KAMPALA ESTATE

page 9

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*


           NA


*BILKISU GALADANCHI*


*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*


09.


Yau Fatima a duk faɗin gidan ba kowa sai ita kaɗai ba wasu surutai ba shiga haƙƙinta,  rufe ko ina na gidan tayi tun 9 na dare sannan ta kwanta bayan doguwar addu'a tana fatar Leo ya mata reply na messages data tura masa amma sai taga delivered but not seen hankalinta ya sake tashi saboda ita yanzu damuwarta mahaifiyar ta ne, ta yi iya yanda zatayi da juyin da zatayi amma ta kasa baccin, a karo ma dubu kuwa ta gwada number mahaifiyar ta bata shiga, wata zuciyar gaya mata take lallai washe gari ta shirya ta fita kasuwa daga can ta bi ta gidan ta duba ta, wata zuciyar kuma yana gargaɗinta kada ta kuskura ta tafi neman abin da ze iya janyo musu matsala dukkansu she hope cewar mahaifiyar ta tana nan lafiya lau, ganin damuwar ze mata yawa ya sanya ta buɗe app na karatun Alkur'ani me girma ta shiga rerawa ko dama ace zata samu sassaucin zuciya.


  Mjay duk adadin jiran da ya yiwa Rahima bata zo masa ba sam, kwata kwata gaza gane kan matarsa yake, muddin tazo wurinsa ta kawo kanta to tabbas kuɗi take so, idan ba kuɗin ba abin da yake kawo ta wurin sa shi kuma yanada yawan buƙata duk da ta rigada ta sabar masa da daurewa yanzu se ya shafe sati ko wata ma bata bashi haƙƙinsa ba sam! Ɗan shafa sajen fuskarsa ya yi sannan ya zauna ya shiga neman wayarta kiranta ya yi kusan so 3 bata ɗaga ba hakan ya saka yaja tsaki ya miƙe zuwa ɗakinta inda yay ta knocking bata buɗe masa ba ya ƙara kiran wayarta nan ma daga inda yake yana jiyo ihun wayar amma ta sharesa ga ƙofar a rufe juyawa kawai ya yi yabar bakin ƙofar a ransa yace maganin Rahima kawai second wife!


MEENAH!


   Meenah a yau ɗinnan da tunanin Mjay ta kwana, duk wannan zuzutasa da Rahima keyi ya gama juyawa Meena tunaninta faɗin take hala ina zata tsoma ranta akan son sanin sirrin wandonsa, idan tana emerging girman lenght ɗinsa har wani lumshe ido take cike da shauƙin son kasancewa tare dashi, bazata rainawa mijinta Zuby ba wurin iya sarrafa mace amma lenght ɗinsan indai yanda Rahima ke faɗa ne na Mjay ya fisu, kowannensu yana ji da naira dama mana bazaka ga mutum a kampala estate musamman a mini gate ba ka rainasa duk Estate ɗin sunfi kowane tsada, amma ita dama tun kafin tayi aure take son babbar harka akan lenght na Zuby ta auresa ma da ƙwazonsa amma Mjay yanda take jin labarinsa a wurin matarsa shi duniyar game ce don haka dole ma se ta ɗana ko yana so ko baya so.


Yammacin yau mijin Meerah ne ya fara shigowa gidan Oga Bashir kenan inda kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa shi a duniya ya tsani wannan dabar a ganinsa ko me suke so tattauna akai parlour ko backyard na wani compound ya ishe su amma sunfi so suzo nan suyita sowa Allah ya kyauta, da yake shi can gab da apartment ɗin su yake parking sai yay nisan kiwo ba kasafai ake hangoshin ba. Meenah ta ce


"Meerahni ga oga Bashir can ya dawo yau shine ya fara dawowa." Taɓe bakinta ta yi kafin tace "To an masa murna ya dawo da wuri." Dariya duk suka yi Amrah ta ce "Ba zaki tashi ba kije ki masa sannu da zuwa." Wani mugun harara ta ɓalla mata kafin tace


"Lallai ma kin gama rainani Amrah se kace wata mara aji wallahi ni ba inda zanje." Dariya suka ci gaba da yi dukkansu kafin nan Raheemah ta ce


"Ni duk ba su bane matsala da mazan yanzu, jina basu wata ƙofa sai su nemi raina miki wayau a banza shiyasa gwara ka nunar musu su da babu duk ɗaya." Amrah cikin jan ƙaramin tsaki ta ce


