KAWA ZUCI

08

by @salmaahmadisah

*KAWA ZUCI*


*©SALMA AHMAD ISAH.*


*08*


*No.23, Rua Visconde de Piraja, Mooca, Sao Paulo, Brazil.*


Mooca wani ɗan ƙaramin yanki ne da yake cikin babban birnin Sao Paulo, unguwa ce ta masu ƙaramin ƙarfi, mafiya akasirin gidajen dake unguwar na haya ne, mazauna unguwar yawancinsu ma'aikata ne, sai kuma masu zuwa ci rani daga ƙauyuka ko ƙananan garuruwan dake ƙasar ta Brazil.



PEDRO POV.


_"Eu sinto que algo está errado Thiago!"_


_(Ina jin kamar akwai abin da yake shirin faruwa Thiago!)_


Kalaman suka fito tar ta cikin speaker'r ƙaramar plasma'n dake cikin ɗan ƙaramin falon gida mai lamba 23 dake unguwar Rua Visconde. A cikin Film ɗin Medusa, wanda aka haska shi a shekarar 2021 shi ake haskawa a cikin talabijin ɗin.


Zaune yake a kan carpet, yayin da yake operating laptop ɗinsa dake kan ƙaramin center table ɗin cikin ƙaramin falon, Juliana kuma na zaune a kan tilon kujerar dake falon, domin bayan kujerar ta zaman mutum uku babu wata kujera sai Bean Bag chairs guda ɗaya dake gefe.


Ita ce ke kallon ba shi ba, hankalinta na kan tv'n, amma kuma ta saka hannayenta biyu duka ta riƙe gashin kan Pedro tana ɗaure gashin nasa da ƙananun band. Ko ta waje idan ka kalli gidan za ka san cewa ba shi da girma.


Daga entry door falo za ka fara riska, falon ba shi da girma, domin bayan tv da kujerar dake falon babu komai ciki, daga can ɓangaren dama na falon akwai ƙofar kitchen, daga ɓangaren hagu kuma ƙofar ɗakin Pedro, ɗan gaba da ƙofar ɗakin nasa kuma akwai gajeren stairs, wandda yake manne da ƙofar ɗakin Juliana dake sama, kuma bayan ɗan ƙaramin ɗakin nata babu komai a saman.


A ƙalla yanzu sun haura shekaru biyar suna rayuwa a cikin gidan, dan tun bayan fitowar Pedro daga prison ya kama musu hayar gidan suka ci gaba da zama a ciki. Duk da unguwarsu cike take fal da mutane kala-kala, ba su damu da yin mu'amala da kowa ba, idan aka ɗauke Ibrahim maƙocinsu, wanda a yanzu ya zarce maƙoci sai dai su ƙira shi da ɗan uwa. Ba su damu da shiga rayuwar kowa ba, dan haka babu wanda yake shiga tasu. Hatta Juliana a makaranta ba ta da ƙawaye, ba ta kula kowa kamar yanda Pedro ya raineta tun tasowarta.


"Mts wannan Bruno ɗin haushi yake bani, shi bai san dai-dai ba ne?"


Ta tambaya duk da ta san wanda ta tambaya ɗin ba lallai ya iya bata amsa ba, dan tun da ta fara kallon ko sau ɗaya bai ɗaga kansa ya kalli tv'n ba, ita da ta kunna ita kaɗai take abinta.


"Waye Bruno?"


Ya dawo mata da tambaya yana ci gaba da abin da yake, hannunta ta janye daga cikin sumar kansa da ta ƙulle fiye da rabi, musamman ma ta gaban goshinsa, ta ɗora hannun nata a kan kafaɗarsa.


"Bruno! Wannan Bruno ɗin"


Ta nuna masa tvn.


"Oh na gane"


Ya ce ya gane ɗin ba tare da ya gane ba, dan bai kalli tvn ba ballantana ya san wanda take nufi, dukan kafaɗunsa ta yi tana faɗin.


"Hard Rock! Ta ya za ka gane ba tare da ka kalle shi ba?"


"Mm"


Kawai ya sake cewa, dan ba shi da lokacin wannan shirmen nata, abin da yake kan yi yanzu ya fi maganarta sau dubu amfani. Jin bai sake cewa komai ba yasa ta sunkuyar da kanta kusa da kafaɗarsa tana kallon abin da yake.


"Huh? Zuzurutun kuɗi haka? Wannan account ɗin waye?"


