FATY~ISLAM

SHAFI NA GOMA SHA SHIDA

by @ummishatu

TWO WRITERS EMPIRE ✍🏻✍🏻





💜💜 *FATY~ISLAM*💜💜




 *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




16




***Misalin karfe 8 daidai na dare su mommy suka gama shirin tafiya asibiti domin kaiwa Khalifa dinner, daddy ne zai kaisu sai mommy da islam da kuma Ladidi wacce kusan duk inda zasu je tare suke zuwa da ita,


"wannan abincin Khalifa ne kawo kar ya zube..." mommy tace da Islam tare da karbe warmer din da ta kinkima irin wacce taga Ladidi ta ɗauka,


"Khalifa....? Khalifa?" Islam ta maimaita sunan tana kallon mommy, "ehh mijinki ba..."


"mijina? Mommy mijina bashi da lafiya..." sai kuma ta fara kuka tana watsi da takalmin dake kafarta, "mijina bashi da lafiya.... Mijina bashi da lafiya"


Daddy wanda fitowarsa kenan yazo ya tarar da abinda ke faruwa kamata yayi ya riketa ya soma yi mata magana cikin kwantar da hankali,


"mama na.... Yi hakuri zai samu lafiya, ai dazu ma kin je kin gaishe shi ko? To yanzunma zuwa zamuyi mu sake duba shi.... Allah zai bashi lafiya..." gyada kai tayi fuskarta a rakwarkwabe alamar kuka, takalman Ladidi ta bata ta saka sannan suka tafi,


Khalifa na zaune kan abin salla ya idar da sallar ishah shi kuma ashraf da yake masallaci yaje yana kwance gefen gadon shi yana chaten a wayar shi, daddy ne ya fara shiga sai islam da Ladidi mommy tana biye dasu,


"daddy sannu da zuwa..." su Khalifa suka fada atare,


"yawwa sannunku, lallai jiki yayi sauki, Allah ya kara lafiya"


"amin daddy"



Daya bayan daya suka rinka gaisawa dashi amma banda islam wacce ta koma gefe ta rakaɓe tana ta lissafa ƴan yatsunta, ko kallon wurin da take Khalifa bai yi ba sai ma hade rai da yayi dan baya son ayi masa ko maganarta ya koma kan gado ya kwanta, yana jin su daddy da ashraf suna ta shan hirarsu amma bai saka baki ba, suna nan tare dashi har karfe 9.30pm sannan suka tafi suka bar shi tare da ashraf wanda shine yau zai kwana a wurinsa, 


"Khalifa wai menene haka kayi? Kana ganin islam amma ko bi ta kanta baka yi ba a gaban iyayenta..." 


"to wai me zanyi mata? Ashraf na fahimci kwata kwata ba ka san irin zafin da nake ji a cikin zuciyata ba, da ka sani da baka yimin wannan maganar ba, wallahi so nake kawai a sallameni daga asibitin nan in yi musu bore, wannan ai yaudara ce da kuma zamba cikin aminci, sune fa suka ce min babu abinda yarinyar nan take yi sai gashi tana neman kasheni sannan ina ta tambayar su musabbabin ciwonta sun ki bani amsa... "


" kai dai na fahimceka mutumina, rashin cikar burinka shi yafi komai bata maka rai, na san da ace bukatarka ta biya to da babu mai ji.... "


" bani da lokacinka.... Rabuwa dai sai sai na rabu da islam ko ita kadaice autar mata "


Dariya ashraf yayi bai ce dashi komai ba ya wuce ya shiga toilet. 


Zaune daddy yake acikin bedroom dinsa bayan sun dawo daga asibiti yaci abinci, wani file ne agabansa sai kuma laptop din shi wacce yake aiki da ita, idanuwansa sanye da farin gilashin kara karfin ido, gefensa cup din shayi ne wanda duk daren duniya sai mommy ta tanadar masa shi, yana aiki yana dan kurbar shayin wanda ya wadatu da kayan kamshi musamman ma citta da kanunfari sai ciyawar lemon dan ga kamshinsu nan ya cika dakin, 


Mommy ce ta bude kofa ta shigo itama cikin shirin bacci sai kamshi ke tashi a jikinta sai dai fuskarta tana dauke da alamun damuwa kuma kallo daya daddyn yayi mata ya fahimci haka, 


"Hajjaju.... Fuskarki yau din nan tana dauke da wani yanayi wanda ban saba ganin shi ba a tare dake.... Zo ki fada min damuwar inji" 


Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta zauna kusa dashi, 


"yallabai.... An gudu ba a tsira ba, da alama sirrin da muka jima muna ɓoyewa game da islam lokaci ya kusa yi wanda za a tonoshi...." 