"To ni dai kar a fara hirar mazajen nan bazan iya ba yau." Raheemah cikin katseta ta ce "Aike bakya son ayi hirar su saboda kar a fara maganar lenght ɗin games ɗinsu kinsan mijinki baida abin arziki ki rasa bakin magana." Amrah cikin jin zafinta ta ce


"Wallahi ƙaryarki Raheemah nikam inaga a duk cikin ku nan indai yanda kuke bada labarin mazajen iya nan suka tsaya to ba wanda mijinta yakai nawan tsawon abun da jarumta a gado gwara ki iya bakinki.' duk suka bita da kallo cox yau ne ranar farko da aka ji irin wannan a bakin ta ita kuwa ta faɗa ne dama saboda kowa yay ta kasan tsakaninsa da ita a daina kushe mata nata sarkin, Rahima da ke da tsananin hasada nan da nan taji ranta ya ɓaci cikin jin haushi ta furta


"Ohhh se kafirar rowa amma ko mu ana mana kyautar millions ke kuma duk yawan kuɗin mijinki ban taɓa ji kince ya baki ko 10.m a haɗe ba." Tsaki me tsayi ta ja kafin ta ce


"Haka nan kuma ban taɓa ganinki da wani abu dana kasa mallakar irinsa ba Raheemah wai tukunna inji an gaya miki kowa irinki ne da suke da show off." Tana miƙewa tsaye ta ce


"Ehmm ai show off ma se idan kana da abun da zaka nuna kake yi."


"Ai wani abu idan ya samu wuri ba sai ka faɗa ba shi yake nuna kansa, banda ƙarya me kuke zama anan kina lafta mana." Nan da nan faɗa ha kaure a tsakaninsu duk haƙurin Amrah sai da ta zazzageta ta ƙarashe maganar da cewa


"Saboda kunga ana ƙyaleku shiyasa kuke yiwa mutane iskanci sirrin mijina ne bazan taɓa faɗa kuji ba ba zan taɓa zama ina gaya muku abin da ya shafi rayuwarmu ba do your worst you will never ever get to know my man." Anan sh Meerah suka shiga tsakaninsu Amrah ce ta dara barin wurin rai a ɓace.


Tunda Rahima ta koma gida take yawo da neman hanyar da zata rama wannan cin fuskar da Amrah ta mata, a ganinta wannan shine ƙarshen wulaƙanci agaban duka matan Mini gate ta kalli fuskarta ta gaya mata mujinta yafi nata kuma bar tana iƙirarin cewar ya mata nisa bazata taɓa sanin sirrinsa ba! A cewar Rahina ma zuciyarta wannan shine cin fuska mafi muni da aka taɓa yi mata arayuwa da bata ji zata iya kawar da kanta a kansa har abada, zata san sirrinsan zata ga lenght ɗinsan zahiri muddin ta amsa sunanta na Rahima kuma taci alwashin sai ta yi amfani da ƙarfin iya kirsarran ta karɓe ragamar gidan da jin daɗin Amrah gaba ɗaya a hannunta.


Washe gari amaimakon ta tafi shagonta kai tsaye office ɗin Aminullah ta wuce don kuwa ta gama tsara hakan a ranta shiyasa ta yi amfani da guntun information da take samu a bakin Amrah duk da rashin maganar ta na wurin aikinsa ta ci wata arniyar gown me crystal stone's black colour ba ƙaramin kyau ta mata ba, wani irin tsinannen 5 inch high heels ne a ƙafarta black masu igiya rigar nata ya wuce ƙaurinta ata gaba ta baya ya sauka sosai ta zuba wani uban bon straight wig a kanta browninsh haka ya mata kyau se kuma wani siririn mayafi silver color data yane kanta da shi ta yi kyau acikin nude makeup data tsabtsarawa fuskarta sai wani ubansun ƙamshi take.


