16
by @meenamajeed
Assalamu alaikum
Yan gayu da ku na ke🍒🍻🥂
Yan aci dadi a rungumi kaddara da ku nake🍇🍹🥂
Yan son cin dadi da ku nake🍿🍨🍧
Masu son kayan makulashe da ku nake.🥙🍫🍩
Mun na da sabon Ebook wanda ke dauke da recipes na koyan kayan filawa, kamar su cake, cin cin, granola bar, dogunut, pizza, shawarma, meatpie, biscuit, burga, and all crunch and munch.
Duk mai son Ebook din nan ya na iya min mgn ta message ko ta whats app. Na sha aje number ta idan mutun na son in tallata masa kayan hajar shi. Ga dai number ta ***

Wa shegari Umma ta je gidan Alhaji mala ta fara shiga part din uwar gidan da amaryar sannan ta wuce wurin Mummy.
Ta yi sallama. Halimatu da ke goge console din corridon ta amsa sallamar sanna ta rintsina ta gaishe ta.
Umma ta amsa ba tare da ta nuna mata komi ba.
Halimatu ta cigaba da goge gogen ta. Umma ta ce "Ina hajjo din.
Halimatu ta amsa ta na ciki. Ta so ta tambaye ta jikin Asim ta dai kame bakin ta.
Umma ta wuce dakin Mummy. Tayi salama Mummy ta amsa tana mata maraba da zuwa.
Umma ta karaso ta zauna a kan kujera suka gaisa sannan ta kira Halimatu. Halimatu ta karaso ciki ta ce "Hajiya gani."
Mummy ta ce "A kawowa Umma drinks."
Ta amsa ta na mai rintsina mata. Ta wuce, umma ta bita da kallo tabbass tin ba yau ba ta yaba da Halimatu sai dai ko sau daya ba ta taba tunanin hada zuri’a da su ba."
Halimatu ta kawo mata drinks ta aje try din a gaban hajiya ta wuce.
Bayan wuce war ta Umma ta ce "Hajjo wai ina kika samo yarinyar nan mai hankali?
Mummy ta ce "Ay ni ban taba mai aiki mai nitsuwa irin ta, kwatakwata bata da damuwa, ba kiwar aiki balle ha'inci."
Umma ta ce "Gaskiya kam na yaba da nistuwarta."
Mummy ta ce "Ay ba ke ka dai ba hatta Alhaji kin ga dai masu aiki ko ajikin sa amma shi kan shi ya yaba da ita."
Umma ta ce "Amma ina ki ka samai ta?
Mummy ta ce "Ladidi neigbours din mu ita ta kawo min ita ta ji ina naiman mai aiki. Ta ce min iyar yayan ta,ta gama NCE din ta ba aure sai ta ce zata ma mahaifin ta magana in ya yarda sai ta zo ta tayani aiki kafin harira ta dawo kin ji dalilin fara aikin ta kuma gaskiya na yaba da aikin ta shiyasa ko da harira ta dawo daga gida ban dagatar da Halimatu ba dan ina jin dadin aikin ta.
Umma ta ce "Eh dan shigowata na ga ta na ta goge console."
Mummy ta ce muna ta fira ya jikin Asim?
Umma ta ce "Da sauki har ya warware.
Mmuumy ta ce Allah bashi lafyi
Ta amsa da amin.
Asim kuma jikin sa da sauki dan har yama fita kasuwa domin pricing din kayan da ya siyo a lagos, ya sa masu kudi sannan kowannen su aka aje shi a wurin sa.
Da yamma bayan yayi sallah ya wuce gidan su Halimatu.
Ya parker motar su a bakin layin ya taka ciki kamar kullun, ya karasa kofar gidan. Yaran dake wasa ya kira daya daga cikin su ya ce ya je ya kira masa Huzaifah.
Yaron ya shiga ciki ya gaishe da umma.
Umma ta amsa.
Ya ce mata wani na kiran huzaifah.
Umma ta ce waye?
Umar ya ce "Nima ban san shi ba."
Umma ta ce "Je ka ce mashi ya fadi waye shi."
