15
by @meenamajeed
Assalamu alaikum ina masu yin sana'ar hanu ta gida har ma da ta shago. Ina masu so su habaka kasuwan su daga karamin mataki zuwa babban mataki
Ina masu son sun samu customers, na gaske ba masu ce wa sai ba ji k.
Kwantar da hankalin k nisa ta zo kusa kina daga gida za ki iya tallata kayan k wurare wurare da wayar hannun ki, ki na zaune batare da kin ba kan ki wahala ba zaki tallata kayan ki cikin sauki kuma za ki samu customers. Har ma ki samu masu wholeseler da kan k
Mun kirkiri class mai su na enterprenuashin sales bosters. Duk mai ra ayin shiga ko kuma son karin bayani k tuntubai su ta ***
Ma su son a tallata masu kayan da su ke saidawa a media wato sponsor add su ma suna iya min mgn ta number ta 081070456601.
Washe gari Umma ta karaso asibitin ita da Buba. Suna zaune Dr Nawfal shi da abokin aikin sa Al-hussain, suka kara duba shi duk da Dr Nawfal yana mamakin ganin heart beat din sa ya dawo normal bakamar jiya da ba.
Ya cire mashi robar oxygen daga hancin sa da sauran nakura sai aka bar mai drip kadai.
Umma ta ce "Alhamdullahi, ya jikin na sa?
Dr nawfal ya amsa "Da sauki tin da har an cire masa oxygen sai dai what make me marvelled taya heart beat din sa ya daidaita in suddened? Any where thank to Almighty.
Daga Asim har Asif suka dubi junan su musanman Asif da yayiwa Umma karya.
Umma ta ce "Dr mike damun sa? Ni daman na san high fever ba zata mashi ila haka ba.
Dr nawfal ya dubi Asif Asif ya mashi nuni da kar ya fadi mata.
Umma ta ce tambayar ka fa nake? What wrong with him?
Dr nawfal ya ce "Umma high fever ce kamar yanda na ce."
Umma ta ce "Kar ku dauke ni jahila mi ne gamin fever da zuciya." Ta mike zata dau magungunan shi.
Da sauri Asif ya dagatar da ita yana ce wa "Umma ya ma samu sauki zuwa ma gobe ko yau da anjima za a sallamai mu ko ba haka ba?
Dr al Hussain yace "Eh da drip din nan ya kare."
Umma ta Harari Asif ta warce maganin daga hanun Asif ta koma kujera tare da jawo wayar ta.
Dr nawfal ya ce "Umma no need to browse, Asim ya samu little heart attack amma yanzu ya samu daidai his paulse was normal sai dai ya kiyaye sa wa zuciyarsa tension da makamancin haka."
Umma rain ta ya baci ta ce "Dr shi ne har da kai za a hada baki a boye min?¿
Shi nawfal bai san an yi haka ba ya ce "Umma a’a ba maso hankalin ki ya tashi shiyasa muka ce high fever."
Umma ta ce "Gaskiya ba ku kyauta ba kuma ban ji dadi ba."
Nawfal ya ce "I'm sorry Umma, also he will be discharge in the evening."
Umma ta ce "Allah kaimu. Suka mata sallama su ka wuce.
Bayan fitar su ta Harari dukan su kafin ta tambayi Asim wata damuwa ce ka sa a ranka har ta kai da kwantar da ita.
Asim yayi karamin murmishi ya ce "Umma ay ya wuce."
Umma tayi tsaki ta ce "Kai Asif fadi min gaskiya dan na san ba zaka rasa sani ba."
Asif ya dubi Asim Asim ya kifta mashi ido umma ta ce "Ni za ka kalla, kuma ka fa da min gaskiya.
Asif yayi shiru bai san mi zai yi ba ya fadawa Umma ko kuma ya kyale.
Umma ta daga mashi tsawa "Magana nake ma."
Da sauri ya ce "Zan fada. Umma daman a kan yarinyar da yake so ne."
Umma da jin haka sai da gaban ta ya fadi, tsoran da ta ke ya zama gaskiya, saboda yar aikin nan ya kwanta asibiti.
