Chapter 21
by @oumfatima33
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 21*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
**** "Ai ba ke kika ga masifa ba nina ganta Habibah, ace wai ni Malam da Hajjo zasu haɗa baki su munafunta? Ace ya fara neman aure ban sani ba sai da komai ya kammala ɗaurin aure kawai ya rage za'a faɗa min don an raina min hankali!" Mammah ta faɗa cikin ɓacin ran da aka san ko wace Mace kan nuna idan za'a yi mata kishiya.
"Ke za'a kawo ma kishiya, ni kuma Macen da na tsana fiye da komai a duniya, Wacce ta ƙwace min farin cikina, wacce ta tare min gaba ta hanani ci gaba tako wace fuska tun ƙuruciyarmu a komai itace a sama dani, a komai sai ta fini samun nasara itace a yanzu ma za'a kawo ta muyi rayuwa a gida ɗaya a cikin ahali ɗaya, dole a kira yarana da nata ƴan uwan jini wata ran abin da na tsana kenan, na tsani ko wace irin alaƙa ta haɗani zama da ita a inuwa ɗaya, kinga kenan ciwon da nake ji ya lullunka wanda ke kike ji!" Habiba ta ƙare maganar cikin ƙunar da zuciyarta ke mata harda ƙwallah ta tara a idonta tsabar sa kai a masifa.
***** Duk yanda Habiba da Hajiya Zulaiha suka tsanani wannan auren sai da aka ɗaura shi ba yanda zasu yi domin kuwa basu isa canza hukuncin Allah ba. Bayan sati ɗaya Harira ta tare a gidan Mijinta a part ɗin ta da aka ware mata taci gaba da karatunta a nan. Sosai Habiba ke nuna mata tsana har kowa dake cikin Familyn ya fahimta, domin kuwa bata iya ɓoye ƙiyayyar da take mata ko a gaban waye, Hajjo tayi iya ƙoƙarin ganin ta shirya tsakaninsu amma abin ya gagara dole ta haƙura ta ƙale ta. Sai ya zamana tamkar itace kishiyarta domin tafi Mammah kishi da ita, duk da itama tana matuƙar kishi da ita don ko yaranta bata bari su raɓeta.
Hakan bai damu Harira ba don ita yanzu rayuwar ma duka bata ɗauke ta a bakin komai ba tun da ta rasa Mijinta mai ƙaunarta komai na duniyar ya sure Mata.
Rayuwarta taci gaba dayi tana kuma ci gaba da zuwa Makarantarta tana kuma ƙoƙarin sauke nauyin aure da ya rataya a kanta da kuma kyautatawa surukarta shi yasa take ƙara sonta. Tunda tazo gidan Jabeer yana ƙarami amma haka Allah ya haɗa jininsu yake sonta itama tana ƙaunarsa don haka ta jashi a jiki take kyautata masa, Nabeel ma yana son zuwa wurinta amma Momynsa bata bari don har dukansa take yi duk sanda yaje.
Bata daɗe ba ciki ya bayyana a jikinta sosai tayi farin cikin hakan sabo da zata sake haifar wani ɗan. Lokacin da cikinta ya isa haihuwa ta haifi ɗanta da yazo ba rai, ta shiga damuwa amma dole ta haƙura ta ɗauki ƙaddara.
A cikin shekara uku da tayi a gidan Alƙali Bello ta haifi yara uku duk suna komawa, wanda hakan ba ƙaramin damuwa ya haifar mata ba, ga haibaicin Habiba dake faɗar muguntar dake cikin zuciyarta ne yasa Allah yake hukuntata. Bata kulataba duk in tana faɗar magan-ganunta.
Tana cikin wannan halin ne wani cikin ya sake bayyana a gareta wanda ta ƙwallafa rai a kansa, sai dai kullum cikin fargaba take. Haka taci gaba da rainon cikinta cikin fargaba har ya isa haihuwa, kusan tare suka haihu da Habiba. Harira ta fara haihuwa a wannan karin ta haifi ƴarta Mace kyakykyawar gaske saɓanin haihuwarta ta baya duka Maza take haihuwa, sosai tayi farin ciki da murnar samun ƙaruwar da tayi, haka masoyanta ma sun taya ta murna.
Zuwa lokacin ta gama karatunta ta ƙara samun wayewa da gogewa inda ta karɓi ragamar kulawa da dukiyarta da taimakon Mijinta da Yayansa Alhaji Babba kasuwancinta ke tafiya, domin kuwa shaguna aka buɗe mata a kasuwa ake sayar da suturu tun daga na Maza da Mata manya da ƙanana.
