HALIMATUS'SADIYAH

18

by @meenamajeed

Assalamu alaikum ina masu yin sana'ar hanu ta gida har ma da ta shago. Ina masu so su habaka kasuwan su daga karamin mataki zuwa babban mataki

Ina masu son sun samu customers, na gaske ba masu ce wa sai ba ji k.

Kwantar da hankalin k nisa ta zo kusa kina daga gida za ki iya tallata kayan k wurare wurare da wayar hannun ki, ki na zaune batare da kin ba kan ki wahala ba zaki tallata kayan ki cikin sauki kuma za ki samu customers. Har ma ki samu masu wholeseler da kan k

Mun kirkiri class mai su na enterprenuashin sales bosters. Duk mai ra ayin shiga ko kuma son karin bayani k tuntubai su ta ***

Ma su son a tallata masu kayan da su ke saidawa a media wato sponsor add su ma suna iya min mgn ta number ta 081070456601.

Washe gari bai je wurin ta ba sai dai da dare ya kira ta suka gaisa. Ba su wani jima ba.

Through out this week bai je gidan su ba sai dai a waya. Ranar Friday, da dare Abba ya tara su a parlour, yan’an sa da matan ya tambayi Asim ina kudin sadakin.

Kowannan su ya yi mamaki jin haka, Asim ya ce "Abba su nan."

Abba ya ce "Ka turo min su a account."

Ba bata lokaci ya dau wayar shi ya tura wa Abba 100k kamar yanda abba ya ce mashi.

Kudin na shigowa Abba ya ce "Yauwa sadakin sun shigo kuma zancen da nake ma dazu bayan an sauko daga masallaci a ka daura auren ka da haulat yar gidan Ambassador Sadiq Ya’u.

Fara’ar da ke fuskar shi ta yaye nan ta ke zuciyar sa ta far bugawa da karfi.

Ambaton Allah ya fara yi yana kokarin daidaita lumfashin sa.

Umma daman ranta bai bata Abba zai aura mashi Halimatu ba.

Hajiya shafa da sauran mutane mamaki suke buba, Asif abin da suke tsoro kenan Ayan kuma ya san hakan za ta faru.

Asim ya dubi mahaifin na sa da raunanan idanu ya ce "Abba ka isa da ni kai mahaifi na ne bazan ki hukunci ka ba amma ka sani abin da ka ke ba daidai ba ne cutarwa da kake wa ya’an ka ba daidai ba ne, musanman mata, amma duniya ce gata ga ka."

Daga haka ya mike ya bar parlourn with so much hearted of his father, dama ya mutu ba tare da ya ga wannna bakin cikin ranar ba Ya wuce part din su.

Ya na mikewa Asif ma ya mike Abba ya kirashi ko tsayawa bai yi ba ya bi dan uwansa.

Ayan shima ya mike ya ce "Abba Allah ya wadata ka amma ba ka godaiba tsorona ka guji ranar da Allah zai amshe su ko dan hakkin ya’yan ka mata life is not trusted. Da haka ya wuce ya bi bayan su.

Ba wanda ya ce komi da daya da biyu da uku aka din ga fita har a ka bar hajiya shafa kadai ita ma ta ce "Alhaji ina jiye ma tsoran ranar da yarannan za su ju ya ma baya because of your selfies reason ka godaiwa Allah kaf din su ba mai saba maka amma kakiyayi ranar da za su juya ma baya.

Daga haka ita ma ta bi bayan su a ka bar shi.

Ko digon tausayi ko bakin cikin haka babu a zuciyarsa dan duniya ta riga da ta mashi daurin da ba ya jin kira sai dai a bishi da addu'a.

Asim ya na isa dakin su ya rufe da mukuli ya zauna kan gado zuciyarasa cike da bakin cikin mahaifin sa ina ma ace ya mutu kafin yau, ina ma ace Alhaji Inuwa bai zama mahaifin sa, yanzu shi ke nan yara bu da ita, ina, a’a hakan ba zai yu ba ay shi namiji ne zai iya auran mace sama da daya sai na aure ta sai dai yayi abin da zai yi ba dai ya auran min wata ba saboda selfishiness irin na sa, ya ji da shi amma Halimatu sai na aure ta.

Asif da ke waje ya roke shi da Allah da ya budai mashi kofa Asim ya kiya hatta Umma da ta zo bai budai kofar ba bai yi masu mgn ba.

