2.
by @billysfari
2
LATYFAH IMAM
NA NANA DISO
Saurin tsayar da maganar tayi ta hanyar faɗin " Babu wata mummunan macce and babu wata macce da shiga gaban mota zai gagareta, you're beautiful latyfah imam, tafaɗa tana ƙara maida hanƙali akan driving har suƙa karasa babbar ma'aikatar tasu, inda suke ajiye mota ta nufa ta ajiye sannan dukkan nin su suka fito, sai da latyfah ta dan tsaya ƙadan a baƙin motar zuciyar ta na duƙan dai dai, batasan me isaba har yanzu tana tsoron mutane gabanta yaƙan wadi idan zata shiga mutane riko hannunta da Nana tayi yasata saurin dawowa daga tunanin da takeyi tana bin bayanta tare da cire hannunta dake ciƙin nata, ko da suka tawo kofar nana ta rigata shigewa a hanƙali tatawo tana hango nana datayi shigar skirt da riga sai veil data naɗa ƙallon kanta taƙarayi atake taji ta muzanta saboda gani take kome zata saka bayayi mata, yadda taji ta bangaje mutum yasata saurin dago fuskarta tana ambatar sorry sir wallahi ban ƙula ba tafada tana yunƙurawa domin dakko masa littafin da ya wadi, narkakkun Idanuwansa ya zuba mata yana saƙar mata wani kayataccen murmushi, cikin girmamawa yace " Kinyi kyau kanwata." Sai kuma taga ya huce ƙamar bama shine yayi maganar ba kamar daga baƙin waninsa tafito. Bugun ƙirjinta ne yaƙaru sosai kamar fa kalmar tayi kyau taji? Anyway bazai huce ciƙin tunaninta data sabayi ba kullum but how possible ma wani zaice tayi kyau, ma'aikatan gurin tafara gaisawa kamin ta isa offices dinta, hy nawal tafada tana mai kallon abokiyar aikin nata. Cikin yatsine fuska tace " giwa har ƙin iso," repeating kalmar tayi cikin ranta tana murmushi tashige ciƙin offices din, sai data fara ajiye jaƙarta kamin ma taƙaita da ajiye littafan daƙe hannunta, zama tayi sannan tashiga aiki acikin system dinta, a hankali a hankali take saka tissue tana goge fusƙarta saboda oil face ce da'ita, wasu document da zatayi submitting yau ta karasa sannan tatashi ta nufi offices din Abdulkarim mai lema wanda daga gurinsa zata samu wannan signing din ƙamin takaiwa shugaban nasu. Knocking ta tsaya yi ko data ƙarasa kofar offices din deep breath taja tana kara knocking daga can akace mata yes come In. A hankali ta buɗe kofar tana murdawa, idanunta tazaro waje ganin nawal ƙancinyar mijin da alama kissing din junansu suƙeyi duba da jambaƙin baƙinta ya bayyana aƙan lips din mijin nata, wani zafi taji idonta yana alamun ciccikowa. Cikin nuna rashin damuwa yace " hy what ? Yafada yana nuni da hannunsa." Dakyar ta iya jan numfashinta tace " Sir inason ayimun signing ne." Alama yayi mata da hannunsa tazo, nawal ƙam sai narke masa takeyi yana murmushi da ko ita matarsa bata taɓa gani ba, ko da yaƙarbi document din sai yafara magana da nawal din yana murmushi " Hy baby kinada kyau, kalli hancinki idonki and baƙinki kalli yadda kike fara ohh my good baby karki bari kiyi katuwa fa maza basusan katuwar macce to tayaya zan doraki aƙan cinyata idan kikayi katuwa? My baby no pimples i love you yabata wani light kiss nawal najin duniyarta asama.
