RAUNIN ZUCIYA

EPISODE 4

by @zahraroyal

*RAUNIN ZUCIYA*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

EPISODE 4

*UMMI POV*

Tsawon lokaci ta ɗauka tana ta uban wankin su Umma da Hali.

Har Baba Mlm ya shigo cikin gidan tare da wani almajirinsa, tana jin lokacin da almajirin ke ba Baba Mlm ɗin labarin yadda ta kaya a cikin gari shekaran jiya da ɓarayi suka shigo. Har sun sun so tafi da wani mai shigo a bakin hanyar Allah ya taimaka ya gudo daga hannunsu, bayan sun ɓoye wa'inda suke son tafiya dasu, Allah ya taƙaita masa wahala ya gudu, amma wai sun tafi da wani wadda dama domin shine suka tare hanyar. Shekaran jiyan ansha guje-guje sosai wani abun ma idan aka baka labarin dariya ce zaka sha.

Tana jin lokacin da ya sake cewa, akwai wasu makwabtansu da a bakin hanyar suka rinƙa gudu har suka faɗa gidan wata mata, matar ma tsabar tsoro ta ruɗe, ga wata Akuya data ke kiwo sai wani uban kuka take, tsabar firgici bata san lokacin data ce, "bayin Allah ku ƙulle mata baki mana".

Baba Mlm ne ya saki dariya yana duban Sale almajiri ya ce

"Kai duk waya baka wannan labarin?"

Sale na murmurshi ya ce "Baba Mlm ai kowa ya sami labarin irin firgicin da aka shiga, ai cikin gari ba labrin da ake sai wannan, su kansu ƴan bindigar wallahi sun fara sanin yadda yanzu ba'a tsoron su, saboda shekaran jiyan nan, wallahi yara da manya suka rinƙa zuwa da gudu kamin sukai inda suke fashin suna ihu suna cewa ƙarya ne, da sunce ƙarya ne sai kaji ƴan bindigar sun saki harba bindiga, Mutane kuma da sunji harbin sai a sake bazawa da gudu"

Baba Mlm na murmurshi ya girgiza kansa, shima yasan dama za'a rina ne, saboda garin gaba ɗaya yanzu sun riga da sun gama sama jama'a wasu rashin tsoron su, saboda yadda sukai mugun sabo da shigowar ƴan bindigar cikin garin, sai dai shi Baba Mlm ɗin yana addu'ar kariya kawai amma yasan wa'inda suke shigowa garin da alama ba masu haɗari bane.

Sai yanzu ya kai dubansa inda Ummi take, murmurshi ya saki ganin yadda ta tsaya tana jin Sale na bada labari, itama kanta saida ta dara. Wani irin farin ciki ne ya rufe Baba Mlm ɗin, harga Allah yana bala'in son ganinta kamar haka, shi yasa ma yasan Sale akwai barkwanci yake barinshi ya shigo gidan.

"Baba Mlm sannu da shigowa"

Ta faɗa tana kallon Mahaifin nata cike da ƙauna.

Shima amsa mata yayi cike da kulawa.

Juyawa yayi ya amshi littattafan addininsa dake hannun Sale, yana cikin sallamar shi Umma ta fito cike da shirinta na fita.

Kallonta yayi kaɗan, yanzu ko kaɗan bata zuwa inda yake, bata son zuwa turakarsa, idan ma taje basa samun wani fahimtar juna, zai iya tunawa rabonsa da gaya ta amsheshi hannun biyu-biyu tun lokacin dai da auri Mahaifiyar Ummi, komai ya kwaɓe masu. Mi yasa bazata haƙura bane?, bata tunanin rabo ne yasa yaje ya auri Mahaifiyar Ummin?.

Wani nannauyan huci ya saki yana jin yadda Ummin ke gaida ita, sai dai ta ɗaga mata hannu kawai alamar amsawa, ko kallon inda Ummin take bata ƙaunaryi, ya gani a cikin idonta da yanayin ta. Domin ita kanta Ummin rabon data ganta tun jiya, sai yanzu da suka haɗu a tsakar gidan, domin ko sashinta bata shiga idan ba shashin nata zata gyara mata ba, to yau koda ta shiga tana banɗaki harta gama gyara ɗakin bata fito ba.

