5
by @mommuhseen
🅿️........5
"Ummi yaya bai dawo ba har yanzu? Naga har nine ya gota shiru"
Ummin dake shirin bacci zata tafi turaka wajen Baffa ta kalle ta kadan sannan tace, "me zai miki idan ya dawo?"
Zama tayi gefen gadonta tana narke fuska tace, "shine fa yace na samai falonsa,to kofar ma a rufe take alamun bai dawo ba"
Ummin na shafa turare tace, "sai kije ki kwanta tunda kinga da gasken bai dawo ba"
"Bazan iya baccin b...........saida tayi maganar taji abun da ya fito daga bakin nata, ummin tai sakale tana kallon ta ga Safiyya data fito daga bayin Ummin don d'an sab'anin da suka samu da Bilkisun yasa ta baro mata d'akin nasu zata kwana na Ummin, duk tsura mata ido sukai dan danan sai ta nemi canza maganar da cewa "ina nufin bazan iya baccin ba Ummi saboda Assignment d'in nan inban yisa ba akwai matsala, kuma yayan zai taimaka min"
In kunnen ta ba karya yajiyo mata ba kamar ajiyar zuciya Safiyya taja, ta rab'ota tana zama don shafa mai, ummin tace "karfe nawa kuke d.............da siririyar muryar sa yai musu sallama, cikin Sauri Sofy taja hijab ta zira tana ci gaba da shafarta, saman bed side ya zauna kusada Bilkisu yana gaida ummin tace masa
"Yanzu ake jajen ka, lafiya dai ko har ten takusa"
Yana shafa kanshi yana d'an murmushi dai-dai sun had'a ido da Safiyya, yai saurin dauke kai yace "wallahi ummi ina can office badan ma na gama ba, gobe dole nai sabko"
Tace" kadai ringa sassauta ma kanka don Allah, ga Bilksu nan ita ke ta cigiyarka"
Kallon ta yayi tana jan yatsunta tace, "Yaya sannu da dawowa"
Ya d'an lumshe idonsa cike da gajiya yace, "yawwa Bilkisu, muje to ki taho mun da ruwan tea mai zafi inajin bazan samu cin abincinki ba Ummi"
Murmushi tayi tace, "daman bani nayi ba Safiyya ce"
Uffan ita dai batace masu ba yace "fad'uwa tazo dai-dai da zama kenan"
K'unshe dariyarta Bilkisu tayi don tasan Safiyyar ta k'ulu, saboda jin bazaici ba tak'i jinin tayi abu ak'ici sai ta kama kuka
Ummin tace, "ni kam na wuce in kwanta ba zan shiririce wajen ku ba ke kuma in kin gama kukan saida safe"
Ta rab'asu ta wuce tabar su on ready daman Ishaq ya fece, Bilkisu tace "sister abun kuka baya miki kadan, kin san dai Yaya baya cin abu mai nauyi da dare"
Ta d'ago tana maka mata kallon banza tace, "eh tunda bake ce kikai ba ko, ai inke kikai ko tuwo ne ci yake karewar cus-cus da miya"
Tace, "to kiyi hakuri, nasan duk yau haushina kike ji ki yafe mun Sister bada niyyar nai hurting d'inki nai ba"
Tsaki taja tatashi tana ciro kayan baccin ta, jiki a salub'e Bilkisun ta fice daga d'akin kitchen ta wuce tana had'a masa coffeen da yake so duk dare saiya sha shi, ta gama had'a mishi ta juye tatafi falon nashi sadda taje har yayi wanka ya shirya cikin wasu kayan bacci masu taushi rigar kajeren hannu sai wandon ya d'an wuce guiwar sa kad'an, ba abunda yake tashi jikin sa da falon baki d'aya sai wani mashurin k'amshi zaune yake k'asan kafet ya mik'e k'afafun sa yana kallon new's, sallama tayi tana shigowa ansawa yayi yana kokarin ansa waya, ta durk'usa cikin ladabi ta aje masa yana wayar yace mata, " thank you"
Waje ta samu can gefe ta zauna tana jiran ya gama wayar, sai alwalar k'uda take har ya gama bataji inda yace A ba sauke wayar yayi yana duban ta bayan ya dauki cup d'in coffee yana surfing kadan-kadan, kamar bazai ce komi ba ya juya bayan sa ya dauko wata fashion leda ya mik'a mata, ansa tayi tana masa kallon karin bayani.
"Wayar Sofiyyah ce, bana son sake jin rikicin waya ya had'aku"
Wani abu ta had'iye tace, "Insha Allah,Angode"
Jinjina mata kai yayi tatashi jiki amace zata tafi har ta d'ora hannun ta kan k'ofa yace, "BILKISU"
cak ta tsaya ta kasa juyowa daker ta had'iye wani abu ta jiyo tana kallon sa yadda yake kallonta, tun tana iya cigaba da kallon sa har ta sare tai k'asa da kanta, cikin sassanyar muryar sa yace "What happen to u?"
