TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

12

by @nanadiso10

*TSARIN ALLAH*

(_Bamai Iya Canzawa_)



DAGA ALKALUMMAN YAN TAGWAYE BIYAR


Arewabook@Nana diso 10

NA

ASMY B ALIYU

&

NANA DISO


12

Sanye take cikin kananan kaya masu laushi da sukayi luff ajikinta wayanta dake kunnenta tashiga amsa kiran tana faɗin " No Billy I want the blue gown." Sannan ta katse wayar tana mai kara kallon hanyar bangaren da zata Nufa wanda yazamana bangarene da matan gidan ke zama idan mai gidan nasu yana gari yau girkin mami ne tasan dole tana can dan haka kanta tsaye tayi sallama a kayataccen palour din dake dauke da white kujeru tasaka kai tashiga Tun daga Nesa tafara " Mamina" tana karasawa kusa da inda take zaune. Wani mugun tsaki Aunty Maryam tayi tana mai dalla mata harara cike da bakin cikin batool, din gata da manyan jiki Amma ko kunyar kowa bataji haka take saka riga da wando tana yawo acikin gida subuti subuti. Karamin hug batool tayiwa mami tana faɗin " I miss u Mamina." Dan dariya Hajiya Amina tayi cike da kaunar diyar tata tace " Ku dai bakwa girma da shiririta ya makarantar tun dazu naji shiru Har ina Aysha tazo taga ko lafiya." a takaice batool tace " Nagaji ne Mamina shiyasa nazauna na huta." To sai kitashi ki nemi abinci gashinan angama a kan dinning." Narai -Narai tayi da manyan idanuwanta kamin tace " Abhuu fa? " takaici ne ya sanya Aunty maryam jan tsaki tana cigaba da danna waya. To banda abinki ko yace miki zaiyi tafiya ne zaki saka mun kuka." A hankali ta juya idanunta tana faɗin " To Ni sai yadawo zamuci bari naje Nayi sallah." " Okay kawai mami tace tana kallon batool din har ta danyi nisa sai tace " Batool baki gaida Auntynku ba kina ganinta azaune ko yunwar ce?" Batare data juyo ba tace " Sannu da gida tayi wucewarta." Wani mugun tsaki da takaicin yarinyar aunty maryam tayi tashiga faɗin " Ko bakisaka taba bana bukatar gaisuwar lalatattun yaranki marasa kunya da mutunci gidan ubansu ne babu wacce ta'isa ta fiddani ko ita wannan da yar goal din tasa bata isa ba ballantana ke." Farrah ce ta tako cikin shigar fitted gown datayi mugun kamata duk taji abunda aunty maryam tace dan haka bata kulata ba tayi wucewarta tana tauna chewgum dan tasan zata iya yimata sharri gurin Abhuu dama ace yar madara ce batool baya sauraran kowa akanta. Tun daga Nesa suka jiyo hayaniyar batool tana faɗin " ai idan zakiyi maganganunki sai kiyi damu bada mahaifiyar mu ba idan bamu fidda ke ba ai bamu muka shigo dake ba kidaina sakawa uwarmu damuwa nagayamiki wallahi wallahi zanrufe ido..." " A'a batool ku shige banason fitsara." Cikin Narai Narai da idanuwa tace " Please mami." Sai ta saka kuka da batasan dalilin zuwansa ba." Aunty maryam ce tayi murmushi tace " Ai da kin barsu sai naga ko dukana zasuyi inga tsiya marasa tarbiya, gida kuma zama daram acikin sa ." Juya ido tayi .gamida nufar part Dinsu bata dauki matar nan mai cikakken hankali ba " Nagayamiki maryam babu ruwanki da ya'yana Amma kina ganin kamar lamarin da wasa ko? Idan ba gidan ubansu sukayi walwala da farin ciki ba a ina akeso suje suyi? kinsan mahaifinsu yazo yayita fushi babu gaira ba dalili bayan yayimiki tsakani da yaransa."nifa ba tsoronki yasanya kikaga ban biyemiki muyi fitina ba.wani kallo Aunty Maryam din tayiwa mami,gamida barin wurin zuciyarta na tafasa.




Wanka tayi da ruwa masu dumi kasancewar garin akwai ɗan sanyi.sai da ta ɗauro Alwallah.ana tada kiran sallar magarib ta saka kayan sallarta ta tada sallah.tana nan zaune akan sallaya,taji qarar shigowar saqo a Wayarta

