Tushen Jarin Kowane Ɗan Kasuwa
1 SIYAR DA AJEYAYIYAR ƘADDARA
Page 1: SIYAR DA AJEYAYIYAR KADARA.
Mafi yawancin mu mun mallaki wata ajeyayiyar ƙadara mai daraja da ta daɗe a ajiye ba mu san abin da za mu yi da ita ba.
Wataƙila ta gado ce, ko kuma mun siya ne da kuɗin mu, ko kuma bamu akayi kyauta.
Ƙadarori irin su Fili, Gona, Daba, Dinare, lu’u-lu’u da dai sauran su . . .
Idan kana da ko kina da wata ajeyayiyar ƙadara mai daraja toh fa lokaci yayi da zaka zauna, ki zauna ki yi tinani mai zurfi akan abin da ya fi kamata, ya fi dacewa ki yi da wanan ƙadarar taki.
SHAWARA:
Idan ka yi duk tinanin duniyar nan kuma ba ka san abin da yafi dacewa ka yi da ita wanan kadarar ba, ina ba ka shawarar ka siyar da ita, ka yi jari.
Idan kuma ya zamana cewa ita wanan ƙadarar tana da tasiri sosai a rayuwar ka, tasirin da yasa ba za ka iya jure siyar da ita ba. Shawara ce ka cigaba da ajiye ita
wanan kadarar.