Dakatawa daddy yayi daga abinda yake yi ya rufe laptop din gaban shi ya zare gilashin dake idon shi ya kalli mommy shima annurin fuskarshi yana gushewa, 


" waye wannan wanda yake son bankado abinda muka tona rami muka haƙa muka binne tsawon shekara da shekaru?" 


"yallabai Khalifa ne..." 


"me ya kai Khalifa son jin wannan sirrin?" 


"bisa abinda ya faru tsakaninsa da islam, yace itace tayi masa sanadin wannan ciwon dake kansa wanda har ta kai shi ga kwanciya a asibiti dan haka yana son jin menene makasudin ciwonta....." 


"yaushe kuka yi haka dashi Hajjaju?" 


"dazu ne a asibiti yake fada min ni da shi..." 


"wacce amsa kika bashi?" 


"ban iya bashi kowacce irin amsa ba yallabai saboda wallahi tallahi hankalina yayi mutukar girgiza da tashi, ban taba tsammanin zai iya tambayar mu wannan maganar ba...." 


Tashi tsaye daddy yayi ya fara kai komo acikin dakin alamar tunani hannayensa goye a bayansa, 


" amma ya kike gani Hajjaju? Shin mu fada masa wannan sirrin ko kuma mu ci gaba da rufe kayanmu? "


" a gaskiya yallabai bana goyon bayan mun sanar dashi wannan maganar, babban kuskuren da zamu yi shine bayyana wannan sirrin, komai rintsi kada muyi gangancin bayyana shi.... "


" innalillahi wa inna ilaihir raji'un.... Matsaloli dai sun ki ƙarewa daga wannan sai wannan.... "


" shine nima abinda nake cewa yallabai, daga an samu an toshe can sai can ya ɓalle... Allah yayi mana maganin masifa "


" amin ya Allah"


Washe gari iya daddy ne kadai yaje wurin Khalifa ya kai masa breakfast lokacin ma shi ashraf ya tafi saboda zai je aiki, fuska babu yabo babu fallasa Khalifa ya gaida daddy wanda ya sha manyan kaya farar shadda mai kyau da tsada, 


"zuwa anjima suma su mommy din zasu zo, Allah ya baka lafiya" 


"ahhh babu komai ai daddy, da sun yi zaman su ma sun huta ai sun yi kokari, Allah ya saka da alkhairi" 


"amin, babu komai Khalifa ai an zama daya, kai yanzu matsayin ɗa kake a garemu" 


"hakane daddy, nagode Allah ya kara girma" 


"amin ya Allah, bari na karasa office" 


"to a dawo lafiya daddy" 


"Allah yasa nagode" 


Tashi zaune Khalifa yayi bayan fitar daddy yana kallon kwanukan da aka kawo masa abincin masu mutukar tsada da daukar hankali, shifa ajikinsa yake jin akwai wani abu da su mommy suke ɓoye masa kuma basa son ya sani wanda shi kuma ya zame masa dole sai yasan ko menene idan kuma ba haka ba to hakika ya gama zaman aure da islam. Tashi yayi ya fita daga cikin dakin saboda ya gaji da kwanciya shi kadai sannan gashi asibitin kowanne patient da dakinsa bare ka samu abokin hira, yayi game din har ya gaji, yayi chat din shima ya gaji kuma dama bai da abokin hira yanzu online tunda muslimat ta yaudare shi ta tafi offline,


Ɗan zazzagayawa yayi sannan ya dawo dakinsa ya zauna ya zuba abincin da daddy ya kawo masa yaci, yana ci suna yin video call da ashraf wanda ke office,


"inyehh..... A'a Kaga sirikin alhaji"


"ashraf wai dan Allah me yasa baka son ka ganni cikin kwanciyar hankali ne?"


"to yanzu kuma me nayi? Kai ba sirikin alhajin bane? Muma fa ka ganmu anan muna cin arzikinka"


"ka san me? Yarinyar nan Asiya na rasa gane wanne irin kalar rashin mutunci zanyi mata in huce ta dameni...."


"abinda zaka yi mata ka huce kawai shine kaima kayi mata irin yadda tayi maka, yanzu ka nuna ka hakura sai itama tayi zurfi sai ka dauke mata wuta ka watsa ta cikin kwandon shara kayi dumping dinta...."


"lallai ashe ma mun zama daya nida ita, ai bani da wannan lokacin nikuma yanzu..."


"malam a daukar fansa babu maganar rashin lokaci...."


"kai mashirmaci ne..."