Juyawa yayi ya sallami Sale dake tsaye, saboda baya son wasu su fahimci irin halin da gidansa yake ciki, duk da yasan tabbas mutane da dama sun san irin zaman da Ummin keyi a cikin gidan Mahaifinta, kamar wata bare ba ƴar gidan ba, kamar wata wacce aka ɗakko aiki, bata da ƴanci a cikin gidan Mahaifinta, bata damar sakewa da ƴar uwarta da matar mahaifin nata wacce ta ɗauke ta tamkar uwar data haifeta, bata taɓa mata kallon wani abu ba illa na mahaifiya, duk da irin halin ko in kula data ke nuna mata. Sale cike da girmamawa ya fice daga gidan yana masa sallamar sai ya fito.

Yana duban Ummar data zauna yanzu tana ƙoƙarin saka wani takalmi nata, da kuma ganin shigowar Mlm ɗin a yanzu shi zai hanata fita dan lokacin, duk da rashin kulasa da batayi amma bata taɓa fita bada izininsa ba, haka kuma duk halin rashin da yake ciki na karyewar arzikinsa, hakan baisa ta hanasa abinci ba idan har da kuɗinta tayi, zata basa bata taɓa hanasa wani abu ba, wani lokacin zai kawo abunda ya samu a gidan, amma haka zata ƙara domin dai su ci mai daɗi, haka kuma bata taɓa hana Umminsa cin abinci ba, yadda kowa yake cin abinci haka itama zata ci ta ƙoshi, kawai maganar ce basayi mai tsawo, haka kuma bata shiga rayuwar Ummin da duk abunda ya shafe ta, baka taɓa ji ta saka baki, daga Ummin sai Baba Mlm ne kaɗai suke da damar dakewa da juna. Ummar ma ganin Hali yanzu na son sakewa da ƴar uwarta sai hakan yaso taɓa zuciyarta, domin harga Allah idan ta fita sha'anin abu to da wuya ta sake waiwayarsa, shi yasa take murnar auran da Halin zatai ta tafi, itama kuma Ummin za'a samu wadda za'a ba ita, domin bata ji zata iya zama da ita a gida ɗaya babu Halimar, gara kawai itama tayi auran ta daina ganinta kwata-kwata ta daina jin wannan abun mai nauyi data ke ji har idan ta kalli Ummin a matsayin ɗiyar mijinta.

Koda cikin almajiran Baba Mlm ɗin ne kuwa, karo na farko da zata ma Baba Mlm ɗin magana akan Ummin ɗin akan zata so a aurar da ita, itama ta tafi gidan mijinta komai ya zama tarihi.

Zama Baba Mlm ɗin yayi kusa da ita, Ummi na ganin hakan ta miƙe dama saura riga ɗaya ta gama wankin, tana matseta ta shanya ta shige ɗakinta, dama Hali tunda ta fita bata dawo ba, amma tasan tana gaf isowa gida, saboda duk abunta idan ta fita bata yarda ƙarfe shidda tayi mata a waje, atata takai ƙarfe biyar idan ta daɗe ma, yanzu kuma duka ƙarfe huɗu ne da ƴan mintoci.

"Umman Yara fita zakiyi da yammar nan?"

Ya faɗa yana addu'ar Allah yasa suyi fira mai tsayi a yau a tare da ita.

Bata kallesa ba ta ce

"Da dai zan fitan, amma naga yamma tayi, kuma baka son fitar dare, gobe idan Allah ya kaimu zanje Katsina ma kawai domin zan fara siyayyar kayan kitchen ɗin Halima ne".

Ɗan murmurshi ya saki yana jin daɗin yadda ta basa amsa mai tsayi a yau ɗin, duk da yaga bata wani saki jiki dashi ɗin ba, tana maganar ne kamar bata so.

Amma shi hakan ma ya gode, domin yaushe rabon da tayi masa hakan, idan ma zata sayayya irin haka, sai dai kawai yaga ta dawo da abunta.

Gyaran murya tayi tana sake cewa.

"Ina so muyi magana akan Ummi, a karo na farko da zan shiga al'amarinta kuma a karo na ƙarshe idan Allah yaso, mi zai hana ka bincika cikin almajiranka kaba ɗaya auranta?"

Cike da ɗan mamakin maganarta ya kalleta sosai kamin muryarsa cike da mamaki again ya ce.

"Kina nufin na bada Ummi sadaka?, kin gaji da riƙe ta ne a wajan ki?, ko kuma kin gaji da ciyar da kike da ita?".