"Tsohon minister Mr Lucas?"


Dariya ta yi tana faɗin.


"Wannan matsolon da ko matarsa da 'ya'yansa ba sa iya cin kuɗinsa ne za a biya kuɗin aikin da za a mini da kuɗinsa?"


"Zan buɗe account ɗin duk wanda ya kama domin naima miki lafiya!"


Jin daɗin maganar yasa tasa ta rungume wuyansa ta baya tana lusmhe idonta a lokaci guda kuma tana murmushi.


"Na gode Fireball!"


Sunayen da take ƙiransa da su ke nan, "Fireball" ko "Hard Rock" ba ta cika ƙiransa da Pedro ko Badar ba, dan tace waɗannan biyun sun fi dacewa da shi.


"Ka yi sallah?"


Ta tambaya tana sakin wuyansa.


"Mm"


Ya sake amsa mata a taƙaice tare da gyaɗa kansa sau ɗaya.


"To..."


Kirrrrr! Doorbell tai ƙara alamun wani ya baƙunci gidan.


"Ibrahim ne, bari na je na buɗe!"


Ta miƙe tana ɗaukan karenta Caio, kamar yanda ta yi zato cewar Ibrahim ɗin ne tana buɗe ƙofar wani kyakkyawan farin bafulatani ya bayyana a bayan ƙofar.


"Good day Miomio!"


Ibrahim ɗin ya faɗa yana murmushi, martanin murmushin ta mayar masa tana sakin handle ɗin ƙofar sannan ta ja baya ta ba shi damar shigowa ciki.


"Good day Malam Iro!"


Tare suka yi dariya saboda sun saba gaisuwa irin haka, shi ya ce mata Miomio saboda wai tana kama da mage, ita kuma tace masa Malam Iro saboda ya gaya mata cewar haka ake ƙiransa a can ƙasarsu Nigeria. Takalmansa da ya shigo da su ya cire a nan entry, Juliana ta ɗauko masa slippers ɗin Pedro dake wurin ya saka, sannan suka shiga ciki tare.


"Ibrahim? Yanzu ka dawo?"


Pedro da har yanzu yake zaune a wurin da yake bai tashi ba ya tambaya sanda suka ƙaraso ciki, a gajiye Ibrahim ya zube kan Bean Bag chair ɗin dake falon yana furzar da numfashi.


"Ko gidana ban shiga ba, saboda wata yunwa da na kwaso kamar zan mutu!"


Ibrahim ya amsa.


"Julia ki kawo masa abincinsa"


"Toh"


Ta amsa tana aje karen dake hannunta, sannan ta nufi kitchen ɗin.


"Ki tabbatar kin wanke hannunki kafin ki taɓa abincin fa!"


Ya yi maganar da ɗan ƙarfi, dan zuwa lokacin ta shige kitchen ɗin.


"Ba zan wanke ba"


Ta ba shi amsa da ƙarfi ita ma.


"Me kan katako kawai"


Ya ƙarashe yana dawo da dubansa kan Ibrahim dake murmushin da ya kusa zama dariya.


"Dariyar kuma ta miye?"


Ibrahim ya rufe bakinsa yana nuna masa kansa, bai tuna da abin da ke kan nasa ba sai da ya sa hannunsa ya taɓa gashinsa, ya ji ƙulle-ƙullen da Julia ta masa kamar wata mace. Tsaki ya ja yana ciccire band ɗin.


"Wata rana sai na karya ƙafar yarinyar nan na watsata waje!"


"Ƙafarka ta karye ba ta Julia ba"


Juliana da ta fito daga kitchen ta faɗa tana nufosu hannunta riƙe da plate. Shi dai bai tankata ba har ta ƙaraso ta bawa Ibrahim abincinsa.


"Dare ya yi, ki je ki kwanta da wuri saboda makaranta kar ki makara"


"To Mr Right! Gobe Lahadi, ba Monday ba!"


"Oh haka aka yi ko? Duk da haka na san za ki je church, ki je ki kwanta da wuri kar ki makara!"


Bakinta ta gurmuɗa hagu da dama, sannan ta ɗauki Caio ta nufi stairs ɗin ɗakin nata, har ta kusa isa wurin ta dawo da baya, tana zuwa kusa da shi ta ja gashin kansa da ƙarfi sai da ya yi ƙara, sannan ta fita da gudu ta yi sama tana musu sai da safe shi da Ibrahim.


"Zan zo na sameki a ɗakin nan ne ai!"