Umma ta ce "Sbd yar’aikin nan ka ke neman rasa ranka Asim???
Toh ba ka isa ba, wanna abin kunyar ba za ayi ta a gidana ba.
Asim yadubi Umma cikin sarkarkiyar murya ya ce "Umma dan Allah kar ku ce haka wlh ina son ta."
Umma ta ce "Rufe min baki, kowa na neman cigaba amma kai ka na son ci baya..."
Ya katse ta "Umma laifi ne dan na aure yar talakka, auran ta tamkar jihadi ko ba komi zan taimake ta in taimaki iyayen ta."
Umma ta ce "Tin wuri kama cire ta daga zuciyar ka in ba haka ba zaka sha wahala."
Ya juya masu baya. Asif kuma ba karamin tausayin dan’uwan na sa yake ba, gashi Umma ta ki yarda balle Abba.
A bangaren halimatu ta karaso gidan Mummy, Mummy na daki ta shiga ciki ta gaishe ta ta amsa sannan ta tambaye ta jikin Asim.
Kafin Mummy ta bata amsa Ulfah ta daga mata tsawa, "Da alla wuce ki yi aikin ki ba ki tsaya gulma ba."
"Ulfah! mummy ta kwabe ta. Sannan ta ce wa Halimatu "Jikin shi da sauki." Ta ce "Allah bashi lfy."
Mummy ta amsa da Amin. Ulfah ta ja tsaki ta harareta.
Zata wuce Yasmin ta ingije ta. Halimatu ta wuce kitchen ta dauko tsintsiya ta fara share parlourn bayan ta gama ta wuce dakin Mummy ta gyara shi ta share, ta gama gyaren ta kamar kullun.
Through out ranar bai tankawa kowa ba, da maraice Dr nawfal ya zo duba lfy shi dan ya sallamai shi sai ya ga kuma jikin sa ya kara rauni. Ya dubai su, bai ce da su komi ba. Ya gama dubai duban san ya sa nurse ta mashi allura.
Ya juya zai fita. Umma ta ce "Dr na dauka zaka sallamai mu."
Dr nawfal ya ce "I'm sorry Umma ba zan iya sallamar sa yau ba dan naga paulse din ya kara yin baya ba kamar dazu da safe he was normal, sannan zai fi indan ku ka bashi wuri ya samu yayi bacci sannan dan Allah a kula wurin emotional feelings din sa kar condition din sa ya zama critical. "
Daga haka ya wuce. Nurse din ma ta bishi a baya. Umma ta dubai su wato biyun na ta.
Salma da ke zaune ta ce "Umma wai mike damun sa?
Umma ta ja tsaki ta tashi ta fita daga dakin.
Salma ta juya ta tambayi Asif mi ke damun sa.
Asif yayi shiru bai ce mata komi ba. Yayi tagumi da duka hannun sa. Haushi su ka bata itama ta ja tsaki ta bar dakin sauran su biyu.
Bayan fitar ta Asif ya ce "Asim tin safe ba ka ci abinci ba."
Asim ya katse shi "Na koshi. Ya juya mashi baya.
Cikin tausansan murya ya ce "Asim.. kana ciwo a kwance ina yi a tsaye, dan Allah ka ba zuciyarka hakuri, ka hakura da ita, ban son abin da zai zo ya cuce ka bana son abin da zai sa ka rasa rayuwar ka dan Allah ka ba zuciyar ka hakuri ka hakura da ita, ka sami wadda ta ke daidai da mu.
Asim ya ce "Asif kai ma dan’uwana ka kasa fahimtar halin da zuciyata ta ke ciki, ni kai na ina so in cire ta daga zuciya ta amma na kasa, Umma bata son ta haka ma Abba na san ko da mun yi aure za mu ta samun sabani sbd ba albarkar iyaye na, a yanzu ji na ke tamkar na cire zuciyata daga jiki na dama za a iyayin wanki zuciya da na sa a wanke min ita a shafe min babin halimatu, wlh ina son ta so sosai Asif da ban ji zan iya rayuwa in ba ita. Ya ida maganar yana share hawayen sa.