Umar ya juya ya koma wurin Asim ya ce "Wai Umman su ta ce waye ne?
Asim yayi murmishi ya ce ka ce mashi AI ne.
Ya shiga ciki ya ce wai mutumin ya ce "AI ne."
Huzaifah dake zaune Halimatu na mashi karatun qur’ani ya na ji an ce AI ya mike da sauri ko takalmi bai tsaya sa wa ba ya wuce Umma ta kira shi amma bai ji ba har sai da ya fita.
Umma ta ce wa Halimatu tashi bi shi kar wani abu ya samai shi."
Halimatu ta yi jum. Umma ta ce "Tin da ba kowa gidan dole ke za ki fita in kuma ni ki ke so na fita ay ba matsal bane."
Ta ida maganar ta na niyar mike wa.
Halimatu ta ce "A’a Umma bari na je." Ta dau hijabin ta dake kasa wurin da tayi sallah ta sa ta fita.
Kafin fitowar ta huzaifah na zuwa wurin shi cike da murna ya gaishe shi ya masa ya jiki.
Asim ya amsa. Sannan ya tambaye shi ka shirya mu je.
Huzaifah ya dan yi shiru kafin ya ce "Ban fadawa Umma ba."
Asim ya ce "Toh je ka fada mata ka ka ga ko takalmi ba ka sa ba."
Ya jinjina kai ya juya zai tafi ya ci karo da Halimatu. Da sauri ya wuce ciki.
Halimatu da ta karaso tayi mamakin ganin sa dan ba ta tsanmaci har ya warke da zai iya fitowa ba.
Ta gaishe tare da mashi ya jiki ya amsa. Sannan ta ce "Mi yasa zaka aika a kira shi sannan ka boye sunan ka bayan duniyannan ba abin yarda ba ce."
Asim yayi murmishi ya ce "Tuba nake, sannan ina ne man wata alfarma wurin ki." Ya dubaita sai ya ce "Za mu fita da Huzaifah dan na mashi alkwarin haka."
Halimatu ta ce "A'a ba zaka fita da shi ba.
Ya ce 'Why?
Zata ba shi amsa Huzaifah ya fito cike da murna ya ce "Umma ta yarda mu je."
Suka dubai shi, ya jinjina mashi kai dan murnar dake fuskarsa ya manta Halimatu na wurin. Sai da ya ji ta ce "Ba inda za ka." Fara’ar dake fuskarsa ta washe.
Asim ya ce "Boi Umma ta ce ka je, rankiyadadai ba yanda ki ka iya da mu ko?
Huzaifah dai yana son ba shi amsa ya na jin tsoran yayar ta shi.
Asim ya mika mashi hannu. Sai da ya fara kallon yayar shi sannan ya yarda Asim ya rike mashi. Har sun juya za su tafi ya juyo ya tambaye ta what will I bring to you?
Ta ce "Ba na bukata." Ta juya ta koma ciki ya bita da as you wish.
Suka cigaba da tafiya har suka isa motar shi ya budai mashi gidan gaba ya shiga sannan ya rufe ya koma side din sa ya shiga ya rufe sannan yafara driving yana tamabayar shi yana bashi amsa har suka isa Rufaida, Ya fito da shi suka shiga ciki bakin Huzaifah ya ki rufewa sai waige waigen wurin yake.
Asim ya siya mashi icecream da Shawarm sannan suka zauna. Suna shan icecream yana jin cikin huzaifah.
A takaice ya fita da Huzaifah ba dan komi ba sai dan ya kara sanin more about Halimatu da gidan su dan Huzaifah sai da ya zayyane mashi duka yan gidan su 14 da jikokin gidan da kuma inda yayan sa mata ke aure har ma da mazan da halayen su musanman Halimatu. Da ya fi tambaya gamaida ita.
A bangaren halimatu rai bace ta shigo gida ta ce 'Umma ya za ayi ki bar Huzaifah ya fita da shi, Umma ba ki san halin suba dan Allah ku daina shi-shige masa, Umma basu da mutunci yan gidan su."
