NIKAAH (Marriage for rent)

Rental marriage 3

by @hanaady



*NIKAAH* 

    *Marriage for Rent* 


           *By* 

       *HANAADY* 

    Rahama Aminu Bala 




 *WhatsApp* 

 ***** 


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?



Marubuciyar

BAHAAR paid book

And now NIKAAH(Rental Marriage).......

Free book


 *Page 3* 



___Karime bata dawo part nasu ba sai bayan sallar la'asar koda ta shugo zaune ta tarar dashi falo , wucewa bedroom tayi abunta ba tareda tayi masa magana ba. 

Toilet ta shiga domin watsawa ruwa baki sake tabi pants da bra d'inta cikin ruwa.

Fuu ta fita zuwa falo , 



 idanuwan sa a lumshe shuke yana sauraren karatun Qur'ani mai girma.


Tsaye tayi saman kansa ,hannuwanta saman 'kogunta masifa na cinta tace ya naga kayana a cikin ruwa ??

Jin hayaniyar ta saman kansa yasa , a hankali ya bud'e idanuwan sa ,ji tayi gabanta yayi mugun faduwa ,janye idanuwan ta tayi daga kallonsa .


Tashar da yake kallo ya canza zuwa wata tashar sannan murya k'asa k'asa yace bakya ganin karatun Qur'ani ake amma ,kike ta d'aga murya kaman kinje kasuwa.

Banza tayi dashi 

Ganin yanda tayi banza dashi yasa ya Mi'ke tsaye,yana mai tattara wayarsa da keys d'insa .

Bedroom ya shige abunsa , da ido ta bisa  harya 'bace mata da gani ,zama tayi saman kujerar tareda d'aukar remote ,canza tashar ma Hjy Karime ba iyawa tayi ba ,gashi kuma tana son yin kallo.


Bedroom d'in ta shiga ,zaune ta tarar dashi yana latsa system, d'an nesa dashi ta tsaya sannan tace,nace dan Allah ko zaka d'an canza mun tasha ,banza yayi da ita d'an satar kallon sa tayi sannan tace dan Allah ka taimaka mun .


Daina latsa system d'in yayi ,murya k'asa k'asa yace a wane 'kauye aka auro ki , bata ji meya fad'a ba sosai iya auroki taji sabida haka washe baki tayi sannan tace kasan Jangefe , d'an ta'be baki yayi sannan yace aaa.

Kyara tsayuwa tayi sannan tace garinmu na can wajen Poly Katsina , murmushi tayi sannan tace yanzu garinmu ya kusa had'ewa da cikin garin Katsina .


Jin yayi shuru yasa ta mayarda kallon ta saman fuskar sa , had'a idanuwa sukayi saurin janye idanuwan ta tayi .


Mi'kewa yayi tareda ficewa zuwa falon , remote control d'in ya d'auka ,wane channel ya fad'a k'asa k'asa, canza na gani sai in za'ba ta fad'a tana mai kwurama 'katuwar tv d'in ido.


Canza channel d'in ya fara , yana kai wata tasha wasu turawa ne mace da namiji keta sumbatar juna saurin canza tashar yayi ita kuwa Karime saurin janye idanuwan ta tayi daga kallon wurin ganin yanda yake ta canza channel ta'ki za'ba yasa a kai mata Zee Cinema kasancewar Star time ce ,juyawa yayi ya fara tafiya , nagode ta furta bai ansa mata ba illa bedroom d'in sa daya shige bedroom.


Zaune take ta kurama tv d'in ido ,wata matashiya ce ta shugo falon da sallama ,cikin ladabi tace ma Karime Hjy tace nazo na tafi dake sashenta ,cikin mamaki Karime tace wacece Hjy , cikin mutuntawa tace itace mahaifiyar mijinki ,jin abunda tace yasa Karime mi'kewa , bedroom d'in ta shiga zaune ta tarar dashi yana karanta wani littafi na addini , d'an matsowa tayi kusa dashi tazarar su ba wani mai yawa bace remote control ta mi'ka masa da kallo ya bita , murmushi tayi sannan tace dan Allah ka tsayar mun da tashar da ka kai mun naje na dawo ana kirana kuma kallon ya fara mun dadi'.


Ganin bai anshi remote d'in ba yasa ta d'aura shi saman gado ,cikin sauri ta figi hijab d'inta tareda ficewa ,da kallon tausayi ya bita domin yasan wula'kanci , tozarci da cinmutunci suna can suna jiranta.