numbar datayi saving sunansa dashi tagani Saleem " Dan Allah kifito baby yanzu mu hadu dan Allah kinji gobe zan bar kasar kizo hotel suit mu hadu kitaimaka min batool." Tasan mugun nacin saleem ,bazai daina yimata naci ba har sai sun haɗu din kamar yadda yace. Kayanta ta canja ta dauki key din motarta bata damu da yanayin shigar dake jikinta ba taja karamin veil ta dauki karamar jakarta ta wuce, a hankali tashiga bangaren mami tace " Mami zan dan karbo sako please." " batool fushi kike dani haka? Mami tafada tana karantar yadda fara'ar fuskarta ta ragu." " Naga yamuku kudaina biye mata tunda ita babu abunda tasani sai fitina." " Ni mami bana fushi dake kawai zanje nasha iska ne ." To karki dade ko kinga Abhuu yana tafe karyazo yayita fada baki dawo ba." " Thank you mamy." Aysha dake gefen mamy tace " Ko nazo nayi rakiya ne? " " No need sis yanzu zandawo." Okay tace batare da damuwa ba. Mai aikinsu hajiya ladi dake karasa jera kayayyakin a palour ne ta kalli uwar dakin nata tace " Nidai kada nayi laifi mami,Amma shigar batool bai kamaceta ba kinga idan alhaji yana nan naga basa shigar nan sai bayanan sufa yaranmu amanar mu ne." " Me shigarta tayi ladidi? Shikenan kuma yarana basuda freedom sai ace komai ba daidai suke ba " Allah yabaki hakuri mami" Ladi tafada tana barin gurin cike da mamakin irin tarbiyar uwar dakin tata ga sani amma tana take sanin nata.


A hankali take tuki tana sauraron wakar da take mutukar so ta Ayra star har takarasa gaban baban hotel din da yagaji da haduwa a hankali taja burki tana kallon wanda yake gabanta haɗe da faɗin baka ganini ba malam." Babban mutumin dake cikin manyan kaya ne ya kalleta batare da yamayar mata da martani ba. Itama samun guri tayi hade da parking tayiwa motar key alamun rufewa sannan tayi hanyar shiga hotel din." A dan zabure babban mutumin yakalli abokinsa dake kusa dashi yace usama kaga wata sabon kamu." Murmushi usama yayi dan yasan batool sosai yace " Kai wannan kifin bazai kamu ba Alhaji tahir diyar SADAUKI CE." Dan gyara zama yayi yace " Ko diyar wanene sannan ya dauki wayarsa yayi snapping bayanta tana shiga entrance na hotel din " kai abokina ji kaya iya kaya yarinya full option kacemun wai kifin bazai kamu ba ubanta tazoyi anan?" " bi Ahankali abokina wallahi wannan kifin bazai kamu ba ina gayamaka bata harka yarinyar nan munsha gwadata fa amma ina abun ba'a cewa komai." " Baku iya kamun baneba amma ni zakuga yadda zanyi nawa." " Ina gayamaka kadama ka wahala dan kila wajen kawarta tazo kokuma sako zata karba amma duk wannan shigar dakagani wallahi bata harka." Tsaki alhaji tahir yaja yana kallon hanyar databi. Knocking din data farane yasaka saleem budewa yana sauke mata manyan idanuwan da suka cika da jaraba yarasa yadda zaiyi da kaunar batool gashi shi ayanzu babu aure acikin tsarinsa Yakasa ma fahimta kaunarta yakeyi kokuma sha'awarta yakeyi? " Are you okay" itace daddadar muryar dataja hankalinsa har yana sauke wani sanyayayyan ajiyen zuciya sannan yabi shigarta da kallo." Baby you look so much beautiful wallahi kamar nasaceki." Siririn murmushi taja tana kama hannunsa suka shige daƙin hade da bata ranta tace " How many time zance kadaina shan sigari saleem? Kasanfa kanada matsala acikinka? Why?." Kallonta yatsaya yi zuciyarsa tana kokarin kasa aiki cikin kalaman da bai taba tsammanin zai fita abakinsa ba yace " will you marry me batool." Bakaramin shock da bazata kalmar tasa tazo mata ba, zuzzuba masa ido tayi alamun mamaki ya kara riko hannunta yace " yes i mean it please baby kinsan inasonki ina kaunarki.." ' Tabbas ko bai fada ba zatace bata taba wani saurayi kamar saleem ba duk da babansa yana daga cikin kusoshin gwamnati dan mahaifinsa shine mataimakin shugaban kasa ayanzu, tasan saleem da yammata but yadda yake treating dinta har tsoro abun yake bata shi bakamar sauran samarin nata baneba da kowannen su sunada manufa ta zuwa gurinta akallah tayi morethan 5 boyfriend wanda zasuzo da niyar aure but suyi ending suna yaudararta wasu jikinta wasu kuma kawai su gudu deep down tana mugun son aure sai dai ganin Rashin dacen masoyi na kwarai yasanyata watsar da komai ta fuskanci karatunta ranar da sukaje dubai itada abhuu da aysha da aunty maryam sunje garin abu dhabi anan ne suka hadu da saleem yazame mata kamar chewgum dan sosai shakuwa tashiga tsakaninsu har takai Abhuu yasanshi shima dad dinsa yasanta. " Bakice komai ba baby " ta tsinkayi muryarsa yana magana." " Sai nayi tunani." " So kikeyi na haukace akanki yafada idonsa na kawo ruwa." Cikin dan mamaki take kallonsa...!"




#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#Hot love/Romance