Umma ta ce "Ba ki ji mi ki ka ce ba yan’gidan su shi kuma mutumin kirki ne ko ba ki ga haka ba."
Halimatu ki so mai san ki da arziki, ki daina wulakanta mutane wataran baki san in da gari zai waye ba.
Almost 2 hours suka kwaso sannan yace bari yamaida shi gida kar Umma ta mashi fada. Ya siya mashi sweet chocolate bisciut candy da sauran su duk da in zai siya abu guda biyu zai siya dan ya bashi lbrn Aseey kuma shi kan shi Huzaifah in Asim zai siya mashi abu zai ce a hada da na Asee.
Sai da ya cika mashi bakar ledar da kayan makulashe sannan ya siya mashi motar wasa ya siyawa Aseey yar tsana sannan su ka fito sai a lokacin Huzaifah ya lura da har an yi magriba nan ta ke hankalin shi yayi gida. Suka shiga mota Asim ya tambaye shi lfy.
Cikin muryar san kuka yace "Umma za ta min fada magriba tayi ban dawo gida ba. Dan Allah ka mai dani gida in ba haka ba gobe ba zata bar ni in fito ba."
Asim yayi murmishi ya ce "Yanzun nan zaka gan ka a gida." Ya ida maganar yana jan motar. Deep down ba karamin dadi ya ke ji ba dan ya yaba da tarbiyar da Ymma ta ke ba ya’yan ta kuma ya san tabbas irin haka Halimatu zata bai wa ya’an ta.
Da suka isa layin ya sauka ya rike masa ledar har sai da suka isa gida ya mika mashi sannan ya mashi sallama huzaifah ya mashi godiya ya wuce ciki Asim kuma ya wuce mota.
Huzaifah yayi sallama ya shigo ciki ya karasa da ledar wurin Umma da kar dan ledar ta mashi nauyi.
Asee na ganin haka ta mike daga wurin Nusiba ta dawo wurin Umma.
Umma ta ce "Kai ko sai da ka roke shi ko?
Ya ce "Wlh Umma ban roke shi ba.
Umma ta ce "Da ina da ina ku ka je?
Ya ce " Rufaida sai dayan wurin Nima ban san wurin ba mun dai mun sha ice cream ya siya min wani abu mai dadi sannan da zamu dawo ya siya mana wannan kayan dadin ni da Aseey.
Aseey ta ce "Dagaske wannan nima har da ni??
Huzaifah ya ce "Eh har ma da yartsana ya siya maki ni kuma ya siya min mota, Umma nima yanzu na yi sabuwar mota zan aje ta in na girma in din ga kai ki unguwa da ita."
Duka wurin suka kwashe da dariya. Haidar ya ce "Wa ya gayama motar yara ta na zama ta manya sai dai ka ce in ka girma ka yi kudin kan ka."
Halimatu da ke saurin sallamai sallah ta na sallamai wa ko azkar bata yi ba ta ce "Ba za ku yi amfani da su ba maida mashi abin sa zaku yi."
Haidar ya ce "Kamar ya? Ya za ayi ya ba yaro kyauta a maida mashi ay bai da ce ba."
Nusiaba ta ce "Fadi mata dai ita ganin ta ke kamar ta fi kowa gaskya da yin daidai."
Halimatu ta ce "Ba ku ganin abin da yake yi yayi yawa ce mashi aka yi mu na so ne da zai wani kawo masu kayan zaki sanin sanin su yi ciwon hakora."
Haidar ya ce "Ke dai ki ka sani."
Nusaiba ta ce "Gwara shi dai so dubu a kan wanna nuran da ko alawar 10 ba iya siyawa masu."
Haidar ya ce "Nura, shekaran jiya ya samai ni ya min maganr ta, wai shi so yake ayi auren a gama bai so wani ya mashi kwace."
Nusaiba tayi dariya ta ce "Sai ka ce matar shi da za a mashi kwace."
Haidar ya ce "Ni dai ce mashi nayi ya tuntubi Baba."
Nusaiba ta ce "Garai ki halimatu sai ki zaba tsakannin Asim ko Nura."