Girgiza kai tayi yace, "ok u can go"
Kamar walk'iya haka ta fice ya bi k'ofar da kallo kafin ya dauke kai ya cigaba da shan coffee sa.
**********
Washe gari tun seven ya gama shirin fita don yau za'a handling d'in case d'un *Abu zayyad* zuwa garesa wani farin ciki ya tashi dashi, ji yake kamar duk wata damuwar sa tagama yayewa sadda ya fito falon da kitchen da dinning duk ba kowa saboda asabar ce duk bacci suke, sai kawai ya wuce kitchen d'in da kanshi yana had'a tea mai madara koshi yasha inyaje zai saka sa'id ya nemo masa abinci, yana cikin had'awar Safiyya ta shigo kitchen d'in ido duk bacci tana murtsike sa ko kusa bata ma lura dashi ba, tsabar yunwa ce tataso ta don bata ci komi na da zata kwanta.
Bugewa tayi da locker ta saki yar k'ara yai saurin jiyowa aje cup d'in yayi ya durk'usa yana d'agota,saurin ware idonta tayi akansa suka tsuru ma juna ido kamar zasu cinye junan su, dan luuuuu tayi da idon ta bud'e a kanshi kome ya tuna sai yayi saurin sakin ta yana tashi, ya daure face ya dauki cup d'insa ya zauna kan wata kujera dake cikin kitchen d'in, ta dad'e bata motsa ba saida ta dawo natsuwarta sannan ta bude frig ta dauki youghout jikinta na rawa tai hanyar ficewa da sauri har tana tun tub'e, jitai yace "keeeee!"
Cak ta tsaya bata jiyo ba ya cigaba da shan tea d'in sannan ya sake cewa, "zo nan"
Jikinta na tsuma ta fara takowa ahankali har ta iso inda yake,sai jan yar rigar baccinta take ko zata rufe cinyunta amman abanza, ba tare daya kalle ta ba ya mik'a mata cup d'in hannun sa mai tea aciki k'in ansa tayi muryar ta har sannan bacci bai saketa ba can ciki tace, "bana shan abu da zafi da safe sai wurin ten"
Wani jiyowa yayi yana dalla mata wani makirin kallo ai bata san ma ta ansa ba ta kafa kai tana runtse ido ta shanye, mik'a hannu yayi alamun ta bashi youghout d'in narkewa tayi kamar zatai kuka tace, "don Allah nidai kabar mun ina son abun...........kallon da yake mata kadai ya isheta dole ta bashi idonta har ya cika da kwallah, cikin Isa da Izza tare da worning yace "idan na sake ganin kin sa abun sanyi da safe saina karya ki, shashasha kawai"
Aguje tabar masa kitchen d'in tana kuka safiyyah badai kuka ba ita komi na kuka ne, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana d'an shafa kanshi ahankali-ahankali, kafin ya tashi ya bar gidan gaba d'aya.
*********
Kamar yadda Anty Nawwara tace zata ringa koya mun karatu duk weekend hakan akai, ina gama sallar asuba zata dauko littattafai na addini ta zube gaban mu haka zata ringabin su d'aya bayan d'aya tana koya mun, saboda ina son karatun sai gashi ina ganewa kuma ina fahimta.
Radda muka fara Yaya saida sukai fad'a da Anty wai akan me xata hanani baccin safe, wannan ai cuta ce da zalinci ai bani nace ta koya mun ba jin zasu hau sama suyi rikicin da suka saba sai nace masa ni nace inaso, duk da haka ransa baiso ba don dai kawai ina so ne haka ya hakura ya kyaleni, washe garin asabar d'in da daddare yaya suka dawo cikin mawuyacin hali don rikici ne ya b'arke tsakanin sa da gwaska acan wajen meeting d'in da sukai, wanda ba'ayi sa ranar juma'ar ba sai asabar, duk garin kowa ya shaida anyi tashin hankali don k'ungiyar gwaska itama babbar dabace da suke tsula tsiyar su, saidai su suna tsananin tsoron hukuma sab'anin yaya da yakeda uwa agindin murhu, don duk manyan yan siyasar sunada hannun jari a sabon company sa da yasama suna *ABTIMA OIL AND GAS COMPANY*, don anaji da wannan company nashi shiyasa duk tsiyar da yake tsulawa ba wanda ya isa ya kamashi ba tare da kwararan hujjoji ba, wannan fad'an da rikicin yaja ma Gwaska don shugaban k'asa yasaka ankullesa babu ranar fitowa an kuma rufe case d'in cewar ai shiyaja ABU ZAYYAD har haka ta faru don a wajen har rasa rai akai, wasu daga cikin body guard d'in yaya sun mutu wajen musayar wutar wasu kuma sun dawo da uban rauni, shi kanshi yayan k'afarsa na zubda jini suka iso a fujajan, motocin jami'an tsaron shugaban k'asa ma suka rakosa har gida.
