FATY~ISLAM

SHAFI NA BAKWAI

by @ummishatu

©️2 WRITERS EMPIRE ✍🏻✍🏻




*💜💜FATY ~ISLAM*💜💜



  *NA*


*UMMI A'ISHA*




*7*



***Tamkar daddy ya san abinda Khalifa ke sakawa acikin ransa ya gyara zama yace,


"Khalifa kayi hakuri da wannan nauyi da muka dora maka, ka sani insha Allah ba zamu taba barinka kai ɗaya ba, zamu cigaba da tayaka har zuwa lokacin da Allah zai yanke numfashinmu... Ubangiji Allah ya sanyawa aurenku albarka ya baku zuri'a ɗayyaba"


"ba amin ba" Khalifa ya fada cikin ransa bayan ya sake yin kasa da kansa,


"zaku iya tafiya Khalifa saboda naga dare ya fara yi, yana da kyau mu barku kuje ku huta haka" mommy ta fada cikin farin ciki marar misaltuwa, Ladidi ta kira domin ta rakasu, 


Yana gaba suna binsa abaya har sashensu wanda in banda tashin kamshi babu abinda yake yi kuma tun daga waje zaka iya shakoshi da kofofin hancinka, 


A falo yaci burki yayin da sukuma suka wuce upstairs, a bedroom ladidin ta zaunar da ita sannan ta fito ta yiwa Khalifa sai da safe ta wuce ta fita, 


"wannan wacce irin masifa ce ni Khalifa? Wacce mummunar kaddara ke biye dani? Wanne girman zunubin na aikata da Allah ya jarrabe ni da auren wannan yarinyar? Ni ban taba yaudara ba balle nace ko alhakin wata ne da na yaudara yake bibiyata..... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un " ya fada yayinda yake jifa da hular kansa wanda hakan yayi daidai da jifan da itama Islam tayi da kwalbar turaren wuta dake gefen gadonta cikin wani dan ƙaramin kyakkyawan show glass fari tas, ji kake taratsatsa tauu..., yana jiyo wannan karar fashewar abun ya tashi da sauri ya hau sama yana bude kofar ya taka kwalba, hangota yayi tana watsi da duk wani abu wanda yake kan gadonta tana karaji tamkar makogaronta zai fice ko kuma zai yage, 


"ba zan kwana acikin wannan dakin ba.... Ba zan kwana ba....." ai tana hada ido dashi ta kurma wani ihu mai amsa kuwwa cikin azama ya ja da baya dan gani yake kamar tasowa zata yi ta iyo kansa, ta waje ya rufeta ya sauka kasa kafarsa tana zubar da jini, 


"wannan masifa.... Wannan masifa.... Ni dai na shiga uku.... Wannan wanne irin bala'i ne" 


Zama yayi ya zare kwalbar sannan ya dauko tissue ya manna ya take kafar, shi gaba daya yama rasa wanne irin tunani zai yi, tunanin kuruciyarsa ya fara yi wai ko zai tuno idan ya taba yi wa mahaukaci ko mahaukaciya dariya ko wannan dalilinne yasa ya kare da auren Islam amma sai dai har yayi tunaninsa ya gama bai iya tuno komai ba, shifa yanzu tsoron yarinyar nan ma yake yi baya jin zai iya zama ɗaki daya tare da ita bare har ya iya zuwa kusa da ita, 


Haka yayita zaune ya saka wancan ya kwance har karfe 2 na dare sai lokacin ya dingisa ya koma sama, a hankali ya murza key din dakin nata ya bude ya leka, zaune ya hangota can kasa lungun gado takure ta saka kanta tsakiyar gwiwowinta a haka take baccin bayan ta gama hargitsa ɗakin kamar wanda aka yi yaki a ciki, 


"Allah mai iko, mai yadda ya so da bawansa.... Ita kuma tata rayuwar kenan" ya fada a hankali, 


Bai karasa cikin dakin ba ya ja kofar ya wuce daya bedroom din wanda yake opposite da nata, ciki ya shiga ya canja kayansa zuwa na bacci ya hau gado amma kuma gaba daya sai ya gagara bacci, tunani kawai yake yana tambayar kansa yanzu wanne irin zama zasu yi da wannan yarinyar? Shi a haka rayuwarsa zata kare? Wasu hawaye masu zafi na bakin ciki ya fara zubarwa kuma baccin da bai yi ba kenan a wannan dare sai da asubah tayi sannan wani nannauyan bacci ya dauke shi.