Wani duba da tayi masa ne yasa Baba Mlm ɗin tuno da abubuwa da dama wa'inda suka wuce, wani abu mai ɗaci ya haɗe a maƙoshinsa ganin yadda Ummar ta miƙe tana barin wajan ba tare data tsaya ta bashi amsa ba.

Hannunsa yasa yana murza goshinsa, cike da damuwar hali na tsananin miskilanci da Ummar ta koya tun shigowar Mahaifiyar Ummi cikin rayuwarsu, da kwata-kwata ba haka take ba, tayi wani irin mugun canzawa, dama ashe haka Mata suke idan suka ɗora abu a ransu?, suna da wuyar manta abu na cutarwa wadda akai ma rayuwarsu. Shi tayaya zai fara tallar wani ya auri Ummi sai kace wacce ba'a so?, waye ma zai ba Ummi wadda yake da tabbacin zai kular masa da ita?.

Wani lumfashi ya sauke yana tuno wani babban abokinsa sa'annin juna ne, zasu kai shekaru ɗaya dashi, ya koya masa sosai duk da suna abokai, amma yanzu rabonsa da shi kusan shekaru goma kenan tun kan su Ummi suyi wayon hakan. Tabbas yasan Mubarak zai kular masa da Ummi, bazata taɓa yin kuka ba indai tana hannun Mubarak, shi kaɗai zai iya ba auran Ummi saboda yana da tabbacin zata samu kyakkyawar rayuwa a hannunsa, to amma ta ina zai fara ne?, ta ina zai fara neman Mubarak, wadda ya tabbata yanzu number sa da yake da ita ta daina aiki, saboda yasha gwada kiran layin wayar Mubarak ɗin amma bata shiga, ta ina zai fara nemansa?, tabbas yasan tunda Ummar tayi magana da gaske take yi, shima yana so Ummin tayi aure kamar yadda Halimar zata yi, gara ta tafi gidanta itama kota samu ta samu farin cikin data rasa.

Jiki sanyaye Baba Mlm ya miƙe yana sake zurfafa a cikin kogin tunani, tabbas yasan Mubarak yayima Ummi tsufa, to amma yasan shi bazai kai tsufanshi ba, saboda yasan irin ɗunbin dukiyar da shi Mubarak ɗin yake da ita, wani ne a ƙasar nan, shima Allah ne ya haɗa jininsu, babba ne a ƙasar nan ba inda sunan Mubarak Khabeer Ƙanƙara bai kai ba, asalinsu ƴan Ƙanƙara ne, amma yanzu suna zaune a cikin garin Katsina, duk da bai cika zama a ƙasar ba baki ɗaya, yasan idan ya ce ma Mubarak ya bashi ƴa bazai ƙi amsa ba, duk da bai da tabbacin shi Ummin zatai masa, abunda yasa ya yanke zai bashi ita kuwa shine, yana samun labarin family ɗin Khabeer Ƙanƙara ɗin, har yanzu ana ta raɗe-raɗin cewa har yanzu Mubarak ɗin baiyi aure ba, har tsufa ya fara tasar masa baiyi ba, family da duniya baki ɗaya har sun fara masa surutu wai ko aljana ce ta auresa, ko kuma bin matan banza yake kawai, Mahaifiyarsa bata raye haka kuma mahaifinsa sun daɗe da mutuwa, tun yana matashinsa, dangi ne kawai suka sako shi gaba, wasu ma dangin nasa sai yanzu daya tara abun duniya suke zuwa inda yake, wasu ma suke kawo masa Mata ya aura dan kawai anga yana da dukiya a yanzu. Baba Mlm har ya shiga ɗaki yana tunanin Mubarak abokinsa tun yarinta, yanayin rayuwa da abubuwa suka canza yasa kowanne ya kama gabansa, tabbas yasan Mubarak bai san irin halin da yake ciki ba, tabbas da yasa da yanzu baya cikin wannan halin, bai san dai mi yasa har yanzu bai sake waiwayarsa ba, akwai dalili mai ƙarfi daya hana shi..

*Ƙauye Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*

A hankali ta shiga sauke bokitin dake kanta, sai hannunta dake cike da kuɗin cinikin awara, ƴar sauran awarar da bata saida ba, bata da yawa sosai bata fi ta ɗari biyar ba a ciki.

Inna jin motsi, tayi wuf ta fito tana duban Habiba, ganin ita ce riƙe da kuɗin awararta yasa da sauri ta matsa tana saka hannunta ta fisge kuɗin.