Haka Momynsa tayi wa Sa'adatun sa washe garin kawota gidan, tasa aka kira ta ita da Hjy Mariya suka tozarta masa ita wanda lokacin da hakan ta faru baya da masaniya ,abunda zai iya tunawa shine bayan dawowar Sa'adatu daga part d'in Momy zaune ta tarar dashi saman gado bata yadda sun had'a ido ba ta shige toilet acan ta sasha kuka kaman ba gobe.

Ta dad'e sosai cikin toilet d'in sannan ta fito Koda ya tambaye ta akan yaya ga idanuwan ta sunyi ja ce masa tayi wai ruwane data sakarwa kanta shine ya shiga idanuwan ta ,sai bayan rasuwar Sa'adatu sannan ya samu labrin irin u'kubar da Sa'adatu tasha wajen Momy, ba komai bane yasa take tsanar Sa'adatu sai rashin auren d'iyar kawar ta da beyi ba.


Ajiyar zuciya ya sauke domin ji yayi yana tausayin Karime, yasan ba k'aramin wula'kanci zasu yi mata ba .

Ya fahimci yarinyar bata san komai ba , babu abunda ta iya inba kauyenci da masifa ba , remote d'in data ajiye ya kalla wai ya tsaida mata kallo , tsaki yayi kad'an ,kodai shine yake wannan tunanin maybe ita Karime Momy ta sota tunda a iya saninsa ance Momy ce tayi jagorancin auren su. 


A can d'akin Momy kuwa koda suka shiga ,da kallon raini tareda wula'kanci suka bita ,zama tayi saman kujera ,cikin tsawa Momy tace ubanwa ya baki izinin zama ,cikin mamaki Karime ta kalle ta da niyyar maida mata magana ,but ganin yanda suke tsananin kama da Ramadan yasa ta gane mahaifiyar sa ce ,mi'kewa tsaye tayi tareda sadda kanta k'asa , murmushi Hjy Mariya tayi wacce ke zaune kusada Hjy Sadiya.


Ashe kema kaman ubanki kike d'agowa tayi tana kallon Momy , kalleni da kyau Momy ta fad'a har kin isa ki kai k'arana wajen Dada wai ba'a maki lefe ba ,ina tsumma kayan da kike sakawa agidan matsiyacin ubanki ,duk da Baban Jimmai ba wani kyautata musu yake ba amma taji haushin maganar koba komai ba uba ubane , hawaye ta fara .


Wai kuka kike Hjy Mariya tace ,ki adana hawayen nan domin za suyi miki amfani randa kika yi kuskuren yaudarar mu .

Kaman yanda Hjy Mariya ta fad'a miki auren ku na d'an lokacine ,Aliya na dawowa zaki nemi saki wajen Ramadan cewar Hjy Sadiya.


Bayan haka daga yau kina cikin masu yi mana hidima , a kowace rana duk lokacin da Ramadan ya tafi wajen aiki ,ki tabbatar da kinzo part d'ina domin aikatau .


Maganar kayan lefe kuma tunda kin kai kara ta zan siyo su amma koda wasa ba zaki saka su ba .

Magana ta karshe itace a ina jiya kika kwana ??

D'agowa Karime tayi tana mai zubar hawaye tace a uwar d'akin sa ,.

Da mamaki Hjy Mariya tace Hjy Sadiya ya akai haka ta faru??


Ki kwantar da hankalin ki waccen tsohuwar ta gindaya mana sharudd'a a dole d'aki d'aya zasu yi amfani dashi .


Kina ganin ba matsala Hjy Mariya ta fad'a cikin b'acin rai.

Kada ki damu Hjy nina haifi Ramadan nasan wannan kucakar babu abunda za yayi da ita ,Wanda yake begen mutuwar matarsa ina zaya kula da wannan ba'kauyar .


Sosai suka ci mata mutunci harda cewa ubanta hayar ta ya bada sabida tsananin talauci da kuma shegen son kud'i.


Kwance take cikin d'akin ta dake part d'in Momy hayaniyar su ta tada ta ,duk irin cinzarafin da su kayi ma Karime taji komai duk da akwai yarinta tattare da ita hakan bai hana ta gane inda suka dosa ba kasancewar ta yarinya mai mugun wayau ,yawan zama da Dada ba k'aramin taimaka mata yayi ba .


