabaka tsoro sallama da sukaji Anyi ne yasa  dukansu juyawa suna amsawa Hajja dake cin danyen dabino tace " wanake gani kamar hajiya bilki? Yau kece tafe? Kyakyawar farar budurwar dake bayanta ce tafito tana samun guri kusa da mahaifiyarta ta zauna suna gaishe da hajiya atare." Hajiya bilki kwana dubu ai ni wallahi nayi fushi Aunty maimuna tafada tana dan bata rai." Wacce aka kira da hajiya bilki ce tace  " Kuyimun aikin gafara wallahi tunda na tafi jos natarar da yaran nan acikin wani hali shine fa nayi zamana nakama sana'a ina kula dasu." Subhanallahi hajja tafada " kinga dai hajja Ga Amina dai tazama budurwa tana da shekara yanzu ashirin har da hudu." " Allah mai iko ina yayanta da mahaifin nasu." " Ai ingayamiki tunda yarasu mahaifin nasu sai kannensa suka kwashesu wahalar yau daban ta gobe daban yayan nata almajiranci fa yafara hajja sai da naje nakarbi yarana natsayawa karatunsu har dai Allah yasa kinga duk sungama itama wannan din har jami'a takare shikuma yana can da iyalanta a Jo's yara har biyu." " Ikon Allah diyata hajja tafada tana kiran Amina dake zaune kasa taso mu gaisa." Nan kuma hajiya bilki suka hau gaisawa da aunty maimuna anata maida bayan rabuwa. Hajiya bilki tace " Ina ubana ne?" " Sadauki? Hajja tafada tana murmushi." " Shidai hajja Nasan yanzu anzama magidanci   dan Nasan ya aje  iyalai yanzu?" " Nan hajja tabata labarin duk abunda ke wakana sosai hajiya bilki ta nuna rashin jin dadinta tace " ubangijin Allah yabashi tagari." " Diyar tawa fa Hajiya ankusa?" " Wallahi hajja samarin ne sai addu'a kowannen su yazo yaga rashin karfinmu sai yagudu wai zamani yazama abunda yazama kowanne so yake yaga ya aure diyar masu kudi ancika masa gida wani fa kamar gaske abunsa wai yana zuwa gidan namu yace mata ai bamuda abunda zamu zuba masa acikin gidansa ya gudu." " Mijin ne baizoba hajiya " inji aunty maimuna tana fadin bari akawo muku abinci hajja bari nayi mata tsarki kinga kashi tayi. " " Aunty kawo nayi mata cewar Amina tana karbarta ko da aka nuna mata bandakin tsarki tayimata harda wanka tanata wasa da'ita sosai ko dan Allah baisa mahaifiyar ta mai haihuwa bace ba shiyasa take son yara dan ko acan gidan su mahaifinta ita ke renon yara har su girma yanzu ma sai data tambayi kayanta sannan aka bata tasakata mata  ta goyata." Hajja ce tace " Aminatu haka kike da son yara?" Dariya sosai Aunty bilki tayi tace  " Ai wannan maman yara ce indai yaro ne wallahi ko uwarsa albarka." Sai alokacin hajja take sanar mata ai diyar wacece nan aka shiga jimamin rasuwar inna bintu tanajin tausayin yarinyar har ranta. Aunty maimuna ce ta kalli hajja tace " Yau da dare zamu tashi abuja hajja inason muyi sati biyu kuma kinga Sadauki yace ban tafiya da batool yaya za'ayi nikuma banason barmiki wahala wallahi." " To ai zan iya maimunatu Allah yayimiki albarka kema yara baku da duniya lafiya." Hajiya bilki ce tace " To ai ga aminatu banida tunanin bazata iyaba zata kula da'ita sosai." Hakan yasaka sukaji dadi itama Aminatun ta nuna jindadinta akan hakan.


   A kwanakin nan bakaramin kulawa batool take samu agurin aminatu ba dan tunda tafara kulawa da'ita Hajja take mamaki sosai har ta kai tana rayawa akanta ashe ba kinibibin yaran yanzu bane har ranta takeson yaran yau kusan sati uku kenan da tafiyar sadauki China  kuma a yau suke saka ran dawowarsa dan haka Amina ta kama mata tayi masa girki kamin kuma ta dan taimakawa masu gyara masa shashinsa.


   Saukarsa kenan daga babban Airport din garin tun kafin jirginsu za sauka  Anas yadade da karasowa hakan yasa sai da yagama komai yafito suka nufi gida yana tsananta addu'a akan Allah ubangiji yabashi mata aciƙin wannan satin yasamu yayi aure dan idan bahaka ba sha'awarsa tafara firgitasa har suka shiga cikin gidan yana faman tunani sai da suka shiga ne Anas yayi masa magana akan sun karaso. Part dinsa yasa suka kaimasa komai kamin ya wuce bangaren hajja dan bakaramar yunwa yakeji ba yana shiga yaga batool har tana kokarin kamo gashin Aminatu sunata wasa first time da murmushi ya subuce masa itama yarinyar sai tasaka dariya alamu sun nuna taganesa. A hankali Aminatu ta gaidasa tana masa sannu da zuwa sannan ta mike zata bashi guri. " Hajja wacece wannan za'abarta da batool har tana mata haka." Kallonsa tayi tana fadin " kai dai ba'a iyamaka to in banda ma Allah yasa sunzo ina ni ina wannan yarinyar mai kukan tsiya sam bata jin rarrashi  . A riqa lallabata dan Allah da kukan nan kar kanta yayi ciwo"  "   ai ina can ina tunanin nauyin batool da aka barmiki Kinga  itama Aunty Maimuna ta samu ta huta hajja." Hakan kuwa ka kyauta waccan diyar hajiya bilki ce." Da dan hanzari yace " Tazo? " " Ga diyarta nan kagani tafada tana murmushi nan kuma ta basa labarin bayan rabuwa." " Hajja wannan ya'rta ta goyen itace haka har ta girma." " Ita dai ce wacce nake kira uwata itace kaga tazama budurwa har an kare karatu shikuma yayanta yanacan harda iyali." " Allah sarki hajiya daman da Alkawarina kanta ai." Wallahi kamar ka shiga raina haka nace dan yanzu wani gidan haya tasamu take zaune ita da diyar tacemun wai dubu goma suke biya a wata." " Alhamdulillah ya Allah hajja karamun gidannan na baya da nasiya zan mallaka mata ko yakika gani?" " wallahi ban hanaka alkhairi ai Sadauki ubangiji yayi maka albarka yakara tsaremun kai." " Bari naje na huta hajja zanje da batool yafada." " Bakaji ba sadauki." Juyowa yayi yana dan murmushin yadda yarinyar ke shafa gemunsa tana wasa dashi. " Nidai sai naga kamar Allah yakawo maka matar aure har gida kaga yadda yarinyar nan ke kula da batool da zaku daidaita..." " Hajja duk wacce kikaga dama ki zabomin na baki dama kada ki damu da ra'ayi na dan bashinake abunda nakeso kan macce ba wallahi kowacce indai tanada tsoron Allah zan iya zama da'ita. " murmushi tayi cike da kaunar dan nata tace" inshaaAllah Aminatu sai tazama alkhairi gareka sadauki zaman danayi da'ita banga aibuntaba."



#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#HOT LOVE/ROMANTIC





*_