Tushen Jarin Kowane Ɗan Kasuwa

5 TALAFIN GIDAUNIYA KO ZAKKA.

by @115395593230860196762

Wanan hanyar ta wa’enda ke da rauni ce, kamar:-

Matar da miji ya bari da ƴaƴa.

Yarinyar da a gidan su babu shi.

Mutane masu fama da wata lalura.

Yara marayu.

Da sauran su….

Yadda za ka samu jari ta wanan hanyar shine, za ka je offishin wata gidauniya da ka san tana talafawa mutane da jarin fara sana’a.

Ka yi musu bayanin halin da kake ciki, da kuddirin ka na son fara sana’a.

Za ka iya rubuta musu wasiƙa idan ganin su zai maka wahala, ama kamar kullum zuwa da kai ya fi aike.

Ka yi yunƙurin yin ɗaya daga cikin wa’enan, kada ka karaya ka cigaba da neman tallafi daga wanan gidauniyar zuwa wanan.

Maula ba mafita ba ce, domin ita nakasa ba kasawa bace.

DARASI:

Da farko ba lalle bane a dace, ama idan ka cigaba da neman talafin insha Allahu za ka samu.