TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

11

by @nanadiso10

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)



DAGA ALKALUMMAN YAN TAGWAYE BIYAR


Arewabook@Nana diso10

NA

NANA DISO

&

ASMY B ALIYU



11....

Hajiya Amina wacce suke kira mami,ta kalli Ayshaa Sadauki wacce ta fito da car key a hannunta ta qaraso cikin dinning area taja kujera kusa ga maminta ta gaisheta da respect kafin ta shiga kwalawa mai aikinsu kira.me kuma zatayi maki aiki fa take yimun a kitchen a ɗan shagwabe Aysha Sadauki ke faɗin."Mami sarving dina zatayi."ta faɗa cike da gata da sangarta da alamar gata har yayi masu yawa.shiru Mami tayi bata qara faɗin komai ba.Aysha sadauki na break fast sai ga batool Sadauki ta fito itama cikin shigar alfarma da dan yololon mayafinta dake kan kafada

dinkin fitted gown ce ajikinta wacce tabi jikinta ta zauna haka ta fito da shape din jikinta sosai.good morning Mami!"ta faɗa tana qarasowa gaban mahaifiyar tasu da kulawa take tambayar ta tashi lafiya."Alhmdullahi Mami,Batool Sadauki ta qarasa kan hadaddun warmers din tana buɗesu ɗaya bayan ɗaya , ɗan haɗe rai tayi dan bata ga kalar cimarta ba aciki

gashi tana da lecture qarfe goma yaushe ta samu abunda taci ta fita.

"Mami duk wayayi wannan abubuwan kuma ansa bana so.!"Meya hanaki tashi ki shiga kitchen kiyi irin cimar da kikeso ,Daria Aysha Sadauki tayi tana kallon yayar tata take faɗin."kiyi hakuri kawai yaya Batool

Ki zauna ki tsakura hakanan.!"harara Batool din tabi Ayshan dashi ,ta ciro Wayarta qirar iphone cikin qaramar bag dinta ta shiga kiran Abhuun su.tasan zuwa wannan lokacin yana ɓangaren Auntyn su watau matarsa ta biyu kenan addu'a take Allah yasa abhuun nasu baiyi break fast ba sai ta samesa Acan suyi tare.tana fara ring ya dauka tareda yin sallama a natse cikin muryarsa mai dauke da wani irin sanyi da kamala sallama tayi masa

Tana gaishesa da wani irin respect wanda take baiwa mahaifin nata tamkar tana tsaye agabansa.bayan sun gama gaisawa ya tambayi lafiarsu ta ɗora da faɗin."bata yi break fast ba

Yau Mami tayi cimar da bata so.ta qarasa maganar cike da zallar Shagwaba.kizo bangaren Auntynku sai muyi tare Nima yanzu zan yi.owk Abhuu shukraan!"ta faɗa tana sauke wayar,da ido Ayshaa Sadauki ta riqa binta.tana jin wani abu na tsaya mata arai,kasa daurewa tayi.da gaske yah Batool bangaren wannan matar zakije kici Abunda ta girka."rolling din manyyan eyes dinta tayi akan kanwartata ,tasani bata kaunar matar mahaifinsu idan akwai abunda take kishi take rashin so aduniya bai wuce Aunty Maryam ba,Amman tunda da abhunta zataci bata da matsala daita.

Ta qalli Aysha Sadauki tana faɗin."me zai hana tare da Abhuu zanyi.kanta zan zauna ne?"ko daga gidansu ta kawo abinci ,Batool ta kalli Mami wacce tamkar bata cikin dinning area din suke maganar tace Mami daga can zan wuce school sai 6 zan dawo."addu'a mamin tayi mata kai tasa ta fice daga wurin cike da takaici Ayshaa Sadauki ta riqa bin yayar tata da kallo har ta bacewa ganinta da gaske yaya Batool bata kishin mahaifiyarsu tana mamakin kalar zuciyarta watarana.idan zakici abinci ki buɗe baki kici lokaci yana tafia idan baso kike kiyi latti ba."Mami ta faɗa tana kallon Ayshaa Sadauki wacce tayi kicin-kicin da rai Gabaki ɗaya Batool Sadauki ta bata mata mood.



Da sallama ta shiga cikin babban parlorn da yaji kayan alatu,sanin Abhuun ta na cikin parlorn yasa tayi sallama haka ta shige da talkaminta dake sanye a kafarta hill babu kowa cikin parlorn sai qarar Ac dake aiki da ya haɗe da sanyi room freshener mai dadin gaske kai tsaye part din mahaifinta ta nufa.nan ma wani babban parlorn ne wanda yafi na farkon haduwa da tsaruwa.


Daidai lokacin da Sadauki ya fito cikin master bedroom dinsa cikin shirin fita yayinda Maryam ke riqe da brifecase dinsa.


turus Maryam din ta tsaya tana bin Batool da mamaki.dan bata Tareda Sadauki lokacin da sukayi waya.


da murmushi acikin fuskar Batool ta qara gaisheda mahaifinta ya amsa da respect ya riqo hannunta yana faɗin."muje kiyi break fast karkiyi late.anan suka juya suka nufi dinning room din dake cikin parlorn sa.tsayawa Maryam din tayi da shegen mamaki banda tafasa babu abunda zuciyarta keyi.ta rasa meyasa yarinyyar nan har tafi uwarta shige mata a hanci ta rasa meyasa take kishin yarinyyar nan sosai wanda bata taɓa jin irin haka a wurin mahaifiyarsu ba.ta rasa meyesa duk cikin ya'yan Sadauki tafi tsanar Batool

Ta ɗora haka a matsayin kaunar da yake nunawa Batool din fiye da sauran harta dasu matan nasa kafin yayi masu abu sau ɗaya yayiwa Batool sau goma.ta rasa wace irin kaunace Sadauki ke nunawa Batool Sadauki har haka.da baya nunawa sauran ya'yansa haka.