Wayar shi ya jawo ya kira Halimatu bayan sun gaisa ya ce da ita ta fadi mai mi mutun ya kamata yayi in ya na cikin bakin ciki.

Ta tambaye shi miyafaru

Ya ce "Ina so in sani rai na ne ke bace kuma ba wandan zai iya kwantar min da shi sai ke."

Ta ce "Ka yi alwalla kayi raka biyu ka mika damuwar ka wurin Allah, dan ni ba abinda zan iya ma Allah ka dai zai iya sauya wanna damuwar ta ka zuwa farin ciki."

Ya ce "Ke ce damuwa ta, ke na ke so Allah ya bani ke a matsayin mata. kuma yanzu zan yi sallah in kara rokan Allah ya narkar da zuciyar ki ki yarda da ni".

Ta tambaye shi baka gida ne naji hayaniya.

Murmishi yayi mai dauke da radadi ya ce "Ina gida hayaniyar is personal issues.

Yanzu zan tashi nayi sallah in na gama in biki yi bacci ba sai mu cigaba da fira." Bata ce komi ba har ya kashe.

Ya na kashewa ya shiga toilet yayi alwalla ya fito ya kabbara sallah.

Umma da hankalin ta ya tashi ta wuce part din Abba ta iske shi yana kallon news ta ce "Yanzu abinda ka yi ka kyauta? Ka aura mashi yarinya ba da sanin sa ba haba alhaji sai ka ce wanda bai da galihu, in wani abu ya samai shi fah?

Kai karan kan ka ne bai gama treatment din shi ba na heart attack ka kara dora masa wani ciwon zuciya, mi ne ne laifin yarinya ita ta yi kanta ko kuma ita ta zabi zama talakka? Kai shike nan talakka bai da galihu a wurin ka.

Abba ya dagatar da ita da hannu ya ce "Ya isa haka Halima, ki na sa min ciwon kai da suratan ki marassa tushe, ya dadai bai samu heart attack din ba tin da a kan shi a ka fara soyaya." Mtsww fita ki bar min parlour tin da a kan shashashan yaron chan ne, baku taba duba gaba.

Umma ta sauke ajiyar numfashi ta ce "Kudi ko, ga ka ga su kudin da ka ke Gadara za su kare na ga dai ba ka kai qaruna ba a kudi, ga ka ga duniyar. Ta fice.

Yayi tsaki ya ce "Sakarkaru ba sun san komi ba, yanzu kudi suke Magana, money is the power."

Umma ta koma part din su Asim su ka kara mashi knocking bai budai ba hakan ya kara fisata ta wuce part din ta takaicin duniya ya ishe ta.

Kwana tayi bata yi bacci ba tana tunanin halin da Asim yake ciki haka shi ma dan uwan na sa Asif bai yi bacci ba shima Asim kwan yayi bisa sallaya.

Washea gari da safe sai da rana ta fito sannan ya fito ya wuce part din Umma a nan ya iske Asif suka gaisa.

Umma ta tambaye shi dalilin da ya sa ya ki budai kofar.

Ya ce "Umma ana so ka kame kan ka in ka na cikin fushi shiyasa na rufe kai na."

Asif ya ce "Toh indan wani abu ya samai ka?

Asim yayi murmishi ya ce "Ba dai gani ina qlau ba ay shi ke nan."

Umma ta ce "Ka bi ka tadawa mutane hankali."

Yayiwa mahaifiyar ta shi murmishi ya ce "Umma ba gani lfy ba."

Safna ta ce "Toh maganar haulat din fah? Daga umma har Asif basu so Safna tayi magnar ba dan daga su sai Buba sai Abba kadai suka san Asim na da ciwon zuciya.

Yayi murmishin sa wanda bai rabuwa da fuskarsa ya ce "Ban sani ba abin da na sani duk daren dadai wa sai na Auri Amira."

Safna ta tambayi wacexe kuma Amira?

Abba ya karaso rai bace ya ce "Taurin kai zaka yi zaka saba min toh ka je ka yi gaban kan ka amma ka sani in har ka auri yarinyar nan I will disown you from my child."

Ba wanda ya tsanmaci haka  musnaman Asim.

Tsanar da Abban na sa yayi wa talakka har ya kai da zai tsinai mashi. Ya zauna zaman kujerar dake gefen sa dan kafufuwansa basa iya daukar shi.