Aminulla yana zaune a office yana shan hot coffee sakatariyarsa take gaya masa yana da baƙuwa agogon dake ɗaure a wutsiyar hannunsa ya kalla yana mamakin baƙuwa saboda shi beda wani appointment da kowa wunin ranar amma a haka ya kalleta ya ce


"Let her in." Cikin kadabi tace "Ok sir." Haɗe da juyawa ta bawa Rahima izinin shiga. Da wata iriyar arniyar tafiya ta ƙaraso wurin san shi kuwa ya sake baki ya bita da kallo don kuwa ko da ma ba'a gaya masa ba ya sani sarai wannan Raheemah ce ta Estate ɗin su, kishingiɗa ya yi yana mata wani kallo ƙasa ƙasa fuskar san ba yabo ba fallasa har ta ƙaraso kusa ga desck ɗinshi, da hannu ya nuna mata wurin zama "Have a sit." Tana yarfe gashin kanta gefe ɗaya ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya gana masa wani shu'umin murmushi a hankali ta ce


"Oga Al'ameen barka da wannan lokaci." Yana ɗan sakin fuskarsa ya ce


"Sannu how may I help you.?" Ɗan kallonsa ta yi dama sun san halinsa da wani irin arnen girman kan bala'i hakan ya sa ta shanye takaicin da ya bata a sarari ta ce


"Ba komai ba wata damuwa yallaɓai kawai dama nazo nan office ɗinkunne zanga wata ashe ba nan Company take aiki ba shine na tuna Amrah ta ce mun kai ne MD na nan shiyasa na ƙaraso mu gaisa." Ta ƙarashe maganar tana wani fari da ido irin na 'yan duniyannan tana yarfe sumar kanta a baya." Jinjina kansa ya yi alamun gamsuwa kafin ya ce


"To na gode sosai Raheemah ko?" Tana masa wani murmushi ta ce "Raheemah ne yallaɓai." Jinjina kansa ya yi be ce komai ba har zuwa 2mns sannan jin bece komai ba yana duba wayarsa ta ce


"Ko dai matarka tana zuzuta mana kai ne kawia ba haka kake ba ko ruwa ba zaka bawa baƙuwarka ba." Dariya me sauti ya yi kafin ya miƙe da kansa ya buɗe tangamama fridge ɗinsa ya ɗakko mata malt da ruwan gora ya dire a gabanta ta bishi da wani kallo har ya zauna yanzu a kujerar da ke fuskantar nata, a hankali ta ɗauki malt ɗin ta ɓalle murfin ta kurɓa a nutse cikin kamewa da nuna wayewa kafin ta kallesa ido cikin ido ta ce


"Aminullah duniyar jin daɗi godiya nike." Ɗan Murmushi ya ƙara suɓuce masa amma be iya yace mata komai ba tana daɗa shan maltina tana masa wani kallo ta fitto harshenta waje taɗan huro iska me huci a bakinta kafin ta ce


"Auchhh its too cold." Murmushi ya yi yana zagaye fuskarta da idon sa ko ina kafin ya ce


"There is more to this visit I guess." Ajiye lemon ta yi sannan ta ce


"Kamar ya kenan?" Cikin ƙoƙarin son nuna ƙwarancewa a lauye mutum ta yi maganar da kai tsaye ke nuni da cewar bata fahimce sa ba. Yana daɗa riƙo idon ta a nasa ta hanyar narke manyan idon sa a natan da ita tuni suka dulmiyar da ita saboda kyau da girmansu


"I mean i barely know you, i don't even know your name to be precise why the sudden visit? On what purpose exactly." Miƙewa ta yi tana ɗan haɗe fuska


"Bana fahimtar maganar ka sam Aminullah! Can't i visit my neighbours husband dole sai da dalili? After all ba fa wai takanas na kawo maka ziyarar ba hanyane ya bi dani." Miƙewa shima ya yi suka ɗan kafe juna da ido kafin ta ɗanyi taku biyu baya ta ture kujerar ta zari hand bag ɗinta tana shirin barin wurin, Fizgarta ya yi ya mannata da bangon dake kusa dasu ya ɗaura hannunsa a gicce ya zo daga kafaɗarta zuwa wuyarta ɗayan hannunsa akan waist ɗinta seda ma ta ɗan tsorata ganin yanda ya manne ta da bango ya matse, ido suka ƙurawa juna ta gaza cewa komai kafin ya lashe lip's ɗin sa yana sakin wasu double smirk masu rikitarwa, cikin faɗin murya ya ce


"You sure cewan shikenan?" Ɗan tureshi kaɗan tayi ya tana kiciniyar ƙwace kanta ya yi azamar sake matseta tare da kai lip's ɗin ta ya yi kissing wuyanta yana lashe gefensan, a wahale ta ce "Aminullah meye haka.?" Waist ɗinta yana shafa kafin ya ce


