FATY~ISLAM

SHAFI NA GOMA SHA BIYAR

by @ummishatu

TWO WRITERS EMPIRE ✍🏻✍🏻




 πŸ’œπŸ’œ *FATY~ISLAM*πŸ’œπŸ’œ




 *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




15




***Mommy ce a gaba sai daddy dake biye da ita duka hankulansu a tashe, bedroom din Islam din suka fara shiga amma bata ciki dan haka suka nufi dayan anan suka hangota can lungun gado ta hada kai da gwiwa sai faman kuka take kuma da alama ta jima tana kukan dan fa fuskarta nan ta kumbura tayi ja,


Da sauri mommy ta karasa ta dagota,


"Islam.... Kukan me kike yi?"


"mommy.... Zai kasheni.... Kasheni zai yi mommy, mommy zai kashe ni"


"Islam waye zai kasheki? Babu wanda zai kasheki kinji.... Yi shiru daina kuka, tashi muje" daddy ya fada shima yana kokarin kamo ta,


"daddy kasheni zai yi.... Ni ku tafi dani"


"to shikenan zamu tafi dake amma babu wanda zai kashe ki.... Ki daina fadar wannan maganar kinji"


Kaya mommy ta canja mata sannan ta kamata suka sauka kasa inda daddy ke can yana jiran su,


"to amma wai me ya faru ne yallabai? Ni na kasa fahimtar wannan abun da ya faru da Khalifa..." mommy ta fada cikin damuwa bayan sun koma part dinta,


"ni kaina wallahi na kasa fahimtar abinda ya faru, kawai ina ganin babu wanda zai sanar damu ainihin abinda ya faru sai shi Khalifa din idan ya samu sauki...."


"to Allah ya rufa asiri, bari naje na shirya sai mu tafi asibitin idan sun gama hada masa breakfast din"


"to shikenan, ni ina da wani meeting ne around 9 dan haka idan na ajiyeki wucewa zanyi"


"to babu problem amma kana ganin muna sanar da mahaifiyarsa ne ko yaya?"


"a'a Hajjaju ai ko zamu sanar da ita tofa ba yanzu ba saboda hankalinta ai sai ya tashi mu bari dai yaji sauki yadda idan tazo ta ganshi ba zata shiga cikin rudani ba"


To shikenan Allah ya bashi lafiya "


Shiryawa mommy taje tayi cikin wata atamfa super Holland ta fito suka tafi tare da daddy, har lokacin Khalifa bai ma san wanda yake kansa ba bare ayi maganar abincin da suka kai masa, anan daddy ya tafi ya bar mommy sai azahar sannan ta tafi gida zuwa yamma sai ta dawo, da yamman tare suka dawo da Ladidi da kuma Islam wacce tun safiyar ranar a tsorace take taki sakin jiki da kowa,


Suna shiga dakin da Khalifa yake kwance ya bude idonsa ya kalli kofar da suke shigowa sai kuma ya kalli kansa nan yaji gaba daya ilahirin kansa a daure tamau sai uban zugi da radadin da yake yi masa,


"sannu Khalifa.... Ya jikin naka"


"da sauki mommy" shine amsar da ya iya bata,


"Allah ya baka lafiya"


"amin, mommy nan a ina nake??"


"a asibiti ne amma insha Allah zaka samu lafiya"


Jijjiga kansa yayi ya koma ya kwanta, islam dake tsaye tana lissafa yan yatsun hannunta kamar mai kirga wani abu fashewa tayi da kuka ta fita nan Ladidi ta bita,


"mijina bashida lafiya, me yasa mu mijina?, me yasa mu mijina??" shine abinda take ta fada tana kuka, nan Ladidi ta shiga rarrashinta,


"ciwo yaji amma insha Allah zai samu lafiya, kiyi masa addu'a Allah ya bashi lafiya"


Hannunta ta kama suka koma ciki nan taje can jikin bango ta tsugunna tana ta kallon Khalifa har ya samu ya tashi ya danci abincin da suka kawo masa ya sake kwanciya saboda wani irin ciwo kansa yake yi masa, sai zuwa dare lokacin da daddy yazo sannan su mommy suka tafi shikuma daddy yaci gaba da zama awurinsa dan anan ma ya kwana tare dashi duk da cewa asibitin kudi ne akwai masu kula da majinyata amma duk da haka daddyn bai tafi ba anan ya kwana sai da gari ya waye sannan ya tafi saboda zai je aiki, tafiyarshi babu jimawa su Ladidi suka karaso ita da driver wanda ya kawota ita mommy sai an jima,


Zaune Khalifa ya tashi ya karbi tea din da Ladidi ta hada masa ta mika masa, kurba daya yayi sannan ya kalleta da fuskarshi wacce ta kumbura,


"Ladidi dan Allah in tambayeki mana..."