Ya dafe kan sa dan ba karamin sara kan shi yake ba ga zuciyarsa dake mai nauyi a kirjin sa sai ya tuna da sakon halimautu da ta turo mashi jiya "A duk lokacin da kake bakin ciki ko damuwa ka tuna da Allah yana tare da kai kuma jarabawa ce ya baka bakin ka ya furta hasbunanlahu-wani’imal wakil."

"Hasbunal-wani'imal wakil" ya cigaba da maimaitawa.

Umma ta ce "Alhaji abin nan yayi yawa ka aura mashi wadda bai so ba tare da sanin sa ba ka bar shi ya ji da halin da yake ciki."

Yayi tsaki ya wuce.

Umma ta zauna a gefen sa Asif ma ya zauna a dayan gefen.

Umma ta ambaci sunan sa. ya dago kan shi wanda har idon shi sun yi ja ya ce "Umma duk daren dadai wa zan aure ta ay akwai mutuwa ko in bata zama mata ta ba a nan zata zama matata a lahiri in da ba talakka balle mai kudi.

Babu Mulki babu saurata balle kudi. Ya fi karfi na a nan amma bai fi karfin Allah ba.

Umma ki min addu’a in cire ta daga zuciyata cikin sauki ba tare da na sha wahala ba.

Umma tayi huggin din sa ta na bashi hakuri ta na ce mashi ya jajirce kar ciwon sa ya tashi.

Ya dago kan shi dake bisan ta ya goge kwalar sa ya ce "Umma ina lfy yanzu ma kasuwa zan tafi."

Umma ta ce "A'a baka da lfy."

Ya mike ya na cewa "Umma karki damu da na fita kasuwa sai na fi jin dadin jiki na."

Umma ta ce "To Allah kiyaye amma tare za ka da dan’uwan ka.'

Asim ya ce "Duk yanda ki ka ce."

Umma ta ce kuje Asif.

Asif ya mike Asim yayi sakar wa mahaifiyarta shi kyawatantance murmishi ya na ce wa "Umma sai mun dawo."

Ta ce "Alkiyaye." Suka fita.

Asif ya tuka su ya kai su kasuwa, ya aje shi a shagon shi sannan shima ya wuce shagon shi duk da katangan su daya kafin Asif ya dubo shagon shi ya dawo har Asim ya wanke kafa ya fita.

Ya shigo shagon ya tambayi ya na ina Adam, yaron shagon ya ce bai jima da fita ba.

Ya tambayi ina ya je?

Adam ya amsa "Bai ce mana ga in da ya je ba ya dai fita mun ma dauka ko wurin ka zai je."

Da sauri Asfi ya fita ya dau hanyar gidan su Halimatu sai dai sun sha banban gidan Mummy ya tafi ko shiga ciki bai yi ba ya sa mai gadin ya kira mashi Halimatu.

Mai gadi ya shiga ciki ya kira halimatu cikin sa’a Mummy ta na ciki.

Ta fito ta karaso waje, Wa za ta gani? Ta ga Asim.

Ya ce mata ta biyo shi mota.

Ta bishi, bayan sun isa ya roke ta da ta shiga yana so ya fada mata abu.

Ta budai kofar ta shiga dan ita ma ba ta so wani ya zo ya ganta tare da shi shima ya shiga ya rufe motar sannan ya kalle ta ya ce "Amira."

Ta amsa da "Na’am."

Ya ce "Ki juyo ki kalle ni."

Ta tsaya dan ba zata iya kallen shi ba ya ce "Dan Alah."

Ta dan juyo suna hada ido tayi saurin maida idon ta kasa dan kwarjini ya mata. ya dan yi smiling kafin ya ce "Anywhere ba tare da bata loakci ba na zo in miki sallama dan zan yi tafiya kuma na san baki gida."

Ta ce "Ay da ka min ita a waya.'

Ya ce "A'a gwara in miki ita face to face, zan yi tafiya sai dai ina jin tsoran kar in dawo in taras wnanan Nura a ke ce mashi, ya aure ki."

Ta tambaya shi "Miyasa ka ce haka?

Ya amsa "Sbd na san kin fi san shi ko?

Na san shi ki ke so ba ni ba, amma dan Allah ki min alkwarin zaki jira ni."

Ta dubai shi ta mashi alamar tambaya

Ya ce "Zan yi tafiya ta wata daya zuwa wata biyu, dan Allah ki min alkwarin za ki Jirani da na dawo wlh zan aure ki na so ace kin yarda kafin yanzu da tafiyar nan da ke zan yi ta."