Harara ta wulla mata ta cigaba da amfani da wayarta.
Haidar da Nusaiba kadai suke fira har a kayi isha’I ya tashi ya tafi massallaci suma suka yi sallah sannan Umma ta raba masu kayan da Asim ya basu sauran kuma a ka je wa gobe.
Da malan Yakubu ya dawo ta fadi mashi ga abin da ya faru yace daga yau kar a sake barin shi ya fita da Huzaifah ba laifi bane in ya siyo ya bashi amma kar ya sake fita da shi.
Huzaifah dai bai ji dadin haka ba.
A bangaren Asim bayan ya dawo majalisar su ya wuce bayan sallah isha’I ya shiga part din hajiya shafa ya dauki lubna ya fito da ita nan majalisar su kusan hour ta daya a wurin su sannan ya masu sallama ya wuce ciki yamaida ta wurin zara shi kuma ya wuce part din su. Ba kowa a parlourn hakan ya sa shi zamana nan ya kira Halimatu.
Na farko ba a daga ba sai a na biyun ta daga tana amsa sallamar shi ta fara mashi fada dan mi zai fita da huzaifah har da kashe mashi kudi
Shiru yayi bai ce mata komi ba dan tin dazu jiran haka yake dan yayi mamaki da bata kira ba.
Har sai da ta yi shiru ya ce kin gama.
Ta ce "Ban gamaba."
Ya ce "Toh cigaba ina jin ki dan fadan na ki faranta min rai yake."
Tayi shiru bata ce komi ba dan ta kule, ke nan mahaukaciya ma ya dauke ta.
Jin tyi shiru ba tace komi ba ya ce "Amira Amira, Amira my wild cat, mi ya yi zafi shi ba wuta ba, yar siyayar da na mashi shi ke nan ki ka dauka da zafi toh shi ke nan ta gobe sai ta fi haka that my promise to you.
Ta ce "Wai kai so kake ka nuna ka fi kowa bajin ta, bama bukatar kudin ka, ce ma akyi zan aure ka ne da zaka din ga kashe wa mutane kudi."
Yayi murmishi ya ce sai kuma a ka ce maki bazan aure ki, ki rubuta ki aje kin riga da kin zama tawa.
Ta ce "Tin da kai ne dole na."
Ya ce "A’a tin da Baba ya amince Umma ma haka ay shi kenan."
Ta ce "Sai kuma a ka ce ma iyayena auren dole za su min."
Ya ce 'Ban damu ba ni na san ba da daidai wa ba zaki so ni."
Ta ce "Kana ma wahalar da kanka dan wanda ka gani kwanakin baya shi zan aura zai fi ma tin yanzu ka san in da dare zai ma."
Asim ya ce "Toh ay na riga da na san in da dare zai min har ma da in da zan kwana da inda zan tashi."
Ta ce "Zan kwanta sai da safe." Bata jira cewar sa ba ta kashe wayar.
Ta na katse kiran ya tura mata da sako
"Masoyiya ya zaki kashe wayar bayan ban gaji da jin murya ki ba any where I have record your scolding so kin ga ko da kin hanani jin muryar ki ina da wata a aje. Goodnight baby, tight sleep." Ya ida da emojin love."
Ta na gani haka har za ta kira shi ta ce ya goge sai tayi tunanin kar ya kara recording din wata sai ta kyale ta fito waje ta kwanta kusa da Nusaiba da ke waya ita ma.
Dazu mun yi mgnr cin dadi kun san dai in ana cin dadi ana sharholiya sai ana hada wa da diet,
Khadija ta saman mana ebook wanda zai taimake ki ki rage kibar ki ki zama daidai wato fit, ke ba mai kiba ba ke ba mai rama ba sannan ke ba mai nauyi ba ke ba marar nauyi.
A cikin ebook din tayi bayani dalla dalla hanyoyin da mutun zai dinga bi domin rage nauyin jikin sa haka kiba. Sannan akwai nauikan abincin da mutun ya kamata ya kiyaye kuma ya ci duk a cikin ebook din ta wato
" STAY-FIT."