Asif ya ce "Za ka iya, a baya kayi rayuwar ka ba tare da ita ba haka ma yanzu in ka cire ta zaka iya rayuwa ba ita.'
Asim y ace "Ni dai ka min addu'a Allah ya zaba min abin da yafi alkahiri."
Asif ya amsa da"Amin" sannan ya ce "Ka tashi ka ci abin ci ko kuma..."
Asim ya ce "Ko kuma mi??
Asif ya ce "In kirata ta sa ka ka ci." Ya ida maganar cikin zolaya.
Asim yace "A' a zan ci."
Asif ya ce ko kai fah. Ya ida maganr yana sauka daga gadon asibitin ya tambaye shi mi zai ci akwai jollof rice, white rice and stew, sai kuma tuwon shikafa.
Ya tamvaye shi "Miyan mi cece?
Asif ya budai kular miyar Ya ce "Hnmmm ban san sunan miyan ba ita ba taushe ba ita ba egusi ba. "
Asim ya ce "Samin half malmala." Asif na cikin zuba masa abinci a ka kira shi.
Ya aje plate din ya wuce ya mika mashi wayar. Ya fiddo wayar daga aljihun sa ya ce na manta in kashe wayar nan ana takura ma.
Asim ya ce "A'a in dan kuma samu ya wuce ni."
Asif yayi murmishi ya mika mashi dan bai yi saving number Halimatu ba.
Asim ya amshi wayar ganin number halimatu yayi murmishi Asif kuma ya juya ya koma wurin abincin.
Asim ya daga kiran yana mata sallam.
Ta amsa ta gasihe shi ta mashi ya jiki
Ya ce mata da sauki.
Asif ya dawo wurin shi ya zauna shima Asim ya dan tashi zaune. Asif ya ce ka aje wayar nan ka zo ka ci abinci waye ma ya kira ka?
Halimatu ta ce "Fatan an sallamai ka?
Ya ce "A’a sai zuwa gobe."
Ta ce "Allah kai mu."
Ya tambayi su huzaifah.
Ta ce "Ya nan nan lfy ya na ma ya jiki har da su Umma da kowa."
Ya ce "Ina amsa wa a ban shi in yana kusa."
Ta amsa mashi da toh.
Asif ya ce "Dan Allah Asim ka bar wannnan wayar ka zo ka ci abinci."
Asim ya mashi nuni da ya dagata.
Huzaifah da ya amshi wayar ya gaishe shi.
Ya amsa sannan ya ce "Huzaifah mu yi sirri da kai??
Huzaifah ya ce "Eh."
Asim ya ce "Yauwa ka yi nesa da aunty halimatu, kasan ta tana da fada ban so ta ma."
Huzaifah yayi karamar dariya.
Asif na jin haka ya Harare shi ya ce "Sai nacin bala’i." Yayi tsaki ya aje mashi abincin ya koma kan kujera.
Huzaifha ya tashi ya koma daki har da rufe kofa. Sannan ya ce na yi fadi min.
Asim ya ce "Yauwa yanzu fada min wani abu kake so in siyo ma?
Huzaifha ya ce "Kai kai ba ruwana."
Asim ya ce "Kar ka damu da ita ba za ta ma fada ba ay sirrine."
Huzaifah ya ce "Ko mi ma."
Asim ya ce "Toh shi ke nan zan zo har gida in dauke ka sai mu je wurin wasa ko. "
Huzaifah ya ce "Toh sai ka zo."
Asim ya ce "Kasan wani sirri za ka min?
Huzaifah ya girgiza kai yana ce wa "A’a."
Asim yace "Ka min alkwarin za ka kula min da yayar ka, sannan in na dawo zaka fada min duk abin da ya faru."
Huzaifah ya amsa mashi da toh.
Asim ya ce in tamabaye ka bana.
Huzaifah ya ce "Mi?
Asim ya ce "Waye ke zuwa wurin ta zance?
Huzaifah ya ce "Su nan fah da
Yawa."
Asim da jin haka sai da gaban sa ya
Fadi kafin ya ce "Toh wa ya fi zuwa?
Huzaifa ya amsa shi "Wani ne suna sa nura."