Hakan da Habiba ta gani sai da ta kusa haɗiyar zuciya tsabar bakin ciki, itama ta ƙara haihuwar ƴa Mace bayan shekara bakwai da ta kwashe bata ƙara haihuwa ba.
Tunda Harira ta haifi ƴarta da aka sakawa sunannan Hajjo wato Safiyya da ake kira Hanan, Jabeer ya tare a ɓangarenta yake kulawa da Hanan dako ƙuda baya son ya taba ta. Duk da kasancewarsa miskilin Yaro mara fara'a kuma yana da ƙanne Mata amma baya nuna musu soyayyar da yake yiwa Hanan. Haka suke shan rigima da Nabeel da yake zuwa ba tare da sanin Momynsa ba shima don ɗaukar Hanan da take da farin jini sosai a gurin yara da manya. Rigima suke sosai akan sai Jabeer ya bawa Nabeel ita shi kuma sai ya hana sa ya zauna yai ta kuka har sai Ammy ta lallaɓa Jabeer kafin ya yarda ya bashi, wanda suna fita daga sashen Ammy zai tare Nabeel ya masa dukan tsiya ya kuma masa kashedin ƙar ya kara zuwa yace ya bashi Babynshi.
Haka zai yi kukansa ya share ko Momy ba zai fadawa ba sabo da yasan in ta sani dukansa zata yi domin ko shiga sashen ta hana sa.
A hankali rayuwa taci gaba da shuɗewa abubawa suna sauyawa Hanan na ta girma da wayo, sai dai lalurar rashin lafiya da aka fuskanci tana fama da ita na Athma da tun yarinta aka gane tana fama da ita.
Ammy na matuƙar kiyaye abinda zai taso mata da ciwon domin kuwa tana shan wahala. Shekarar Hanan huɗu Jabeer ya tafi New York karatu bayan shaƙuwar da suka yi sosai da shi, shima a nasa ɓangaren haka ya tafi yana kewarta da sauran ƴan uwa.
Bayan tafiyar Jabeer ne Nabeel ya samu damar ɗaukar Hanan ba mai hana shi, musamman ma idan aka kaisu Makaranta duk da shi yana ɓangaren Secondary amma haka yake zarya wurinta. Tsananin kulawar da yake bata ne ya haifar da shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu har ta manta da Jabeer da take rigimar nemansa wasu lokutan.
Haka rayuwa taci gaba da shuɗewa suna ta girma suna ƙara wayo, a hankali Momy ta cusawa Aminatu aƙidar tsanar Ammy da Hanan da ta kasa samu a wurin Nabeel, duk sanda Aminatu ta gansu tare da Hanan ko a Makaranta ko gida sai ta faɗa wa Momynsu ta masa faɗa koma ta dake sa.
Lokacin da Hanan ta kammala primary school ne suka shirya tafiya Katsina da Ammy da Kakanninta Malam Musa da Salamatu domin su gano dangi. Ana ya gobe zasu tafi ciwon Hanan ya tashi sakamakon turata da Aminatu da Bilkisu ƴayarya ƴar wajen Mamma suka yi a babban kiching na tsakar gida suka rufe kuma an kunna wuta ga hayaƙi ba wanda yasan tana ciki har sai da ta suma sai da Nabeel ya neme ta bai ganta bane Asiya take faɗa masa taji su Aminatu na cewa sun ƙulleta a general kiching na ƴan aiki ya tafi da gudu ya buɗe ya ganta a sume ya ɗaukota aka yi Asibiti da ita.
A ranar sai da yayi musu dukan tsiya, shi kuma yasha zagi a wurin Momy. Wannan dalilin yasa dole aka fasa tafiyar da Ammy suka tafi akan zataje daga baya.
A hanyar su ta tafiya ne suka yi Accident Allah ya karɓi ransu sai Ade ce kawai ta tsira amma tasha matuƙar wahala kafin ta warke.
Sosai Harira da sauran dangi suka shiga tashin hankalin wannan rashi da aka yi, dama tuni Baban su Malam Musa ya a rasu sai Mahaifiyarsu kawai da ɗan uwansa Malam Sani sai gwagwa Zuwaira suka rage a can Zango yanzu kuma ga rasuwar Malam Musa da Matarsa.
Wannan rashin da Harira tayi bai sa Habiba tayi mata gaisuwa ba, sai da Mamansu tazo ta sanya ta gaba kafin, zuwa lokacin duk abinda Habiba zata yi ya daina bawa Harira mamaki, don haka bata damu ba ta kanta take yi.