Ta taɓa tsaresa da wannan tambayar akan meyasa yake banbanta ya'yansa akan Batool Sadauki ?"meyasa yafi kaunar ta fiye da kowa a gidan ko ita dake da yaro namiji baya masa irin wannan son da yake yiwa Batool sadauki.a ranar taga Masifa da tashin hankali a wurin SADAUKI masifar da taso ta datse igiyar aurenta.ta shiga shock da tashin hankali shiyasa tun daga ranar ta kara tsanar Batool fiye da kowa da komai a duniya.


Acikin plate ɗaya tayi break fast ita da Abhuun ta cikin nishadi da walwala wani yayi kurmushi wani ya girgiza kai Kurum saboda shi ba mutum bane wanda ya fiye magana.qarshe dai Maryam bar masu wurin tayi tana tsinewa Batool kwando -kwando ran Batool fess.dan tana kula da fuskar Aunty Maryam ,din daman kuma haka takeso bata so taganta cikin farin ciki ko kankani .matar ta iya ɗagawa mutane shoulder lokacin aurenta da Abhuu ba kalar wulakancinda mahaifiyarsu bata fuskanta ba akan Maryam.


Sunyi kuka sunyi bakin ciki sunyi roqon mahaifinsu akan mai mahaifiyarsu ta rage shi dashi da zai yi mata irin wannan sakayyar?"babu abunda ya canja har rashin lafiya Batool tayi akan auren da Abhuun yayi.


Har mota ta rakasa drivern sa ya karbi brifecase dinsa,da kanta ta budewa mahaifin nata kofar baya.ya shiga da murmushi a fuskarta da wata irin kauna wacce take yiwa mahaifinta tayi masa addu'a kamar yadda ta saba.ya kalleta cike da kulawa yake faɗin "tayi Tuki a hankali banda tukin ganganci daga kai tayi alamar bin umurninsa.


Sai da ta tabbatar da motar mahaifinsu ta fita get din gidansu ta nufi Tata motar cike da nishadi.duk abunda ke faruwa Maryam,na kallonta ta window dakinta dake sama,har bangaren kishiyarta Amina Batool ta raka mahaifinsu kuma sun dauki lokaci mai tsayi kafin su fito ya nufi motarsa...cike da tafarfasar zuciya tabar  bakin window.komawa tayi kan bed idonta sun kada sunyi ja xuciyarta banda tafasa babu abunda take,me zatayi wanda zata shiga Rayuwar Batool Sadauki ta tarwatsata me zata yi ta saka Sadauki ya tsani Batool ta tsani wannan yarinyyar

Bata taɓa tsanar wani mahalluki ba a duniya kamar yadda ta tsani Batool Sadauki.


Kwance take a hostel dakin kawayenta,billy ta kalli Batool da hankalinta duka yana kan chart din da take ,ta ɗan yi gyaran murya haka yasa Batool din maida hankalinta kan Billy.

"Wai da gaske Bazakije birthday party din JB ba kin dai san bazaiji ddi ba wallahi Batool duk yadda yake girmama ki yake shiga lamurranki."


Abhuu yana gari Billy taya za'ayi naje wani birthday na faɗa masa tuntuni ya hakura ya bari sai wata shekarar

Kin san duk wannan zuwan partyn da nake idan Abhuu baya kasar ne nake zuwa.to wannan karon yana nan basai a hakura ba,bana son na fara abunda zai sa mu samu matsala da Abhuu har yazo ya daina yadda Dani.


"Duk da haka ke ba yarinyya bace Batool shekarun ki ishirin da ɗaya aduniya ke kin san hanyoyin da zakibi ki kare kanki mana sai kace ba wayayyiyah ba ke duk haɗuwarki dadina dake bakida wayau.ko hostel zaki iya cewa Acan zaki kwana saboda kina son kiyi karatu akwai test din da zakuyi.course din yana baki wahala kara ki tsaya a hostel kiyi karatu."kuma fa Mami bata da matsala nasàni rayuwar gidanku babu takura rayuwar Turai kuke

Ban san meyasa kike shakkar Abhuu ba banci yana sake maku."


Ita dai Batool jin Billy kawai take bawai bata da hanyar da zataje party JB bane kawai dai bata da ra'ayi ,Dariya Fadeela tayi tana faɗin."Amman fa Billy kin kawo shawara ,ta kalli Batool tana faɗin."Ya kamata dai kiyi shawara besty idan babu ke a wurin bazai yi ddi ba.nasan kuma su Zeenah sun samu abunda suke so.!"


Tayi haukarta ta gama ko kwaya nake sha Bazan yi dating da JB ba ita kawai fa ke haukarta.zanyi tunanin maganarku,kusan wani sati ne birthday din nasa zan san yadda nayi.ihun murna sukayi suna yiwa Batool kirarin da suka saba.sai juya ido take cike da jin dadi da alfahari....


Kamar yadda tace 6 nayi ta baro school kai tsaye gida ta nufa , bangarenta ta wuce direct dan agajiye take tana bukatar yin wanka ta huta.ba ita ta fito daga dakinta ba sai da tayi sallar ishaai daman rayuwar yanci suke a gidansu .babu wanda ke takurawa wani baran tana a neme ka.

Mahaifinsu ya gama cika rayuwarsu da gata ta koina.



#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#Hot Love/Romance