Asim ya ce "Toh shi ke nan na godai da an sallamai ni gobe jibi zan zo mu fita okay."
Huzaifha ya ce "Toh yallabai."
Asim ya ce "Ka dai na kira na da haka ka kirani da Asim."
Huzaifah ya ce "A’a yallabai dai."
Asim ya ce "Toh shike nan, ka kira ni da AI sannan ka gaishe min da Umma da Abba kai mata wayar."
Ya budai kofar ya fito ya mika mata wayar. Da sauri ya koma wurin Umma dan ya san ba karamin aikin ta bane ta kai mashi duka.
Ta mike ta koma daki ta na shiga ta tambaye shi wata Magana ce kuka yi har da rufe kofa?
Yayi karamar dariya ya ce "Sirri ne."
Ta ce "Toh dare nayi zan kwanta."
Ya ce "Ki kula min da kanki."
Ba ta ce mashi komi ba ya ce mata sai da safe. Ta ce "Allah kai mu ya amsa da amin ta kashe wayar."
Ya dubi Asif dake amfani da wayar sa ya ce Asif ke nan ta ka soyayar wasa ce.
Asif ya ce "Ay na ga ta ka gaske ce shiyasa ta kwantar da kai."
Asim yayi dariya zai yi magana Abba da Umma suka shigo.
Asif ya amsa sallamar su.
Suka karaso. Abba ya zauna suka gaishe shi ya amsa sannan ya mashi ya jiki.
Ya amsa da sauki sannann ya fara cin abinci.
Abba ya ce "Masha Allah jikin na ka da sauki."
Ya zauna saman sofar da ke dakin ya xe
Asif mika mashi naman na san sai ya fi jin dadin sa.
Asif ya karbi leder ya karasa ya mika mashi take away din rosters chicken. Ya mika mashi plate din tuwon dan yana cin loma daya ya aje.
Ya ma umma nuni da kar ta fada wa Abba abin da ke damun sa.
Yana fara ci ya aje, Abba ya tisa shi ya ci kadan, in da su ka san Asim na jinya domin da lfyr sa bai ganin nama musanman na kaji ya kyale.
A ka sa mashi half cup na malt shima ya sha da taimakon Asif. Dare ya ja kowa ya koma gida.
A bangaren Halimatu suna gama waya ta fito ta tambayi Huzaifah mi Asim ya ce mashi.
Huzaifah ya ce "Sirri ne."
Halimatu ta ce "Fa da min."
Huzaifah yace "Umma ay kin ce babu kyau bayyana sirri koh."
Umma ta ce "Haka ne huzaifah.."
Halimatu ta ce"Ka da Allah ya sa ka fadi."
Washe gari da safe aka sallamai shi suka koma gida ya ida jinyar sa.
Da dare Abba ya sa a ka kira shi. Ya samai shi. Bayan ya mashi ya jiki ya ce mahaifiyar ka ta sanar dani gamaida ciwon ka in har saboda itace shike na, ka je ka naimo kudin sadakin auran ta sai a aura ma ita
.
Asim kwatkwata bai tsanmaci haka ba ya dubi Abba ya dubi Umma ita kanta Umma tayi mamakin chanza yanayin sa. ya ma rasa abin ce wa farin ciki shifidai a fuskar sa.
Abba ya ce "Batun laife ni zan yi gida kuma na kama maku haya kafin a ida wacen gidan."
Shi dai Asim ya kasa ganai haka. Yayi wa Abban sa godiya Abba ya ce mashi ya tafi.
Ya mike yana ta jin dadi ya wuce part din su murna sosai a cikin zuciyar sa ya fadiwa buba da Asif da ayan suke parlourn suma sun taya shi murna sai dai ayan ya san ba a banzan ba akwai abin da zaije ya dawo sai dai bai nuna masa haka ba ya taya shi murna.
Lovely reders ku ma mi kuke tunani gamaida hukuncin da Abba ya yanke🤔🤔
Bari dai mu ga ni in tusa na tada wuta.
HALIMATUS'SADIYAH(sakayya)
Story & written by Meenamajeed🥀
Don't forget to vote, share & comnent😍👍
Love you💋❤️