Tana tsaye a ƙofar ɗakinta ta juya tai masa gwalo sannan ta banko ƙofar ɗakin.


"Mts ita komai wasa ne a wurinta!"


Ya juyo yana rufe system ɗinsa, kafin ya kalli Ibrahim da shi ma shi yake kallo.


"Pedro?"


Ibrahim dake cin abinci ya ƙira sunansa.


"Mm"


Ya amsa yana ci gaba da cire band ɗin da Juliana ta saka masa su.


"Har kullum ba zan daina gaya maka cewar wannan hanyar da ka zaɓa ma kanka a matsayin sana'a ba dai-dai ba ce, tun a baya sanin cewa wannan ita ce sana'arka bai sa na yada kai da Julia ba, a nan gaba ko da mutum za ka kashe ni mai taimaka maka ka binne gawarsa ne, domin taimakon da ka mini ba zan taɓa mantawa da shi ba a rayuwata...!"


Maimakon yace wani abu kawai sai ya yi murmushi mai sauti.


"Wani aikin ka samo mini?"


Bayan shuɗewar minti guda ya yi tambayar da ya riga ya san amsarta, duk bayan wasu lokuta Ibrahim cikin fafutukar naima masa aiki yake, amma a duk sanda zai kawo masa aikin ba ya kasa rejecting. Ya san niyyar Ibrahim a kansa kyakkyawa ce, amma ba ya jin zai hutar da shi ta hanyar yarda da yin wani aiki da ban da wanda ya saba yi, a ganinsa wannan ita ce hanya mafi sauƙi ta samun kuɗi, kuma hanya mafi sauƙi ta rama abin da aka masa. Abin da yake zaton dai shi ya tabbata, dan bayan wucewar wasu sakkani Ibrahim ɗin ya gyaɗa kansa, sannan ya fito da wata takarda dake aljihun jacket ɗinsa, ya aje a kan center table ɗin dake gaban Pedro.


"Aiki ne da na san za ka iya yinsa, domin aiki ne a ma'aikatar sadarwa, ka laƙanci iya sarrafa computer sosai, dan haka na san aikin ba zai maka wahala ba!"


Hannunsa ya miƙa ya ja takardar, santsin glass na center table ɗin ya taimaka ma takardar ta tafi zuwa gabansa, ɗagata ya yi sannan ya buɗe yana nazarin rubutun ciki.


"Not bad, amma ba zan iya yin aikin ba!"


"Wai sai zuwa yaushe za ka yarda ka daina sata Pedro? Ina jiye maka ranar da za ka sake shiga hannun 'yan sanda! Yau nake samun labarin sabuwar jami'ar da aka kawo sashin binciken laifukan sata na yanar gizo, yanda nake samun labari a kan jami'ar tana da ƙwarewar da za ta iya kama mai laifi duk wayonsa..."


"Luana Carla! Jami'a daga garin Rio de Janeiro, ba ta taɓa aure ba, amma tana da ɗa.... Hmm ta ƙware sosai a kan aikinta, ba ta taɓa faɗuwa a ko wani assignment ba, amma ina da sa ran za ta faɗi a wannan!"


Dalla-dalla yake tsaro jawabai a kan 'yar sandar, kamar mai karanta tsohuwar wasiƙar da ta daɗe da isowa gare shi. Ibrahim ya kasa riƙe mamakinsa, domin sukuti ya yi yana kallon Pedro ɗin.


"Badar?"


Ya kalle shi yana buɗe ƙwayar idonsa gray color a kansa.


"Tun sati biyu kafin a kawota Sao Paulo na san komai a kanta!"


Ibrahim ya kasa magana, domin lamarin ya fara girmar tunaninsa.


"Me Dr Lima ya ce maka game da matakin ciwon Juliana?"


Ya masa wannan tambayar domin ture waccan magana, tun da ya ga magana a kan lamarin ba shi da amfani kwata-kwata. Cak hannayensa dake wasa da takardar aikin da Ibrahim ya ba shi suka tsaya, bayan sakannin da ba su fi uku ba kuma sai ya saki murmushi mai ciwo.


"Dr Lima?... Dr Lima yace daga yau... Zuwa gobe... Zuwa jibi... A ko da yaushe, zan iya rasa Juliana!"


Ƙaran faɗuwar cokalin hannun Ibrahim yasa ya ɗaga idonsa da ya fara sauya kala ya kalle shi, har wani abu mai kama da ƙwalla na taruwa a cikinsa.