Ta tambaye shi "Ina za ka?

Ya ce "Wani wuri mai nisa."

Ta ce 'Ka fada min ina so in sani."

Ya ce "Toh shike nan lagos ne zan ce."

Tayi sigh of relief. Sanna ya ce "Kar na bata miki lokaci, ki kula min da kanki kin ji, again in kuma na mutu ban dawo ba shi ke nan na hakura ki aure shi a nan ni kuma in muje lahira sai ki zama ta wa."

A lokacin da ya ambaci mutuwa zuciyar ta sai da tayi mumunar dagawa ta kalle shi ta ce "Miyasa ka ce haka?

Ya ce "Kin ce fah duk abinda mutun zai yi ya dinga tunawa da mutuwa."

Ta ce "Toh shi ke nan Allah tsarai ya maido da kai lfy."

Zata budai kofar ya ce "Baki min alkwari ba."

Ta ce "Shi kyan alkwari cikawa in dan na ma shi na kasa cikawa ban yi dadidai ba sai ka dawo Allah tsare."

Ya amsa da amin ta fita daga motar ta wuce ciki, ta na shiga ciki ya fita ya mikawa mai gadi key din motar ya ce ya aje mashi zai je ya kira mai gyara daga nan ya wuce gidan su haulat.

Ya jira har ta fito da zumudin ta dan tabbass ba macen da zata ki Asim mutun ne mai saurin shiga rai.

Ta karaso ta zauna a dayar kujera da ke gefen grass carpet.

Ta dubai shi ta ce "Finaly my dream of having you as husband came true."

Ba tare da ya kalli in da ta ke ba ya ce "Miyasa ki ke so na?

Ta ce "Haka nan ka na brige ni."

Ke ki ka cewa mahaifin ki ki na so na?

Ta ce "Ehhen, shiyasa ma kuma yanzu ka zama miji na.'

Ya ce "Zaki iya rayuwa da mijin da ke san wata daban ba ke ba."

Bata tsanmaci haka ba ta ce "Ban gane ba?

Ya ce 'Okay ni Asim ina son wata mace wadda ta fi ki daraja, girma da komi a wuri na, ba ki da gurbi a zuciyata kuma ba zaki taba samun shi ba shin za ma ki iya zama da kishiya??

Ta yi murmishin isgili ta ce "Har a bada zama da kishiya, ba ka isa ba sai dai ka zaba ko ni ko ita."

Ya ce "Khalas haka nake so na ji, na zabe ta dan haka ni Asim inuwa madobi na sake ki saki daya."

Kallen shi tayi cike da tsoran maganar da ta fito a bakin sa, dan a tunanin ta ba namajin da zai ki mace mai kyau mai diri irin ta, da jin kalmar saki har da gyara zaman ta dan da farko zaune ta yi cike da kasaita tayi crosiing leg jin ya ambaci saki ya sata saurin sauke kafar ta.

Za ta yi magana ya kara mata na biyu. Nan ta ke ta sukukuce ta fara masa borin ay bai isa ba wlh ka yi kadan zan ga kazan da ya tasare maka da zaka aure ni jiya ka sake ni yau wlh ban saku ba.

Ya mike tsaye ya kara mata na Ukun sannan ya ce "Kin ga yanzu babu wani zancen aure na da ke ko da an je kotu ba duka ukun na miki su a tare ba a rabe na miki su dan haka have a welfare."

Daga haka ya wuce ya bar gidan.

Tirka kashi, agwagwa da rawar gada, Malan Asim daga aure sai saki. Chab mi zai faru next???

Sai mun hadu a next chapter sai dai masu sa'a za su iya karanta sauran littafin nan a kyauta.

Masu karanta shi a nan albishirin ku, kyauta zaku karanta har zuwa lokacin da zan gama shi amma fah da na gama shi da one month zai koma paid book sai k biya kudi kafin k samu complete document din sa.

Dan haka shawara k tsaya ki karanta shi a wattpad k dinga bi na har zuwa lokacin da zan gama za k karanrta shi a bagass ko sisi ba za ki ban ba amma daga wannan lokacin da na sa duk mai son complete din sa zai biya worth of 500 naira only.

HALIMATUS'SADIYAH(sakayya)

Story & written by Meenamajeed

C.E.O MEEMAJ all kind of product service.

Authour of NURUL QALBI💖 RUMAISA MILHAN, HAALIN RAYUWA & KAZAFI.