TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

10

by @nanadiso10



10..


Tunda yafito daga bandaƙi taga yadda gabaki daya idonsa ya canza daga launin fari zuwa ja haķan yakara sakata ciƙin tsoro da firgici sosai har jiƙinta na dan rawa. Duk da ya lura da haka sai ya dan tsaya na sakanni agabanta yace " zamu iya sallah kinada alwalah yafaɗa kamar bashine yayi maganar ba. Cikin inda inda tace " Eh tanada ta faɗa da ɗan rawar jiki." " Fine" yafada yana kallon ciƙin idonta dayaga tsantsan tsoro aciki haka kawai ya tsinci kansa cikin murmushi yana ɗan kara satar kallonta har tashiga toilet din. Mamakinta bai kareba sai dataga wani kawataccen jakuzi na wanka ga wasu irin abun kunna ruwa kusan minti daya tana tunanin ta inda zata taba sai ta kai hannunta nan take taga ruwan yafara zuwa cikin dan firgici tace " Ikon Allah" tana ƙankance idanu daman kawarta tataba gayamata da sukaje madina abun ruwansu da inji yake aiki sai gashi ita Allah ya mallaka mata shi acikin gidanta. Alhamdulillah tafada har cikin ranta kamin tashiga alwalah tafito ko data fito yana tsaye alamun waya yakeyi har takai bakin kofa yace " Kiduba cikin wardrobe akwai hijjab." Batare da tace komai ba tashiga kokarin budewa ganin tana kokarin janyewa yace " Wannan madannin zaki danna zata buɗe." Da dan mamaki ta danna sai taga ta zuge a hankali batasan ma tafaɗa ba tace " Allah mai iko." Yanajinta har tagama suka tayar da sallah ko da suka gama sai da yayi mata addu'a da tambayoyi wanda baiyi mamaki jin tanada sani kan ilimin addini.da kansa yaje kitchen ya dauko masu plate da cups da ya wanke .ya dawo dakin shiya xuba masu gasassar kazar da ya taho daita gamida tsiyaya masu fresh milk cikin glass cup.cikin murya mai cike da natsuwa yake faɗin.bisimillah da ɗan rawar murya take faɗin.ta koshi dan kakaf rayuwarta bata taɓa kebewa da namiji haka ba.kusanci su yana sakata jin wani iri ko cikakkiyyar natsuwa bata da shi.bana son musu."Ya faɗa da Muryar da ta sakata bin umurninsa batareda ta kasa yimasa wata gardamar ba.Yana kallon yadda take yagar kazar kamar bata so bai takura mata akan sai taci dayawaba.dan bai san kalar cikinta ba.ta riga shi cire hannunta sai da yagama tana kokarin haɗa kayan duk da bata ma san a ina ne hanyar kitchen din gidan ba.kiyi zamanki Bara naje na kai.da haka ya haɗa kayan ya nufi kofa.da kallo tabisa sai da ya fita nunfashin da take riqe dashi taji tana saukewa a hankali.bai dade ba ya dawo kai tsaye toilet ya nufa ya jima aciki kafin ya fito kai tsaye jallabiyyar jikinsa ya cire da sauri ta dauke kanta riga da wando na bacci ya saka ajikinsa.ya ɗan kalleta yana faɗin."ta shiga toilet tayi brush.cikin mutuwar jiki ta nufi toilet din.ta ɗan jima aciki kafin ta fito , kofa ta nufa tana faɗin." sai da safe ya dago ya zuba mata manyan idanunsu da yasata kusan shidewa yace " To where?" Ahankali heart dinta yafara bugawa sai tadago taganshi ya miƙo mata hannu kwance aƙan gadon abunda yabashi mamaki kasa karasowa tayi sai da yace mata " Oya come to your husband." Hakan yabata damar dan karasowa kusa dashi tana mai jin duk Nutsuwarta ta gushe yadda yajata ta faɗa jiƙinsa yana danna wani dan abu fitilun dakin suka dauke sai kuma taji jiƙinta yashiga rawa Amma ganin yadda nasa yake rawa yasanya hankalinta mugun tashi, Cikin yanayin da shi kansa bazai iya misaltawa ba yashiga bata saƙonnin da kowannen su yanzu ne nafarko gareshi tun tana basarwa har takai ta sakar masa kuka wanda ya sanyashi kara rikicewa bakaramin wahala yabata ba hakan yasa tadinga ajiyar zuciya tana kuka dan ita har ga Allah bata cikin irin matan nan masu karfin sha'awa dan har tunani takeyi ko batada lafiya saukar lausassar Leɓensa taji yana faɗin " Allah yayimiki albarka Aminatu kiyi fushi da rigima dani akan komai Amma banda wannan bazan iya jurar rashin kasancewar mu tare ba sai dai bana kasar ko idan Bakya a tsarki." Duk lafazansa tanajinsa Amma batace uffan ba. Ranar dai haka ya taimaka mata har ta gyara jikinta.