"Badar ya aka yi ciwon nan nata ya yi ƙamari har haka ba tare da an ɗauki mataki ba?"


Kansa ya ɗauke yana jinjina shi.


"Rashin kuɗin aikin da za a mata, amma na ɗauki alƙawarin a cikin satin nan za a mata aikin nan, zan samo kuɗi ko da ko za a ɓoyesu a ƙasan tekun Copa Cabana ne..."


A matsayinsa na wanda yake amsa sunan musulmi kamata ya yi ace ya naimi yardar mai kowa mai komai a wannan gaɓar, sai dai bai yi hakan ba, saboda ƙarancin tarbiyyar addini da ya taso da ita.


"Badar! Ni dai shawarar da zan baka ita ce, duk abin da za ka yi ka riƙa duba abin da zai biyo baya, ba na so ka tafka kuskure mafi girma a rayuwarka, wanda za ka zo kana da na sani a kansa!"


Bai ce komai ba, domin tun da ya tuna da batun mutuwar tata zuciyarsa ta fara masa ɗaci. Tunawa yake da irin rashin da ya yi a rayuwarsa, duk wasu wanda yake so kuma suke sonsa a rayuwa mutuwa suke su bar shi, sai dai a wannan karon ya ɗauki alwashin yaƙi da ƙaddara, domin ya faɗawa kansa cewar ba zai taɓa bari Juliana ta mutu ta bar shi ba, ya nisantata daga yunwa, ya nisantata da jahilci, ya nisantata daga duk wani abu da zai cutar da ita, shi ma wannan kamar sauran, haka zai yaƙe shi...


Sai dai duk abin da ƙaddara ta riga ta zana ɗan adam bai isa ya goge shi ba, duk yadda ya kai ga ƙarfin hali kuwa, ko ba ya so ko yana so dole abin da aka rubuta masa sai ya wanzu a kansa.


Har wajen karfe sha ɗaya Ibrahim yana gidan, bai tafi ba sai sha biyu saura. Kuma sai bayan da ya tafi ne ya je ya kulle ƙofar gidan, ya kashe duk wasu kayan wuya na falo da na kitchen. Kana ya zarce zuwa ɗakin Juliana, duk da ya tarar da ta yi bacci bai fasa shiga ɗakin ba. Zama ya yi a bakin gadonta yana kallonta, murmushi ya yi, musamman da ya tuna haɗuwarsa da ita ta biyu, lokacin da ya rasa komai, ita ma kuma ta rasa komai nata.


_"Na tabbata ba za ki tafi ki barni ba!"_


Ya faɗa a zuciyarsa, ya daɗe a ɗakin nata ba dan yana komai ba, sai dan kansa ya miƙe ya gyara mata kwanciya, sannan ya fita daga ɗakin ya shiga ɗakinsa da zummar kwana yana aiki, dan bai ga bacci ba matsawar bai haɗa kuɗaɗen da za ai mata aiki ba.



*Shekarata 2010.*


*Lencois town, Brazil.*


Kamar yanda ya saba attending lessons a duk yammacin ranar juma'a, haka yau ma ya shirya da wuri ya tafi, tun kafin closing time ya yi ya ƙagu ya dawo gida, domin sun yi waya da Papsi ya ce masa yau zai dawo.


Shi ne mutum na farko da ya fara fita daga class bayan an kaɗa ƙararrawar tashi. Tsabar saurin da yake har food-flask ɗinsa ya manta, sai Drake ne ya ɗauko masa ya biyo shi da shi.


"Wai wannan gaggawar da kake ta miye?"


Cewar Drake da ya lura da fara'ar da yake tun zuwansa school ɗin.


"Yau Papsi zai dawo, ya mini alƙawarin idan ya dawo zai kaimu Copa Cabana ni da Sophia!"


Hatta muryarsa ɗauke take da zallar nishaɗi, domin barinsa garin Lencois abu ne da bai cika faruwa ba. Idan zai iya tunawa ma rabonsa da ya bar garin tun shekaru biyar da suka wuce, Papsi ya ɗauke shi suka tafi Sao Paulo, a can suka yi celebrating babbar Sallah a lokacin, bayan wannan kuma ba ya jin ya ƙara barin garin.


"Ni ma zan so na je, amma Dad yace ayyuka sun masa yawa, ba lallai ya kaini ba!"