Harara ta watsa mata tana kwala kiran Bilki.

Bilki dake ɗaki kwance tayi saurin fitowa da sauri tana cewa.

"Inna gani"

"Yawwa kinga tayani ƙirga kuɗin nan, kar algugumar yarinyar nan ta cuce ni, dan na rantse yau idan naira biyar ce ban gani ba, yau za'a jimu dake wallahi"

Innar ta ƙare maganar tana jefama Habiba wani mugun kallo, ita dai tana tsaye kanta a ƙasa.

Ƙirga kuɗin suka fara, Bilki na gama ƙirgasu ta dubi Inna ta ce.

"Ai naga babu ɗari biyar a ciki, ina kikai ɗari biyar ɗin muguwa?"

Inna na shirin kamota, da wani irin sauri ta matsa, da rawar baki ta ce.

"Inna ga awarar ɗari biyar ɗin fa a nan cikin bokiti na dawo da ita, ba'a saida bane".

Ta ƙare maganar cike da tsoro.

Dubansu suka kai cikin bokitin ganin awarar yasa Bilki taɓe baki tana ɗakko bokitin ta buɗe tana cewa.

"Yo duk da dai haka, duk ga awarar nan an ɓincini rabi-rabinta".

Inna cike da masifa dama kamar jira take tayi wani kukan kura ta kamo tsintsiyar hannun Habiba da ƙarfi ta murɗe hannun, Habiba ta saki ƙara haɗe da rushewa da kuka.

Inna na faɗin

"Shegiya makira, wato ni zakiyi ma wayo ko?, ke har kinsan ƙulla munafurci?, har kinsan ki rinƙa min ƴar ɓincine a cikin sana'ata?, ubanki ne ya bani kuɗin ko kuwa uwarki ce mai kama da aljanun farko suka dawo duniya suke ban jarin sana'ar tawa iyee?".

Ita Habiba kuka kawai take tana hawaye, tana girgiza kai, wata zufa duk ta rufe mata jiki, tana runtse idonta, saboda yadda take jin hannunta da Innar ta murɗe har lokacin yake mata wani irin zafi haɗe da wani raɗaɗi sosai, domin cike da mugunta ta murɗe sa.

Inna ta kalli Bilki ta ce.

"Jeki wajan murhun can ɗakko min garwashin wuta guda uku manya yanzu nan, gobe idan kin fita ki sake min ƴar ɓincine ko kuma ki bari masu saye su rinƙa saka miki hannu a bokitin tallar naki, idan ma sune suke min ɓinci nan".

Wani irin tashin hankali ne ya rufe Habiba, da wani irin sauri ta ƙara sakin kuka mai sauti tana girgiza ma Innar kai, jikinta ba abunda yake dai rawa na tsananin tsoron gaske da razana, zufa ce ta sake wanke mata fuska, jikinta sai rawa yake tsabar tsoro har wani shiɗewa take lumfashinta na yin sama-sama, ganin yadda Bilki ta ɗebo garwashin a cikin abun kwashe shara na ƙarfe ta miko ma Innar.

Cike da rashin imani tsantsarsa Inna ta amshi abun kwashe sharar, tana sake riƙe hannun Habiba dake shirin sumewa tsabar firgice da razana.

Ba tausayi ko imani ta juyema Habiba wannan garwashin wutar a tafin hannunta da bai gama warkewa ba dama, sana ta riƙe hannun da karfi ta yadda babu yadda za'ai Habibar ta gudu kota zube da garwashin.

Wani irin kuka Habiba ta saki har muryarta na shakewa, kyarma hannunta keyi da gaba ɗaya jikinta, kuka take tana kiran wayyo Allah, ta tuba bazata sake ba.

Sai da Inna taga Habiba numfashinta ya dauke ta zube a sume a wajan, yasa ta sakinta ta faɗi ƙasa, babu alamar ma nadama a tare da ita.

Saima Bilki data ba umarnin ta ɗebo ruwan randa mai shegen sanyi ta watsa mata.

Tana ɗebowa bata tsawa ba ta juye mata shi a jiki, wani kalar jan lumfashi tayi da ƙarfi tana buɗe idonta, wata kalar azaba taji a hannunta da ilahirin jikinta da yayi mata dirar mikiya, da sauri ta tashi zaune tana kallon yadda tafin hannunta ya sake ganewa sosai kuka take tana kallon hannun nata.............