Bayan komai ya lafa ita taci gaba da riƙe ƙanwarta har ta aurar da ita ga Mutumin kirki da ya fito mata.
Tsakanin Nabeel da Hanan tun shaƙuwarsu na a matsayin shaƙuwa kawai har ta juye zuwa zazzafar soyayyar da bata kama su da sauƙi ba. Lokacin da Habiba ta fahimci halin da Nabeel yake ciki akan ƴar Harira har kuka sai da tayi na baƙin cikin yanda ƙaddararta take liƙe da Harira ako da yaushe, don haka tasha alwashin ko sama da ƙasa zata haɗu baza ta bari Harira tayi nasara akanta ba a wannan karon.
A ɓangaren Jabeer kuwa tun da ya tafi bai dawo ba sai da ya ƙammala masters ɗin sa ya zaman ƙwararren likita da ya yi cosa cosai da dama a fannin likitanci. Lokacin da ya dawo da ɗokin ganin yanda zai ga Sofiyyahnsa ta koma ya dawo, sai dai lokacin da ya dawo ya tarda ta a matsayin mara jin magana da tsaurin idon da bata ragawa kowa, ya kuma samu zazzafar soyayya ta ƙullu tsakaninta da Nabeel wanda bata jin kunyar faɗar tana sonsa ko a gaban waye kuwa, bata ƙi ta zane yarinya akansa ba. Kuma da a lokacin ba wani uban girma ne tayi ba, duka bata fi shekara sha biyar ba don lokancin suna S. S. 1 ne.
Waɗan halaye da ɗabi'u na rashin jin magana da ya same ta dasu ne yasa waccan shaƙuwa da soyayyar da sukewa juna tun bata da wayau ta canza. Domin kuwa hukuntata yake matuƙar tayi ba dai-dai ba, gashi dama can bashi da fara'a hakan yasa Hanan take matuƙar jin haushinsa, don ita duk wanda zai hanata sakewa bata haɗa hanya da shi, ga wani irin kallo na tsana ko ta kirashi da ƙyama da yake mata duk sanda suka haɗu wannan dalilin ne yasa bata son shi.
Bayan dawowar Jabeer ya fara aiki a wata Babbar Asibiti a gefe ɗaya kuma yana Kasuwancinsa don bai tsaya a aikin gwamnati kawai ba. Bayan wani lokaci kuma ya gina haɗaɗɗiyar Asibitn sa da taimakon Mahaifinsa ya ɗauki ƙwararrin ma'aikata suka fara aiki a cikinta.
A ɓangaren Hanan kuma zama ƴar jarida shine burinta hakan yasa bayan sun gama secondary school ta zaɓi fannin da take so taci gaba da karatunta a gefe ɗaya kuma sosyyarsu na ƙara ƙarfi da Yayanta Nabeel har ta kammala karatun ta cikin nasara ta fara aiki da wani gidan rediyo.
Duk yanda Momy tayi ta raba Nabeel da Hanan abin ya gagara, tasha zuwa har sashen Ammy tayi mata cin mutumci amma bata ko kallon inda take har tayi ta gama ta fice. Tasha yin kuka inta tuna yanda suka taso tare da Harira amma ta fita komai na rayuwa a ƙarshe tayi mata cin amanar da ta kasa yafe mata, ƙaddara ta sake haɗa su aure a zuri'a ɗaya yanzu kuma wai ɗanta da take so ta ɗora duk wani burinta a kansa ya lalace a kan ƴar Harira. Shi yasa da ta hana auren aka nuna mata iko akan sai anyi shi ta ƙalesu ta nuna musu nata ikon ta hanyar sanya Nabeel ya sakar musu ƴarsu a ranar da aka ɗaura auren yaje mata sallama za'a raka shi ɗakinsa.
★Abin da ya faru a waccan ranar shine: bayan an kai Amarya ɗakinta Nabeel ya gama shirinsa cikin farin cikin mallakar abinda zuciyarsa ke tsananin so da ƙauna. Duk da jikinsa yana yin sanyi idan ya tunabda cewa ba da sanya albarkar Mahaifiyarsa ba aka ɗaura wannan auren, amma yana fata wata rana komai ya wuce Momy taso Hanan kamar yanda take son sa. Bayan sun fito abokansa na jira su raka shi ayi sayen baki, wurin Momy ya nufa domin yi mata sallama da neman albarkarta. Da sallama ya shiga parlourn bai samu kowa ba don haka ya ƙara sa bedroom ɗin ta yayi knowking, sai da aka bashi umarnin shiga sannan ya shiga. Zaune ya same su a bakin gado ita da ƙanwarta Sakina, gaishesu yayi lokancin da ya zauna a saman Capet dake shimfiɗe a gaban gadonnata. Bata ko kalli inda yake ba sai ma fuskarta da ta ƙara haɗewa ba alamar fara'a a cikin ta.