"Idan ka na so zan iya faɗawa Papsi ya faɗa ma Dad ɗinka cewar za ka tafi da mu!"


"Da gaske?"


Pedro ya jinjina masa kai.


"Eh"


"Ai ko na ji daɗi"


"Kar ka damu zan masa magana"


"Ok"


"Me ake a can?"


Pedro ya yi tambayar yana tsayawa, yayin da yake kallon wasu mutane tsaye a kan wani tudu, alamun mutanen ya nuna cewa ma'aikatan gwamnati ne, wasu na bincike a kan wasu takardu, wasu kuma na ta dube-duben garin nasu daga sama, dan a inda suke tsaye za su iya hango ko ina na garin, duk da garin a kwari da tudu yake.


"Oh waɗancan? Dad yace mini malaman kimiyya da fasaha ne, a kwanakin nan an yi hasashen za a iya samun girgizar ƙasa a Lencois, shi ne gwamnati ta turosu domin su bincika abin da zai iya janyo matsalar!"


Pedro ya taɓe bakinsa, dan bai ɗauki maganar serious ba, hasali ma shi ba wannan ne a gabansa ba, haɗuwarsa da Papsi a yau ta fi komai faranta masa. Dan haka ya watsar da batun girgizar ƙasa suka ci gaba da tafiya da Drake suna tattaunawa a kan abubuwan da za su yi idan sun je Copa Cabana, hatta irin wassanin da za su yi a bakin tekun sai da suka yi magana a kansu. Ba tare da sanin cewa su da zuwa Copa Cabana za a samu wani lokaci mai tsayi ba, wata tazara da za ta iya saka shu ya mance wannan farin cikin da yake ciki, domin abin da zai je ya tarar a gida shi ne silar tarwatsewar rayuwarsa gaba ɗaya, tun daga farko har zuwa tsaki.


A kan wata hanya da ta rabu gida uku suka yi sallama da Drake, ya wuce gida yana ta farin ciki abinsa, sai dai me? Tun daga nesa ya fara hangen kofar gidan, wai ko zai ga kotar Papsi ɗinsa, amma saɓanin motarsa sai ya ga Ambulance. Mamaki ya kama shi, to me Ambulance take a ƙofar gidansu? Me ya faru? Me aka yi? Me ake kan yi?.


Gaba ɗaya ma sai ya naimi farin cikin nasa ya rasa, son sanin abin da yake faruwa yasa ya nufi gidan da ɗan gudunsa, kafin ya ƙarasa mutum biyu sanye cikin kayan nurses na asibitin gwamnati suka fito daga gidan, a kan idonsa suka shiga Ambulance ɗin suka bar ƙofar gidan. Tun kafin ya shiga gida yake jiyowa wasu surutai a cikin gidan, saɓanin a baya da idan ya dawo da masifar Racquelita yake fara cin karo, yau bai ji ko bakinta ba.


To fa a nan ne jikinsa ya fara sanyi, domin wani zargi da ya fara ɗarsuwa a zuciyarsa. Sai yake ji kamar kar ya shiga gidan, juyawa ya yi, sai dai taku biyu kawai ya yi, ya ji an ƙira sunansa.


"Badar!"


Ko bai juya ba ya san wa ya ƙira shi, abokin aikin babansa ne, wanda suka saba zuwa gidan tare da shi, a hankali ya juyo yana riƙe da hannun jakar dake goye a bayansa, irin kallon da Marcel ke masa kawai yasa gabansa faɗuwa. Amma bai bari hakan ya yi tasiri a kansa ba, hannunsa yasa ya ture gashin kansa dake ƙokarin rufe masa ido.


"Kawu Marcel! Barka da yamma"


Marcel da ya yi tsaye yana kallonsa cike da tausayawa ya daure yace.


"Barka da yamma Badar, har kun taso ke nan?"


Ya gyaɗa kansa yana kallon ƙasa, dan gaba ɗaya ƙafafunsa rawa suke.


"Ka shigo ciki!"


Marcel ya kuma faɗi yana daga tsaye a ƙofar gidan, Pedro ya kasa amsawa, ya kasa motsawa, ya kasa komai.


"Badar!"


Ya ɗaga kansa ya kalli Marcel....


________________


_A ganinku me yake faruwa a cikin gidan Abdallah?_


_Wai me ya faru a rayuwar bayin Allahn nan guda biyu?_


# SalmaAhmadIsah

#MiniCandy

#Bahaɗejia

#ƘawaZuci