Misalin ƙarfe tara mommy ta tashi kuma ita da kanta ta shiga kitchen tare da sauran ƴan aikinta dake tayata girki suka shirya breakfast lafiyayayye mai rai da lafiya aka shirya komai cikin wasu madaidaitan kyawawan warmers, Ladidi ta nufi part din Islam, akan dining ta ajiye musu amma haka kawai sai ta ji zuciyarta bata gamsu da ta tafi ba, dan haka sai kawai ta hau sama dan ajikinta take jin kamar Khalifa baya tare da Islam a daki ɗaya, knocking ta ɗanyi sau biyu zuwa uku jin shiru ta tura ta shiga,tun daga bakin kofa ta ci karo da fasasshiyar kwalbar turaren wuta ita kuma zaune ta hangota takure sannan ga dakin kaca kaca da alama jiya sai da tayi na sabon kafin ta yi bacci, to amma shi mijin yana ina? Bata tsaya wata wata ba ta hau kintsa ɗakin har ya dawo hayyacinsa, ruwa ta hada mata suka je tare tayi wanka ta taimaka mata kamar yadda ta saba sannan ta zo ta shiryata cikin wani sabon material mai tsada pink color wanda yayi mutukar karbarta,


Hannunta ta kamo dan ta fito da ita falo amma me? Suna bude kofa shima Khalifa na bude kofa zai fito tsayawa islam tayi ta zuba masa ido "mijina.... Mijina" take fada tana ja da baya har ta koma cikin dakin ta zauna a kasa tana cigaba da ambatar mijina mijina, shi dai Khalifa ƙasa ya sauka ya zauna ya fara karyawa har lokacin zuciyar sa babu dadi ransa a cunkushe,


"ina kwana?" Ladidi ta gaida shi bayan ta karaso kan dining din zata dibawa Islam abinci,


"lafiya..." ya fada ransa a cunkushe, Ladidi bata kara magana ba ta diba ta koma wurin islam wacce yanzu kuma tabar kiran mijina ta koma kiran mommy da daddy, da kyar ta lallabata ta bata abincin sannan ta fita ta koma sashen mommy wadda ke can tare da daddy suna ta hirar farin ciki suna hasashen ko yanzu Islam cikin wanne yanayi na farin ciki take? Mommyn taso ta tambayi Ladidi wanne hali taje ta samu Islam sannan wanne hali ta taho ta barta amma sai tayi tunanin kar ta zama uwa mai bibiya ko kuma mai bin kwakkwafin rayuwar auren ƴarta wannan dalilin yasa ta yi shiru bata tambaya ba,


Khalifa kwanciyar sa yayi nan falo yai ta sharar baccinsa ramakon wanda bai samu yayi daren jiya ba, bai sake tunawa da lamarin Islam ba bare yaje ya duba halin da take ciki a haka har yamma tayi Ladidi ta sake dawowa ta kawo musu lunch lokacin karfe 3:30, yana zaune kan prayer mat bayan ya idar da sallar la'asar sai gata ta shigo dauke da abinci,


Gaishe shi tayi ya amsa babu yabo babu fallasa nan ta ajiye abincin bayan ta dibar mata ta tafi dan kai mata, kwance ta sameta takure kuma a tukunkune kamar mai jin sanyi,


"mijina... Mijina..." Islam din ta fada daidai lokacin da Ladidi ta zauna kusa da ita,


"yana zuwa bari zan turo miki shi.... Fara cin abinci tukunna" Ladidin ta fada cikin tausayawa,


Bayan ta kammala bata abincin ta sauka kasa wurin Khalifa inda yake zaune tsakiyar falo yana cin abinci amma kamar zai rusa ihu haka yake ji,


"Islam ce ke son ganinka..."


"ok, ina zuwa"


Ba tare da ta koma ciki ba ta juya ta fita dan komawa sashen mommy.


Koda ya kammala cin abincin bai saurari bedroom din da Islam ke ciki ba bare har yaje yaga dalilin kiran da take yi masa, sabuwar wayarshi ya dauko wadda ya siya a irin kudin da daddy ya bashi wanda yace yayi siyayyar fita biki, ashraf ya kira fuskarsa babu fara'a tamkar ashraf din yana ganinsa,


"wai ko da wayar tawa ma ba zaka dauka ba?"


"a'a ni na isa? Wane mutum, tufa nake babban ango...."


"Ashraf bana son rashin mutunci, zaka fara ko? Ta yaya na zama ango? Ni da nake auren mahaukaciya tuburan"


"kai jama'a, to ai dai a hakan zaka amsa sunanka ango"


"ba laifinka bane, ni na kiraka"


"kayi hakuri zan shigo anjima"


"shikenan sai ka shigo"


Yana kammala wayar babu jimawa yaji motsin mutane alamar bakine zasu shigo, tashi yayi da kansa yaje ya leka nan yaga yan gidan su ne karankaf dan hatta umma ma sai da ta zo, dan daidaita fuskar shi yayi ya je ya bude musu kofa yana yi musu sannu da zuwa,


Duka suka shigo cikin kowa yana cike da farin ciki saboda ganin yanda Allah ya sauya masa rayuwa daga kunci zuwa falala lokaci guda,


"ina ita Islam din?"