Na gigice na rud'e ganin yaya cikin wannan tashin hankalin, kuka nai har muryata ta shak'e ranar a dakin sa na kwana duk karatum Anty nawwara ranar guduwa yayi, ji nake ciwon da yaji har cikin zuciyata da ina da damar da zan cire masa ya dawo kaina da bazai kwana dashi adaren ba, amman banda wannan halin saman kirjinsa nai bacci yana ta aikin lallashi Anty nawwara ta zama dohilo wajen kallon mu, inajin sadda yace mata "karki lashe mu don Allah, kina iya bamu space"
Jinjina kai tayi tana cewa, "bazan fasa gaya maka gaskiya ba Abbakar, muddin ka cutar da Fatima wannan karon bazan kyaleka ba, tunda kai bakada wata san'a sai ta lalata yaran mutane"
Runtse idonsa yayi yana jin zafin maganar yace a zafafe, "kinci arzikin ciwon dake jikina amman da kin gayama aya zak'inta, wannan hakilon da kike akanta ba fina sonta kikai ba domin bata da wani had'i dake, nine dolen ta gatan ta komi nai da ita bai shafe ki ba, idan da zan wani abu da ita ke bama zaki sani na don haka ki rik'e aranki ina binki bashin hukunci fice mun adaki karna sake ganinki sai na nemeki"
Fuuuuu ta fice tana banko k'ofar da mugun k'arfinta, runtse idona nayi ina sake lafewa jikinsa don karya gane naji wani abu.
Duk da wannan maganar da naji bai rage mun komi araina ba game da yayan, kwana uku nayi banje school ba sai da ya lallab'ani sannan na tafi saboda lokacin baya iya taka k'afar sosai.
A makaranta ba wanda yace mun meyasa bakizo kwana biyu ba sai wannan yarinyar mai shegen isa da miskilanci irina, duk da nasan ni ban kaita miskilanci ba don ita abun ya wuce misali, ba wanda nake magana dashi a class d'in namu saboda kowa yasan waye Yaya gani suke kamar zai masu wani abu, tsoron ma kulani suke ni kuma ko ajikina abunda nazo yi shi nakeyi na tashi, shiyasa ban damu ba don ba wanda yai jaje na da wannan yar izzar tai mun maganar rashin zuwana nayi mamaki,har hakan ya nuna ga fuskata.
Sake cewa tayi, "inason yin k'awance dake meyasa kike kakkauce wa, ni kin ganni nan ban damu da kowa ba kowa ya sani yan class, shiyasa ma kowa ke mamakin idan akaga ina magana dake"
Ko k'adan banji zan iya aminta da ita ba, don gani nake kawai yar lek'en asiri ce kauda kai nayi nace, "ki barni a yadda kika ganni, ni a ra'ayina bana son hud'd'a da kowa kamar dai ke d'in"
Murmushi tayi tace, "hakan ya nuna cewa zamu iya yin k'awance kenan, daman ance sai hali yazo d'aya ake abota"
Girgiza kai nayi nace, "no bana buk'ata Yayana ya hanani yin friendship da kowa, inso samune ni karki sake mun magana ma"
Wannan karon harda yar dariya tayi tace, "yadda kowa ke tsoron yayan ki *ABU ZAYYAD* ni bana tsoronsa, ina tak'ama dakaina don haka bazan daina miki magana ba kuma bazan rabu dake ba, gaki dai da shekaru sama da nawa amman kuruciya da rashin wayewa yana damunki, da zaki bani dama ta hanyar yin kawance dani da na fiddo ma mutane ainahin *FATIMAH*, don wannan ba ainahin ke d'in bace"
Sototo nai da baki da ido harda hanci ina kallon ta, murmushi tayi kawai tatashi daga sit d'ina ta koma nata, duk rabin ajin kallon mamaki suke mana muduka dai sunga ba mai shiga sabgarmu muma kuma bama shiga ta wani, amman gashi yau muna magana da juna.
Har aka tashi maganganunta ne suke mun yawo da amsa kuwwa cikin kunnena, wazanje yabani shawara? Wajen Yaya zanje? Aa fad'a zai mani muddin ma yaji ina sauraren wani, zuciyata tana son amunta da yarinyar amman wani sashe yana hanani saboda yaya, bana son duk wani abu dazai b'ata masa rai bama dana tuna irin halin dayake ciki ayanzu, sai kawai na shashantar da maganar tabi ruwa.
Ana tashi guard d'ina suka zo suka dauke ni ina kallon sadda take d'aga mun hannu, kallo kawai nabita dashi ban mayar mata martanin by by d'in ta ba, zuciyata bata saba da dogon tunani haka ba sai dan danan kaina ya fara ciwo k'ok'arin cire abun nayi don tsaf yaya zai iya kartoni.