'I lived in Lagos for morethan 20yrs i know your type women babe let's not waste time how much is your pay?" Wani irin turesa ta yi kafin a fusace ta ce


"And who think i am that cheap? Ni ba irinsu bace Aminullah you can never buy me." Murmushi ya yi sannan ya janye daga jikinta, ha kalli lenght ɗinsan dake cikin wandon suit baƙi yanda ta kumbura a wurin ta haɗiyi wani yawun jaraba, hannunsa ya kai ya shafi wurin yana dariya me ɗan sauti kafin ya ce


"Raheemah you are very lucky ko ƙawarki bata samu na a banza, naga abin da kika zo yi kenan even though nasan hala ba kuɗi ya kawo ki ba." Tana ɗauke masa kai ta gyara riƙon jakarta sannan ta ce


"I want to build a secret friendship with you." Kallonta ya yi sosai "Friends?" Ya ƙarashe maganar yana ɗage mata girarsa guda kafin ya kuma cewa


"Alright we are friends now." Ya koma kan kujerar sa ya zauna." Tana masa wani shu'umin kallo ta ce "Friends with benefits." Yanzu kam dariya me sauti ya yi kafin ya ce


"Alright but ki riƙe wannan sirrin." Dan Murmushi ta yi ta ka kusa da shi ta bashi hannunta ya kama alamar gaiswa ga riƙe hannun be sake ba yana murzawa yana mata wani ɗan iksan banzan kallo me kashe jiki a take ta soma ƙokarin ruɗewa a ranta faɗi take ko shiyasa Amrah take kaffa kaffa ashe this hot guy take aure kenan." Sake mata hannunta ya yi ita kuma ta zari wayarsa dake kan table ta buɗe key ganin ba password ta zuba number wayarta ta yi dialing yana ringing ta katse ta sake kallonsa tana masa murmushi


"Thank dear zan tafi." Miƙewa ya yi tana tsaye har ya zago kusa da ita ya hugging nata sannan ya sake sauke lip's ɗin sa akan wuyanta


"Babe you smell really nice i want to buy more of these perfumes for my friend,." Murmushi kawai ta yi ta janye jikinta saboda a tsorace take, tunda ta yi aure bata sake bin wani namiji ba se yau, don haka ne ma hankalinta a razane yake da yanayinsa, daga nan suka yi sallama ta fice Aminullah ya zauna yana murmushin samun mace me aji da kyau irin wannan he hope zatayi daɗi.


*************

Amrah a wannan ranar ma da bolt ta tafi office wuraren 11: tana zaune a office wayarta ta shiga ruri ganin Mjay ya sa ta ɗaga kiran da sallamarta ba tare da wani tunanin ba, ya amsa inda a cikin nutsuwa ta ce "Ina wuni Sir ya aiki." Cikin jin daɗi ya ce


"Lafiya lau Barrister ya ƙoƙari ya aiki." Cikin sanyin muryarta ta ce "Lafiya lau sir." Yana gyaran murya ya ce


"Dazu driver ya tafi gidan ki househelp tace har kin tafi ya baki jira ya zo ba." Dariya ta yi me ɗna sauti


"Na gode sosai Sir but ai kayimun ƙoƙari sosai bazan dameka ba Sir, bolt ya kawoni office ɗin ai." Yana ɗan bata fuska ya ce


"Haba Barrister ai ba girmanki bane ace duk yawan motocin dake wurinmu kina hawan bolt, kuma kinga makaniken nan yace motarki injin ya buga, i hate a ɗaurawa mota wani engine ba wanda ta zo dashi ba, i suggest we change the engine and sell the car sai a samu sabuwa." A hankali ta ce


"Ohh Engine ya buga bako notice how could it, Allah ya kyauta."