"sannu mai hankali, wai kai ahakan hankalinka aka gani aka baka aure ko.... Nan kuwa basu san mugun dan tawaye bane kai"


"dan Allah kabar tuna min maganar auren nan wallahi idan na tuna gabana har faduwa yake yi"


Kai dai ka dauki komai da sauki "


" sai kayi kuma "


Tsawon kwanaki biyar Khalifa ya dauka a asibiti kafin aka sallameshi saboda yaji sauki raunukan da yaji duk sun kame kuma sun fara warkewa, kai tsaye gida daddy ya wuce dashi, part dinsu ya nufa yana zancen zuci" mutanen nan har yanzu basu ce min komai ba fa, koda yake bada shi daddy muka yi magana ba da mommy ne amma bari in basu kwana biyu in dai naji shiru basu ce min komai ba to ya zama dole shima in tunkareshi da maganar saboda nima ina son lafiya ta da rayuwa ta, sannan a gidan mu nine babba yanzu kowa dani ya dogara dan haka ba zan bari a salwantar min da rayuwa a banza ba "


Yana shiga part din masu tun daga falo ya fara cin karo da kayayyaki wanda islam tayo watsi dasu, ledar maganinshi ya ajiye sannan ya nufi upstairs, dakinsa ya bude nan ya ganta acikin tayi kaca kaca dashi sannan ga ruwa nan bokiti guda tana ta wanke bangon ɗakin tana watsawa ko ina, yana bude kofa tana kwaro masa ruwa, dama mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki, dama a kule yake da abinda tayi masa dan haka nan ya zuciya ya tunzura,


"ke menene haka? Wanne irin hauka ne wannan?"


"mijina.... Mijina ko ina yayi datti, bana son datti... Wankewa nake yi..."


"dalla can matsa mahaukaciyar banza, a gidan uban wa kika taba ganin anyi wannan haukan? Jibi yadda kika hautsina ko ina duk kika jika wuri, ke da idan haukanki ya tashi komai sai kin canja masa fasali...."


Hannu tasa ta rufe bakinta sai kuma ta fashe da kuka" mijina yana ta yimin fada.... Mijina sai fada yake yimin.... Mijina yana fada... " haka take ta fada cikin ƙaraji, 


Bai bi ta kanta ba yaje ya dauke bokitin ya mayar cikin bathroom wanda shi dai gashi nan ta wanke shi tass sai kamshi yake shine shima dakin aka je ana wankewa,


Kayan da zai saka ya dauka ya fita ya nufi dayan dakin shi din ma dai duk kanwar ja ce dan babu wani abu da yake a saiti, amma dai yafi dayan tunda shi ba ajika ba, wanka yayi ya shirya ya sauka kasa lokacin Ladidi har ta zo kawo musu abinci taje ta samu islam tana kuka tana cewa mijinta yana ta fada,


"dole mijinki yayi fada Islam kiduba kiga yadda kika yi da dakin nan, ba haka ake gyaran daki ba.... Ki daina irin wannan kinji"


"mijina yana yimin fada.... Mijina yana fada"


"ba zai sake yi miki ba amma kema sai kin daina wannan shirmen..."


Shi dai Khalifa fita yayi daga gidan ya nufi gidansu dan sama da kwana biyar kenan bai je ba, yana so yayiwa umma maganar da ke ransa kan abinda ya yanke tsakaninsa da islam amma abba ya hana shi acewar ashraf ya bari su gama da su mommy tukunna idan ya so idan matsalar bata warware ba sai yazo ya samu umman, ya dan jima suna hira dasu umman sannan ya fito, yana fitowa ya iske Asiya a ƙofar gida tana tsaye ita da kawata Hafiza suna jiransa, yasan duk yadda aka yi wani ne yaje ya sanar dasu yazo unguwar shiyasa suka sani,


Fuskar sa a daure suka gaisa, "ranka ya dade laifin me kawata tayi ne da take karbar wannan gashin haka, ai yanzu ya dace ace an yafe mata ko" Hafiza ta fada tana hade hannuwanta alamar ban hakuri,


"Hafiza kenan... Kawarki bata yimin laifin komai ba sannan nima kuma ba wai ina horata bane, tafi kowa sanin ni idan na wuce abu nayi gaba to fa bana waiwayowa sannan baya daga cikin ɗabi'ata maimaita abu, dan ko a makaranta ai daƙiki ke maimaita aji bare a soyayya...... Sannan nayi zaton ai yanzu dani da ita kowa ya karbi sakamakonsa ko? Na zaci ta manta da cewa tayi soyayya da wani mai dattin kwakwalwa wanda talauci ya cika, kamar yadda nima na manta da na taba yin soyayya da yar autar mata wacce ita kadai ce ta rage a doron kasa dan haka kowa ita yake ribibi.... " daga haka ya tafi ya bar su tsaye a wurin, tsaki Hafiza tayi tace,


" dama sai da na fada miki kar mu zo amma kika dage sai mun zo, Kinga irin ta ko... "


" gaskiya Khalifa bai da mutunci, magana fa ya farfada min Hafiza, koma menene naji kuma wallahi ba zan yi zuciya ba har sai na mallake shi"


"wai har yanzu baki karaya ba?"