"to Allah yasa na sani"


"wai wanne irin ciwon hauka ne da islam?"


Dan shiru tayi tana kallonsa tana sake juya tambayar da yayi mata acikin ranta,


"ban fahimci tambayar taka ba..."


"kin san a rayuwa komai yana da tushe sannan yana da sanadi haka kuma yana da sila, akwai wadanda zaka gansu makafi ne amma sai ka samu ciwon ido ne ya makantar dasu, wasu kuma wani abune ya shiga idon ya lalata shi har suka makance, wani kuma zaki samu dama can tun asali haka aka haife shi, to haka ciwon hauka ma ya kasu kashi kashi, ita islam wanne irine nata? "


" ehh to gaskiya nidai abinda na sani.... " daidai lokacin likita ya shigo hakan yasa Ladidi yin shiru bata fadi abinda tayi niyyar fada ba, dan duba shi likitan yayi sannan yayi rubuce rubuce a jikin file dinsa yafita,


" ga kaya nan da wayarka an kawo maka, ka dan samu kayi wanka zaka ji dadin jikinka" Ladidi tace dashi kafin ta fita daga cikin dakin. Sai da ya kammala karyawa sannan ya shiga yayi wanka ya fito ya canja kayan jikinsa da wanda aka kawo masa wadanda suma kanana ne, zama yayi gefen gadon ya dauki wayar shi ya kira ashraf,


"Khalifa ya aka yi"


"gani a asibiti bani da lafiya amma karka fadawa su umma please...."


"subhanallahi me ya faru?"


"maganar nan ba ta waya bace sai kazo kawai zamu yi ta face to face"


"to idan na tashi daga office insha Allah zan shigo" 


"ok" 


Katse wayar yayi ya shiga games ya zabi guda daya ya fara zuciyar sa dauke da tarin tambayoyi masu yawan gaske, a haka har mommy ta karaso tare da islam wacce ta sha jar doguwar riga abaya da farin karamin hijab kamar koda yaushe sai kirga yan yatsun hannunta take yi tana dariya, 


"Sannu Khalifa.... Ya jikin?" 


"mommy sannu da zuwa, ina yini, jiki da sauki" 



"Allah ya kara lafiya" 


Amin ya Allah.... Am mommy dama ina son na tambaye ki.... " ya fada yana kokarin tashi zaune,


" yi a hankali Khalifa... Me ya faru? "


" mommy dan Allah wacce irin lalura ke damun islam? "


" Khalifa yanzu me kake so in ce maka? "


" mommy komai ma ki fada min saboda gaskiya rayuwata tana cikin tsaka mai wuya kuma tana cikin hatsari, wannan ciwon fa Islam ce ta jimin shi, ni baku taba sanar dani cewa tana irin haka ba, komai a kudundune kuka bani shi ciki kuwa har da lalurarta, a gaskiya ina jin tsoron abinda zai je ya zo,tabbas na san ina da bukatar kudi amma rayuwata da lafiyata yafi min komai muhimmanci.... "


" Khalifa ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai daidaita... "


" mommy a gaskiya ba zan iya cigaba da wasarere da rayuwata ba, rai guda daya ne idan ka rasa shi shikenan ka rasa shi har abada.... "


Shigowar Ladidi ne ya dakatar dasu daga maganar da suke yi, nan mommy ta kama hannun islam suka fita Ladidi tana biye dasu har waje,


" mommy ni ina ganin anya ba zaku sanar da Khalifa komai ba? Babu amfanin Ι“oye masa wannan sirrin tunda shine yake matsayin mijinta a halin yanzu...."