 Washegari tunda tatashi ta nufi bangarenta abunda yabata mamaki da hakan yadda taga ana fidda kayanta ana shigowa da sabbi sannan ga wata dattijuwa datashigo tana zubewa kasa haɗe da faɗin " barka da tashi hajiya daman nice hajja taturo zan riqa taimaka miki ga kayan girki nan inji hajja." Murmushi ne ya subuce mata dan wannan abun kamar mafarki take ganinsa nan kuma takalli dattijuwar tace baaba basai kin durkusa ba danAllah Nan ta nuna mata daƙin sannan tashiga tayi wanka sosai tayi kyau cikin shigar blue sannan ta zuba masa pepper chicken din da salad sai shinkafa ta hada masa da lemon zobon datagani ta nufi bangarensa ko dataje sallama tayi tashigo makeken palonsa waya yakeyi hakan yasashi sallama yana ajiyewa itama tatako har kan carpet din ta ajiye masa.cikin kunyar data kusa kasheta tace " Ina kwana abouy." Da dan mamaki ya kalleta abouy? Mahaifi kenan fa sai kuma yace " Ya karfin jikin naki?" " Naji sauki." Tafada tana zuba masa abinci kamin ta kai da zubawa yace " Ina son shayi sosai Amina yazaman kowanne lokaci ba'a rasashi agidannan." " Kayi hakuri bansaniba wallahi tafada tana kokarin mikewa." " zauna abinki nadai sanar miki ne sannan akwai babban dining tsakankanin part dinnan nacin abinci ne komai ana ajiyewa anan sai munaci." " Tohm inshaa Allahu." Sai kuma tayi shiru tanason tambayarsa taga ana fita da kayan dakinta Amma kuma takasa. Sai da yayi bismillah yafara cin abinci sannan yace " kinga ana fita da kayan dakinki ko? " a hankali ta zuba masa idanuwa." Badan na nuna gazawa ga ahalinki bane ba ko daya nayi hakan dan na nuna miki ke mallakina ce yanzu sannan bazan iya saka nawa kayan ba batare da kema nasaka miki irinsa ba wannan din da aka fitar sai kibawa wanda kikeso sannan nan da 2weeks zaki bi su hajja aikin hajja sai ki shirya anjima Aunty maimuna zatazo ta daukeki ayimiki passport." Muryarta har rawa takeyi tace " Amma hidimar batayi yawa ba Haka mama kabata gida sukutum kuma..." " Aminatu" yafada da dan zafi banason haka mahaifiyarki masoyiyar iyayena ce tun ina tsumma take dawainiya damu komai nayi mata wallahi ban biyata ba kuma ke mallakina ce yimiki abu babu shamaki abu daya ne banaso shine " kafiya da rashin bin abunda nakeso indai.kika bini zaki sameni yadda bakya tsammani." Cikin shashekar kuka tace " Allah yabiyaka mungode da karamcinka wallahi ko a mafarki banta...." " is okay please wipe your tears banaso." A hankali ta kalleshi wani sonsa yana shigarta shiyasa ake cewa kada kayi shaidar mutum har sai ka zauna dashi. " Wazaki bawa kayan Naki?" " Akaiwa mamata kaga itace.." " After her bakida wata?" Sai tayi shiru aranta tana ayyanawa ga uwata wa zan bawa? " Mama ansamata nata itama." Da dan hanzari ta kalleshi tace " To abawa kawuna yana can rimin auzunawa." " Shine wanda yarikeku? " " Eh shine ." Send me his address please. Daga nan bata kara magana ba har yagama cin abincin yace mata zai dan fita tayi masa adawo lafiya abun mamakin nata bai kareba sai bayan fitarsa da taga mamanta takirata." Mama ..." Aminatu mama tafashe da kuka " kinga ikon Allah aminatu abun bamu taba tunani ba kinga addu'ar uwa ko aminatu." Itama kukan tasaka aka rasa mai rarrashin wani nan aminatu tagayawa mata komai sai asannan mama tace mata ai harda ita da yayanta aka biyawa nan Mama tashiga yimata nasiha." Shifa arziki rabone Aminatu Allah ya kaddara ke zaki shiga gidan masu rufin asiri abunda nakeso dake shine guda daya ki zauna dasu lafiya duk da nasan bakida matsala wallahi Amma ki zauna da diyar nan tasa lafiya danAllah aminatu karki bamu kunya kiduba Allah da ma'aiki. " " Mama wallahi baku taba samun matsala daga gurina insha Allahu zanyi fiye da zatonku." " ubangiji Allah yayimuku albarka yabaku zaman lafiya ameen mama sai anjima. Sai data kimtsa masa bangaren nasa tsaf har toilet tasaka ko'ina acikin dakin akwai airfreshner ta fisa tafita sannan ta sauka baaba na kara gyara mata gurin makekiyar TV dinta ta kalla tana kara godewa Allah ta a tunanin tayaya zata biyashi.