"umma tana sama tana bacci"


"to abinda zan fada maka Khalifa shine, yarinyar nan dai amana ce a gurinka, iyayenta amana suka baka ita duk da auren naku yazo a wata kama ta daban to amma ka sani nauyinta yana rataye a wuyanka, ka kular musu da yarinya kamar yadda ka alkawarta tun farko, Khalifa ka kular musu da yarinya kana jina? "


" ina jinki umma, insha Allah zan kula da ita "


" to Allah yayi muku albarka, dama godiya muka zo yi kuma tunda mun kammala dasu can din ai sai mu tashi mu tafi "


Kalaman umma ba karamin haushi suka bashi ba wai godiya to godiya akan me?,basu ga Islam ba itama bata gansu ba ya rakasu suka tafi ya dawo ya nemi wuri ya zauna a falo cikin damuwa.


Yana zama babu jimawa Ashraf yazo, fita yayi yaje ya shigo dashi har lokacin fuskarsa babu fara'a,


"Haba ango wai yana ga kanata wani shasshan kunu ne sai basarwa kake? Hope komai dai ya tafi lafiya"


"Ashraf wai dan Allah Meyasa baka da mutunci ne? Nifa yarinyar nan ko daki daya ban hada da ita ba bare shimfida soo allow me to rest in peace pls"


"kai amma gaskiya baka kyauta ba abokina, ya za ayi kabar yar mutane ita daya alhali iyayenta ba haka suke yi mata ba"


"ni haka zanyi mata sai me kuma?"


"gaskiya wannan bai dace ba, yarinyar nan fa tana bukatar kulawa kamar yadda kaji iyayenta sun fada sannan kai a matsayinka na mijinta ya zama dole ka sadaukar da dukkan lokacinka dan kulawa da ita tare da nuna mata soyayya wannan shine fa babban dalilin da yasa iyayenta suka dauko ka cikin dubu suka damka maka amana "


" malam nifa kar ka takura min, ka fara damuna yawwa.... " daga haka ya tashi ya kunna kallo ya kamo Channel din sports +, duk irin shawarwarin da ashraf ke bashi shiru yayi masa kamar baya jinsa dan ko tanka masa bai yi ba. 


Har dare suna tare da ashraf sai bayan sallar ishah sannan ya tafi bayan sun ci sun sha, yana tafiya ya rufe kofa yaci gaba da kallonsa sai kuma shi da kansa yaga rashin kyautawarsa da bai je ya gaida su daddy ba koda yake shi kansa kunyar zuwa yake yi dan ta yuyu su yi zargin ko ya kusanci Islam tunda dalilin da yasa suka aura masa ita kenan, ya jima zaune falo yana ta kallo har 11 sai lokacin ya kashe komai ya haura sama, ko kallon dakin da take ciki bai yi ba ya shiga cikin dayan yayi wanka ya saka kayan bacci yayi kwanciyarsa acikin ransa yana jaddadawa kansa dole fa sai ya nemi mafita dan bazai cigaba da zaman takura ba har ga Allah,tsaki yayita ja yana juyi daga karshe ya dauki wayarsa ya kira ashraf lokacin har 12 ta gota, a firgice ashraf ya dauki wayar dan duk tunaninshi ba ƙalau ba,


"wai har kayi bacci ne?"


"lafiya?" ashraf ya bukata cikin zaƙuwa,


"ban gane lafiya ba, nifa kiranka nayi muyi hira dan na kasa bacci"


"mts*** To ni matarka ne da zanyi hira da kai cikin wannan talatainin daren? Malam kaje wajen matarka idan hira kake so ni bacci zan yi"


"ashraf wai Meyasa kake yimin wulakanci ne yanzu? Dan kawai nayi aure"


"Khalifa.... Sai da safe" daga haka ya katse wayar tare da kashe ta gaba daya, tsaki Khalifa yayi ya tashi zaune yana bin ko ina na cikin dakin da kallo, lallai yanzu ya yarda kudi ko mulki ba shine jin dadi da farin cikin rayuwa ba, shi dai ada da bai da ko sisi baccinsa yake sosai da zarar ya kwanta kuma koda yana da tarin damuwa, amma yanzu gashi account dinsa akwai kudi masu yawan gaske ga muhalli dankarere amma bacci ya gagari idonsa, wata irin muguwar tsanar Islam yaji acikin ransa ji yake kamar ya shiga dakin da take yaje yayita dukanta ko zai huce, zumbur ya tashi tsaye daga zaunen da yake sakamakon bugun kofar da yaji ana yi kamar za a ballata......✍🏻





Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku, 


MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH 


FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA 



 Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.




_*Ummi Shatu*_👌🏻