"Ladidi banki ta taki ba amma a yanzu ni dai ban shirya tona wannan sirrin ba, sai dai mu jira zuwan yallabai muji idan har ya yarda a fallasa wannan sirrin sai a fada amma daga ni har shi bama bukatar fitar da wannan sirrin.... Bama son duniya taji" mommy ta fada idanuwanta har sun cika da kwalla,


" mommy kiyi hakuri ban fadi wannan maganar dan ranki ya baci ko na tayar miki da hankali ba "


" karki damu Ladidi ba wai maganar ki itace ta bata min rai ba, a duk lokacin da na tuna da wannan sirrin na kan tsinci kaina cikin tsananin bakin ciki, nadama, bacin rai da kuma damuwa.... "


" hakane mommy amma ki tuna ya riga da ya wuce dan haka babu amfanin tunashi har rai yazo yana Ι“aci... "


" Ladidi ba zaki taba fahimtata ba "


" na sani mommy amma Allah yana sane da komai... Yana ji yana gani " haka Ladidi taci gaba da bawa mommy baki tana yi mata kalamai masu taushi da sanyaya rai. Khalifa jinsa yake yi gaba daya cikin duhu saboda mommy da Ladidi sun saka shi cikin duhu da suka gaza bashi amsar tambayar da yayi musu, gaba daya kansa ya daure sai tambayar kansa yake yi shin wai me hakan yake nufi? Wuni guda babu wanda ya kara ce masa kanzil akan abinda ya shafi maganar daga mommy har Ladidin da ya tambaya,


Misalin Ζ™arfe 5:30 sai ga ashraf wanda dawowarsa kenan daga aiki ya taho nan direct, su mommy ne acikin dakin amma zuwanshi bayan sun gaisa sai suka tafi suka ce zasu je su dawo zuwa dare, zama ashraf yayi gefen gadon yana kallon Khalifa dake zaune shima yasa pillow ta bayansa yana jingine sannan ga wayar shi nan yana game amma ya sakata a flight mode,


"guy inata kiranka before na taho amma your phone is not reachable...."


"eh na sakata ne a flight mode saboda wannan yarinyar tana ta damuna nikuma bani da lokacin ta"


"wacce yarinya kenan?"


"Asiya"


Gyara zama ashraf yayi bakinsa a bude yana kallon Khalifa "wai dan bata da kunya kiranka take yi yanzu?"


"ka rabu da ita she thought am that stupid, ko kuma ban san ciwon kaina ba..."


"lallai mata sai a hankali"


"Rabu dasu kawai"


"wai Khalifa accident kayi ne? Me ya faru?"


"Ashraf.... Kullum kana ta damuna da injewa yarinyar nan Islam in bata hakkinta, in tausaya mata, in bata hakkinta this and that blah blah blah to wanna shine result din abinda naje mata dashi"


"innalillahi.... Kai.... Subhanallahi..... To wai garin yaya taji maka wannan ciwon Khalifa?"


"dama ai na fada maka ni jikina bai bani inje inda take da sunan sex ba amma ka dage ka nace suma iyayenta suka saka min pressure to gashi nan daga zuwa kusa da ita first attempt ga abinda tayi min, sannan inata tambayar su mommy musabbabin ciwon nan nata amma sun ki sanar dani nikuma wallahi bazan cigaba da zama da ita a haka ba dan gaba ban san me zai faru ba "


" Khalifa... Dan Allah kabi komai a hankali, ka bari ka fara samun lafiya tukunna "


" kanka ake ji ni ina samun lafiya gidan mu zan wuce direct, ba zan je ta kashe ni a banza ba.... "


" insha Allah ma haka ba zata faru ba "


" to ba gashi ta dauki hanyar hakan ba, kuma ka san dai idan ta kashe ni to ta kashe banza tunda ba a shari'a da mahaukaci.... "


" dan Allah ka daina wadannan maganganun "


" in yi shiru inyita cutuwa? Wallahi ba zan yi shiru ba ya zama dole inyi magana"


"ehh zaka yi magana amma this is not the right time da zaka yi maganar, ka bari ka samu lafiya ka koma gida in ya so sai ku yi magana da su a nutse cikin fahimta"


"ashraf wallahi ina jin na gama zama da yarinyar nan..."


"kudin su fa da suka babbaka?"


"asara ta hau kanmu gaba daya tunda nima kalli ciwon da taji min, jinin da aka zubar min ai ba zai tashi a banza ba ko? Dani dasu duk sai mu raba asara"


"Allah ya rufa asiri kai dai kawai.... Ka daina wannan maganar dan Allah, kai da Islam mutu ka raba"


"saboda wahayi aka yi akace sai na rayu da ita ko?" Khalifa ya fada cikin jin haushi, dariya ashraf yayi ya dafa kafadarshi yace "maida wukar abokina, nidai fatana Allah ya baka lafiya amin"......... ✍🏻



Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku, 


MASARAUTA tare da alΖ™alamin FATYMA XARAH 


FATY ~ISLAM daga alΖ™alamin UMMI A'ISHA 



 Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu Ι—aya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.





_*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ»