HALIMATUS'SADIYAH

14

by @meenamajeed

Haka suka tsaya har sai da yamma sannan ya falka. Ko da ya falka ya iske su a dakin ba wanda ya tankamawa.

Umma ta dubai shi ta tambaye shi ya jikin na sa. Ta ido ya bata amsa sannan ta ce "Allah kara sauki."

Har dare bai tankawa kowa ba. Dan har yanzu da oxgen a hancin sa.

Bayan dare ya ja Asif ya ce wa Umma ta koma gida zai kwana da shi.

Umma ta ce "A'a bari dai in tsaya."

Zai yi magana sai ya kyale chan kuma sai ta ce "Shi kenan kuna bukatar wani abu?

Ya amsa da "A'a."

Umma ta ce "Okay, Aysha tashi mu tafi."

Aysha ta mike suka masu sallama suka koma ita da Aysha da buba dan Abdullahi ya riga da ya koma gida.

Umma na tafiya da minti 10 Asim ya tambayi wayar sa.

Asif ya tambaye shi mi zai yi da ita kai da baka da lfy.

Asim yayi murmishi ya ce "Small headache ne."

Asif yace kuma ya kwatar da kai har da oxygen."

Asim ya ce "Ka miko min waya ta."

Asif ya ce "Wa za ka kira, kai da baka da lfy."

Asim ya roke shi da Allah. Tuna da maganar Dr hakan ya sa ya mika mashi wayar ya na tambayar shi wa xa ka kira?

Asim ya amshi wayar yayi scrowling har wurin number Halimatu sannnan yayi dailing wayar a kashe. Ya kara kira wayar a kashe.

Asif ya tambaye shi "Wayar wa ce ce a kashe?

Asim ya aje wayar bai ce mashi komi ba ya lumshe idon sa ya budai sannan ya tambayi Asif mi Dr y ace.

Asif ya ce "You got heart attack na san kuma sbd waccen yarinyar ce ni har na fara jin haushin ta mtsww."

Asim ya dubai shi ya ce "Asif ke nan soyayar da ka ke yi ba soyayay ba ce face kanzan kuraige, ba kasan mi cece soyaya ba, ba kasan zafin ta ba balle dadin ta."

Asif yayi karamin tsaki ya ce "Zai fi ka ma baiwa zuciyar ka hakuri ka san abin da ba zaka samu ba ka wani dage sai ka sota. Dr nawfal cewa yayi dazun na da ba akawo ka da wuri ba da at any moment zuciyar ka zata iya bugawa, sai ka cigaba da son ta tin da daman baka damu da niba baka damu da Umma you only love her. Ko ajinkin ka ba ka damu da halin da zamu shiga ba ka cigaba har ta kai da sai ka rasa ranka. Ya ja tsaki ya kwanta saman kujer.

Asim bai ce mashi komi ba dan shi kan sa bai san wata irin soyayar da yake wa Halimatu ba gashi da ya tuno da abinda ta mashi jiya sai ya ji zuciyar sa ta kara raunana.

Allulan baccin da a ka mashi ita ta sa shi bacci da ba dan haka ba yau ma da ya kwanta ya na tunanin

A bangaren Halimatu da safe ta je gidan aikin ta ta dawo da yamma ta wuce islamiya.

Sai da ta dawo islamiya ta tuna abinda ta yi mashi jiya duk sai ta ji ba dadi musanman yanda ya tsaya jiran ta. Ta yi kudirta da ya zo yau zata bashi hakuri sai dai tin da ta gama sallah Magriba ta ke jiran shi amma yau shiru har a ka gama isha'I bai zo ba har su malan Yakubu suka dawo gida bai zo ba kuma bai naimai ta ba hakan nan ta ji gaban ta yana faduwa tabbass ta bata mashi rai abin da ta mashi bata kyauta ba. Ta kira shi ko kar ta kira haka ta tsaya tana contemplating har wayar ta mutu kasancewa tin jiya da dare da suka dauke huta ba su maido ba har dare. Haka ta kwanta da guiltiness.

Washe gari bayan ta gama abin da ta ke ta wuce gidan Mummy dan yi mata aiki.

Ta na cikin mopping parlourn. Mummy da ke zaune saman kujera Yasmin kuma na kwance saman kujera. Mummy ta ce "Yasmin kira min harira."

Yasmin ta kalli Mummy ta ce "Mummy Halimatu ta kirata ba na." Ta ida maganar ta na hararen halimatu.

Mummy ta ce "Bi ki ga aiki ta ke ba."

Yasimin tayi gatsunai sannan ta kwala wa harira kira. Harira da ke kitchen ta amsa. Ta karaso cikin parlourn.

Mummy ta ce "Harira an dora abinci?

Harira ta ce "Kayan miyan ne na ke gyarawa."

Mummy ta ce "Ayi maza a dora ina so a gama abincin da wuri dan in kai asibiti."

Harira ta amsa da "Toh hajiya." Ta wuce. bayan wucewar ta Yasmin ta ce "Mummy waye bai lafiya?

Mummy ta amsa ta "Asim ne."

Halimatu da ke mopping da sauri ta kalli Mummy. Ganin hararen da yasmin ke mata hakan ya sa ta mai da kanta wurin mopping duk da hankalin ta na wurin su.

Mummy ta ce "Jiya a ka kwantar da shi."

Yasmin ta tambaya "Mike damun sa? Abin da bai ta faruwa ba.

Mummy ta ce "Ke ma kin gani sai na je in ji mike damun sa dan tinda suke basu taba ciwon da ya kwantar da su a asibiti ba."

Yasmin ta ce "Mummy har da Asif din?

Mummy ta ce "Ban sani ba ta dai ce min Asim bai lfy suna asibiti, toh kin sa kunsan kullun tare suke ciwo."

Halimatu tin da ta ji Asim bai da lafiya taji ta kasa samun sukuni. Ta dau bucket din mopping din zata wuce kitchen Mummy ta ce mata "Halimatu maza ki gama ki kamawa Harira."

Halimatu ta amsa mata da toh sannan ta wuce kitchen din ta gogge shi ta hada wani ruwan na gogege ta goge gidan ta koma wurin Harira suka gama dafa abinci Mummy ta kasafta ta sa wa harira nata ta ba wa Halimatu sanan ta sa wa masu gadi na su dan duk wanda ke girki shi ke sa wa masu gadi sai dai kowa mace tayi girkin ta ranar girkin mutun shi zai ba mai gadi da mai gida.

Ta zuba na yan asibiti da kuma na gida. Halimatu ta juye abincin cikin ledar sannan ta yi wa Mummy sallama.

Mummy ta ce masu su jira su fita sai a sauke kowa a babban titi. Yasmin da Ulfah ba su so haka ba. sai Harare su suke har suka shiga motar.

Mummy na tuki Yasmin a gaba ulfah kuma da su Harira a baya. A ka fara sauke harira kasan ce wa ba hanyar su daya ba daga nan kuma suka aje ta ta gangara a kasa ba tare da ta a hau abin hawa ba.

Ta na isa gida ta kaiwa Umma abincin daman abincin rana ba su fiye yin sa ba, cinikin da yayi da rana da shi ake tuwo ko kuma danbun masara ko sindirke duk dai abin da ya samu.

Umma ta ce "Ta dauko plate ta iba sai ta aje wa su huzaifah sauran."

Ta ce "A'a Umma ku ci ni na koshi."

Umma ta ce "Toh shi ke nan."

Ta koma cikin daki ta duba wayar ta ta iske ta yi charji ta kunna ta, zata kira shi sai kuma ta fasa dan ta san yana asibiti kila wani dan gidan su ya dauka sai ta mashi test: "Aslm ina wuni ya jikin ka, Allah tashi kafadun ka."

Ta tura mashi ta aje wayar ta kwanta ta na tunanin mi ya samai shi fatan ta kar ta kasan ce sanadin rishin lafiyar shi.

Umma kuma ta lura da yanayin ta sai ta kyale ta har dai dare bata da walwala. Yauma Asim bai zo ba Umma ta tambaye ta lfy ba dai ta mashi wulakanci ba.

Ta ce mata "A'a bai lafiya."

Umma ta ce "Toh ay na san halinki."

Huzaifah ya ce "Umma ina so in je dubo sa."

Umma ta ce "A'a bari dai in ya zo sai ka mashi ya jiki."

Asee ta ce "Toh a kira shi a waya sai mu masa ya jiki."

Halimatu ta ce "Ba za ayi ba." Ta ja tsaki. Umma ta bi ta da uhmm.

Su na zaune ta na game da wayar ta dan ko whatsapp bata yi, da mai wayar kadai suke chart dan ba kowa ya san ta yi waya ba sai yayyan ta.

Message din shi ya shigo "Lfy amira. Ykk ya su umma, jiki na da sauki. Kar ki kwanta da wuri ina so in ji muryar ki in dan yan dubiya suka tafi."

Ta na gama karanata message din shi murmishi ya subuce mata, ta yi saurin kallon su Umma ganin ba ita suke kallo ba ta sauke ajiyar zuciya.

10:30pm

Kowa ya kwanta ita kuma ta na nan ta na jiran kiran wayar Asim har nusy ita ma ta gama waya da na ta saurayin kasancewa shi ba gari daya suke ba. Ta tambaye ta ba zaki kwanta ba.

Ta ce "Yau ban jin bacci.

Ta ce "Ki tashi kiyi sallah ki dau qur'ani sai baccin ya zo."

Halima ta ce "Bana jin dadin jiki na ne".

Nusaiba ta ce "Awwnn, masoyi bai da lfy ita ma masoyiya bata da lfy."

Ta mata tsaki ta kunna wayar ta. Nusaiba tayi dariya ta mike ta na cewa sai da safe zafin dakin nan ba da ni ba. Ta wuce.

A bangaren su Aism Mummy da ta karaso bata iske Umma ba Sai Asif da Safna. Suka gashe ta shima idon sa biyu ya gaishe ta ta mashi ya jiki. Sanan ta tambayi Umma. Safna ta ce ta ta na kan hanya. Yasmin da ulfah suma suka mashi ya jiki.

Mummy ta ce "Nama dauka ku biyu ne baku lfy ganin tare ku ke ciwo."

Murmishi Asif yayi kafin ya ce "A'a wanan karan shi kadai yake abin sa."

Mummy ta ce "Fatan kar in ya tashi kai ma ka kwanta."

Asif ya ce "Ni lfyt qlau."

Mummy ta ce "Toh Allah ya bashi lfy, mike damun sa?

"High fever ne."

Mummy ta maimaita sannan ta ce "Ita kadai ba wani ciwon??

Ya ce "Result din bai fito ba amma ya ma ji sauki nasan zuwa gobe ko jibi za su sallamai mu."

Mummy ta ce "Allah yarda."

Haka suka zauna suna fira har Mummy ta karaso ita ma hajiya shafa ta zo duba shi da sauran yan'uwa.

Sai bayan isha'I ya ga message din ta kasancewa wayar shi a kashe sai yanzu da ya kunnan ta. Ya ji dadin ganin message din ta ya Maida mata sannan ya aje wayar ya so ya kira sai dai Umma na dakin.

Bayan da za a yi ya iya kiran ta. jira kwai Umma ta tafi ya kira ta amma umma ba ta tafi har sai 11 sannan ta masu sallama suka tafi ita da buba.

Asif na fita raka su ya jawo wayar shi ya yi dailing number wayar halima gab da zata kaste ta dauka dan har ta gaji da jiran sa ta fara gyengyadi. Fara'a dauke a fuskarta ta dau kiran ta masahi sallama.

Jin muryata duk wani zafi da yake ji a zuciyarsa ya shafe. Haka shima fara'a dauke a fuskarsa ya amsa sallamar. A tare suka tambayi junan su ya ka ke/yakike.

Suka amsa a tare. Sai ta tambaye shi ya jikin na sa.

Ya ce "Na ji sauki ina jin muryar ki."

Ta ce "Allah ba ka lfy."

Ya amsa da Amin. sai ya ce "Da zu I can't call you, sbd dakin akwai mutane. Ba zan samu nitsuwar jin muryar ki ba."

Murmishi kawai tayi.

Ya tambaya yaushe za ki zo duba ni.

Ta waro ido ta ce "A'a."

Zai yi Magana Asif yayi sallama. Ya dubai shi sai ya tambaye ta miyasa.

Asif ya karaso ciki yana cewa "Ahh ka samu sauki har ka na iya waya." Ya zaunaa sannn ya tambayi "Da wa kake waya?

Bai amsa shi ba.

A chan bangaren Halimatu ta ce "Ni a suwa in zo dubaka."

Ya ce "Ke a su matata."

Asif ya dubai shi da mamaki, ya ambaci sunan sa.

Halimatu ta yi shiru ba ta ce mashi komi ba.

Asif ya karaso wurin ya amshe wayar yayi sallama. Ba zakata ba yarda bashi yay magan ba sai dai yin sallama da yayi hakan ya sa ta san Asif ne domin hatta muryar su iri daya ce. Ta amsa sallama.

Ya ce "Mai sunan Umma ykk?

Ta amsa da lfyl yamai jiki?

Ya ce "Jiki da sauki sai dai likita ya ce ya dai na ba kan shi wahala amma kin san halin sa bai jin Magana bari ki ga."

Sai ya katse wayar ya kira video call kamar kar ta daga sai ta kunna fitala charji ta dau video call din duk da kafin ta dauka sai da su ka yi sa'insa shi da Asim a kan dan mi zai amshe wayar.

Ya ce "Yauwa mai sunan Umma bari ki gan shi. Ya kara camera wurin Asim, asim Harare shi kawai yake dan bai so ya ga halimatu ta gan shi a wannan halin. Ya ce "Kin gani mai suna Umma yana dauke da oxygen amma da karfin hali sai yayi Magana wanda hakan yana rage masa energy kuma yana bukatar energy.

Halimatu tin da taga oxygen a hancin shi ga wa innan nakurorin asibiti zuciyarta ta mata nauyi lokaci daya ta fara fargarba kar dai wani abu ya samai shi sbd wulakancin da ta mashi.

Asif ya ce "Dan Allah mai suna Umma yi mashi mgn wata kila ya ji ta ki tin da ni bai daukar ta wa."

Halimatu da muryarta na rawa ta ambaci sunan sa wato ranka yadadai.

Asim ya katse ta "Kar ki biye mashi na ji sauki wannan robar ita ke kara sani weak su bar ni na shaki natural air wannan ba abin da ta ke karawa mutun."

Ta ce "A'a ka kwanta, mara lfy bacci yake bukata..

Ya katse ta "Ay na warke tin da ga ki a kusa." Kunya ta dauke ta da sauri ta ce mashi sai da safe ta katse wayar.

Ta dafe Kanta da hannunwanta biyu ta na fadan "Na shiga uku halimatu saboda ke ya kwanta asibiti har da oxygen, yanzu in ya mutu ke ce sila, A'a, Ya Allah ka bashi lfy kar in zama sanadiyar mutuwan sa." Ta na wana tunanain har ta yi bacci.

A bangaren su Asim tana kashe wayar Asim ya ce ba nason abin nan ina Ruwan ka da ni lfyl ka ce ko ta wa, na tabbata tana chan ta damu.

Asif ya ce "Mi zai sa ta ta damu bayan ba ta san ka ay mai son ka shi ke damuwa da kai."

Ya ce "Na ji kar ka kara min haka."

Asif ya ce "Wait daga kayi waya da ita ka samu zeal din Magana ko kuma rainin wayo ne dazu kayi shiru ka kyale kowa."

Ya ce "Ban sani ba."

Asif ya ce "Ni dai shawara nake ba ka tin wuri ka rabu da ita dan ba auren ta zaka yi ba har da cewa matata." Ya garasa maganat cikin gatse.

Asim ya ce "Ba sai ka hana ba mtsww. "

Asif yayi dariya ya koma kujera yana rera masa baitikan soyaya.

😂😂😂😂😂😂😂

Readers ku taya Asif da wakar soyayya. Kun san yanda biyulle suke da konawa junan su rai. Ko da ya ke masu twins su za su iya ba mu lbr.

Asim na HALIMATUS'SADIYAH(sakayya).

Na san za ku ta tunanin ta ya zai kasance sakayya???🤔

Ku cigaba da karanratawa domin har yanzu soman tafi mu ke🤗

Kar ku manta kuyi voting, comment and share👍

Much love💋❤️

Meenamajeed🥀