SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA
by @ummishatu
TWO WRITERS EMPIRE ✍🏻✍🏻
💜💜 *FATY ~ISLAM*💜💜
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
11
***Tunda ya fita daga wannan bedroom din bai koma ba chaten din shi yaje yayita faman yi da Muslimat, idan chaten din ya ishe su sai su koma waya haka suka wuni abu daya, bai sake bibiyar yanda Islam take ba har sai da yazo kwanciya bacci domin kayansa suna dakin da take ciki lokacin ne ya shiga kuma yana shiga ya ganta zaune rungume da pillow tana cewa,
"shhhhhhhh baby...... Shhhhhhhh daina kuka, zaka sha ruwa? Ungo"
Girgiza kai yayi ya wuce zai nufi wardrobe,
"kai.... Kai.... Fita" yaji ta fada cikin tsawa da wata iriyar murya wacce ba zai iya bambance tata ce ko sabanin haka ba, ai duk jarumta irin tashi take ya fice lokacin har ta fara jifansa da pillow,
"kai anya yarinyar nan lamarin nan nata kuwa ba harda aljanu ba? Duk yadda aka yi tana da aljanu bayan ciwon haukan...." kasa komawa dakin yayi har sai da ya tabbatar da tayi bacci sannan yaje ya lallaba ya kwaso dukka kayanshi bai bar ko daya ba ya dawo dasu daya dakin, key yasa ya rufe dakin kafin ya kwanta bacci, kamar jiya yauma raba dare suka yi suna waya da Muslimat,
Washe gari ya kira su umma ya sanar dasu sakon daddy na maganar bawa su Sudais aiki nan umman ta shiga godiya kamar zata yi tsalle akan ƙaya kuma a ranar suka je suka samu daddy a office dinsa wanda harda ashraf suka tafi. A ranar da yamma su umma suka zo domin yin godiya kan irin kyautatawar da daddy yake ta yi musu ba dare ba rana kuma babu gajiya bare kosawa, kyakkyawar karba mommy tayi musu saboda daddy din yana office bai dawo ba, su jidda kuwa da mimi tun bayan zuwansu suke damun umma da zasu je part din yaya Khalifa suga anty Islam,
"kufa bakwa ji, me zakuje kuyi musu? Ko dai so kuke kawai kuje ku damesu?" umma ta fada tana harararsu,
"a'a barsu su je mana, yayarsu fa zasu je gani ko? Maza kuje tana can part dinta shima Khalifa din yana nan ai" jin abinda mommy ta fada ai da gudu suka tashi suka kwasa suka fita sai part din Khalifa,
Yana bedroom ya idar da sallar la'asar kenan yaji hawowarsu jidda da gudu, zasu fara knocking kenan ya fito yana bin su da kallo daya bayan daya,
"yaya Khalifa ina wuni ina anty islam..." suka hada baki wurin fada,
"lafiya lau, ku da wa kuka zo?"
"muda umma ne"
"tana ina?"
"tana wurin mommy"
"ga islam din can cikin wannan dakin" ya basu amsa yana nuna musu bedroom din da Islam take ciki,basu sake bi ta kansa ba suka shiga, tana zaune kan gado kanta babu dan kwali duk gashin kanta ya barbazu wani ya rufe mata fuska ga pillow abayanta kamar ta goya shi duk da babu zani sai faman jijjigashi take kamar tana rarrashinsa,
"anty Islam...."
Da kallo ta tsaya tana bin su saboda bata san su ba bare susa ran zata ganesu, ta jima tana kallonsu kafin ta mikawa mimi hannu ta zaunar da ita kusa da ita,
Pillown bayanta ta dauko ta dora mata akan cinya tana dariya,
"Baby....... Baby ne......shhhhhhhh banda kuka"
Murmushi mimi tayi ta soma girgiza shi kamar irin itama tana rarrashin baby dagaske hakan yasa Islam taji dadi ta mikawa jidda itama hannu ta zauna kusa dasu,
"yi shiru baby.... Daina kuka" mimi ta fada tana sake jijjiga Pillown dake kan cinyarta,
"bata baby..... Shhhhhhhh" bawa jidda shi mimi tayi tana murmushi amma duk tausayinta ya cikasu ganin irin shirmen da take tayi musu, lokacin da Khalifa ya leko ya gansu abun har mamaki ya so bashi ganin yadda islam ta sake dasu take ta wasa da shirme dasu su kuma sun biye mata sai tayata suke dan har gashin kanta suka gyara mata da wayo da dabara,
"nice amarya..... Maman baby...."
"ehh kece amarya bari a gyara miki kanki irin yadda ake yi wa amare...." jidda ta fada tana yi mata murmushi, bata ki ba ta bari suka taje mata shi sannan suka daure mata da ribbon wanda haka kullum Ladidi ke fama wurin yi mata wannan gyaran gashin dan shigowa goma gyara goma amma tana tafiya anjima idan ta dawo zata ganshi kamar bata yiba,
Dakin suka gyara mata suka ajiye komai yadda ya dace,
"a canja wannan.... Bana so...." ta fada tana nuna musu kan gadonta, sun fahimci abinda take nufi shiyasa suka yi hanzarin canja mata tana ganin haka ta saki fuska tana yi musu dariya,
"ya sunan baby?" take tambayarsu,
"sunan baby Khalifa...." mimi ta fada a hankali,
"Khalifa?... Khalifa? A'a ba Khalifa ba" ta fada cikin fada,
"to sunanshi baby" jidda ta fada a dan tsorace,
"baby.... Sunanshi baby"
Dariya suka yi gaba daya, nan taci gaba da yi musu shirme har su umma suka shigo tare da mommy, yadda mommy taga islam ta sake dasu jidda suna ta yimata hira kamar wata mai hankali sai abin yayi mata dadi kuma ya bata sha'awa har taji bata son tafiyarsu, cikin farin ciki suka rabu nan aka koma gidan jiya tsakaninta da khalifa wadda shi yanzu bama ta ita yake yiba ta yarinyar da ya hadu da ita yake sai dai amma a koda yaushe tambayar da yake yi wa kansa shine ta yaya zai auri Muslimat? Iyayen islam zasu bari hakan ta kasance? Ire iren wannan tunanin shine yasa har yanzu bai je gidansu Muslimat ba kamar yadda ta jima tana bashi damar hakan, koda yaushe ce mata yake yi zai yi tafiya ne yanzu ta bari sai ya dawo zai zo mata,
Akwati madaidaici Ladidi ta samu ta hadawa Islam kayanta duk wanda za a bukata, shima khalifa ya hada nasa acikin akwati irin nata, lokacin da zasu tafi harda su umma ayi musu rakiya zuwa airport, umma sai sake jaddada masa take cewar ya kula da Islam lokacin da suke yin sallama dashi, murmushi yayi ya rike kunnensa yace,
"umma naji fa dukkan abubuwan da kika ce sannan wai kin manta ne wannan tafiyar ba iya ni da ita bane kadai akwai iyayenta?? Harda mahaifanta ba, ai ina kyautata zaton suma zasu tayani kulawa da ita...."
"duk da haka Khalifa kaima ka kula...."