 Da yamma Aunty maimuna tazo bayan yan uwanta da zasu koma jos suma sunzo sunata santin sabbin kayan nata suna mata addu'ar zanan lafiya ko da Aunty maimuna tazo sun dade a immigration offices kamain su dawo abunka da hanya da kudi aranar suka tawo da passport dinta tana dawowa agajiye tasamu tayi wanka ta shirya masa abincin kamar yadda yagayamata takara fesawa jikinta turare tana fatan yau bazai nemeta ba.


 Haba sadauki kwana daya da tarewa kakaimata yarinya wai hajja bazakiyi masa magana ba saboda Allah wacce amaryace zataso haka? A dan kausashe ya kalleta sai kuma yayi shiru. " Hajja sai da safe ya rungume batool akafadarsa yatafi. " DanAllah sadauki idan yarinyar nan taga bazata rike maka itaba kadawo daita ni nan zan riketa sadauki ina maka farincikin samun aminatu kada karasata dan wata karamar matsala." " Hajjata ki kwantar da hankalinki danAllah babu abunda zai faru kekuma Aunty Maimuna babu ruwanki da safgata." " Yayar taka kake yiwa kashedi." " To hajja shekara daya fa tabani menene marabarmu." " Ko awa daya nabaka ai na girmeka yaro sai kafiyar tsiya kaje ka kowa batool din kazo ka wahala wallahi." " Hajja kiyimata magana." " Au abunda kuka daɗe bakuyi ba shine zakuyi yanzu to ku daga min hankali kunji." " Allah yabaka hakuri " aunty maimuna tafada " " Kema kiyi hakuri sai da safe kuma Aminatun tace na kaimata batool din kin tsaya sai faɗa kikemun." " Tohm babu damuwa ayimata Allah yahuta gajiya." Murmushi hajja tayi dan tasan halin yaran nata sai dai ayi sa'in sa amma ko mintina basayi sai su shirya shiyasa take godewa Allah Akowanne lokaci. 


  Yana karasawa gida ya shigar da motarsa filin gidan kamin ya dauketa da jakarta ya nufi sashensa sallamarsa yasata miƙewa tana fadin " Abouy batool sannu dazuwa har naji dadi wallahi ai dazu kamar nace da Anty ta kaini nataho da'ita. " tasaka hannu tana daukarta. Har zai haura sama ransa fes yadda tayimasa sai kuma yadawo yashiga wani babban lungu dakuna ne kusan hudu ajere babban ciki yabude yana kallonta ga daƙin nata." " DanAllah kabarta muna kwana tare." " A'a yafada kai tsaye tana nufarsa zuwa dakin mamakin kawatuwar dakin tayi yaji kayan ado ga gado babba dakarami sai da ya karbeta yayi mata addua sannan ya shimfiɗeta yashe fitilar." Da dan rauni takalleshi tace " idan tatashi fa?" " Akwai alama aciki zaki gani." " DanAllah kayi hakuri to ko baaba tazo su kwana tare...DanAllah takara maimaitawa." " A'a yace yana hayewa sama tana kara yimata addua ta rufe dakin da bismillah wato komai na masu kudi daban ne ita dakin data tashi su 9 ne yaran gidan suke kwana kuma dakin ko corridor dinnan bai kaiba jin gyaran muryarsa yasata binsa tana taimaka masa kamin takai da cire rigar yashiga bata wasu zafaffan kisses....




#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#HOT LOVE/ROMANTIC