Jin yadda Karime ke kuka yasa Sa'ada fashewa da kuka , komawa tayi saman gadon ta dan bata son su gane taji me suke shiryawa.


Koda ta shugo d'akin zaune ta tarar dashi ,saurin shigewa toilet tayi ,sosai take kuka .

Da kallo ya bita duk bai ga fuskar taba ya nada ya'kinin kuka take , ajiyar zuciya yayi ya kasa gane dalilin da yasa Momy ke ta kurama duk macen da ta ta'be shi .


Yana zaune Little ta shugo jikinsa ta fad'a tareda fashewa da kuka ,cikin tashin hankali yace lafiya Sa'ada ??

Me kike wa kuka haka .

Kwashe duk abunda taji tayi ta fad'a masa .

Rungume ta yayi cikin lallashi yace Momynki baza ta zama yar aikin part d'in Momy ba ki daina kuka kinji my Little Sa'ada.

 Share hawayen ta tayi sannan tace Momy tace ma Momyna banza ba'kauya ,kuma tace mata hayarta aka basu wai Anty Aliya na dawowa zata tafi.


Shuru yayi yana mai nazari akan maganar Little Sa'ada,sai yanzu ya gane ,ashe dai Momy tana kan bakanta akan auren sa da Aliya,shiyasa taje tayo renting wannan yarinyar na dan lokacin..

He is confused sabida haka dole ya tambayi yarinyar tayi masa bayani ..



Saida tasha kukan ta kafin ta fito zaune ta tarar dashi ga Little Sa'ada kwance tana bacci ,dan nesa da shi ta tsaya sannan tace , Mahaifina ,kasa ida maganar tayi kuka yaci k'arfin ta ,dukawa tayi k'asa tareda fashewa da kuka.

Shuru yayi yana mai sauraren yanda take kuka , treat her nice maganar Sa'adatun sa ya tuna , mi'kewa yayi tareda zuwa wurin ta , d'ago da ita tsaye yayi , kukan ta karuwa yayi a hankali ya fara share mata hawayen fuskar ta cikin yanayin kuka tace Mahaifina shine ya haddasa mun duk wani tozarci da wula'kanci..


K'ara fashewa tayi da kuka mai cin rai.

A hankali ya rungumo ta jikinsa kuka take sosai ,shafa bayan ta yake alamun lallashi .

Ganin yanda ya saka ta jikinsa yasa tayi saurin janyewa , d'an ja baya yayi ,kamo hannun ta yayi zuwa bakin gadon su zaunar da ita yayi,cikin hikima yake tambayar ta akan yanda aurensu ya kasance 


Bata fad'a masa komai ba domin tuni su Hjy sun bige mata warning akan kada ta fad'a masa shida Dada .


Duk yanda yaso ta fad'a masa ta'ki .

Shi kuma baya son tarar Momy da maganar.

Ganin lokacin makarantar islamiyya yayi yasa ya Mi'ke , d'aukar Sa'ada yayi ,ganin zai fita yasa itama mi'kewa da mamaki yace ina zaki ,part d'in Dada ta bashi ansa ataikaice,giftawa tayi ta gabansa ,tafiya take yana binta a baya d'auke da little Sa'ada.


Kwantar da Sa'ada yayi saman kujerar Dada ,cikin fara'a Dada tace lokacin makaranta yayi koh??

Da kai ya bata ansa tareda ficewa , kallon Karime tayi sannan tace mijinki akwai shi da hidimawa addini yanzu haka makarantar islamiyya zashi ya koya , a ina ake islamiyyar Karime tace tambaya, murmushi Dada tayi sannan tace a cikin gidan nan ne idan kina so zaki iya zuwa , wani tunani tayi tabbas tana bu'katar ilimi domin dama can kawar ta Aisha tana dashi bakin gwargwado.

Ita bata wani samu damar zuwa islamiyya ba kullun bata da aiki sai talla.

Dada ina so , dan Allah kiyi masa magana , murmushi Dadaa tayi sannan tace yanzu haka kina iya binsa keda mijinki .

Inane akeyi ta tambaya??

Idan kika fita ki Mi'ke tsaye kiyi ta tafiya zaki ga masallaci ta gate d'in gabas nan islamiyyar take .


Cikin sauri ta zura takalmin ta sai Islamiyyar Ramadan lol.


Mu had'u next page


 *Rahama Aminu Bala* *HANAADY*