"Ameen." Ya ce, ya ci gaba "So ya zamuyi? You have to make decision ke da mijinki tunda shine ya saya motar." Cikin rashin damuwa ta ce


"Sir ayi abin da ya dace ka haɗani da mechanic man ɗin zan bashi kuɗin new engine i can manage the car idan nayi magana da Daddy na nasan ze aikon wata ba mijina bane yake siyanmun mota bakuma ni nake saya ba Daddy ne." Shiru ya ɗanyi yana jinta se da ta dasa aya kafin ya ce


"To allow me to buy a brand new one for you mana, ko kinsan ma me zai faru?." A hankali ta ce


"No sir." Ya ce "Lets fix it bari a ɗaura sabon engine i have a new car on the way se na haɗa miki biyu kinga amfanin mota biyu idan daya ya tsaya akwai another alternative ko?." Shiru ta yi tanajin wani iri kafin a hankali ta ce


"I can't accept anything like that from you i am so sorry sir." Yana saukar da murya ya ce


"Barrister i know you can afford to buy many car's for yourself not even your Dad, please Barrister don Allah kada kice noo i promise it should remain a secret for ever, and wallahi i mean no harm, i just reapect the fact that ke ɗin macen kirki ce." Shiru ta rasa abin da zata ce ya ce


"Please Barrister." A hankali ta ce "To na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, but ina neman alfarmar a bari tukunna nayi shawara don Allah for now amun fixing waccen." Sauke numfashi ya yi sannan ya ce


"Yace Engine ɗin babu a ƙasa se an kawo saga uk order zasuyi, kinsan menene before ki gama shawarinki zan baki aron mota is that ok for you?" A hankali ta ce "Sure Thank you so much."


"Text me your full name and address please." Batare da wani tunanin ba ta masa godiya suka bari akan driver sa ze maida ta gida.


****************

Leo tunda ya isa US sai hankalinsa be sake komawa akan komai ba se aikinsa harkokin buɗe sabon Airline ɗinsan sun ɗauke kaso casa'in da biyar acikin lokacinsa har baya tunanin komai se abin, sam ya manta da wata Zarah a ɓangare daya kuma bashida lokacin wani tiktok ko IG dama su ɗin ba kullum bane ba se idan ya samu damar yin hakan. Zarah kuwa ta ɗaga hankalinta sosai akan rashin jin mahaifiyarta a waya gashi kowane lokaci tsoro take ta ɗauki wani matakin da zai iya jefa mahaifiyarta da ita kanta acikin tsaka me wuya! Habib ya matsa mata yanzu har da rana ma hana mata sukuni ya ke ala dole se ta amince da shi don haka damuwa suka mata yawa se ya zaman kowane lokaci tana kulle a ɗaki acikin damuwa tana famar cin abincin kwali saboda tsoron haɗuwarta da Habib da abubuwan da zai iya mata, ana haka Bukar ya dawo garin inda ta ji wani irin sanyi don gwara jibgar da yake mata akan cin kashin da Habib ke so ya mata, duk da tasha mamakin dawowarsan batare da lokacin daya ɗeba ya cika ba don be saba yin hakan ba.


A parlour tana zaune daga gefensa kamar yanda ya umarceta tana bashi fruits salad data haɗa masa a baki kamar wani sarki yana mata wani kallon ƙurulla ya ce


"Ke ya naga duk kin rame? Ba kayan abincine a gidan." Muryarta yana ɗan rawa ta ce "Ba haka bane Yaya Bukar kewa ne kawai da kaɗai ci ke hanani cin abinci sosai sanda kana nan ai ba nike ba." Daɗi maganarta ta masa yana mata wani mummunan murmushi ya ce


"To yanzu na dawo kici ki ƙoshi kuma anjima da yamma zamuje kiga Mama ta samu sauƙi, ban gaya miki bane kawai amma tare muka yi tafiya sabosa jikinta ya ba daɗi." Godiya ta shiga yi masa sosai ya ce


"Wallahi Fatima ki riƙa yimun biyayya kina ganin dai yanda nike bautawa ciwon mamanki, yanzu iya kuɗin jirgi muka tafi muka dawo na kashe ya kai miliyan goma ga kuɗin asibiti taci kuɗi a wannan lokacin yakai miliyan arba'in ki kama kanki ki mun biyayya mu wanke lafiya kinga dai ban saɓa miki alƙawari ko ɗaya ba " yana share ƙwallan da ya zubo mata ta ce


"In Shaa Allah yaya Bukar zan kiyaye bazaka taɓa kamani da wata matsalar ba." Baki ya buɗe ta ƙara zuba masa fruit ɗin sannan ya tauna ya haɗiya ya ce


"To tashi ki mata girki me kaji ki shirya a flask zamu tafi da yamma." Da zumuɗi ta tashi yabi bayanta da kallo yana taɓe baki....


*KAMPALA ESTATE*

*BILLY GALADANCHI*

*2025*

****.*