Umma Sakina kamar yanda suke kiranta ce ta amsa masa ba wata sakewa itama "Momy Ni zan tafi, ina roƙonki don Allah kiyi haƙuri ki yafe min sannan ki saka min albarka ko don in samu zaman lafiya mai ɗorewa da Matata!" Nabeel ya faɗa a raunace hawaye na zubowa daga idanunsa. Duk da Habiba taji tausayin ɗanta amma zuciyarta tayi bushewar da bata ji zata iya janye ƙudurinta ba, don haka ta kallesa tace "ka gama? Nace ka gama Nabeel?" Kai ya gyaɗa mata don ya kasa magana "amshi nan!" Ta faɗa tana miƙa masa takarda da biro fuskarta ba alamar rahama.
Amsa yayi hannunsa na rawa yace "Momy mai zan yi da wannan!" Fargaba ce fal a cikin ran Nabeel yake kallon Momynsa da jiran ƙarin bayani. Momy ta kalleshi tace "a matsayina na Mahaifiyarka nake baka umarni ka saki Matarka Hanan saki uku yanzunnan, idan kuma ba haka ba zan tsine maka kuma nonona da kasha ban yafe maka ba!"
Karkarwa hannunsa ya fara yi ya saki takardar ya fashe da matsanancin kuka ya rarrafa ya riƙe ƙafafun Momy ya buɗe baki zai fara riƙon ta "Momy don Allah ki...." Katse shi tayi ta hanyar cewa "Idan ka buɗe baki ka roƙeni akan wannanma ban yafe maka ba Nabeel" ƙasa ya kwanta yana raira kuka mai ban tausayi Aminatu dake laɓe a bakin ƙofa tana tayasa tsananin tausayinsa na kama zuciyarta.
"Kana ɓata min lokaci Nabeel ko ka zabi tsinuwata akan rabuwa da wannan matsiyaciyar yarinyar!" Momy ta faɗa a fusace. Da sauri yake gir-giza mata kai don ya kasa magana "Nabeel Allah ya..." A firgice ya riƙe hannunta yana kuka yake faɗin kar ki ƙara sa Momy zan saketa!" Shiru tayi duk da dama ba ƙarasawar zata yi ba, tayi ne don tasa shi aikata abinda take so.
Yana kuka mai taɓa zuciya ya rubuta mata saki uku ya jefar da takardar. Ɗauka tayi ta duba ta tabbatar kafin ta miƙa masa tace "kaje yanzu ka bata ta tattara ta koma wurin munafukar uwarta, kuma sannan idan ka sake ka faɗawa Abbanku ko Hajjo cewar ni nasaka ban yafe maka ba" haka ya fito yana haɗa hanya ko kula da Aminatu dake kiransa baiyi ba. Yanayin da Shaheed ya ganshi a cikine yasa ya sallami sauran abokansu ya ɗauke shi suka tafi, kuma duk tambayar da yayi masa yaƙi kula shi.
Sai gashi abinda Habibah ta aikata yayi sanadin mutuwar ɗanta kuma ta ɗora laifin akan Ammy da ƴarta, (Allah ka rabamu da son zuciya).
"Wannan shine abinda ke tsakanina da Habiba"! Ammy ta ƙara sa faɗa kuka na kuɓuce mata na tunawa da abubuwa da yawa da tayi. Kuka sosai Hanan tayi lokacin da ta gama sauraren Ammynta tace "lallai kin fuskanci ƙalubale da yawa a rayuwa Ammy, kuma in sha Allah Allah zai yi miki sakamakon mai kyau, amma Ammy aduka labarin da kika bani banga miye laifinki a ciki ba da zai sa Momy ta kasa yafe maki ba har nima ya shafeni".
"Son zuciya ne da ƙin karɓar gaskiya Hanan kuma in sha Allah, Allah bazai bata ikon cutar dake ba, wai ace mutuwar ɗanta ma baisa ta saduduba to sai yaushe? Sai dai muce Allah yasa ta gane gaskiya".
"Ameen ya Allah" Hanan ta faɗa suka ci gaba da hirar su don ɗebewa juna kewa.....
*OUM FATIMA*