"Sam... Ai wallahi kwarin gwiwa ma yasake bani"


"lallai abun nayi ne". 


Tsawon kwanaki biyu da sallamo Khalifa daga asibiti amma har lokacin bai ji kira ko alamunsa ba daga su mommy kuma kullum sai yayiwa Ashraf maganar zai je ya same su amma sai Ashraf yace wai ya kara basu lokaci, yau dai kawai so yake ayi ta ta kare dan ya gaji da wannan nuku nuƙun, 


Sai da ya tabbatar da cewa daddy ya dawo daga office sannan ya nufi part dinsa, suna zaune tare da mommy ya gama cin abincin dare, 


"Khalifa ina fata dai lafiya...." daddy ya fada bayan sun gaisa, 


"lafiya lau daddy, dama akan maganar islam ne, tun a asibiti nake tambayar mommy menene silar lalurarta amma mommy bata fada min ba, ni kuma ina son in sani saboda da farko baku sanar dani tana cizo ko duka ba, asali ma ban san cewa tana da lalura ba sai bayan an daura mana aure, daddy kuyi hakuri kar ku ce nayi rashin kunya amma a matsayina na mijinta dole wata rana zan so inje kusa da ita, to idan har irin haka tana faruwa ai wata rana zata iya halaka ni ko kuma tayi min lahanin da bazan amfani rayuwa ta ba, ku kuma a son ranku ta samu zuriya, ni kuma a gaskiya duk da ina da bukatar kudi amma rayuwata tafi komai muhimmanci.... Dan haka ina son sanin menene ciwon Islam da kuma tushensa? "


Shiru daddy yayi kamar mai yin nazari kafin daga bisani ya kalli Khalifa" Khalifa sanin abinda kake son sani bai da wani amfani atare da kai, dama na aura maka islam ne ba wai dan kai ka ganta kaji kana so ba dan haka kayi hakuri kaci gaba da zama da ita a haka nikuma zanci gaba da biyanka naira miliyan daya duk karshen wata, kawai bukatata ka bata kulawa sannan ka zamar mata uban ƴaƴa... "


" yallabai ko dai zamu sanar dashi wannan sirrin da muka jima muna binnewa shekara da shekaru... " mommy ta fada idanuwanta fal hawaye, 


" babu bukatar hakan hajiya Anisa... " 


Khalifa ji yayi maganganun su sun sake saka shi a cikin duhu kuma sun sake tabbatar masa da cewa lallai akwai wani abu babba wanda su daddy din basu shirya sanar dashi ba suke ɓoyewa, miƙewa tsaye yayi ya kallesu, 


" daddy kayi hakuri matsawar baku sanar dani wannan sirrin da kuke magana a kansa ba, zan sakar muku ƴarku Islam a daren yau sannan zan tattara nawa inawa in bar muku gidanku saboda kamar yadda na faɗa muku a baya rayuwata da lafiya ta sunfi komai muhimmanci a gareni " daga haka ya juya ya fara tafiya, yayi taku na uku yaji muryar daddy cikin wani irin yanayi wanda ba zai iya tantancewa ba yace, 


" Khalifa....! " tsam ya tsaya daga tafiyar da yake yi ba tare da ya juyo ba yana sauraron sautin shasshekar kukan da mommy keyi wanda baka jin motsin komai sai ƙarar shasshekar kukanta yayin da shima daddy ke zubar da hawaye marar sauti.......... Tirƙashi ƙaraƙaraƙaƙa wai shin wanne irin sirri ne su mommy da daddy ke ɓoyewa wanda basu son duniya ta ji ko ta sani? Shin zasu fadawa Khalifa ko kuwa boye masa zasu cigaba da yi? Idan sun fada masa zai iya cigaba da zama da Islam? Shin zaman zai ɗore ko kuwa zai rabu da ita Ashraf ya maye gurbinsa? Ina makomar su mommy yayinda sirrin da suka jima suna rufewa ya bankaɗu? Mahaifiyar Khalifa zata amince ko kuwa shima Khalifan zai binne musu sirrin ya boye shi? Dukka amsoshin wannan tambaya da ma cigaban labarin na cikin faty Islam tare da alƙalamin ummi shatu wanda zaku sameshi kan naira dari biyar 500 kacal✍🏻



Ku shigo cikin daular mu domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku, 


MASARAUTA tare da alƙalamin FATYMA XARAH 


FATY ~ISLAM daga alƙalamin UMMI A'ISHA 



 Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗaya kacal, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.





*_Ummi Shatu_*👌🏻