"to umma insha Allah"
Sallama suka yi yabi bayan su mommy wadanda sun jima da kama hanyar shiga jirgi, daga mommy din har Islam sun sha bakaken dogayen riguna masu kyau da tsada musamman ma islam wacce ita tata tafi ta mommy yawan kwalliya dan ita ta mommy iya rigar ce kawai babu wani ado ko zane a jiki haka take plane, amma ita islam anyi zane sannan an zuba stones gaba da baya, a kusa da wata matashiyar budurwa ya zauna saboda ita mommy tana tare da islam shikuma daddy wani dattijo ne ya zauna kusa dashi, daga shi har yarinyar dan basarwa juna suka fara yi saboda kowa ya dan yaba da dan uwansa shi kansa Khalifa ya san a yanzu dai sai dai idan ba zai fadi gaskiya ba amma shi karan kansa ya san ya sauya dan hatta fatar jikinsa ta sauya saboda jin dadi da cin abinci mai kyau sabanin da ada sai abinda ya samu zai ci ga rashin zama wuri ɗaya amma a yanzu sai yayi kwana biyu bai fita ba kuma dukkan abinda yake bukata akwai akusa dashi,
Babu wanda yayi magana acikinsu har zuwa lokacin da jirgin ya tashi "ohh Allah mai iko wai yau nine asaman iska.... Ko a mafarki ban taba kawowa zan hau jirgin sama kwana kusa ba, lallai inda rai da rabo...." haka yake ta fada a cikin zuciyarsa ita kuwa yarinyar kusa dashi da alama ba wannan ne karon farko da ta shiga jirgin sama ba dan yaga sai sabgar gabanta take, ta fito da wani English novel tana karantawa, haka yaketa satar kallonta har jirgin su ya sauka,
Duk da yana cikin farin ciki amma sai da yaji wani rass lokacin da yaga tare zasu zauna ɗaki daya da islam a masaukinsu, bai nuna komai a fuskarsa ba dan kar su mommy su zargi wani abu ko kuma su saka masa ayar tambaya koda yake ai hakanma shine daidai shi daddy da mommy dakinsu daya shima shida islam ɗakinsu daya, to yau kowanne irin zama zasu yi kuma? Tambayar da yaketa yi wa kansa kenan sai dai ga mamakinsa suna shiga ɗakin islam din ta kife akan gado nan ya wuce bathroom yayi wanka yazo ya shirya dan daddy yace masa yaje ya fito su je masallaci tare, ita kadai ya bari a dakin ya fita bayan ya rufe ɗakin da yake yana sauri ko abinci bai tsaya ci ba a ransa yace sai ya dawo,
Sun ɗan jima a masallacin kafin suka dawo, ai yana bude dakin yana shiga ya ga islam tayi kaca kaca da abincin da aka kawo musu duk ta zuzzubar kan gadon da take kwance, yasan bayan ta gama cine shine tayi haka da sauran, zama yayi kan kujera yana kallonta tana bacci, rasa abin yi yayi daga karshe yaje zai kwanta haka, ya soma karkade inda zai kwanta din yaga ta bude ido, spoon din da yake kusa da ita wanda ta ci abinci dashi mai bala'in nauyi ta ɗauka ta wurga masa tana cewa " kai ba mijina bane.... Fita daga nan" saurin sunkuyawa yayi spoon din yaje ya doki bango ya fadi, babu shiri ya fita, haka yayi ta zagaye har sai da ya tabbatar tayi bacci sannan ya koma ya sidada ya wuce cikin toilet a can ya kwana, ransa idan yayi dubu to sai dai ya baci dan bai yi wani baccin kirki ba,haka dai yayita daurewa bai taba fadawa daddy ko mommy ba, kwanan su biyu da zuwa da suka fita ya siyo turare da jallabiya masu tsada guda biyu daya milk color daya kuma white, dama yanzu sai islam tayi bacci yake shiga dakin ya kwanta kan kujera ko kuma a ƙasa shiyasa yau dinma ya ɓata lokaci a harabar hotel din yana waya da Muslimat har sai da ya tabbatar da islam tayi bacci sannan ya shiga,
Tun bayan da ya bude kofa yake jiyo kamshin turare kamar me yana kaiwa tsakiyar dakin yaga gaba daya kayanshi yashe a kasa Islam ta zazzagesu kaf daga cikin jaka, turaren da ya siyo mai bala'in tsada ta fasa shi bai kai ga gama wannan tunanin ba ya hangota ta tuje bedsheet din dake kan gadon ta maye gurbinsa da daya daga cikin jallabiyoyin da ya siyo wato milk din ita kuma white din itace ta saka a jikinta, zama kawai yayi ya dafe kansa da dukka hannayensa guda biyu ya zuba mata ido yana kallonta yayin da ita kuma take ta sharar baccinta....... ✍🏻
Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku,
MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH
FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.
_*Ummi Shatu*_👌🏻