Yadda gabanta ke faduwa sai kazata zuciyartace zata fito, idonta ya cicciko da kwallah she is trying to control her self tana koƙartawa dan ƙar hawayen nata su zubo, wannan wanne ƙalar jarabawace agabanta? Mijinta da wata suna making love, a hanƙali ta furta Astagfirullah tana mai karasowa dan dauƙar littafin tare da faɗin " thank you sir." Tafita da sauri jiƙin kwanar offices dinsa ta tsaya tashiga raira kuka ahanƙali kusan mintuna 30 ta ɗauka tanayi kamin ta mike kada wani yabiyo hanyar, sai data koma toilet ta wanke fusƙarta kamin kuma taƙara dawowa offices din oga tahir ko datayi knocking take aka bata izini, tana shigowa ya ajiye wayar yana zuba mata idanu take zuciyarta tafara bugawa a hanƙali yanajin tausayin yarinyar har ciƙin ransa, dan kaf ma aikatan shiƙadai yasan cewa matar abdulkarim ce, uhmm kanwata yafaɗa yana ajiye pen din dake hannunsa, "why are you crying?." " bakomai sir kaina ke ɗan ciwo." Uhmm yace dan yasan dayan biyu ne ko abdul ya wulakanta ta kokuma taganshi da wata maccen dan baitaba ganin mai son mata irin yaron ba shi tausayima yake basa dan mahaifinsa da sauran ƴan uwansa ba haka suke ba Sudai yaran hajiya fatima ne tarbiyarsu daban data mai lema, ga innocent yarinya kyakywa anbashi. A hankali ya ƙarbi document din yanabi, zauna mana yafaɗa yana nuna mata kujera, murmushin da bata shiryaba tayi dan kowanne cikin manyan baya barinta ta zauna wai kada kibarta ta ƙarya musu kujera shiƙam sir tahir yanada kirki, tsinkayar muryarsa tayi yana faɗin " Idan ana ciwon ƙai magani akesha ba kuka ba, yakarasa maganar yana mai miko mata maganin da robar faro na ruwa, kunya sosai taji kamin taƙarba tayi masa godiya. A hankali yabi duk document din yana fara'a a fusƙarsa " Mashaa Allah good work, gaskiya kinada basira ai koni bazan iya wannan bayanin ba, shiyasa alhaji mai lema yace ko ɗansa sai ƙin kayar indai gurin ilimine." Taƙe ranta ya sosa dan batason ma taji sunansa. " Anyway yanzu akwai course da za'ayi kina daga ciƙin wanda zasuje Canada I hope babu matsala." Fara'arta ce ta bayyana afusƙarta tana masa godiya, " Why not ki koma kiyi phd dinki? Yafada yana hada bayanan nata, " Sir hakan ma ya'isa." Tafada " No try kikoma latyfah imam wannan zai kara baki da mammaki sosai. " okay sir thank you zan iya tafiya." Daga mata kai yayi sannan tafita.
Wannan ne tsaƙin dataja na babu adadi a cikin offices din kawar tata, kai ina wallahi latyfah imam bata dace da wannan dan iskanba? A'uzubillahi tafada tana tuna yadda taganshi a offices din da nawal, sallamar kawartata ce yasata saurin jiyowa tana faɗin " yanzu nake kokarin zuwa offices dinki ai." Uhm nana tace tana mai kauda ƙanta kartaga hawayen da takeyi." Sai da latyfah ta zauna tana ɗan mai da numfashin tafiyar datayi dan babu laifi da tazara sosai tsakaninsu da bangaren. Cikin bugawar zuciya tace Nana? Kuka ? Ke? Tama rasa me zatace tayi saurin mikewa tana zama a gefen kujerar ta, haba nana kukafa kikeyi, menene? Kokuma kina tayani baƙin ciki ne." Dagowa tayi taƙalli kawar tata tace " wallahi latyfah baki cancanci dan iska irin abdul ba kinsan fa babu kay... sai tayi saurin tsayawa tana kallonta kartaje ta tarwatsa zuciyar kawartata, " Ko baki karasa ba nagani tafada tana danne zuciyarta." " sai da muka baki shawara akan karki amince da wannan auren baki cancanci..." " Haba nana me isa ke da iyami kunkasa ganewa ne, wallahi ko mahaukaci Alhaji mai lema yabani zan zauna dashi, shekararsa nawa yana hidima dani? Yabani ilimi yabani abinci hatta da gidan da muke zaune nida yan uwana sabodani yabayar yanunamin gata tundaga primary har jami'a har matakin da nake ƙai Nana shi yabani shine sila dan ya nuna in zauna da ɗansa shine aibu? Zan iya nasan Allah baya jarrabar bawa da abunda bazai iyaba." Hakane nana tafada tanaso su share zancen, wayarta ce tayi ringing a hanƙali Nana ta daga tana fadada fara'arta, " Yayana tafada cike da farin ciki. " Nana ya ambata shima a hanƙali ƙin kira mun fita da sadiya. Gaisawa suka shigayi tana faɗin yaushe zasu dawo ne? Nan yasanar mata sai sadiya ta haihu yanzu cikin ya tsufa, sosai suka zanta kamar yadda yakeyiwa ƙannin nasa harma wanda ba daƙinsu daya ba wannan ka'idar mahaifinsu ce. Cikin nuna kosawa da hirar tata tunda duk akan abunda anty tayiwa mom dinsu ne shikuma bayaso yaji shiyasa yayi saurin ƙatseta da faɗin " Nana akwai abunda kuke bukata dai." Murmushi tayi tace " Yayana.. " uhm danAllah inason sabuwar mota. " Nana yaushe aka camza miki taki abiy fa yasanar mini." " DanAllah yaya kaidai zangayamaka daga baya nidai inaso asiyamin." " Babu damuwa ki saurareni cikin satinnan." " Allah yasaka a aljannah ga latyfah zaku gaisa." Aransa yace kuma dai yana fadin " okay." Itama cikin girmamawa tace " yayanmu ina kwana ya antynmu." " LATYFAH IMAM ya iyami and kowa nagidan ya offices din, ina maigidan ?" " Duk suna lpya." " MashaaAllah agidasu yafada yana katse wayar." Har cikin ranta taji daɗin gaisawar nan tasu ɗan ita batasan ɗadi wa ko kani na tunda baƙaramin ƴan ubanci akeyi da ita agidan ba tunda ita daya mamanta ta haifa ta rasu. " yanzu nana saboda Allah wacce kuma mota? DanAllah kudaina bannar kudi haka haba Nana." " Uhm tace tana kallon latyfah kawai saboda batasan wanene mahaifinta ba inadai gurin arzukine komai zai iyayimusu dalilin dayasa batace abiy yasiya mata ba tasan anty itama sai tasaka maryam tace abata shiyasa tace yayanta zata gayawa duk da tasan mahaifin nata sai yayi fada akan rashin gayamasa dan yadda yake saƙar musu kudi kadai sai ya lalatasu amma kokarin mahaifiyarsu gurin kula da tarbiyarsu yasasu nutsuwa sosai.
Yauma agajiye ta dawo gida order na abincin tayi biryani da salad da kaza, tatashi kuma ta hada lemo daƙanta dan ita batashan mai gas kwatakwata, yadda yashigo gidan batare da sallama ba yasata ƙin daga kai ta kallesa dan ko sannu da zuwa batajin zata iya gayamasa kamar yadda ta saba, tsaki yaja yana tofar da miyau da yazama dabi'ar sa yanzu, " ke bakutu nabaki 10mint kishirya akwai inda zamuje yanzu." Banza tayi dashi sai kuma tayi saurin tashi batasaniba ko mahaifinsa ke nemanta dan haka sai ta shirya cikin white abaya da white bag da takalmi, ko da yashiga shima a gaggauce yayi wanka kamin kuma yafito yashirya a tsadadden yadinsa, ganinta ba laifi yace zuje, wannan shine first time da zatashiga motarsa, tsaki yaja ganin yadda tayi wani gwan gwan agaban motar daga nisa ya ajiye kotar suka shiga restaurant din, maza da mata tagani akallah sunyi 20 kowanne yazuba shiga ta alfarma kana ganinsu kasan yaran wasu ne, gaba tayi tana kokarin jan seat ta zauna wani daga cikinsu da ake kira da amir ne yace " Mama nan gurin samarine please mun riga mun ari gurin kuma bakya ganin kujerar nan tayi miki kadan? Gaskiya kirage kibarki you're ugly ga kuma kiba yafada ko ajiƙinsa." Daya yarinyar kuma tace " Kishafa mai mana wannan baƙin naki is too much nan suka saka dariya, abdul da yakaraso gurin yanzu yace " Ke magana fa ake miki nan ba gurin manya baniba mama yafada yana dariya suna tayashi, daya daga cikinsu ne yace " abdul is that not your wife." Duburburcewa abdull yayi yace " Are you insulting me? My wife? This elephant....
ANYA ABDUL YANADA IMANI? ANYA JAHILCI BAI NANESHI BA?
KISANI KINADA KYAU KINADA KYAU KE SARAUNIYA CE A DUK YADDA KIKE